Showing 243001 words to 246000 words out of 260321 words
Chapter 82 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
ya fada yana tashi zaune bayan daya dafe qirjinsa da yake suya, Aliyu da har ya fara gyangyadi yayi fitgigit yace
“Abbi bakayi bacci ba? Na zata a magungunan akwai me saka bacci ai ya kamata ka huta saboda yanayin jikinka”.
Murmushi me ciwo Bashir yayi yana kallonsa yace
“Daga randa na rabu da Ma’u bansake samun nutsatstseb bacci ba Aliyu a lokacin da nake da yaqinin zata dawo cikin rayuwata ma kenan taya kake tunanin yanzu dana tabbatar da na rasata zan sake runtsawa ai nida kwanciyar hankali munyi bankwana Aliyu, na rasa Ma’u na rasa farin cikina. Ta tafi da dukkan wata walwala da jin dadi na”.
“Abbi haquri zakayi mu dauka haka Allah ya qaddaro a tsakanin ku dan na tabbatar da Mami tana sonka amma babu wanda ze iya ja da ikon Allah. Gara kai kana da wata matar da kake so daman mu kuwa fa ita kadai ce Mamin mu yanzu shikenan bamu da maraba da Marayu haka zamuyi rayuwa ba tareda Mahaifiyarmu tana tare da mu” Aliyun ya fada qasan ransa yanajin wani irin zafi da tsanar Amirah.
Ya rigada ya saka ma ransa ita ce silar faruwar komai a gidan su. Ita ta wargaza musu farin ciki ta raba iyayensu kuma yayi alqawarin badai itama taji dadi a cikin gidan su ba. Yanda zasu qare rayuwa cikin quncin rashin uwa tabbas itama haka zatayita cikin uqubar da zasu ringa gana mata a ruwan sanyi setayi dana sanin shiga hurumin da banata ba.
“Laifi nane Aliyu ni na biyewa rudin shedan da zafin zuciya na aikata duk abinda ya faru, a zamana da Ma’u bata taba cutar dani tana sane ba. Tayi haquri dani da duk wasu halayya ta amma a qarshe ni na kasa yi mata uzuri akan bijirewa son raina gashi yanzu ni zan qare rayuwata a cikin dana sanin rabuwa da ita, kaico na dana zama me son kai a rayuwa, kaico na dana zama me rama Alkahiri da sharri.
Ina fatan abinda ya sameni ya zama izina a kanka da sauran qannenka, kada ku kuskura ku dauki soyayyar Mace a matsayin rauni ko gazawa kar kuma hakan ya zama abinda zaku riqe wurin juya rayuwarta yanda kuka ga dama. Tabbas duk wanda be godewa ni’imar ubangiji ba toh ze godewa Azabar sa” ya fada kamar ze fashe da kuka. Se Aliyun ya kama hannunsa yana cewa
“Abbi haka Allah yaso kuma in sha Allahu ze zama Alkahiri. Kayi bacci bari naje na duba su Jafar naga ko sun shigo se na kulle qofa na dawo” ya saki hannun Uban ya miqe
“Kaima ka kwanta ka huta Aliyu gobe kuna da makaranta fa”
“Na sani a nan zan kwana saboda ko zaka buqaci wani abun cikin dare” Aliyun ya bashi amsa kafin ya qarasa fita daga dakin.
Lumahw idonsa yayi yanajin wani qarin yayyafin qaunar Yaron yana shiga zuciyarsa. Ko iya wannan abin da Ma’u tayi masa na kula da tarbiyyar yayansa ta cusawa musu halaye da dabi’u na kwarai ta cancanci duk wata girmamawar duniya daga gare shi, ko kaffara baze ba idan shine a matsayin Aliyu wadannan abubuwan suka ringa faruwa akan idonsa baya tunanin wani abu bayan gaisuwa ze sake shiga tsakaninaa da Mahaifinsa shima saboda sauke haqqine kawai.
Daren ranar be iya runtsawa ba, Nadama yake yi mara amfani dan se a yanzu yake gano tarin qatuwar wautar daya ringa tafkawa a rayuwarsa. Ya yarda da gaske ya kasance mutum meson kansa, a koda yaushe buqatarsa ce a gaba be taba duba wani ba idan har ze samu abinda yake so babu ruwansa ko wani yaji dadi ko karya ji muddin buqatarsa ta biya shikenan.
Se a yanzuyake tuno tarin sadaukarwa da tarin soyayyar da Ma’u ta shimfida masa, Mace ce da ta yarda tayi Kuka idan harshi zeyi dariya, ta yarda ta rasa shi ya samu bashi kadai ba duk wani wanda ya shafe shi a duniya Ma’u tana rawar jiki gurin kyautata musu.
Ze iya rantsewa cewar hidimar da take da iyayensa da yan uwansa shi da suka haifa baya yi musu kwatanta. Saboda duk abinda zeyi kafin a buqata ita tayi musu da kudin ta da jikinta hidimta musu takeyi.
A lokacin baya idan Ahajin su yana ce masa ya riqe Ma’u da kyau matar rufin asiri ce da samun irinta a zamanin nan yana da wahala gani yake kawai dai saboda makauniyar soyayyar da Baban yake mata ce tasa baya ganin laifinta shi kuwa gani yake kawai tana amfani da abin duniya da take dashi ne ta siye kowa ta yanda babu me ganin laifinta kowa sonta yake yi.
Idan ya zauna ya nutsu tsaf a zaman su ze iya rubuta sau nawa ta taba kawo masa wata buqata tata na wani abin buqata a matsayinsa na mijinta komai yi take tayi masa tayiwa Yayanta ba kuma ta taba qorafi ko nuna gazawa ba duk a lokutab baya gani yake rainin arziqi ne ya saka take masa haka tana ganin ta fishi wadata dan haka bata taba bashi ma damar da ze tabuka wani abu ba a matsayinsa na Namiji, kodaga baya daya samu Chanjin rayuwa bata sauya zani ba.
Taci gaba dayi se iya abinda ya ga kamatuwar ya dakko ya bata ne ze bata ba kuma ta taba qorafi akai kota raina ba ganin cewar yanzu yana da halin yi a maimakon ya gode mata ya jinjina mata se ya sake qullatarta da ganin tabbas ta rigada ta raina shi, duk tarin Arziqin daze samu tana ci gaba da kallonsa a wannan faqirin data aura ta ringa hidima dashi.
Ya kasa ganin haka a matsayin soyayar da take masa ce tasa take tausayinsa ba kuma ta qyashin hidimta masa ta kowacce siga. Bayan duk wannan sadaukarwar daya tashi ya saka mata da Kishiya irin wacce shi da kansa daga baya seda ya ringa jin kunyar abinda ya aikata mata wanda duk yana cikin irin ingiza me kantun da Bala ya ringa masa a rayuwa.
Shiya fara tunkara da batun abinda ya faraji dangane da Amirah ya kuma nemi shawarar sa akan abinda zeyi dan ya hango tarin rashin da cewa a cikin abinda zuciyarsa take niyyar yi amma Bala ya nuna masa cewar ai ba haramun bane. Kuma daya aurowa Ma’u wadda bata san halinta ba ai gara Amirah da take rainonta tasan bazata cutar da ita ba.
Be zurfafa tunani ba dukda wani bangare na zuciyarsa babu yanda beyi ba na hanashi amma ya dage, sanda ya sanarwa da Dada maganar yana ta taraddadin ya zata karbi Al’amarin ganin irin so da qaunar da take tsakanin ta da Ma’un, a lokacin kullum bata da magana seta ya riqe yarinyar nan da kyau yarinyar kirki kullum yaje gidan nan da sabon abun da zata nuna masa tace Ma’u ta kawo Albarka kuwa baya zaton ko su data haifa tana saka musu ita lodi lodi irin yanda take mata amma daya kai mata zancen Amirah se gashi tashi daya ta amince.
Hartana gaya masa sun dade suna son qulla wannan zumunchin dan da Amiru taso su hada su amma halinsu da banbanci zaman bazeyi dadi ba. Shi kuwa daman shine uban riqonta duk wani hali nata tun yarinta daga shi har Ma’un sun sani dan haka babu komai Allah ya tabbatar musu da Alkahiri.
Yasan ya tafka kuskure na boyewa Ma’u zancen auransa da Amirah da yayi amma ta ina ze fara? Bashi da wannan kwaringuiwar da ze tunkareta yace mata zeyi aure kuma Amirah ze aura.
Ya rubuta Text message yafi sau dari amma ya kasa tura mata, daga baya a takadda ya ringa rubutawa yana ajiye mata amma baya qara ko taku biyu daga gurin yake canza shawara ya dauke dan besan a yanda zata karbi Al’amarin ba.
Sanda au Dada suka kawo Amirah gidan shi kansa yaga rashin dacewar hakan se kuma daya nuna musu kuskuren aikata hakan amma suka qeqashe qasa suka ce ya fita a sabgar babu ruwansa dalilin daya saka shi yanke shawarar biya mata umarah kenan ita da yara suka tafi danharga Allah seda abin yazo dab sannan ya qara ganin kuskurensa.
Babu kuma yanda beyi ba akan afasa amma Su Addah suka ce ata fau babu wannan zance, karshe ma daya matsa seda Dada tayi masa barazanar tsine masa idan ya kuskura ma zancen yaje kunnen mahaifinsa na cewar ya fasa haka ta kuma yiwa su Naziru barazanar da karsu gayawa Ma’u dan daman a wani kalar munafunci suka qulla zancen auran ta yanda hatta da mutanen gari an bagarar dasu kowa se a bazata abin yazo masa bayan da aka daura se gashi tun ba’aje da nisa ba yake karbar sakamakon sa da hannun haqu.
Kyale kyalen daya rude shi ya aurota ashe duk buge ne, matar da yake zaune da ita shekaru Goma sha ta fita ta kowacce siga, shi baze iya cewa ma yau ga wata tsiya daya tsinta acikin auransa da Amirah ba banda tashin hankula da damuwa da take jefashi aciki kala kala qarshe tayi masa me dungurungun, sukayi amfani da halinsa na daukar zuga da zuciyarsa me cike da izza suka raba shi da matarsa da ta so shi tsakani da Allah tun bashi da abinda ze saka a so shin.
Gashi yanzu yanaji yana gani tayi masa nisan da har Abada se dai Idan wata da wata gagarumar qaddarar a gaba ko rabo me tsananida ze sake dawo masa da Ma’u cikin rayuwarsa amma ya tabbata ko haukacewa Yusuf yayi baze sako masa Ma’u ba.
Kai shi shaidane tun a wancan zamanin cikin samarin da sukayi takarar neman auran Ma’u dasu babu wanda yake tsananinsonta saboda Allah kamar Yusuf, a gabansa ta kore shi wanda yake da yaqinin shine haduwar su ta qarshe a wancan lokaci ya kuma tafi bayan yace mata
“Idan har rabuwata dake zesa kiyi Farin ciki Asmy wallahi bazaki sake ganin fuskata ba. Da ina da dama ko me irin sunana dana hana kunnuwanki jinsa saboda kar hakan ya ringa tuno miki dani a rayuwarki ranki ya baci, amma ki sani ina qaunarki saboda Allah kuma bazan cire tsammanin samun ki a rayuwata ba se randa na farka na ganni a cikin kabari tukunna zan haqura dake”
Shiyasa tun daga lokacin kai ko me suna Yusuf yaji an ambata seya tuno shi yana matuqar baqin ciki da kishi da irin qaunar Ma’u dayake gani a cikin idanun sa wanda a haduwar su ta farko bayan shekaru goma sha bakwai ya sake ganin wannan tarin So da Qaunar tata a idon Yusuf, a yau daya sake haduwa dashi kuwa ya tabbatar da ze iya aikata duk abinda ya fada akanta dan ba qarya yake ba yana Son Asma’u, irin son da tayi masa yanzu gashi Allah ya bata wanda yake mata kwatankwacinsa itama.
Seda ya share hawayenda suka ziraro masa kafinya saka hannu ya janyo wayarsa tare da hotonsa da Ma’u da yake kan durowar gefen gadonsa. Hoton ya fara zarewa daga jinin Katakon da yake ya zura mata ido yanda tayi kyau tana wannan murmushin nata da yake nuna irin kyan zuciyar da take dashi se yayi saurin yin a’uziyya tunowa da yanzu fa matar wani ce ba tasa ba.
Durowar ya jawo ya saka hoton tareda katakon, zuwa gobe da safe duk ze fito dasu ya bawa Aliyu dan idan ya barsu tare dashi tabbas baze samu kwarin guiwar chanjinda yake so ya kawo a rayuwarsa ba. Ze cigaba da dakon sabon zunubi ne na kallo da kuma tunanin matar da bata sa ba a yanzu.
Hotonta da yake kan wayarsa ya sauke ya mayar dana yaran da suka dauka wannan qaramar sallar data wuce gaba dayansu wani tausayin su yana ratsa shi musamman Yan biyun sa yanzu duk shine silar komai, ya janyo musu zasuyi rayuwa ba tare da uwar su ba Alhalin tanada ranta ba mutuwa tayi ba.
Doleya jajirce ya inganta rayuwarsu baze bari suyi kukan rashin uwaba dan a yanzu shi kadai ne gatan da zeyi musu, ya koyi darasi daga abinda ya same shi na rayuwar auran sa da Ma’u in sha Allahu kuma ze dauki dangana ze kuma jajirce ya gyara rayuwarsa.
Duk abinda ya zama silar jefa shi a halin da yake ciki yanzu ze kiyaye shi hakan ya zamar masa izina ba kuma ze sake bari ya maimaita kansa ba amma anya ze samu chanjin rayuwa da Mace irin Amirah??
“Kaima kana da taka gudummawar daka bayar gurin lalacewarta ta zama duk abinda ta zama a yanzun” zuciyarsa ta raya masa kuma ya yarda da hakan sannan ya dauki turbar gyara ze yi iya qoqarinsa na ganin ta dawo hanya su lallaba rayuwar su a haka tunda basu da yanda zasuyi da Junansu.
Washe gari kafin Aliyu su tafi makaranta seda ya tabbatar daya ajiyewa Bashir kayan karyawa da magungunan sa akusa dan se da yayi sallar Asuba sannan bacci ya dauke shi dalilin sabon zazzabin daya rufe shi.
Se gurin sha biyun rana ya fito daga dakinsa bayan yayi wanka ya shirya kuma Ahamdulillah ya samu sauqin takurar da zuciyarsa take masa dan yanzu kam ya tabbatar daya rasa Ma’u, duk da baya son ko tuna abun saboda wani daci dayake taso masa kansa yayi zafi har duhu yake gani yana gilma masa duk sanda ya tuna a gabansa jiya wani ya rungumeta kuma yayi kissing nata.
Cikin sanyin Jiki ya fita falo ya zauna, gidan shiru babu Addah babu Amirah yanda kasan ma basu san a halin daya shigo jiya gidan ba cikin su babu wadda ta sake leqowa bare taga yana da rai ne koya mutu.
Yana zaune akan kujera bayan ya kunna Tv ya kai tashar Sunna Tv akaci sa’a Malaminda yake wa’azi a lokacin yana magana ne akan Aureda haqqoqin da suka rataya a kan Miji da Mata.
Nutsuwa yayi sosai yana saurara yana qaruwa da abinda ake fada a ciki. Kusan minti sha biyar da zaman sa sega Amirah ta bude qofar dakinta ta fito.
Turus tayi da ganinsa, cikin wayancewa ta qarasa tana dan sosa kai idonta akan hannunsa da aka nade da Bandeji ta shiga gaishe shi ya amsa mata ba tareda ya kalli inda take ba.
“Uhm daman yanzu nake cewa zan shiga na dubaka, wallahi jiya ina gama shiryawa bacci ne ya kwashe ni shi yasa ban shigo ba” ta fada tana sunkuyar da kai.
“Babu komai ai, ya naki jikin?” Ya tambayeta yana dan kallonta. Cikin mamakinsa dan tayi zaton ze balbaleta da fadane yanda ya saba tafe
“Lafiya lau ai babu abinda yake damuna yanzu”
“Masha Allah, Allah ya qara lafiya. Ina Addah bata tashi bane?” Ya sake tambayarta
Kafin ta bashi amsa Addah ta fito daga daki tana mita
“Ni wallahi na gaji da wannan rayuwa haba gida kamar gidan Haya dan jaraba abinda zaka ci ma seka tashi ka dorawa kanka, naga ni dai zuwan da muka tabayi ba haka aka mana ba Alqur’an Asma’u kafin mu tashi daga bacci yarinyar nana ta hada mana abin karyawa kala kala haka kan ya gama narkewa na Rana ya sauka ga kayan dadi tuli, kai Allah dai ya jiqanta badan ta mutu ba yanzu gashi dan daka haifa ne yake maka baqin ciki kar kaci me kyau shikenan ai nima kwadayina ya zaunar dani”.
Daga Bashir har Amirah babu wanda ya kulata, ta samu guri kusa dashi ta zauna tana cewa
“Au Bashir ya jikin naka? To Allah qara kiyayewa halan Sabon Mijin nata garjejen qato ne kaje ya hada maka jini da majina? Kaima maganin ka kenan ai da naci mace tayi auranta seka qyaleta ai, ni da zaka ji ta tawa ma da ka hada mata yayanta ka bata kasan riqon dan yanzu se uwarsa musamman wadannan marasa mutunchin gara dai can suje su qarata da uwarsu”.
Seda yayi qoqarin gaske ya hadiye bacin ransa kafin cikin dakakkiyar Murya yace mata
“Daga yau gaba daya yaran zasu dawo nan gidan dan haka dole a canza tsarin komai da akeyi kamar girki da sauran abubuwa. Sannan zuwa qarshen satin nan seki shirya komawa Gombe tunda komai ya daidaita”.
“Bangane na koma Gombe ba? Munyi dakai daman idan nazo zan koma ne?” Ta fada tana zate masa ido. Se ya dago ya kalleta dakyau yace
“Ban gane ba, da kinzo gaba daya kenan bazaki koma ba ne?”
“Yo ga amsa nan ka bawa kanka in koma Gombe nayi me? Uwar wa n ajiye a can ko kuwa so kake naje ayita nunani tsofai tsofai dani ana zawarci nake to ba inda zani, kuma koma ba haka ba daga haihuwar tata kwana biyu zaka ce mun na tafi uban waye ze gyaramun yar? salon ta lalace ka sako mun ita na shiga uku to ba inda zani zama daram me naquda ta samu kayifa”.
Shiru ya mata ya ci gaba da istigfarin da yake a zuciyarsa yana kallon Program din da ake a Tv, ta ringa Tijararta wai dan yar uwarka ne yake maka haka, ita dai bata san me tayi wa Nafi data saka yayanta suka raina ta ba idan ba haka ba ko arziqin surukuta ai ya isa ya ringa daga mata qafa idan Nafi ce ze koreta daga gidan sane.
Shidai kamar meyi da dutse har tayi ta gaji tafi ki mutu be ce mata ba dan kanta tayi shiru, se kuma ya dawo zancen tana so ya saka akaita kasuwa akwai abubuwan da zata siyo na amfanin Jegon Amirah. Ganin bazata barshi yayi jinyar zuciyarsa ba yasa ya tashi ya bar mata falon ya koma Daki, babu bata lokaci yayi musu Booking din jirgi su uku shi, Addah da Amirah ranar Juma’a zasu tafi Gombe idan yaso taje cab tayi jegon idan ta gama ta dawo.
ASMA’U
“Yusuf ka bari dan Allah” na fuzgo kalamandakyar ganin dagaske so yake se munyi abin kunya a gaban yara. Saki na yayi ya zauna akan kujera yana qaremun kallo yanda jikina yake rawa kamar wata wadda aka kama tana mugun abu seya saki murmushi me sauti ya miqo mun hannunsa na dama alamar na taho na maqale kafada kamar wata qaramar yarinya ina sakar masa harar da se yanzu na samu ido na ya tuna yanda akeyi ta.
“Ni kike harara ko ki bari na taso sena cinye idonki idan yaso naga