Showing 246001 words to 249000 words out of 260321 words
Chapter 83 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
da abinda zaki sake hararta ya fada” yana yunqurowa kamar ze tashi ai kuwa na kwas nayi dakina da gudu na rufo qofa seda na jingina kafin takaicin kaina ya kamani, meye haka nakeyi? Ni da ya kamata na fututtuke na nuna masa bacin raina akan me ze saka a daura mun aure ba tarefayarda ta ba shine duk zanbi na wani rude daga ya dantaba ni sekace wata kwaila aikin banza kai.
“Asmy ki bude ina muyi magana” na jiyo yana fada bayan daya kwankwasa qofar a hankali.
“Bazan bude ba ka kuma fitar mun daga gida kaima malam” na fada a tsiwace.
A zatona ze fara roqar na bude qofar ko wani abu se ji nayi yace
“Shikenan toh se anjima” ya fada ba tareda wata damuwa ba kafin nayi wani yunquri najiyo qarar bude qofa da rufewa, se nayi saurin matsawa jikin window na daga labule ai kuwa na hango shi ya shige mota Driver yaja sun qara gaba.
Wani qululun baqin ciki yazo ya tsaya mun a wuya, farawa da Bismillah saboda an bashi aurena a wulaqance shine ze fara wulaqanta ki ya nuna mun cewar su Maza duk halin su daya na wani ne kawai ya fito fili. Idan kina kasuwa kamar zasuyi miki sujjada tsabar tarairaya daga inda kika zo hannu ke da bola banbancin ku kadan ne, se kawai na nemi gefen gado na zauna na fashe da kuka.
Ba laifinsa bane laifin yan uwana ne su suka ja mun da suka nuna masa neman kai suke dani. Wayata ce ta dauki qara na janyota da sauri ganin Yusuf ne yake kira
“Bada amincewata aka dauramun aure da kai ba kuma ni dana ce ka tura ma wasa nake maka saboda kawai na bawa Bashir haushi ne amma shine kaje ka saka aka daura mana aure ko to ni bana so babu kuma wanda zeyi mun dole dan haka ina jiran ka ka dawo ka sawwaqe mun” na fada cikin kuka bayan dana daga wayar.
Shiru yayi na kusan minti biyu dan na zata ma ya kashe wayar kafin naji ya fara magana cikin sauti irin can qasan nan yace
“Nima ban san haka zata faru ba dana dakatar dasu saboda bazan aure ki ba tareda ke da kanki kin yarda ba, sannan ko a yanzu bazan matsa miki ba Asmy, daga nan har zuwa shekara daya kina da dama idan har kika ga bazaki iya zama dani ba zan haqura na sallameki saboda ni ba maye bane da zan auri mace dole bata sona bayan ga masu sona nan birjik a gari suna neman na aure su.
Sannan kuma ina tabbatar miki tunda kika koreni bazaki sake ganina a gidan ki ba idan har ba ke kika gayyatoni da kanki ba. Daga qarshe abinda na kira na gaya miki shine yanzu da da ba daya bane kina amsa sunan MATAR YUSUF ne, ban yarda da fita barkatai ba tareda dalili ba, ki tabbatar duk Namijin dana samu labari kin tsaya kuna maganar da bata aiki dashi ba ko wanene kome kuka hada dashi indai ba jini ba sena dauki mataki akai.
Duk abinda kike da buqata ki turamun da saqo ban yarda ko man mota ki siya da kudin ki ba, idan na samu jirgi zan juya Abuja yanzu idan ban samu ba kuma se gobe da safe” yana gama fada qit ya kashe wayarsa.
Sororo nabi wayar da kallo, Yusuf dai dayake bina yana lallaba ni kamar kwai yau shine yake mun magana cikin isa da bada umarni haka? Ni Asma’u yake cewa baze sake zuwa inda nake ba sena neme shi to na neme shi yayi mun me? Ta yaya ma yake zaton ni zan kai har tsahon shekara da auransa akaina wannan ma zance kawai yake yi ze kuwa san dani yake dan da kansa ba se kowa ya aiko shi ba ze aiko mun da sallamata.
Tunawa da banyi sallar Isha ba yasa na tashi na shiga na dauro Alwala, har na saka hijabi Bashir da jinin dana gani yana zuba a hannunsa ya fado mun se nayi saurin bude qofar dakin na fito daidai sanda Amnah take goge gurin Aliyu kuma ya tattare fasassun Gilasan ya zuba a abun shara.
“Kayi a hankali kar ka jiwa kanka ciwo” na fada ina kallonsa wani tausayinsa yana ratsani dan har ga Allah duk ciki nafi tausaya masa, kamar shi kadai ne ya damu da halin da ake ciki daga kan Jafar zuwa qasa hidimar su kawai suke karma shi Jafar din yaji labari sam na rasa ina wannna qulafucin uban da yake dashi a da? Gaba daya yanzu sabgarsa yake kamar ma ya manta da cewar Bashir ne ya haife su.
Daki na koma na tayar da sallata, seda na idar da shafa’i da wutri na dade sosai ina Addu’a kafin na shafa na tashi ina jina wata iri wai fa a karo na biyu wasu igiyoyin auran sun sake hawa kaina na wani mutum daban ba Bashir ba.
Ina kwance lamo akan gado na tunanina ya kasu gida da yawa, sabuwar rayuwar da nake shirin fuskanta, yaya matsayin aurena da Yusuf yake in karbe shi ne ko kuwa nayi abinda zuciyata take ayyana mun na tilasta masa har seya bani takadda ta amma wai a wanne dalili ma zanyi haka?
Zuwa yanzu idan nace bana son Yusuf har cikin raina nayi qarya dan daman tun Asali ba son sa ne banayi ba, soyayyar da nake yiwa Bashir ce ta shafe ta kowa da har na gaza gane menene so in dai ba akan abinda ya shafe shi ba.
Addu’a dai nayita nasa anyi mun duk akan neman zabin Allah yanzu wannan Al’amari ya kasan ce a haka idan naja dashi ai ya zama butulci ne ga Allah na kuma ja da lamarinsa kenan tabbas baza tayi mun kyau ba idan Allah ya barni da zabi na ina ma da tabbacin idan na kashe auran da ko kwana daya beyi da dauruwa ba zan sake samun wanda ze so ni tsakani da Allah ne harya aure ni?
Wai meye ma laifin Yusuf ne? Koda yake tarihine yake maimaita kansa irin haukan son da nayiwa Bashir ne ya ringa yankwana ni na nace ma liqe shine yanzu Yusuf yake gwada mun na samu dama nima zan shuka tawa tsiyar amma fa banga alamar shi ze jure irin wulaqancin dani na shanye a tawa soyayyar ba, koma dai yaya ne har yanzu ina a kan Batu ma neman zabin Allah, idan aure na da Yusuf Alkahiri ne Allah ya zaunar damu ya dawwamar da farinciki a tsakanin mu har qarshen rayuwa.
Washe gari dole na shirya fita aiki saboda ina da presentation da zanyi yau na wani project, tareda yara muka fita saboda Aliyu ya gaya mun Abbinsu yana kwance bashi da lafiya, na tausaya masa amma abin mamaki banji irin wannan rudu da tashin hankalin da nake shigaa duk sanda wani abu ya samu Bashir ba. Kai gaba daya yau ma ni a karon kaina naji chanji.
Wata kamala naji ta lullubeni, a gurin saka kaya ma yau seda na chanza shigata. Doguwar rigar Atamfa na saka sakakkiya na yafa yalwataccen mayafi daidai da turarena wasu nayi amfani dasu daban irin wanda se mun samu kusanci sosai da mutum sannan zeji qamshin su sabanin kwanakin baya da nake fesa kwalliya ta daukar magana idan zan fita aiki.
Seda na sauke su a makaranta wani tunani ya fado mun, koba komai Yusuf matsayin miji yake a gurina yanzu, Allah babu ruwansa da ina sonsa ko bana sonsa matsayi da hukuncin sa daya ne akaina. Wayata na janyo na tura masa da saqon cewar na fita aiki sannan na biya na sauke yara a makaranta.
“Se bayan da kika fita sannan zaki sanar mun babu komai na yafe miki, kiyi aiki kadan karki wahalar mun da kanki. Yanzu nima zan wuce jiya ban samu jirgi ba, Love you” ya dawo mun da amsa.
Murmushi nayi dan a yanda muka rabu jiya na zata ko ze amsa ni zanga fushi a cikin maganar sa, fatan sauka lafiya na masa na tura se kawai na kashe wayar gaba daya dan bana so wani ya kirani akan maganar auran nan, tun jiya da mukayi magana da Alawa ban sake daga wayar kowa ba dukda se kirana suke nasan wulaqanci ne zasu mun ba wani abu ba dan Khadija harda tura mun saqo wai naqi Allah yaso da baqin ciki se ya mutu ku jifa dan Allah.
Sanda na shiga office dina seda mamaki ya kusan kashe ni ganin yanda akayi wa gurin kwalliya da ballons kamar wanda za’ayi wani qaramin party. Akan teburina naga kati me azabar kyau an rubuta
‘Happy married Life Mrs Asma’u Yusuf Wunti’ da mamaki na kalli sakatariyata data shigo tana dariya kafin nayi magana ta rigani da cewa
“MD dakansa ya saka akayi tun jiya da baki shigo ba, shi ya kawo mana labarin kinyi aure mutane se mamaki suke yi wai dama baki da aure mudai bamu cewa kowa komai ba. Gaskiya na taya ki murna Madam kowa kika aura yana sonki dagaske wallahi Allah ya baku zaman lafiya”.
Kasa ce mata komai nayi dan bakina ya mutu da mamaki haka na karbi System dina data gama gyaramun aikin da zan gabatar muka fita. Duk inda muka wuce taya ni murna ake har abin ya ringa bani kunya yanzu da girma na haka kawai aka zo aka shelanta nayi wani aure koma wane me shegen surutun ne oho.
Dab da zan tashi MD ya aiko kirana, da taraddadin dalilin kiran na tafi, bakinsa har kunne yake tayani murna sannan yake tambayata na rubuta takardar daukar hutu dukda naci sati biyu a cikin hutuna na wannan shekarar wai sun bani hutun wata biyu duk sanda na shirya sena fara.
Nidai haka na fito na baro shi a raina ina cewa hutum me zan dauka se kace wani auren fari dan Allah ji yanda suke ta wani digimi.
Bayan sallar magriba ina zaune sega kiran Yusuf, kamar bazan daga ba se kuma na dauka a taqaice muka gaisa ya tambayeni yara da aiki nace lafiya se ji nayi yana mun sallama wai se da safe kawai nabi waya sororo da kallo na ma rasa abin cewa.
Mutumin nan fa dagaske yake, ai kuwa mu zuba mu gani waye ze gaji da wasan.
Washe gari Alhamis da daddare ina zaune a falo badan ina gane abinda suke kallo ba se don kawai na ragewa kaina rayuwar quncin data aure ni tunda dai me afkuwa ta afku.
Aliyu ne ya shigo gidan da sallama dan tunda suka taso makaranta yana gida gurin Babansa da a bakinsu naji sunce jikinsa yayi sauqi sosai ba kamar kwana biyun ba, zama yayi kusa dani ya gaishe ni se yake gaya mun wai Abbin su yace ya tambayeni zasu zauna a gidan na sati daya ze tafi Gombe, wani iri naji, dagaske har Bashir ya sare da wurwuri haka koda yake me nake so to yayi? Ci gaba da kulani zeyi ya take dokar Allah ga wannan Yusuf din shima da ba gama sanin zuciyar sa mukayi ba ban sanme ze iya aikata wa ba dan haka nace masa ya gaya masa babu matsala Allah ya kaisu lafiya.
Bluetooth ya ciro daga aljihunsa ya saka a kunne yayi yan danne dannensa a waya can se ji nayi yace
“Mami, Abbi yace in roqa masa ke ki yafe masa, Uncle Yusuf yayi muku iyaka badan haka ba da kansa ze zo ya baki haquri ya nemi yafiyarki” Aliyu ya qarasa a hankali, ba tareda na kalle shi ba nace
“Ka gayawa Abbin ku na yafe masa ni daman be yi mun komai ba duk abinda ya faru qaddara ce da bamu isa mu kauce mata ba”.
“Mami yace na gaya miki wallahi yana sonki, kuka be taba yi miki wani abu saboda ya wulaqanta ki ko kuma dan baya sonki ba, rashin sanin yanda ze bayyana abinda yake zuciyarsa ne yasa ya ringayin duk abubuwan da suka faru” Aliyun ya sake fada kansa a qasa ba tareda ya kalleni ba.
sena kama hannunsa ina murmushin qarfin hali nace
“Nagode, kace ina masa fatan Alkahiri ina kuma yi masa Addu’ar Allah ya bashi wadda ta fini”.
“Amin, seda safe bari naje na hada masa kayan da ze tafi dasu toh saboda hannunsa” ya fada yana miqewa. Kamar nace masa ina matarsa da bazata hada masa kayan ba amma se naga ina ruwana ma. Alhamdulillah, ko babu komai yanzu rabin hankali na ya kwanta, Bashir ya dawo cikin nutsuwarsa, Aliyu ya dangana ya dauki girman da yake akan sa nasan in Allah ya yarda ko bana tare dasu Yarana bazasu shiga damuwar da nake hasashe ba.
BAYAN WATA UKU🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 64
BAYAN WATA UKU
“Wallahi nagaji, ka gayamun kawai SH idan so kake na mutu kawai ka huta amma wannan jan ran ya isa” na fada dakyar saboda yanda nake jina kamar wadda take yawo a gajimare.
“Ki mutu fa kika ce ni kuma in zauna dawa?” Ya fada da saurin sa,
“Ka zauna da baqin halin ka irin na yan Bauchi mana ai naga alamar abinda kake jira kenan safiya tayi ace maka Asma’u ta mutu”
Wata muguwar dariya ya sheqe da ita dukda nasan shi kansa qarfin hali kawai yake dakiyar zuciya ce kawai irin ta yan maza amma nasan ya fini a zabtuwa da kewa yace
“Da wuri haka haba Asmy karki bawa mata kunya mana, wata uku fa kacal kike cewa kin gaji dame kika gaji toh?” Ya yi tambayar cikin sigar zolaya yana dage mun gira daya.
Baki na zumbura gaba kamar yarinya na kwabe fuska ina harar screen din wayar nace
“Wallahi nasan Asiri kawai kayi mun amma ta yaya yaushe ma ni na fara sonka haka da har nake jin kamar zan zauce saboda ban ganka ba”
Wannan karon ina kallonsa tsabar dariya seda ya fado daga kan kujerar da yake zaune wayar ta kife a qasa, iya quluwa na qulu banyi aune ba sejin hawaye kawai nayi suna diga daga idona dan wallahi kamar wadda aka kunnawa wuta a zuciya haka nakeyin wani irin so da kewar Yusuf suna qonani. Idan za’a saka mun bindiga bazance ga sanda hakan ya fara ba abu daya kawai dana sani A cikin watanni ukun nan Yusuf yayi nasarar yin rugu rugu daduk wani qashi da tsoka da suke a cikin jikina.
“Haba mana Asmy kuka kuma ki bari dan Allah bana so” ya fada a rikice kamar ze fito daga cikin wayar. Sena qarawa kukan shagwabar tawa qaimi ina cewa
“To ba kaine ba saboda kaga na damu dakai shine na zama abin tsokanar ka kake mun dariya, ai Allah yana kallonka wallahi kuma nima duk ranar muka hadu sena rama duk irin abinda kayi mun”.
“Me zaki rama bayan duk wanda kikayi mun Asmy, wata na uku ba da zama ango amma nida qaton gwauro bamu da maraba saboda tsabar mugunta fa korata kikayi kika ce karba sake zuwa inda kike ya kike so nayi? Ina son ki da yawan da zan iya miki duk abinda kike so koda ace ni bazan ji dadi ba indai ke zakiyi farin ciki burina ya cika” ya fada cikin sanyi da taushin muryar da ya yaqi duk wani burnishin taurin kai daya rage mun”
“Nace kayi haquri lokacin ina cikin jin haushin an mun auran dole ne kamar wata wadda ba’a so daga zuwa tambaya kawai aka daura mun aure” na fada cikin shagwaba yanda kasan wata Sweet sixteen, koda yake idan ina tareda Yusuf, yanda yake shagwabani yana riritani jina nake kamar jaririyar da aka haifa yanzu baje kolina nake ina barje shagwaba yanda raina yake so.
“Ni daman baki mun laifi ba, kuma haryanzu kece baki so dana zo inda kike ba tunda baki bani dama ba”
“Ni wallahi naqi jinin wannan halin ayiwa mutum abu yace ba’a masa ba amma kuma yabi ta qarqashin qasa yayiya gallazawa mutane, indai da gaske banyi maka laifi ba ko ka haqura kusan wata yara kenan fa ina baka haqurin nan amma kaqi kazo kullum kuma kace kai banyi maka komai ba” na fada cikin shashsheqa kamar wadda take kukan gaske.
Seda ya dauke wuta na dan lokacin, yana yin kallon da yakeyi mun kansa ya canza kafin qasa qasa yace mun
“Ki bari karki jawo mun kuma ki rasa yanda zakiyi dani, kuma yaushe kikayi wata goma kina bani haquri banda qarya fa Asmy”
“Mugu aini ka iya saka ni a ukun ka barni da jiyi akan gado ai” na ayyana a zuciyata a fili kuwa nace
“Toh ai ni duk wata daya ba tareda kai ba a matsayin wata uku yake, kasan kuwa yanda nake rayuwa a nan? Ikon Allah ne kawai yake riqe dani amma qila da tuni an dade dayinsadakar arba’in dina”
“Asmyyyyy” yaja sunan seda tsigar jikina gaba daya suka miqe kafin yaci gaba da cewa
“Asmy baki so ki ganni ba, kawai fada kike amma ba dagaske kike ba”
Haka kawai naji hawayen gaske suna neman balle mun wai wannan mutumin me yake so nayi masa da ze tabbatar da ina son sa ina son ganinsa? Tun fa waccen ranar daya tafi be sake dawowa ba. Sedai ya kirani a waya yayita zalintata yana kassaramun zuciya sannan yanzu yace mun wani wai fada kawai nake bana son na ganshi bayan badan kar nayi abin kunya ba da tuni ni na bishi duk inda yake.
“Kinga, daga nan ina ga China kawai zan wuce akwai kayan da nayi order zasu taso zan je na dubasu tunda idan na dawo Nigeria ma bani da abinda zanyi, kai Allah ka bani me sona na qara aure kawai na huta da wannan shakulatun bangaron da ake mun ta ko ina” ya fada yana wani shan kunu kamar gaske.
A harzuqe nace “daga can ka wuce bangon duniya ma kawai karka dawo dan ma kaga ana sonka an damu dakai shine zaka ringa yiwa mutane haka, ka tafi din kaida Allah tunda dai kasan ina da haqqi akan ka kuma se naga dama zan yafe”.
Dage kafadu biyu yayi yace
“Toh ai gara na tafi sabgar neman kudina da in zauna ana garani kamar kwallo, kuma da