Showing 45001 words to 48000 words out of 260321 words

Chapter 16 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42661

Table ta na cewa Me aikinta “maza Usaina ki gyara masa jikinsa ga kaya nan ki saka masa nima yanzu zan zo na yi wanka na shirya” ta juya ta fice ita kuwa Usaina ta qaraso ciki tana gaishe su da niyyar ajiye yaron Asma’u tayi saurin dakatar da ita.

“Dauki kayan maza ki bita” ta fada tana nuna mata hanya, ba musu kuwa Usaina ta kinkimi leda da yaron tayi waje harda ja musu qofa se sannan Rahma ta sama ma kanta gurin zama.

“Keda mutanen naki kuma yau Maman Aliyu” Rahma ta fada tana dariya.
“Da kenan Maman Nasir ai sun shani na warke kuma yanzu, kunga ku tashi kuje sama ina zuwa”. Zahra da Rahma suka miqe zuwa sama qaramin palour Ma’u da take sauke manyan baqinta.

Kallon Jafar da Abdallah dake kallo tareda Jawad Dan Zahra tayi tace “ina su Ahmad?”

Jafar ne ya amsa mata yace “Yaya ya fita, yah Amna da Farida ma sun tafi gidan su Amina Shehu sunce sun gaya miki tareda su Ahmad din”

“Eh na tuna, kana jina duk bugub da za’ayi ko waye karka kuskura ka bude kofar nan”.

“Tam Mami” ya amsa mata yana daukar Handle din Game din da suka kunna.

Kitchen ta shiga ta hado ruwa da lemo da tarkacen kayan motsa baki a Babban Try Jawad ne ya karba dan yafi Jafar din girma ya kai saman ita kuma ta dibar musu Abinci da sauran kayan da zasu buqata duk ta basu suka kai, da kanta ta murzawa kofar key ta kuma sake jan kunnensu akan karsu bude mata qofa kafin ta haye saman suka hade da su Zahra aka shiga hirar duniya da abinda ze amfane su ba tareda sun koda taso da zancen Abinda ke faruwa a cikin gidan ba.

A dakin me jego fa tuni abubuwa sun dauki Harami, tana zaune ta ci Ado da wata danyar shadda data sha aiki su Sadiya suka shiga palour suna kumfar Baki da zage zagen abinda Ma’u tayi musu, anan palour aka maida magana basu dasa Aya ba Me aikin Kamila Ma ta dawo tana miqawa Kamilar ledar kayansu.

“Kan bala’i lallai matar nan au kema koroki tayi?” Kamilan ta fada.
“Ta koromu ma bare wata me aikin ki ai wallahi bari a tashi taron nan bata ci banza ba se mun nuna mata nan gidan dan uwan mune muna da ikon yin yanda muka ga dama a ciki, ke Amirah bamu muqullin dakin Yaya naji kofar a kulle take”. Cewar Sadiya.

“Nan fa daya yaya sadiya key din dakin mijin nawa zan baku kema kin san baze yuwu ba” Amirah ta fada tana yatsina fuska, tab waima ta basu key wallahi bazata bayar ba kuwa.

“Oh kema diban Albarkar zaki mana dakin dan uwan mu fa mukace ki bude mana mu shiga mu shirya tunda kinga dai nan ko ina da mutane” Kamila ta karba se kuwa Amirah ta miqe tana sabar yarta da take ta nan nan da ita ga kuma key din a hannunta dan kayan da zata saka dana rabo duk suna ciki bata kuma yarda ta bawa kowa ba banda Ummi se Anty Aisha su kadai ta yarda suka shiga dakin.

“Bafa zan bayar ba Yaya Kamila idan kun matsu da wankan ku shiga na dakin baqi dan na kulle toilet din dakina ma kar a batamin ko ga wani nan ai a kofar daki kuyi amfani dashi” ta shige dakin ta ta barsu sototo baki a bude tsabar mamaki.


Mura ce take damuna wallahi kuyi manaji da wannan 🙏🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 18

Taro yayi taro dan kafin la’asar gida ya cika ya batse da mata kala kala se an bulowa suke. Tuni mata sun zazzauna kan kujerun da aka shirya an wangale get duk inda ka duba qawayen Amirah ne yan gayu sunci kwalliya da kuma manyan Mata Qawayan Addah data gayyoto daga gefe DJ nata sakin duma wasu na tattakawa wasu kuma suna cin abinci dan tuni an fara rabo.

Shinkafa gata nan kala kala, soyayyoyar taliya, dambu, Alala ga dabgen kaji da na naman Sa ga Fura me kyau da aka zuzzuba a kofuna Zobo dasu kunan Aya da lemon robobi dai kaya masha Allah an tanadi komai harda gurasa suka siyo daga kano akayi bandashe me kyau se rububinta kuwa akeyi.

Wuraren Uku na tana su Ma’u na tsaka da Hira Jafar ya kwankwasa kofar palour da suke ciki, seda aka bashi izini sannan ya shiga ya tsaya daga bakin kofa yana cewa
“Mami ana ta Knocking na tambayi waye wai Anty Aisha ce ta gidan su Anty Amirah shine nace bari nazo na gaya miki kafin na bude”.

“Tam jeka ina zuwa” ta fada ya juya yai tafiyarsa. Kamar bazataje ba sedai kuma ta miqe dan Ko ba komai tana ganin girman Anty Aisha amma fa batajin yau akwai wanda zata bari ya shigo mata daki a cikinsu. Sun saba in ana hidima azo a yi mata kaca kaca da guri a tafi a barta da gyara to an dena bakuma za’a sake ba.

Har kuwa ta sauka qasan Anty Aisha na tsaye a bakin qofar. Dan kadan Ma’u ta bude qofa taja ta tsaya Anty Aisha data taho da niyyar shigowa ganin ta tare qofar se jikinta yayi sanyi. Gaisawa sukayi ta tambayi Anty Aishan ya taro tace lafiya lau se sukayi shiru gaba daya kafin Aishan tayi qarfin halin cewa

“Daman nace ne bari nazo ki bada abunda za’a zubo muku abincine”

“Lah ai kubarshi ma wlh nayi abinci da yake ina da baqi”. Asma’u ta tareta kafin ta fara qoqarin juyawa tunda maganar kenan se Antyn ta katseta tana cewa

“Am nace dan Allah in ba damuwa ko zamu dan kawo wasu baqin mu su dan zauna anan can din ya cika wallahi”

“Ai haka taro yake daman se haquri ba lallai mutum ya samu yanda yake so ba, se suyi haquri su zauna tunda abun nadan lokaci ne” garam ta rufo qofarta tabar Anty Aisha da baki a bude.

Data koma saman ma tambayarta sukayi ya akayi
“Wai baqi zasu kawomun nan”
“Kika ce me?” Suka hada baki gurin tambayarta, se tayi yar dariya kafin tace.

“Me zance kuwa in banda karsu zo, nifa na yanke alaqa se wadda ta zama dole ba se an san cikin ka ba sannan za’a maka yankan bayan? To muje baya baya kowa yayi ya tasa dan ba qara”. Cewar Asma’un

“Allah ya rufa asiri dai amma dangin mijin nan naku basuda kunya wlh” cewar Zahra.

“Waa ai ni baza’a fara wannan wasan dani bama wallahi ni naga qoqarin Maman Aliyu da batai musu hauka dan order ba wallahi ai sam mutanen nan basu san mutunchi ba” Rahma ta fada, ita dai Ma’u shiru tayi bata ce musu komai ba. Bazasu gane ba duk yanda za’a musu bayani idan ba kansu ta fada ba. Hirar su suka ci gaba dayi har aka kira la’asar suka tashi dan yin sallah.

Yan suna kuwa Qarfe hudu daidai Aka sanar da fitowar Me Jego Hajia Amirah da ta cancada kwalliya da wani dan ubansun Leshi Dark blue da adon light Blue din zare dayayi bala’in karbar farar fatarta. Tayi kyau harta gaji komai Hassadar mutum dole ya yaba anyi mata lafiyayyar Fitted gown dinki ya fita ko ina das.

Ga Goggoron da aka daura mata ya zauna das ya qara qawata kyakykywar fuskarta hannu da qafa ya dau Ja da Baqin qunshi ga Danqareriyar sarqar gwal a wuyanta da zobuna harda awarwaro Allah kadai yasan ina suka samo su. Rungume take da yarta da akayiwa Kwalliya cikin daya daga cikin rigunan Ma’u fara harda shawl din dan shima farine ta nadeta a ciki Qawayen ta na take mata baya suka shigo filin tuni DJ ya ware wusu WARRR.

Seda suka rakata har mazauninta aka dauki hotuna sannan kowa ya nemi gurin zama. Bayan kowa ya nutsa DJ Fele da takanas suka dakkoshi tun daga Kano ya nemi da wata ta fito ta bude taro da bayanin maraba, Hajiya Hassana daya daga qawayen Addah ce ta fita ta fara jawabi kamar haka.

“Dafarko munawa kowa da kowa barka da zuwa wannan shagalin suna na Yar Gata yarinya haihuwar dangi, muna fatan yanda aka fara taro lafiya a tashi lafiya kowa kuma ya koma gidansa lafiya. Muna qarawa yiwa kowa barka da zuwa” aka dauki tafi raf raf.

Can na hango Addah bakin nan kamar ze tsage saboda fara’a taci wanka ta saka wata Hadaddiyar Atamfa ta manyan mata ga dauri an cakare se maraba takeyiwa baqin ta ranta fes ganin yanda suka amsa gayyatarta suka zo mata taron da yawa dukda a qurarren lokaci tayi gayyatar.

Suna ya kankama tuni a ka shiga shagali ka’in da na’in, duk yanda Amirah taso kwakwume yar haka seda ta bayar da ita Dangi da qawaye suka ringa daukanta ana ta hotuna. Ba daukan yarinyar yafi damunta ba, sanyi ya riga ya kankama musamman lokacin da yake La’asar sakaliya ga bishiyun tsakar gidan suna ta rangaji suna qara yawan isaka sannan Get ma a wangale yake saboda yawan Jama’a.

A fili fara’a takeyi amma zuciyarta addua take ta ja Allah ya rufa mata asiri a tashi taron nan qalau batare da wani abu ya faru ba dan se a yanzu take jin kamar tayi wauta a lamarin. Haka ta daure zuciyarta ta zage suna ta kwasar rawa ana videon tiktok da qawayenta da kuma daukar hotuna wasuma live suke video amma fa rabin hankalin ta na kan duk inda akayi da yarinyar.

Biki fa yayi baki mata an zage DJ Fele na kada musu ganga suna cin uwar sabada, daga can cikin gida bayan da Amirah ta gama shiryawa zata fito, harta zuwa key din dakin Bashir a jakarta ta tuna da kayan rabon da zasu sallami baqinsu yana ciki. Gudun kar azo a manta har a watse ba’a fito da kayan ba yasa ta danqawa Anty Aisha akan da taga an fara haramar tafiya ta fito da kaya a fara rabo.

Haka kuwa akayi ganin magriba ta doso yasa ta bude daki ta fara fito da kayayyaki tana bawa wadanda suke zaune a palour basu fita gurin kida ba. Kunsan mutanen mu da souvenir nan da nan fa akayo mata caaa yan uwansu ganin kamar zabe take tana raba kayan aiko suka duru dakin Bashir duk yanda Su Ummi suka so su hana be yuwuba tun kuwa kafin aje da nisa a garin kwatar leda wata ta kaiwa Murfin wardrobe naushi, abunka da me qashi daya nan take gilashi ya tarwatse 😂😂😂 mata aka debi salati.

Basu dawo daga wannan tashin hankali ba aka samu yaran biyu daga ciki da suna shiga su kan mirror sukayi ganin kayan wasa suka kuwa shiga watso tsadaddun turarukan Bashir suna fashewa Tush a qasa, babu me jiran a ce masa ya fita sum sum suka fara ficewa daga dakin dan sun san sun tsokalo tsuliyar dodo yau amma dukda haka seda aka samu was masu son zuciyar da suka saci turare suka fita dasu.

Tsilli tsilli Ummi da Anty Aisha sukayi ko wacce ta kasa magana,
“Yanzu Anty yaya zamuyi?” Ummi ta fada tana rarraba ido dan tasan Allah ne kadai ze kwaceta a hannun Yaya Bashir idan yaji harda ita a dakin.

“Ummi nima tunanin da nakeyi kenan, amma kinga samo tsintiya mu tattare tunda me afkuwa ta afku maji da abinda ze biyo baya”. Tayi Na’am da maganar dan haka ta fita ta dakko tsintiya da abin shara suka shiga kwashe kwalabe da gilasan bayan sun gama suka hado kan kayan rabo tas suka dire a palour, dakin Amirah Anty Aisha ta shiga ta nemi guri me kyau da ba wanda ya gani ta ajiye mata muqullin da niyyar idan ta tambayeta ta gaya mata inda yake bata tsaya ba ta hada kan yayanta sukayi gida dan bata san yanda za’a qare ba.

A can filin kida kuwa bayan yaran mata sun gama nasu, nan kuma Manyan mata qawayen Addah suka shiga suma su zubda nasu galangalan din. magriba tayi amma haka suka ci gaba da buga ganga mata na rawa. Addah da jikinta har tsuma yake ta shiga zuge jaka da niyyar fito da sababbin kudin data yiwo chanji daman saboda liqi sedai kudi sukace dauke mu inda kika ajiye.

Hankali tashe take sake laluba jakar, da kudin liqi da da wayarta data Amirah data karba ta saka mata a jakar ga uban gudummawar da ta samu ta tabbatar da qila har chanji zasu samu bayan sun biya basussukan da suka ciyo se gashi gaba daya babu su babu alamarsu.

Wata Ashar me maiqo ta janyo ta dire tana zazzare ido kamar ance zata ga kudin ne a qasa, wannan shi ake kira da tashin hankali ba’a saka masa rana. Amirah ta hango da wasu mutum biyu sun nufi cikin gida da sauri ta shiga kwala mata kira amma ina qarar kida bazata bari ta jiyota ba har suka shige se kawai ta nufi get afujajan ta shiga jansa ruf ta rufe gida.

Kwadon yana jiki daman hatta da key din da suka bude basu cire ba tsabar rashin hankali ko kidane yai dadi oho Allah dai ya rufa asiri ba’a samu wani ya zare ba da wannan tayi amfani ta garqame gida tsaf ta jefa muqulli a riga ta nufi gurin gangar DJ gadan gadan tana zuwa kuwa batayi wata wata ba ta fizge wayar inji kida ya dauki dif.

A fusace yaron DJ ya juya da niyyar ganin waye yai musu danyan aikin se ganin uwar biki yayi ta riqe qugu tana kumbura tana sace wa.
“Zoka mayar amma ka kashe kidan ka bani abin magana” Addah ta fada, shikuwa beyi musu ba ya maida waya ya miqa mata lasifiqa ya tsaya yaga ikon Allah dan dai daga yanayinta yasan ba lafiya ba.

Juyawa tayi ta kalli mata da suka qame suna kallonta da jiran jin wani wulaqanci ne yasa aka katse musu cashewa suna cikin Warwarewa.
Addah na haki kamar wadda tayi gudu ta fara magana tana cewa “nidai bazan ja doguwar magana, idan kin san ke kika kwashe mun kudi a jaka kusan dubu dari biyu kika hada da wayata ta dubu saba’in data me jego Me kyamara uku ni ban san kudinta na to ki fito dasu yanzu ko kizo ga jakar can na ajiye kin sanya salin alin ki maidamun komai ciki idan ba haka na rantse da abinda ze kashe ni daga nan se police station dan se an fito mun da kudina ni ba taron farin ciki na tara ba dan azo a sabautani ni ba”.

Hayaniya ce ta tashi a gurin mata suka shiga duka jakun kunan su ai se kuji an yanko salati kafin wata ta dire wata ta dauka kan kace me guri ya rikece da surutan mata da yawa an yashe musu jaka tas suna can basu ankara ba.

Hajia Mariya daya daga cikin qawayen Addah ta zazzage jakarta tas a qasa komai na ciki ya zubo ga tsabar kudi nan da wayarta harda qaton zoban gwal data saka taji ya dame ta duk suna ciki amma babu muqullin motar da tazo da ita. Hannaye biyu ta dora a hannu ta fashe da kuka tana kururuwar ta shiga uku.

“Ni Mariya na shiga uku yau in koma in cewa Alhaji me? Be san na fito ba da safiyar nan Fatu kika azazzaloni se nazo sunan nan na dauko sabuwar motarsa sau daya ya hauta kafin ya tafi Lagos gashi yanzu an dauke shikenan na kade har ganye na” Hajia Mariya ta sake rushewa da kuka. Ai se akayi tsilli tsilli, masu kukan wayoyinsu da yan kudade sunji wadda akayiwa dungurungun yo satar mota a zamanin nan motar ma ta miji besan ta dakko ba ai abin ayi mata jaje ne.

Nan fa guri ya rikice, ita dai Addah duk wannanba matsalar ta bace jira take ace ga kayanta tunda ta rigada ta kulle Get kuma ta qudiri niyya bazata bude ba se an fito mata da kayanta. Ta kallon wasu suka nufi Get da niyyar su fita suka jishi a qarqame nan aka sakeyo wa cikin gida ana ci gaba da cece kuce Addah kuwa tayi qememe duk yanda Aminan nata suke mata maganar ta bude gidan su fita amma taqi.

Tana tsaye a nan Inna Gaji ta kwaso da gudu daga palour Amirah ta dire a gaban Addah tana haki.
“Yawwa Gaji gara da kika zo ki tayani ganin wannan bala’i wai duk kudin cikin jakar nan da wayata data Amirah an samu wata la’ananniyar ta yashe ni ko na kulle gida babu wanda ya isa ya fita wallahi se sun fito mun da kayana”.

“Yanzu kibar batun wasu kudi Fatu ga bala’in da ya fi wannan can a cikin gida yana jiranki muje” ta shiga jan hannun Addah seta bita kamat raqumi da akala suka shiga dakin.

Qulululu cikinta ya bada sauti tareda murdawa kamar zawo ze kece mata taji lokacin da tayi Arba da yar jaririyar da ke kwance idanunta na qaqqafewa kamar me suma ga qirjinta na sama da qasa da sauri har wani wahalallen tari take saki a shaqe ba’a maji sosai Amirah na gefenta tuni Goggoro yayi ta kansa kwalliya ta jagale tana rusar kuka hannu aka.

Habiba Kishiyar Addah ce tayi qarfin halin cewa a dauki yarinyar a kai Asibiti mana se a sannan ma tunanin su ya kawo nan da nan Ummi ta shiga kiran wayar Naziru tunda shine wakilin Bashir din amma se aka ce mata call waiting, bata haqura ba taci gaba da kiran wayar amma be daga ba.

LAGOS Nigeria
Wato ranar bayan Bashir ya tashi daga aiki se yabi wani abokinsa gidan sa saboda koya dawo gidan baya masa dadi. Suna zaune suna cin abincin da sukayiwo take away a hanya dan shi abokin bashi da Aure suna yan hirarrakinsu. Bayan sun gama Bashir ya dauki remote yana chanza tasha kafin lokacin sallar Magriba yayi su fita shikuma abokin wayarsa ya dauka ya shiga Tiktok dan shi ma’abocin duba Tiktok ne.

Bashir na daga gefe lokaci lokaci ya daga kai ya kalleshi jin yanda yake dariya shikadai, sedai ya girgiza kai kawai yana mamaki besan me mutane suke ji ko gani a wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login