Showing 27001 words to 30000 words out of 180809 words

Chapter 10 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12963

sub'uce masa, niyarsa ya bud'i bakinsa ya bata amsa cikakkiya a kan Bilkisu da k'in cin abinci, sai kuma ya gane wace ta yi maganar ba Mama bace, Tati ce.

A hankali ya kawar da dubansa sannan ya mayar da yannayin murmushinsa cikin cikinsa

Murmushi ta yi a bayane ta kara dora kafarta daya kan daya ta ce" Ba yanda ban yi da ita kan ta yi kwaliya ba, ko dan jan baki ta shafa ba aman ta kiya wai ka hanna, to idan kana hannata dan gyarawa baka so ta samo mana siriki ne? Babyna ta kai wajen da zata fara zance idan wani wajen ne may be har an mata aure shekara goma sha tara ai ta girma "

Da wani irin sauri yanzunma ya kara kallota, da wani kallo mai hade da kakausan yannayi

Zai yi magana kennan Mama ta dire masa plat din abinci da koshiya ciki ta juya wajen frij ta dauko masa jus na gida da ta yi da ruwa ta ajiye a gabansa sannan ta zauna tana hade fuska ta ce" oya Bismillah "

A hankali ya ringa sasauta yannayin kallonsa a kan Zainab har ya cire idannuwan nasa daga kanta ya maida kan abincin da Mama ta ajiye masa

Sai da ya yi da gaske sannan ya maida hankali ya fara tsakurar abincin yana ci , ransa a mugun bace , a kan me zata nemi yon shishigi a rayuwar yarinyar da ta tarar budurwa isashiya? Me ta sani a kan yarinyar da har zata zo ta nemi sakata abinda ba yi take ba?

Da kyar ya iya gama cin abincin Mama ta yi kiran mai aiki ta kwashe

Cike da kulawa mama ta ce" Yaya jikin marar lafiar namu Hisham? Yaushe za'ai masa aikin?"

Hisham ya dan kara gyara zamansa da tishu a hannunsa ya goge bakinsa duda ba wani abu a jikin bakin nasa sannan ya ce" Alhamdulilah, da sauki "

Mama ta ce" Masha Allah haka ake so ai, baka fada min yaushe za'a masa aikin ba?"

Hisham ya kara kallon Mama ya ce" In sha Allah sai ya gama shan maganin da na dora shi sama, wanda zai huce kumburin da ciwon ya yi, idan ya huce kamar nan da sati daya sai a shirya shi a saka shi , idan Allah ya sa aka ci nasarar aikin sai ya yi kamar sati biyu a wajenmu kafin mu salame shi wasu ana yin har sati uku "

Mama ta ringa gyada kanta, Zainab ta ce" Allah ya sa a yi a sa'a "

Mama ta amsa da "Amen amen ya Allah, to Zainab kuma mutanen da suka zo tare sunna nan zaune da su har a yi a gama ko Niamey din zasu juya? Gani na yi jinyar ta namiji ce ba mace ba, gasu mata ne su biyu, irin wannan ciwonma na ga basa barin mutun wajen marar lafiar "

Zainab ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Hisham da ya shiga dadana wayarsa ta ce" Nima abinda nake ta tunani kennan Aunty, gashi a garin nan ba wanda suka sani in dai ba komawa zasu yi ba inaga sai dai ya kama masu hotel har komai ya daidaita yarinyar ce mai sarkafa da kakan, baki ga yanda take kuka a kan rashin lafiar kakan nata ba"

Mama ta ce" Hotel kuma? Haba dai du dakunnan gidan nan? HISHAM ai ba zasu je Hotel ba gaskiya " ta karashe tana kallon Hisham

Dago kansa ya yi kawai ya kurawa maman ido, yau ya ga ikon Allah, daga jiya zuwa yau wani irin farin ciki da azarbabi da ya samu mamansa abin har mamaki yake bashi, to yanzu bakin matar da ta yi shekara da shekaru bata gani bane take son saukewa kuma?

"Kin ga, dakunnan cen baki daya fa ba kowa ciki sai gado da sif da bayi, idan dai zasu iya zama da mu gaskiya su zo nan, ina dalili mata da zama a hotel haka kawai bayan da darajarsu "

Murmushi ne ya mamaye fuskarta, kai aman da ta tabata matar DG ta gama abota da ita ta kare, matar akoy son girma da halayan girma , idan ta ce girma tana nufin da manya manyan mutane masu yayan banki, wa'inda suka san darajar yayan banki suke kuma murza su ba tare da jin ciwon kai ba

Da zumudi ta ce" sosai zasu zauna mana, ai zai masu gidan aman ina so a saka masu abubuwan da zasu ji dadin zama da mu, kin san mutanen da suka saba da hutu duda na sarawa gidan nan na HISHAM aman idan ya zamana a wajen da za'a sauke su bai kayatu ba sunna iya nuna min

Mama ta yi murmushi ta ce" ai kau idan har sun yardan ke dai ki fada min kawai kafin su zo zan baki mamaki "

Cike da tausayi yake kallon Mama, a gaskiya a yanzun ya fara tausaya mata, kishirwar rashin yar uwarta a kusa da ita ne ya sakata zama haka a yanzun, tabas ya fara tsoron irin yanda Maman ke bin umarnin kanwarta ba tare da ta saka ayar tambaya ba

Mikewa ya yi yana kallon agogonsa a sanyaye ya ce" Mama zan je asibiti na ga mararsa lafiar da na yiwa aiki jiya daga nan na dauko Bilkisu karfe nawa take tashi yau? "

Mama ta ce" a babur dinta ta tafi fa yau "

"A babur kuma?" Ya fada yana tsatsare mama da idannuwansa

Zainab kuwa ta janyo mayafinta tana mikewa tana fadin' Aunty bara na bi shi mu je tare dan na ga mai jikin nima sannan na ji yanda suka yanke

"Yauwa hakanma ya fi nima bara na ga me zamu yi masu na rana" cewar Mama tana mikewa tana son ta kalli yannayin Hisham aman kuma ta hanna kanta, dan kuwa irin taayuwar nan da ya yi ta tabata yana da ta cewa ya kasa budar baki ne sai ta tambaye shi ko lafia? Ita kuwa so take kusanci ya yi karfi ysakaninsa da mahaifiyarsa

Sarai tana hankalce da irin yannayin magangannun zainab, sai dai ita farin cikin wanzuwar Zainab a cikinsu a irin wannan yannayin ya saka take mayar da dukan wani shaku ko tsoro gefe a zuciyarta

Murmushi ya yi ya dan girgiza kansa a hankali ya juya ya fita

Wajen motar da ya nufa ta je itama ta tsaya

Tana kallo Kader ya bude masa bangaren da zai shiga ya shiga ya zauna, hakan ya sa ta bude gefensa ta shiga itama ta zauna da wayarta a hannunta

Kader ke tukin sannu a hankali ba tare da yana fera gudu ba hakan ya sa kowa ya nutsu yana abinda yake gabansa

"Bata kai shafe shafen abubuwa a fuskarta ba, hasalima bata fita daga gidanmu dan ta birge wani ba, Dan Allah yan kwanakin da zaki yi tare da mu kar ki rikita min yannayinta " ya fada kasa kasa sosai sannan idannuwansa na kallon tsakiyarsu ya kurawa wajen ido

Zainab ta yi dan murmushi a hankali itama ta ce" Ba zan rikitata ba, aman na maka alkawarin koya mata kwaliya da kwarkwasa domin ita din budurwa ce ba jaririyar da zaka hanna kwaliya ba, Birge wani kam sai ta yi kuma na mata aure in sha Allah, to kai wama ya ce da kai ina da niyar tafia ne bayan na zo gidan d'ana?"

Idanuwansa ya dago da sukai masa dan ja yana kallonta, a hankali yace " Ba na so, kar ki yi."

Itama shi d'in take kallo tace "Kana son ta ne?"

K'ara wara idanuwansa ya yi a saman kanta, a hankali ya tab'e bakinsa ya ce" *AA*."

ZAINAB ta juyar da kanta gefe a hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ce" *Har na ji tsoro, kar a je kuna cikin duhu baku sani ba*!"

Sai kuma ta k'ara kallonsa tace "To ka barni na sama mata mai son ta, daidai da ita!"

Da sauri ya rik'o hannunta na hagu dake kusa da shi yana k'ara tsatsareta da dubansa, kalmar *DUHU* d'in nan ta saka shi a cikin d'ayan biyu, wani irin duhu take nufi? , Muryarsa ciki ciki yace "Anya kuwa? Tati anya idan kin tashi zab'e ba mai kud'i zaki zabo mata ba maimakun masoyi? Anya tati kin san girman soyyaya ko wace kala kuwa?"

Zainab ta tsatsare shi da duba, karon farko da ya rike hannunta tun dawowarta jiya zuwa yau, maganarsa ta sakata a hali na tunani da jin mutuwar jiki, aman sai ta dake, ta murje, ta dan langwab'e kanta ta sanyaya muryarta tace "Tabbas ban san soyayar so na zuciya ba, domin har yanzun da na kawo tsufa ban auna hakan ba dan kuwa na ajiye hakan a matsayin bacin lokoci." 'Dora hannunta na dama saman nasa na ta dora da fad'in "Aman na san ta d'a da uwa."

Murmushi ya yi ya janye hannunsa daga cikin nata ya maida dubansa kacokam bakin titi.

Har sai da motar ta tsaya ya juyo gaba d'ayansa a lokacin da Kader ya fita a motar ya fuskanceta yace "Tabbas zan iya yi maki biyayya, ina son ki a raina domin haka na ji a zuciyata da na kalle ki, sai dai ina rok'on ki da ki so mutanen nan biyu da zuciya d'aya, sannan ki yi k'ok'arin wanzar da kusanci na d'a da uwa tsakanina da ke, ba zan tab'a iya rainaki ba, ba zan tab'a iya wulak'anta ki ba, wannan marar lafiyan ko da turo su kika yi da sak'o zan dube su domin *uwa* ai *uwa* ce kuma a yanda Mama ta shaida min d'an halak ne ni!"

Yana gama fad'a ya bud'e ya fice a motar hakan ya sakata bin bayansa da kallo. Murmushi ta yi tana dan juyar da kanta gefe guda a bayyane ta furta" Tabas uwa daban take......zakai min biyaya a lokacin da baka shirya ba HISHAM."



Cike da yannayi na murna ta dube su su biyu ta ce" Fareeda, Laila, ba zaku gane ba, wai nima na wayi gari da k'anwar mamana a gida harma ta bani damar na saka jan bakin da mama ta hana min da kuma yaya, na kasa daina farin cikin ganinta a kusa da mu."

Laila ta tab'e bakinta tana kallonta bata ce komai ba, Fareeda kuwa tace "Na taya ki murna k'awata, ke bara na amso mana cak d'in ina zuwa."

Fareeda na tafia Laila ta fuskanci Bilkisu tace "Ni kuwa sai na ji sam ban yi zumud'in dawowarta ba, anya kuwa ta dawo da niyyar a fahimci juna? Billy kin ce ta cewa Sir d'anta? A duniyar nan akwai macen da zata kiraye shi da wannan sunnan kuwa bayan Mama? Me ya sa take son saka ki fara bijirewa umarninsa? Kwalliyar ba iyawa bane baki yi ba, ke kike mana, aman dan gudun b'acin ransa sam bakya sakawa ki fito, bana so ya yi fushi da ke Billy."

Bilkisu ta yi murmushi tana lumshe idanuwanta a hankali, cikin murya mai matuk'ar sanyi tace "Dama na san sai kin fad'i haka, domin muna hasashen abu iri d'aya, baki san wani abu ba? Da Babyna take kirana, sannan maganganunta sun tsaurara, ba wai rashin kunya ta yi ba ko bata isa ta ringa hakan ba, a'a, a rayuwar da muke gefen Mama mun san wani wai shi kawaici, kawar da kai a lamarin rayuwa, amma ita sai kawai ana zance Mama na bata labarin irin ci gaban da yaya ya samu na rayuwa sai tace " Ni na san idan ni ban yi kud'i ba a duniya, D'ANA NA CIKINA zai yi." Abun sai ya saka ni kallonta a zabure, aman sai mama ta kore ni. A dukan lamarin nan zan iya ce maki hatta uwar da ta haife ni kallon yar jaririyarta take min, yayana ya kasa fuskantata a matsayina na mace, ban san ko hauka nake ba, ban san ko me ke damuna ba, Laila ya saka a kullum ina k'aryata ki, ina fad'a da ke ido rufe, yana cutar da ni ta hanyar giftawa ta gefena, yana cutar da k'ananun shekaruna ta hanyar yi masu d'aukan watani...."

Dan murmushi ta yi idanuwanta sun kad'a sun yi jajajir k'wallah na neman cika su ta d'ago ta sauke a kan fuskar Laila da mamaki ke neman kasheta, watau du abinda suke fad'a suna cenkowa dai-dai tana ki'n basu fuska ne dan ita kanta a cikin tsaka mai wuya take? Bilkisu ta katse mata tunaninta ta hanyar fad'in "Babu abinda ban iya ba, babu abinda bana fahimta, shekaruna goma sha tara ba kwana tara ba, ba wata tara ba, ina tausaya mana ne, ina gudun sakomu a layin da zan had'amu da hakk'i ne, Laila ina iya halaka tunaninsa, motsinsa katab'us d'insa, Laila ina iya tsayar da numfashinsa domin nima mace ce, mace kuma wace ta san kanta, mace ba sai an koya mata ba, ni ba mahaukaciya bace...ina sane nake tafe kamar makauniya, kurma, kuma bebiya...sannan mahaukaciya! Sai gashi mahaifiyarsa ta bayyana, bayan ta bayyana ina shakun wasu lamura nata, Laila ina son ta, ina jin murnar zuwanta.....Amman da me ta zo? Shin itace alkhairinmu ko akasinsa? Kar ki yi mamaki dan na amshi tayinta ta bayyanar da yan matancina, a yanzu zan baiwa mad'inki damar d'inka min dai-dai da jikina, zan yi kwaliya koda bakina cikin gidanmu....Laila zan k'ara d'an kwatantawa iyayena cewar na d'an girma aman ba wai na girman ba, Laila zan k'ure yayana na ga iya gudun ruwansa."

Hawaye ke fita ta idannuwanta masu zafi ta saka Tishu ta goge a hankali ta kuma fadin" Jibeni, kamar wata wawa daga na fara maganarsa sai hawaye "

"Leila ki tashi ki raka ni wajen mai siyar da waya, ina son na sayi yar k'arama domin a yanzu na yi niyar rashin jin magana a duniyar YAYANA."

Da mamaki Laila ta ce"...











🥺🥺🥺🥺
[7/24, 10:18 AM] BAK'A CE: 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


11



1)
Domin magance bakin kasan hamata, gwuiwar hannu ko gwuiwar kafa, rabe raben cinyoyi ki samu Beet ki gurza sai ki tace ruwan ki hada da + potato jus ki saka dan brosh mai laushi ki shafa idan ya bushe sai ki goge da tawul karami zai baki kyakyawan sakamako Hajia =vitamin c in beets lightens dark spoots (Sajida ce )

2)
Idan kafarki mai yin yaba yaba ce, irin kamar jikin kadangare dake cenza fata sai ki samu sabulun ruwa, da vinaigre da ruwa ki hade su ki zauna ki tsoma kafar taki yan mintuna kamar goma sai ki wanke = Natural oils and acids gently exfoliate skin. zai fita sumul hajia ( Sajida ce )



Labari

Da mamaki Laila ke sauraron dukan Abinda Bilkisu ta fada

A hankali Laila ta kamo hannayenta cikin nata tana kallonta, muryarta sanyaye ta ce" Sai nake gannin wannan ba itace dabarar da ya dace ki yi a duniyar Yayanki ba, idan na fahimci yarenki kawata kina cikin soyayar yayanki mai tsanani, kina yiwa dukan umarninsa biyaya ba ja ba daga kai ba maganar takawa bare jinkirtawa, idan fa wannan Bilkisun itace burinsa ba wace kike son budewa ba? Idan Bilkisu marar kwaliya itace burinsa, mai yi masa biyaya, innocent girl din nan itace burinsa kika tono masa wata Bilkisun daban yaya kike so ya yi da rayuwarsa?, na san cewa du mace ta duniya na iya tafiar da rayuwarta a kan yannayin da ta zo mata ne, tana iya sarafa irin kalamai da mu'amalarta da al'umar dake tare da ita ta sigar da ta ga dama, mace na iya rayuwa da mutun shekara da shekaru a matsayin wace bata san komai ba tana raka shi da ido ne ba wai dan bata iya hadasa husumar dake iya tayar da fadan duniya baki daya ba, aa ta yi niyar zama da shi a hakan ne!............., aman Bilkisu idan wannan yannayi naki shine yayanki ya fi dokantuwa , ya fi kauna, ya fi saka masa kaunarki a zuciyarsa fa?"


Hawayen dake kara taruwa a idannuwanta ta goge a hankali ta ce " *Ban sani ba* "

Da yannayi na jin haushin wannan amsa tata mai amsa kuwar bata sani ba Laila ta ce " ki yi magana da ni a bude, ke kin san ni na san ki Bilkisu ! "


Bilkisu ta yi murmushi tana kallonta, a hankali itama ta ce" Tabas a duniya akoy mazan da sun fi son mace ta zauna natural, ba digon kwaliya a jikinta.....sai dai baki san wani abu ba, mai yiwuwa matar nan da suke tare da itan ce kwaliyar bata yi mata kyau!, Laila kwaliya kala daban daban ce, haka kuma sunna ta tara , ki kasance mai tsafta kina kanshima kwaliya ce mai daraja,
Nawa zasu auri mace su kawota cikin gidansu su kilace, su hannata dan gyare gyaren jikinta cewarsu ta fi birge su a haka, su bi su tatareta tun tana da ra'ayin saka kwali idan zata fita su cire mata komai a rai har ta dawo ta zamana bata da ra'ayin saka shi ko a cikin gidanta na aure, zaki ga ta dawo tamkar wata tinkiya bayan ita din nan a da mace ce mai son kwaliya, dawisu take ga idannun al'ummah, sannu sannu karfin ikon mijinta a kanta da soyayarsa da rashin sannin darajar kai zai saka ta yi masa biyaya....wanda hakan abu ne mai kyau ainun watau yiwa miji biyaya,
sai dai ba nan gizo ke sakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login