Showing 51001 words to 54000 words out of 260321 words
Chapter 18 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
suka tsira kuwa sunyiwa tasu boyo me kyau kafin a sane ta.
“Addah lafiya, meya faru? A ina kuma? Dada ta tambayeta cikin damuwa da jin kukan nata tasan ba lafiya ba amma Number Asma’u data gani yasa hankali be tashi da yawa ba tasan koma mene ne da sauqi.
Addah kukan ta taci gaba dayi, ganin da Asma’u tayi bata da niyyar ansawa Dada ya sakata karbar wayar ta danyi mata bayanin iya abinda ta fuskanta da lamarin.
“Ashsha abu beyi kyau ba, yanzu waye ya kulle gidan? Shi Bashir din ya sani?” Dada ta tambaya se Asma’u tace mata
“Muma bamu sani ba Ai, Baban Ali kuma ban sani ba gaskiya ko yasan maganar dan wayarsa a kashe take tundazu dana kira”.
“Shikenan bari nayiwa Amiru magana gashi can yana cin abinci daman nan gidan naku ze taho ya dauki Rahma in yaso se suzo da Naziru yanzu Allah ya kiyaye gaba” Dadan ta fada zuciyarta sam babu dadi, yanzu wannan wane irin abune ai yanzu Allah kadai yasan inda maganar sunan nan zata tsaya sun jawo musu abun fada a gari. Fitowa tayi daga dakin ta ta tarar da Amirun a tsaye yana niyyar fita dan sunyi sallama ta shiga ciki.
“Amiru ka nemi Naziru ku tafi tare gidan Yayan naku ba lafiya ba”.
Da”Allah ya kyauta” ya amsa mata ya fita yana dannan kiran wayar Naziru dan shi duk a zatonsa be wuce a ce rigima ce tsakanin Ma’u da Amirah ba, a hanya ya dauki Naziru daya maze kamar besan me yake faruwa ba, gama wayarsu da Bashir kenan ya kirashi da wani layi yace masa duk me za’ayi karya kuskura ya bude gidan nan qasa da qarfe goma na dare yanzu kuwa har tara ta gota dan haka ya qara musu awa daya se sha biyu ze bude su kuwa.
Kamar wata boarding school ranar hutu haka suka tarar da qofar gidan cike da motoci, yawanci mazajen wadanda Allah ya taimakesu suka tambaya kafin suka fito ne an kuma san inda suka tafi da sukaji shiru suka biyi sahunsu se wadanda yan uwansu suka kira su dauke su.
“Kai lafiya kuwa gidan meyake faruwa haka” Amiru ya fada se Naziru ya marairaice kamar na Allah yace
“Yanda ka gansu yaya nima haka na gani, mu qarasa mugani Allah yasa dai lafiya. Bakin get suka qarasa inda wasu suke qoqarin yanke kwado amma kamar na tsafi yaqi yankuwa wasu daga gefe kuma suna musu magana akan su bari, ta yaya zasu budewa mutum gida bada izininsa ba duk abinda yake ya dawo su tabbata yana kansu.
“Wai meyake faruwa haka ne” Amiru ya tambayi masu yanke kwado dan shi tunaninsa ya tafi kodai gobara ko wani babban Al’amari ne kuma yake faruwa amma kuma hmga kwado ta waje ga kuma kururuwar mata suna jiyowa daga ciki suna ihun a taimaka musu.
“Kagane Alhaji nima bansan me yake faruwa ba gaskiya Beb dita ce ta kirani tace nazo na dauketa a gidan nan tazo suna daman ni na kawota dazu se kuma tace na taho da me yankan kwado idan zan zo kaji iya abinda na sani nidai” shugaban masu kiciniya da kwado ya fada.
Se Amiru ya kalle shi cikin masifa ce“wannan wane irin rashin hankali ne, meye a cikin gidan da har zaku zo ku budewa mutum ba tareda izininsa kona wanin sa ba idan wani abun nema ai se ku fara neman izinin me gidan tukunna”.
“Megida ka ganmu nan dukka jiran a bude gidannan muke takamaimai babu wanda zeje maka yasan me yake faruwa dayawan mu munji shiru ne matan mu basu dawo ba muka biyo sawu wasu kuma kiransu sukayi a waya suzo su dauke su kaji yanda abin yake” wani mutum ya sake fada, se Amirun ya zaro wayarsa bayan yacewa Me Yankan ya tsaya ya dannawa Bashir kira cikin Sa’a kuwa ta shiga.
Basu ko gaisa ba Bashir da yasan kiran ko na menene yace masa
“Ni na saka Naziru ya kulle gidan kuma wallahi duk wanda ya budemun gida kafin sha biyu na dare se nayi sharia dashi” qit ya kashe wayarsa. Se Amirun ya juya yana kallon Naziru daya sha kunu
“Bani key din Idan yaso se yayi shari’ar dani” ya fada fuska babu wasa.
“Amma yaya kasan dai ni laifina ze gani ai kuma...”
“Zaka bani ko bazaka bani ba, daman kasanabinda yake faruwa muka taho amma baka gayamun ba kayita biye masa kunawa mutane shirme. In ba haka ba matan auran zaku kulle har se sha biyun dare saboda shirme” fada sosai Amiru ya rufe Naziru dashi, wayarsa da ta shiga qara ce ta katse shi ya daga Ummi ce cikin kuka take gaya masa halin da ake ciki dan a zatonta yana Katsina shiyasa tun tuni bata kirashi ba.
“Tundazu ina bakin Get din na rasa ta inda zan fita na kai yarinyar Asibiti Yaya tsoro nakeji karta mutu a hannuna” ta fada cikin kuka. Nan da nan hankali sa ya qara tashi, Naziru da yake kusa dashi duk yaji me take fada tun kafin ma ya masa magana ya zaro key ya bude gidan ba tareda ya saurari Mazan da sukayo masa caaa akan daman shi ya kulle amma ya barsu suna shan sanyi a tsaye.
Yana bude qofar da Ummi yaci karo da azama ya karbi Babyn suka juya shida Amirun tabi bayansu suka shiga mota kafin Mata suka fara tseren fitowa kamar an sako kaji daga keji wata dankwali a hannu wata da takalmi qafa daya babu dai me cikakkiyar nutsuwa a cikinsu kowa tayi ta kanta. Suna dai kam da yawa sunce ko su suka haihu sun yafe bare a sake gayyatarsu suje.
Cikin qasa da minti Goma sha biyar gida ya rage Me jego da Addah da Inna Gaji se wasu dangin su Addah da basu fi biyar ba ga Hajia Mariya data sha goyo Aljanar ta tafi har sannan shame shame bata farfado daga Iskokan data hau ba.
Inna Gaji da ta rakube a lungu ce ta fito tana cewa “Allah na tuna Allah karka kuma hukuntani da irin wannan bala’i na tuba wallahi bazan sake zuwa taron suna ba” babu wanda ya kukata se ajiyar zuciya suke saukewa, dakyar Hajia Hassana ta numfasa tace
“To Fatu se a san yanda zaayi da Mariya a kaita gida dan kinsan duk sanda tayi irin haka seta kwashi kwana biyu ko uku bata farfado ta dawo daidai ba nidai wannan suna naku ya shiga tarihi wallahi kar Allah ya sake maimaita mana...”
Jiniyar Yan Sandan data karade gidan ta sakata yin shiru, toh fa wane bala’in ne kuma ya tunkaro???
Kuyi haquri qarfin hali kawai nakeyi abubuwa sun sha kaina 🙏🙏🙏🙏
A karanta da haquri banyi editing ba🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 20
A kofar gida Alhaji Kabiru Dangaske ya faka motarsa data yan sandan dake tare dashi. Kofar gidan wayam kamar anyi ruwa an dauke kai bazakace gidan Engineer Bashir ne daka kwashi uwar Sabada dazu ba dan tuni ko wacce ta kama gabanta dan dare ya farayi musamman gashi garin sanyi daman. Mata biyu yan sanda doguwa da gajeriya da suka zo dasu ne suka shiga gidan dan qofar a bude take.
Mamaki ne ya kamasu tsakar gidan ga kujeru Birjik wasu ma sun karye kamar wanda akayi wasan dambe a gurin ko ina dai kacakaca daidai da kayan DJ fa nan sukabarsu tunda suka samu hanya suka fece to ana ta kai wayake ta wasu Kayan kida 😂😂.
“Naga part biyu ne ina zamu shiga” gajeriyar ciki tayi tambayar
“Nima haka na gani mu koma gurinsu muji ina tracker ta tsaya” dayar ta bata amsa suka juya inda ragowar tawagarsu suke.
“Oga mun shiga amma gidan part biyu ne wanne guri matar take?” Yar doguwar ta fada.
“Inaga ku shiga tare kawai bana son bata lokaci nifa” Wani Dan baqi tsamurmurin mutum dayasa uwar babbar rigar shadda Getzner se maiqo take daga gani shine Alhaji Kabiru Dangaske ya fada.
“Ai baze yuwu ba mu shiga gidan matan aure ba Alhaji sedai su matan da dai zamu samu ayi mana sallama da me gidan ne idan ya bada izini se mu shiga kuma kaga layin babu kowa, ku je na daga hannun hagu dai direction din yake nunawa”.
Komawa sukayi kai tsaye kuwa suka nufi part din Amirah dan shine a hannun hagu din suka tsaya abakin qofa sukayi knocking.
Bugun da suka jiyo anayi ya qara hargitsa musu ciki dan daman tunda suka jiyo jiniya kowa tasha jinin jikinta, Inna Gaji kuwa daman kuka ta saka tana tambayar wai wane tsautsayi nema ya tsayar dasu ne a gidan bayan wannan uban bala’in da aka sha yanzu idan wani abun nefa yazo ya sake rutsa dasu ta tafi ta kulle qofa ilai kuwa gashi ana bugu.
Hajia Hassana ce tayi qarfin halin tambayar waye jin muryar mata ta dan sauqaqa musu tsoron har taje ta bude qofar sedai ganin mata da uniform yasakata ja da baya tana karanto wa’innahu sulaimanu dan itafa duk tashin hankali ayi shi amma aduniya tana tsoron Allah tana tsoron hukuma.
Tsakiyar palour suka tsaya suna qarewa palour da akayi wa wada wada kallo,
“Amm muna neman Hajia Mariya ne” yar gajerar ta fada tana qara tsuke fuska ganin yanda duk suka zuba musu ido ai kuwa a tare suka nuna musu Mariya dake kwance shame shame tana bacci”.
“Meye haka ku tashe ta mana tana kwance cikin wannan tarkacen wai meya faru haka a gidan ne?” Doguwar ta fada kafin ma su amsata Gajetiyar ta katseta da cewa “Ba wannan ya kawo mu ba muyi aikin mu kawai” ta qarasa inda Hajia Mariya take kwance ta shiga tashinta amma shiru bata motsa ba.
Dagowa tayi ta kalli su Addah da sukayi tsilli tsilli a gurin tace “Nauyin baccine da ita haka?”
“Ranki ya dade yanzu ta sauka daga iskokai ne wani lefin tayi ake neman ta station?” Hajia Hassana ta tambaya. Ba tareda officer ta amsa mata ba ta juya tana cewa dayar “ina zuwa” ta fita.
A qofar gidan tayi musu bayanin abinda aka fada musu, Alhaji Dangaske ya hau kumfar baki shifa a shiga a dakkota kawai haka takeyi duk sanda ta aikata wani abu seta hau iskokai To wallahi wannan karon ko bulukiya t hau se dai a kulle su ita da Aljanun nata.
Inspecta da suke tarene yace taje tayi musu sallama da me gidan ta koma minti kadan ta dawo tace baya nan.
“Wato ni za’ayiwa wasan kwaikwayo kuna tsaye kuma Naga alamar bazakuyi abinda ya dace ba ni bari na shiga dakaina na fito da ita dan wallahi wannan karon Mariya bata isa ba, ta saba salwantar mun da qananan abubuwa ko nata tace an sace to wannan karon bazan dauka ba ina gani ta sabautamun miliyan Ashirin a sama ba taci bulus seta biyani ko mota ta ko kudina fita kuma ba izinina da takeyi taje ita da Allah dan na gaji”. Ya tattare riga ya doshi Gate inspecta na tsayar dashi amma yaqi.
Yana zura qafarsa Amiru na faka mota Suka fito da sauri ganin yan sanda, da sauri Naziru ya qaraso yana tambayarsu lafiya se Alhaji Kabiru ya dakata ya yo baya yana cewa
“Yawwa Samari gidan kune ko? To shiga ka fitomun da Mariya qawar Fatu data zo suna gidannan ka gayamata wallahi idan bata fito ba tunda wadannan dana zo dasu basu da amfani mopol zanje na dakko ai tasan halina”.
Amiru ne ya qaraso gurin shima Ummi daman wucewarta tayi bata ko kallesu ba tayi cikin gida. A taqaice Naziru yayiwa Amiru bayanin abinda ya fahimta cikeda takaici Amirun yacewa Alhaji Kabiru da Inpectta su biyo shi dan abin nasu Addah ya kaishi maqura.
Yanzu haka Iman nacan a NICU sun barota wanda dakyar likitan ya karbeta yace tunda uwarta bata san ciwon kanta ba subarta kawai su koma gida idan ta mutu Allah yasa qarshen wahalar da zata sha kenan dan shidai be taba haduwa da Uwa da Ya marasa tunani irin Addah da Amirah ba, dakyar suka roqeshi suka karbeta yanzu dai sun baro an jona mata oxygen da sauran tarkacen wayoyi sedai su bita da Addu’ar samun lafiya dan su da kansu sun cire rai da yarinyar.
Dirar mikiya sukayiwa Palour Amirah, Hajia Mariya da farfadowarta kenan tayi arangama da Alhaji Kabiru ai take qirjinta ya bada daram dam.
“Gasunan ku duba wadda kuke nema ku tafi dare yayi ya kamata a rufe gida” Amiru ya fada yana qara hade rai. Ba bata lokaci Matan yan sanda sukayi ram da Mariya suka tisa qeyarta akayi waje Alhaji Kabiru na zuba tijara se muce Allah ya bada yanda za’ayi a biya Kabiru kudin motarsa 😂😂😂
suma basu tsaya ba suka fita, a qofar Asma’u ya tsaya ya kira Rahma da harta fara bacci ta fito suka tafi lokacin sha biyu harta gota, a gidan suka bar Naziru ya kwana saboda gudun abunda ka iya faruwa kuma, seda ya duba ko ina kafin ya kulle gidan ya kwanta a dakin Aliyu.
Su Hajia Addah dai kamar masu kwanan keso haka suga safiya ido biyu kowa da abinda ya dameta Asubar fari kuwa wadanda suka kwana suka dade akabar Addah da Amirah se Ummi da itama tace gida zata tafi anjima bazata iya wannan masifa ba kafin takwas na safe kuwa se su biyu kawai ga uban barnar da akayi a dakin sun ma rasa ta ina zasu fara.
Dakin Bashir Amirah ta nufa da niyyar tayi wanka saboda bala’in tsamin da jikinta yai mata kafin su san abinyi sedai ta tarar da qofar a rufe se a sannan ta tuna da Anty Aisha ta bawa key jiya kuma ita bata ma sake ganinta ba gashi babu waya bare ta kirata dole haka ta shiga dakinta ta binciko inda ta boye key din toilet data rufe dan kar a bata cikin Sa’a sega na Dakin Bashir a gurin da alama anan ta boye mata.
Da murnarta ta dauki key din ta fita, Addah na zaune akan kujera ta rafka uban tagumi abin duniya ya taru ya mata yawa dare daya harta zabge tsabar Tashin Hankali yanzun ma tayi zurfi a tunanin yanda zasuyi su gyara gurin kafin azo tunanin neman kudin da za’a biya bashin da suka karbo bata maji fitowar Amirah ba se ihun salatinta data jiyo a dakin Bashir ba shiri ta miqe ta bita.
“Na shiga uku Addah shikenan sun kashe ni wallahi Yaya Inaga yanka ni ne kuma kawai bazeyi ba” Amirah ta fada hannu aka tuni idonta ya fara tsiyayar da hawaye lokacin data ci karo da murfin Wardrobe din Bashir da aka fashe ga kan Mirrow dinsa wayam babu ko kwalli suma an kwashe wai iya abunda idonta ya gani kenan Allah kadai yasan dame dame aka dauka kuma.
Ita kanta Addah seda hankali ta ya qara tashi dan duk a zatonsu tunda qofar na kulle bala’in be taba can ba basusan ta nan Al’amuran suka fara sauka bama 😂
“Dallah can ki mana shiru aikin gama dai ya riga ya gama duk ma abinda za’ayi daga baya ne me afkuwa ta afku ni dai yanzu ciro sarqar nan ki gani mu Adana su kafin suma bala’in ya dirar musu nidai wannan Ya dakika haifa kamar yar Allah bani ta jefa mu a masifa (babu ruwan Iman ku dai kuka jefa kanku uku ah to 😚😚).
Wata sabuwa inji yan caca ai seda Amirah ta shafa wuyanta taji wayam sannan ta ankare babu wannan sarqa dama babu batun awarwaro tun tuni su ta ankare da sun zube amma a sannan bata su takeyi ba, yanda take rarraba ido ne yasa Addah a fusace cewa “bazaki ciro bane kike tsareni da ido ko kuma daman ta kice” ta wara idonta akan Amiran.
“Shikenan ashe ba Mariya kadai ce take da rabon zuwa Birsin ba harda ni wayyo Allah na na shiga uku na lalace wannan wane irin bala’i ne suke bibiyata sahu sahu ni fatu?” Kuka riris Addah takeyi, sarqar da hayota tayi dakyar Hajiya Inna Qawarta tayi mata hanyarta a gurin wata qawarta.
Seda ta bada dubu dari kudin Haya sannan ta bata takaddun gidanta dashi kadaine kadarar datayi mata saura a yanzu akan idan wani abu ya samu sarqarta sedai a siyar ta cire kudinta ta bata chanji to a qalla da sarqar da abin hannu sun kai na kusan miliyan biyu gashi babu ko daya se warin dan kunne daya ne a kunnen Amiran to ita kuwa yau ta shiga ina taga haske wannan Asara kan asara babu biyan buqata?
Rasa me bawa wani haquri akayi cikinsu ita Amirah tana kukan haduwarsu da Bashir ita Addah tana na sarqa seda suka gaji dan kansu sannan sukayi shiru kowa tayi wanka suka shiga gyaran guri kafin kuma su san abinyi a gaba. Tsakar gida suka watso sharar Addah ta fita ta samo yara suka shiga sharar tsakar gida aka tattare kujeru masu lafiya aka ware karyayyu gefe suma kafin masu su suzo ayi lissafi haka suka tattaro kwanuka da kulolin abinci suka bayar yaran suka wanke komai bayan yaran sun gama ta biyasu suka koma ciki sukayi zugun zugun.
Babu wanda yayi tunanin zuwa duba halin da Iman take ciki a cikinsu tunda dai Ummi ta gaya musu tana Asibiti shikenan daman ko wancan kwanciyar da tayi bayan an sallamota ba kullum take zuwa ba, da aka fara bata abincine taje zuwa tayi pumping Nonon da za’a bata daga baya ma a gida takeyi ta zuba a Container da suke bata akai shikenan. Seda sukaji Yunwa na neman hallaka su suka nemi abinci suka ci suka ci gaba da zaman jiran tsammani kuma.
A bangaren Bashir kuwa Tun a daren Dr Ishaq ya kira yana zuba masa ruwan masifa kamar shine Amiran, bayan sun gama ya kira Naziru ya gaya masa yanda akayi harda qarin maggi da gishiri abinda ya qara tunzura zuciyar Bashir din kenan ya shiga kiran wayar Amirah amma Allah ya taimaketa wandaya sace ya kashe dan kuwa daya sameta a waya Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a daren, Ganin be sameta seya maida akalar kiran kan Asma’u.
Tana nade akan gadonta bayan ta gama shirin bacci har sannan Bata bar mamakin abubuwan da suka faru