Showing 12001 words to 15000 words out of 180809 words
mutuwa
Idannuwansa ya lumshe ya ki ya yi mata magana bayan ya ja ya tsaya a wajen kanya, kasan innuwa
A hankali ya kashe motar ya sauke maduban motar , nan kukan tsuntsaye ya cika wajen sunna ta kukansu mai dadi, ga sansanyar iska na kadawa sai sautin kukanta dake neman kasarashi
A hankali ya ce" SHIIIIIIIIIIIT BILKI, ki yi shiru mana "
Bilkissu ta kasa yin shirun sai tatare hijab dinta take muryarta na rawa ta ce" Dan Allah ka yafe min yaya, ba zan kuma ba, kar ka doke ni "
Idannuwansa a lumshe nan jikinsa jingine da kujera ya ce" Na taba dukan ki ne? "
Dan tsai ta yi kafin ta girgiza kai da sauri ta kara sada kanta ta ce" To yaya kar ka yi min fada "
A hankali ya dago idannuwansa ya sauke a kanta ya ce" Tom, ba zan maki fada ba "
Wannan karron da wani irin mamaki ta bude fuskar nata , ba zai daketa ba, ba zai yi mata fada ba? Gabanta ne ya yanke ya fadi, da sauri ta tsalako gaba kusa da shi
Hannayenta duka biyu ta saka ta kamo nasa hannun bakinta na bari ta ce" Yaya baka da lafia ne ko? Me ke damunka? Me ya same ka? Wayo na shiga uku bana so ka yi rashin lafia me ya sa baka fadawa mama cewar baka da lafia ba? "
Tana fada tana kai hannunta wajen wuyansa da goshinsa da fuskarsa baki daya tataba yannayin zafin jikinsa ne take , a rikice take, hankalinta tashe yake
Da sauri ya rike hannun nata ya tsaida dubansa a saman fuskarta, tuj daga wajen girarta har zuwa lebenta ya ringa yi mata eani tsatsauran kallo
Nan take ta ankara cewar hannayenta ne ta kai jikinsa, bayan ko hannunta ba wani rikewa yake yi ba dalili ba
Sai dai bata san dama kusancin yake jira har haka ba, sai da ta ji ya jefo mata tambayar da ta sakata raina kanta
A kausashe ya ce" Su waye su? "
Gaba daya ta ringa marmar da ido, ita bata summa ba, ita bata tashi ba, irin yanda ya hade fuska kuwa bata taba gannin haka ba, hakan ya sa lokaci daya ta tonawa kanta asiri cikin ruwan sanyi ta zayane masa komai tana kara risinar da kanta kasa
Hannayen nata ya saki ya kuma maida bayansa jikin kujerar ya jinginar
Sai da ya dauki kusan minti biyar yana controlling din fushinsa yannayinsa da yannayin muryarsa kafin ya kara buda bakinsa ya ce" *Idan aure kike so, idan har kin san kin rika zaki iya rayuwar aure na yi maki mana Bilkissu?* "
Kanta ta ringa girgizawa da sauri da sauri sai kuma ta ce" Aa yaya "
"Kar a je na tauye ki Bilkissu, kar a je na hanna ki rawar gaban hantsi ban sani ba? Shekarunki goma sha tara da wata bakwai yanzun, kar a je kin giga ban sani ba "
Ya fada yana kara langwabar da kansa
Da sauri ta hade hannayenta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, walahi ban giga ba yayana, na tuba ka yafe min ba zan kuma tsalaka maganarka ba"
Fuskarta ya kurawa ido yana kallonta, kallon da yake jifanta da shi a bayane yake, sai dai bakinsa ya fi gam iya manewa
A hankali ya ce" Tom "
Daga haka ya kara lumshe idannuwansa yana sauraron kukan tsuntsayen nan,
Itama shirun ta yi ta rafka tagumi tana jin haushin kanta fiye da komai a duniya
Motar ya kuma tayarwa ya nemi hanyar da zata karasa da su gida
Sunna tsayawa shi ya fara fita a motar ya nufi fallon Mama
A hankali take biye da shi tana karewa tsayinsa da yannayin kafadunsa da hannunsa kallo
Basu zame ko'ina ba sai cikin tafkeken fallon gidan, a lokacin mama na zaune tana kunsa lale na hausa
Juyawa ya yi ya kama hannunta ya karasa da ita ya tsuguna har kasa gaban mama ya sada kansa ya gaisheta
Cike da kulawa take amsa shi, lokaci daya ta ce" aa yaya na ga yannayinka baka da lafia ne? Ke kuwa ina makarantar? "
HISAHM ya yi murmushi ya ce" Alhamdulilah mama, ta yi lati ne sai gobe zan kaita da kaina "
Yana gama fada ya mike ya koma saman doguwar kujera ya kwonta yana rike da wayar nan a hannunsa
Mama kasa cewa komai ta yi, sai umarnin da ta baiwa Bilkissu kan ta je ta hado masa shayi mai kauri ya sha ko zai warware
...........wannan kennan........
Kanta sade yake gaban directer din ma'aikatansu
Fada yake ido rufe yana barazana wa aikinsu hakan ya matukar tayar da hankulansu , da yawansu jikinsu ya yi sanyi matuka
Dorawa ya yi da fadin" baku isa ku mayar da ni sakarai a garin nan ba, mahaifiyata ce ba lafia, ina nan ina faman yanda zan samu fitar da ita , matsalar a kanta ne , daga bana nan na dan lokaci shine zaku nemi kashe min ma'aikata? Kan masu zuwa a lati, sau wa'inda basa zuwan kwata kwata? So kuke daga sama a ga nine mai wasa da aikina ko me? Ba zai yiwu ba, du wanda ke dauke da laifi hukunci zai hau kansa daidai da laifinsa!
Ba wanda ya iya magana a wajen, sai mai bi masa watau SG dinsa ne ya kara sada kai a sanyaye cikin yaren french ya ce" ka yi hakuri Dg, an yi laifi matuka, ba zamu kara ba, ka yi hakuri kwarai harda laifina domin idan ban ba mutun damar ya ki zuwa ma'aikatar nan ba ba zai ki zuwa ba, toh sukan tambayeni ni kuwa sai na basu dama ka yi hakuri"
Bai ce komai ba sai zama da ya yi saman kujera yana ta muzurai, hankalinsa a matukar tashe yake, ransa a bace, mahaifiyarsa na fama da rashin lafia gashi sai an fitar da ita , wannan ya hadasa masa tashin hankali da tunanin yanda zai yi, koda kuwa shi din wani ne, mai abin hannunsa bashi da hanya
SG gannin ya yi shiru ya kara tausasa muryarsa kasancewar meeting ne mai tafe da rarashi ya ce" Ba'a samu hanyar da za'a fitar da itan bane? Mai zai hanna ka jaraba namu na gida? Duda yaron dan danyen kai ne sosai aman idan har ka samu ganninsa an wuce wajen, ba maganar kudi bane, maganar yarda ne "
Da sauri ya dago yana kallon SG, shine mutun na biyar da ya masa wannan maganar, hakan ya sa ya ce" wai wanene wannan DOCTER HISHAM MUHAMMAD KARIBULLAH din?"
Da sauri ta dago dubanta, gabanta ya fadi jin sunnan nan, bata yi gagawar yin magana ba har sai da SG ya budi baki ya ce" Bafilatani ne, dan kasar nan ne, kuma likitan abinda ya shafi kai ne haka sannan likitan mata ne, Haifaden Damagaram ne, kaf Niger shine ya karanci Dogon karatun da ya zama professor, damuwar yaro ne dan bai fi shekaru talatin da biyar ba a duniya, zamu shiga manya a samu a yi masa magana Dg"
Da sauri ta kara kafe DG din da kallo, wani murmushi ne ya subuce mata a kan lebenta, a kasan zuciyarta ta ringa jin wani alfahari, wani farin ciki, wata dama tata ta kanta
Sai da ta gyara zamanta ta dora kafarta daya kan daya ta tataro nutsuwarta sannan ta ce" *D'ANA NE* "
Irin yanda ta yi maganar ba wanda bai jita ba, kuma ba wanda bai dawo da hankalinsa kanta ba, ciki kuwa harda DG din baki daya
Irin kallon da kowa ke mata na nuni da karrin bayani suke so, sannan ba wanda ya nuna mata da karrin bayanin ake so duba da ita ce karama a matsayin a wajen da ake zaune
Shiru ta yi itama tana mai bin kowa da kallo daya bayan daya
DG ne da kansa ya ce" Madame *ZEINAB* me kike nufi? "
Murmushi ta yi gannin an zo wajen ta kara gyara zamanta tana kallonsa cike da son nuna masa gaskiyarta ta fada ta ce" *HISHAM KARIBULLAH D'ANA NE, na cikina*! "
..............tototo ni ai baku gama bikin sallah ba, ni kuwa ina son mu je tare tafiarπ₯Ί.........m
[7/24, 10:17 AM] BAK'A CE: πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
πΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎπΎ
_RUBUTAWA_
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
6
Cike da mamaki SG ya k'ara k'ureta da kallo, Zeinab dai ta kasance mace mai biya'ya sosai da sosai a wajen aikinta, ita fa a dunia wannan nema nata shine rayuwarta, a kan maganar aiki du abinda aka ce ta yi zata iya aikatawa a sauk'ak'e ba tare da tunanin komai ba,
A kan aikinta tana shirye da duk'ama koma waye.
Sannan a wajen aikin ta kasance irin mutanen nan da ake kira kaska rab'u mai jini, idan ba wani abin zaka anfaneta da shi ba sam Zeinab bata yi maka fadanci.
A zaman nan da aka yi baki d'aya ita ce mai k'aramin muk'ami a cikinsu, hakan ya sa kanta sade cike da biyaya take sauraronsu sai a yanzun da ta hango maganar nan, maganar da ta bata mamaki, wace ta zo mata a yanzu yanzun, kar ku yi mamakin cewar Zeinab bata san irin matsayin da yaronta na cikinta ya taka a dunia ba, tabbas ya taka matsayin da har yanzun bata gama fahimta ba...sai dai bata yi k'asa da gwiwa ba jin sunan da cikaken kwatancen yanayin ya sakata dira da furta kalmar nan wato *D'ANA NE* ba ko kunya da tsoro!.
*TUSHEN LABARIN*
Haifafun wani d'an k'auye ne mai sunna Kanya dake jihar damagaram, filani ne su su biyu rak yan mata da iyayensu suka haifa. Basu yi ta'lar nono ba, sai dai sukan yi yar sana'arsu ta yan mata su siyar.
Asma'u sai Zeinab su kad'ai Allah ya baiwa iyayensu, Asma'u takan yi yar alewa ta kai bakin makarantar islamiya ta ajiye ta shige makaranta, ana tashi ta dawo wajen tsohuwa ta amshi alewarta ta siyar da abinta sannan ta dawo gida.
Zeinab kam yarinya ce mai zafin nema, takan zaga cikin k'auyen da sana'ar maka da dan wakenta da dakaken yaji tana siyarwa lungu lungu, sam bata zuwa makarantar islamiya sai ta boko kad'ai da take zuwa ta zauna ita ma dan ta ji cewar shugaban k'asar da ake haskowa a TV d'in gidan yar mai gari karatun boko ya yi ya zama wani abu.
Mahaifinsu yana iya k'oknarinsa dan fita hakk'insu , basu da yunwa bare k'ishin ruwa, daidai gwargwado sutura ta yayan talaka mai zuciya suna da shi, a hakan ASMA'U take godewa Allah tana rayuwarta a sauk'ak'e domin kuwa takan kalli wa'inda ta fi ne a koda yaushe ta k'ara godewa sarkin sarauta ba wai wa'inda suka fita ba.
Ita kuwa Zeinab a kullum idan ta tashi burinta ta kamo wata da ta fita ko ta halin yaya, hakan ya sa tana girma tana k'ara sanin yan k'auyukan dake mak'ota da nasu, harma ta san cewa baban garin Damagaram ya fi kusanci da k'auyansu fiye da kowani k'auye, tafiar a k'afama zaka iya yi ka shiga ka dawo lafia domin ba wani hatsari bakin baban titi ne mai d'auke da sojawa da manyan kostan.
Sannu a hankali take yin k'awaye, kala daban daban masu halaya daban daban, dan ta ga burinku d'aya, abin zai d'ore ne, idan ta ga kai burinka ba wani bane sai ta yakice abinta.
Tun Asma'u na da shekaru goma sha biyar ta samu mai son ta, malaminsu ne na islamiya ya fito da zuciya d'aya yana son ta.
Mahaifinta bai tsaya ja ko neman fiye da haka ba ya amince ya bada damar ya fito domin a lokacin tuni ta fara jini.
Ba'a wani dauki dogon lokaci ba aka yi auren Asma'u, aka kaita gidan sirikanta wanda mijinta ya tada mata d'aki ya rufe mata aka yi mata jeranta a sauk'ak'e
Cikin aminci suka shinfid'a rayuwar aurensu, iyayen mijinta sun kasance masu kawar da kai da cire ido a harkar zamantakewarsu, ko yar rigima suka yi irin na zaman yau da gobe sukan tsawatar ne ba tare da sun nuna wariyar shi dansu bane ko wani lamarin, hakan ya sa take jin dad'in gidan aurenta fiye da tunanin mutun, ta yi k'iba ta k'ara hasken fatarta dan kuwa mijinta mai zuciya ne, idan ya fita nema idan aka dace baya tab'a shigowa hannu goma, yakan zo da leda ne, ita kuwa takan fitar ta raba ta kaiwa iyayensa a tsaftatacen kwano sannan ta dawo ta kula da mijinta. Yakan yi mata d'inki ne daga ya samu dama ba sai sallah sallah ko wani gagarumin biki ba, hakan ya sa take da atampopi masu dan kud'i kala daban daban da hijabai masu yawa a cikin akwatinta.
Iyayenta na k'ok'arinsu a kansu, basa gajiyawa haka kuma sukan yi masu nasiha, sukan yiwa yarsu nasiha kan a duniya idan ta saka hak'uri, ta sada kanta, ta yiwa kowa biyaya ita zata tashi da ribar zamantakewar rayuwa.
A haka sukai ta rayuwa da wannan bawan Allah sai dai ko batan wata bata taba yi ba, sam ba haihuwa sama ko kasa ba alamunta, tun ba'a damu ba har aka fara dan neme nemen haihuwar ta sanadiyar wannan suka shirya dan shiga baban birnin Damagaram dan su ga likita.
A wannan lokacin Zeinab ta kai shekaru goma sha takwas a duniya, gandamemiyar budurwa ce a k'auye dan kuwa sa'anninta du an masu aure d'aid'aiku ne basu samu auren ba irinta wa'inda fitowa ke gagararsu domin kuwa yaran k'auyen kad'ai sun ishe su, ita kuwa ba wannan ne a gabanta ba, hasalima karatunta na boko gaba ta ci da shi sannan takan kawo sana'arta bakin titi ta siyar ta koma gari, ba wai masoya ne ta rasa ba a cikin Kanya, ko d'aya, ta fi k'arfinsu ne ta fad'a ta k'ara.
Ita ce yar rakiyar, sun je Birni sun je sun sha fama da k'yar su ga likita wato docter Zalika.
Ta basu dukan abubuwan yi sun yi iya yin su sai dai a dukan bincikenta mijin Asma'un ne baya haihuwa dan haka ta shaida masu abinda ta gani a takardunsu.
Sun shiga tashin hankali mai tsanani iya su biyun, inda Zeinab ta ringa bin manyan motocin dake shige da fice da kallo tana k'ara gyara tsayuwarta da yar jakarta jajajir d'auke da madubinta a ciki da yan cenjinta.
Hannayen matarsa ya rik'e yana kallonta yana jin wani iri a k'asan zuciyarsa, a hankali ya furta" Asma'u, nin e bana haihuwa, ba zan iya tauye ki ba asma'una."
Gannin yana neman wuce gona da iri da sauri ta tare shi da cewar "Hakan na nufin ba zamu samu haihuwa a duniya ba mijina, dan Allah wannan maganar ta tsaya iya mu, bana so ko da wasa a ji a gida dan bana son yan zigi ko yan shiga sharo ba shanu su shiga lamarin iyalina."
Kallonta kawai yake, aman bai wani gamsu ba, a haka suka dawo gida, sai dai suna zuwa suka tarar da tashin hankali.
A wannan yar fitar tasu mahaifinsu ya je gyaran bakin rijiyar gidan mai gari rijiyar ta rufta da shi ya fada ta kansa hakan ya sa ko da aka ciro shi babu, rai ya yi halinsa.
Sosai sukai kukan rashin sa, sosai suka bi shi da adu'a, a nan mai gari ya yi iya yinsa, ya basu gona da kudin noma, ya basu taimako da dama ciki kuwa harda kara biyan karatun Zeinab.
Mahaifiyarsu a dole ta fito daga daka ta ringa kula da lamarin gonar nan, domin a yanzun wannan gona a cikinta ne zasu iya ci su sha, su tifata ba tare da sun yi bara ba.
A haka Zeinab ta shiga karatunta hankali kwonce, zata je makarantarta ta dawo sanan zata yi abin sana'arta ta kai bakin titi ba dan komai ba sai irin samarin da take gani masu da shi a hannu...a haka har ta samu wani baban soja ya fito neman aurenta.
An kai ruwa an kai mari a kan maganar auren nan, dan kuwa mutun biyu kawai suka zo neman auren da mak'udan kud'i, mai gari ya so k'warai aiwatar da bincike sai dai kash, Zeinab bata bashi damar hakan ba ta nuna masa a yi kawai.
Mahaifiyarta bata yi kuka ba sai da ta ga d'aukan amarya mijin kawai ya zo a wata galeliyar mota ya d'auketa suka tafi, a lokacin ta yi kuka kamar ranta zai fita , sai dai a dole ta yi hak'uri ta ci gaba da rayuwarta da d'ayar dake gabanta
Mafarin rabuwarsu da Zeinab.
Zeinab ta yi rayuwa da mijinta ne wata irin rayuwa, ya kasance mai sakar mata kud'i, ya kaita waje ya kilaceta ya sakata a makaranta aman bata san kowa nasa ba. A sati sau biyu kawai yake ziyartarta, wannan ba shine damuwarta ba domin kuwa ko da TV din kadai da ya bata ya barta ya gama yi mata komai na rayuwa, gashi har mai aiki ce da ita yar yarinya dake yi mata aikace aikacen cikin gida, ga kudi ga yawo a mota ga karatu, sai kawai ta shafe maganar kauye a cikin ranta take fuskantar birni da koyon rayuwar cikin birni.
Kasancewar bata takurawa MUHAMMAD KARIBULLAH kan dole sai ta san ahalinsa sai ya kasance mai kyautata mata fiye da tunanin mutun, ya mallaka mata gida har biyu domin daga baya ya d'auketa daga k'aramin gidan nan ya mayar da ita wanda ya fi shi, sannan ya mallaka mata takardunsu.
Ba ita ta je Kanya ba sai bayan shekaru hudu cir ta taka kauyen shima dan mahaifiyarta.
Ta tarar da inna cikin rashin lafia, Asma'u na jinyarta, ta raina gidansu domin ko zama kasa yi ta yi dan kuwa gidan du ya duke a haka ta sa a fitar mata da inna , sai dai sam inna ta ki hakan ta nuna