Showing 102001 words to 105000 words out of 180809 words

Chapter 35 - DUK NISAN JIFA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

02 Feb 2025

12965

shin ramawa zaki yi? Hora ni zaki yi? Aunty kar ki ga laifina dan na yi wannan abin dan Allah, shin ta ina kike so na fara kwatanta maki? Na rayu da nema a zuciyata, dan na je na nema zai zama ila? Ko dan shekarun da na bata ina faman zama abinda nake yanzu na ga inda zan samu karuwa dan na kama zai zama laifi? Inace ilimi na nema wanda annabi ya umarce mu da mu nemi ilimi? Ni ban yi haka dan na nuna wani isata da Hisham ba! Aunty shine har zaki ce ke kika haifeta da cikin ki dan Allah? "

Mama ta yi murmushi mai daci tana kallonta, zata so ta barta ta je ta rarashi kanta ko zasu iya fahimtar junna, aman sai kara riketa take bayan ta san ita din ciki ce mai tara da yawa dare daya idan ta buga sai a hankali

A hankali ta riko hannunta tana kallonta ta ce" Nema ba haramun bane, ilimi shine hasken rayuwa ko ni da na tsaya iya na islamiya bai dace ba domin ina da damar zuwa na koyi ilimi na zamani aman sai na hakura dan ina da raino a gabana! ZAINAB ilimin da zai saka ka tashi ka yi auren da baka san meye ma'anarsa ba na kire shi jahilci, ilimin da bai hannaka zama ka yiwa kanka karatun na nutsu ka bambance matsayin uwa, uba a wajenka ba na kire shi asara, kina yawom nan ilimin tare da mijin da baki san ko waye ba mahaifinki ya rasu, satinki daya kika koma wajen mijinki haka mamanki ta fadi ta rasu, a sanadiyar neman nan na duniya duka kika kawo kwai daya kwalin kwal da kika gani a duniya kika yar kila tafi neman ilimin! Zainab ilimin da kika je nema bai saka ki saurarata idan ina maki bayanin ilimin yaronki ba a tunaninki bagidajiya me zata iya yi ko? Bayan kin manta Allah ke fitar da rayaye a cikin matace kuma matace a cikin rayaye ko? Haka kika shure duka ilimin naki na jagorantarki kika manta da mu bayan number nan ita dai ce kike anfani da ita! Zainab sai yanzu da ilimin naki ya ga gwara ki dawo ki yi naki ikon sai kika tsaya a gabana kika gigila min karairayin da suka haukata min zuciyata har na zubar da hawaye uwa uba dan kin daukeni jahila kika ce layin nan ba naki bane bayan a kaina na hardace layinki kin rufe ni ne ta yada ba zan iya ci gaba da samunki ba!, Zainab ilimin nan naki sakaran ilimi ne dama na son kai ko kuwa naki salon ilimin haka yake bagidaje ba zai gane shi ba?"

Da sauri Tati dake jin wata irin kunya na neman kasheta a tsayen nan ta ce" Aunty "

Mama ta ce" Sunana asma'u!, Zainab to bari ki ji, idan ke zubar da iyalinki kike ki je neman duniya wasu saboda kar mahaifiyarsu ta ji labarin sun samu abinda suke da yakinin shine nasu na farko kuma yana iya zama na karshe , su zubar da aikinsu da komai na jin dadinsu su je su bi mahaifiyarsu dan kawai sun san cewa babu abinda ya kaita dadi, ki fara tuhumar iliminki da nemanki anya basu cuce ki ba? Suka barki kike ta walahigi kina ta nemansu ido rufe har kike rasa abinda yake naki manlakin ki kuwa? You see Zainab ta dalilin nema wasu ke rasa pride dinsu, dan Allah ki tare naki mutuncin tun kafin na yi fatali da shi da kafata!"

Tati kam tun da ta fara maganar nan ta karshe sai ta dawo tamkar bata gane yarenta, a birkice mama da har kusan fita ta kuma dawowa tana kallonta ta dora da fadin" Idan kuwa rusau ta gwamnati na neman bi ta kan tubalin da na ringa azawa dan samun mafaka, zan dauki tanadina na bace a idon gwamnati, domin dama rikon kwarya na lokaci ne!"

Ficewa ta yi gaba daya daga dakin, ta nufi nata tana mai toshe bakinta da hannunta tamkar karamar yarinya tana hanna kukanta barkewa har ta shige dakin nata da sauri ta kuma rufewa ta dora kanta a bakin gadon nan a fili cen kasan makoahinta take furta" Ya Allah ka kama mani, ya Allah ka bani zuciyar da zan ci gaba da nuna mata kurenta har ta gane cewar ba wai kawai komai ne ya kare a abin duniya ba, ba wai kuma komai ake yi a lokacin da aka yi niya ba, wasu abubuwan wasu lokutan dole zaka tirsasa kanka hakuro da su dan a samu zaman lafia, wani sa'in dole ka koyawa kanka kawaicin rayuwa

Hannunta da ta wankawa Bilkisu mari har radadi ya ringa mata, "wayo Allah Yarinyata" ta fada a hankali ta dora da fadin" Ki yafe min, ki yafewa sabuwar uwar da zaki gani a gabannan har zuwa ki bi umarnina, ba zan yarda dan kawai kin kamu da sonsa har ki kai kanki ga halaka ba, Bilkisu irin wannan abin da yake damunki da yayanki idan ya ci gaba a haka ban san ina zan saka kaina ba, kin zurfafa soyaya da yawa duda kina iya yinki dan boyewa aman ni na san me nake gani a tare da ke ko wani motsinki, a yau koda aure ya hada ku sai kin sha wuya domin namiji dai namiji ne, bake wanda ya san sonsa ake fa sai a hankali"

Ita kadai ta kuma sada kanta ta jimke sosai ta ce" ban san a wani matsayi zaka ajiye uwar da kake dora kanka a cinyarta ka fashe mata da kuka ba, sai da na fada maka ka cireta a ranka kwata kwata domin na san abinda yake gabana, sai gashi auren ya mutu duda ban yi so aka daura shi ba, sai kawai aka katse min komai ake kuma son a juya ni tamjar rakumi da akala, na kasa hakura, na kasa shanyewa, abinda na sani daya ne tak......ba zan so yar da na haifa da cikina fiye da kai ba, domin kafin na san zan sameta a duniya kai na goya, kai na sani a yarona...................
."

A kadan ta kai minti goma tana kallon kofar da mama ta bi ta fice har sai da ta ji karar rufe bayi ta juyo da sauri

Ganni ta yi Bikisu bata nan, kwarai take son ta tsaya ta fito ta rarasheta ta fada mata cewar ta yi hakuro mamanta zata sauko fushi take zata yi hakuri, aman wani tsoro ya darsun mata harma ya sakata kasa yarda da cewar wai asma'un zata dawo kan bakanta

Uwa uba maganar nan, agogo dai a yanzun ya nuna har karfe dayan dare ne, idan ta tarda wancen birkitacen yaron ta ina zata fara? Me zata ce masa? A yanda yake jin haushinta ta san yana iya fada mata abinda ita zai daga mata hankali, hakan ya sa kawai ta fice a dakin ta je dakinta

A yau sai ta tsinci kanta da daura alwallah ta zo ta gabatar da nafila raka'a biyu ta zauna saman salayar nan ta kurawa waje daya ido

Da me zata fara? Ta ina zata fara? Me zata fara cewa? Bata taba jan wata aya dan iyayenta ba! Idanma ta yi sallar a gurguje take shafawa ta koma bakin aikinta ko karatunta, ita bata taba ba abu mahinmanci ba irin ranar da za'a yi biya ko abinda zai saka ta ci gaba a duniya

Da sauri ta dauko wayarta ta shiga google, sai ta tsinci kanta da dora tambayar ta yada musulmi ya dace ya fara adu'a? Ba wai bata da karatu a kanta bane, sosai take da karatu da adu'o'i abinda bata da shi shine pratique, bata aiwatarwa, da yawan karatunma du ta manta domin bata tilawa

A hankali ta ringa kallo, har kuma ta dora da karin haske a kan adu'ar mamaci

A yau sai ta tsinci kanta da nacewa adu'ar mamata, ta dage tana ta yi da hannunta domin ko carbin ja bata da shi sai kawai ta fashe da kuka itama
Kuka ne marar sauti irin na mata masu kisa, aman mai jijiga ilahirin jikin bawa mai nuni da na gaske ne ba na kisar bane
A rikice ta mike daga kifa kan da ta yi dan jin numfashinta na barazanar tsayawa ta ringa hailala tana sanar da ubangiji a fili ta ce" Allah, shin sun san wani labari game da mijina ne? Kar dai yana raye, kar dai shi kudin ya barmin da kadara ya tafi da iyalansa da mahaifiyarsa duda irin yanda yake zumudi , yake murnar samun da daya kwalin kwal a dunuya wanda ya tabatar min matarsa ce bata haihuwa? Ya Allah idan yana raye me na yiwa rayuwata? Ya Allah wace irin tsana da sabon hali na dasa a zuciyar yar uwata wace ta min halaci har take bani a baibai cewar tana iya bara min gidan yarona? Ni na zauna daga mi sai yaron da bai san komai a kaina ba sai matar da ta tafi ta barshi a zannin goyo? Ya Allah ka sasauta fushinta domin na riga na aikata nawa laifin"

.........


Bilkisu kam gefen kuncinta ya kumbura sosai har kusan idonta, hancinta da kumatunta sun yi jajajir da su , a haka a zaune ta yi sallah da kyar domin kan nata take jin kamar yana rinjapyarta dan ciwo da nauyi
A yau tsal ta rasa bakin maganar da zata furta ta kwatanta abinda ya faru da ita, haka kuma ta kasa tunanin maganar ta fitar da miji a sati daya jal ciki banda yayanta, maganar ta shafa masu lafia su rayu da iyalinsa ya mata tsayuwar sabon soja a kahon zuka, sai uwa uba irin tashin hankali, hawaye, da bacin ran mahaifiyarta a kanta da kowama ya sakata yin sanrada cewar a yau fa ta faru ta kare, an kare komai fa, an gama mai faruwa ta faru, a yau tana zaune a matsayin wace ta rasa hamanta, farin cikinta, walwalarta, jibi na rayuwarta!, sai ta samu kanta da kurawa waje daya ido ta kasa jan carbin dake hannunta, ta kasa ajiye shi, idannuwanta sun kekyashe bata jin barci bata jin yinwa bata jin komai, abu daya take fata so take ta ji an tasheta a asibiti an ce doguwar summa ce ta yi har ta yi mumunan mafarkin nan, aman kash, basu da alamun zasu tasheta, basu da alamun zasu tayar da ita daga wahalalen barcin nan, gaba daya jikinta ya dume da zafin gaske, tana zaunen nan har kiraye kirayem sallar asuba ya fara shigowa kunnayenta ta masalatai biyun dame dan nesa da gidansu

Idonta ta kifta ta shiga kokarin tayar da sallah domin alwalarta bata kunce ba sai bakinta da ta kuskure duda bata yi magana da kowa ba, sai kawai ta tayar da sallar daga zaunen nan domin kanta banda kara daukan nauyi ba abinda ya yi

Tana gama sallar da ta yi ta shiga kokarin gannin ta tashi ta je ga mahaifiyarta, ya kai sau uku tana yinkurawa sai ta kasa ta koma ta nade waje waje daya ta lumshe idannuwanta, tsabar kukan da ta sha yanzun idannuwan ba hawayen sai wani zogi da suke mata ga kumburin fuskar ga ciwon kai da jiki baki daya wa'inda suka yi mata sauka daya tak

Ta jima a yannayin nan har ta ji alamun an bude dakin nata

Da sauri ta bude idanniwanta a zatonta mama ce, sai ta ga tati ce

A hankali take takowa hannunta dauke da trey har ta zauna kusa da Bilkisu

Bata yi mata magana ba, domin ita din kanta muryarta ta mata nauyi, da ido ta ringa mata nuni kan ta tashi ta sha shayin da ta hado mata mai zafi

Bilkisu ta kasa tashi domin sai da ta yinkura din ta kuma komawa

A hankali tati ta kamata ta tayar da ita zaune tana taba goshinta tana jin irin zafin da ya dauka hakan ya sakata da sauri ta taba wuyanta ta hanyar saka hannunta ta cikin hijab dinta ta taba shi
Idannuwanta ta lumshe muryarta cen ciki sosai ta ce" Kuka kika kwana yi ne har ya saka ko zazabi? "

BILKISU ta dan girgiza kanta tana dan kare bakinta domin bata iya zuwa bayi ta kuskure bakinta ba, rashin sabo ya sakata tunanin kar a ji warim bakin nata shi yasa take ta kare fuskarta duda ba maganar ta yi ba.

Tati ta dan janyota jikinta a hankali ta dorata ta dauko kofin shayin nan tana dan juya shi dan ya rage zafin da yake da shi kafin ta kafa mata a hankali tana kallonta.

Da kyar Bilkisu ta iya surba du kuwa da irin yanda take son shan a ranta domin so take ta samu kwarin da zata iya zuwa wajen Mama.

A sanyaye Tati ta ce" Ki daina kukan nan da damuwa kin ji? Ki yi ta adu'a auntu zata sauko, cen dama bata iya fushi ba, shi yasa du abina bana so ta yi fushi, kin ga yanzun na kureta ta dauki fuahin da kowa kuma ina gudun sai ta hora kowa, aman na san ba zata raba ki da yayanki ba."

A hankali Bilkisu ta dago dara daran idannuwanta da suka dauki kalar ja suka kumbura saboda kuka da firgici tana kallonta, rabani da yayana abinda ta fara maimaitawa kanta kennan, waye ya raba ni da yayana? Ta kuma tambayar kanta, a hankali ta dan girgiza kan nata tana murmushin da iyakarsa kan leb'enta.

Muryarta a sanyaye ta ce" Inata, Uwa ce mama, tunda ba umarnin da ya sabawa musulinci bane zan yi biyaya, Walahi zan yi biyaya koda hakan shine sanadiyar barina duniya baki daya, Innata yau ina yar uwata Mami? Tabas Mami ta ci ribar biyaya ga iyaye domin Mahaifiyarta da mahaifinta asalin hawayen rabuwa da ita suka zubar kafin su cire da yi mata shinfida a makwoncinta, nu Bilkisu na hakura da yayana har abadan abada, daga jiya zuwa yau na yakice yayana a kundin tarihina, Allah shine zai dafa min na bar rayuwarsu kwata kwata in sha Allah "...tana fad'a ne idanuwanta a soye, tana bud'e su da k'yar, kalamanta da d'an k'arfi domin daga zuciyarta take k'wato su tana harhad'a su, hakan ya sa suke fita da k'arfin da ya saka Tati rintse idanuwanta, anya zata ci gaba da zubawa zuciyarta abubuwa na emotion haka? Ba zasu illatar da ita ba kuwa?



*Masha'Allah*
[7/24, 10:19 AM] BAK'A CE: ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ๐ŸŽพ

_RUBUTAWA_

*SAJIDA*

*SADAUKARWA*

*GA*

*MASOYA NA*


๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_


40

Assalamu Alaikum
Masoyanmu da fatan kuna lafiya.

Muna miko maku godia da fatan alkhairi masu matukar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kudi.
Alal hakika munji dadi kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya kara budi.

Ina kuma kara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu danasani a siyan littafin.

Yadda kuke siyan littafin yana kara mun kwarin guiwa wajen yi maku typing din littafina na *KOMIN NISAN JIFA* ina fatan zaku cigaba da siye don in samu kwarin guiwar yi maku typing din littafina na kyauta akan kari ba tare da bata lokaci ba.

Na yadda daku na aminta da irin kaunar da kuke mun, nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAKIN MATA*

*INA SONKU SOSAI INA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*

Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)๐Ÿ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.

_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._

_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_

Na yadda daku, na aminta da irin kaunar da kuke mun don hakan ina da yakinin cewa zaku siya don nuna mun kalar soyayya da kaunar da kuke mun da littafaina๐Ÿฅฐ



A yau gata zaune gaban yar yarinya karama tana fada mata maganar da take jin kamar da ita ake, ita fa kwata kwata ji take kamar da ita Billy take, kamar tana nuna mata mahinmancin biyaya ga iyaye ne, ya Allah, kwarai wani irin girman yarinyar da mamakinta ne suka darsun mata a zuciyarta, koda kuwa ta kasance mai biyaya ce to fa lalle tana cikin daidaikun yaren zamanin dake iya take soyayar da suke yiwa namiji su kawar da kai komai tsananinta, ko ita da take uwa a gareta ta tabata da ace itace ke cikin irin halin da take ciki da ta murje ido ta nuna aa ita fa a bata abinda take so ko ran kowa ya baci

Jikinta a sanyaye ta buda wajen kayan Bilkisun da ta nuna mata akoy maganinta ta balo mata da ruwa ta kuma bata ta sha sannan ta kamata ta kaita saman gadonta

Muryarta a sanyaye ta ce" ki huta, Allah zai sanyaya mana baki daya "

Bilkisu ta lumshe idannuwanta da take jin ba zasu hade da kyau su rufe da kyau ba a hankali ta shiga salatin annabi tana karawa idannuwanta lumshe, yi take yi daga cen kasan zuciyarta har ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login