Showing 114001 words to 117000 words out of 260321 words

Chapter 39 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42731

safe se kiran Bashir akayi wai ya rasu da Asuba anji shi shiru be fita Masallaci ba Qaninsa ya duba shi aka tarar babu rai.

Mutuwar Matashi akwai firgitarwa musamman ta mutun irin Aliyu me mutunchi da mutunta Jama’a ya samu shaida ta kwarai sosai, haka muka tafi Jana’iza Allah sarki Mamansa se Kuka takeyi su biyu ne Yayanta daga shi se qaninsa haka budurwar da ze aura da suka zo Abin tausayi gaba daya se jikina ya sake yin sanyi da lamarin duniya.

Tunda akayi rasuwar Bashir ya zama wani iri, ranar kwana uku, ranar kwana uku da daddare muna zaune shiru yake cewa
“Allah sarki Aliyu, ranar kafin ki shigo yake cewa mun Wallahi Bashir kayi dacen mata Allah yasa mu a danshin ka dan Allah ka riqe yarinyar nan da kyau dan Alkahiri ce a rayuwarka kuma matar rufin Asiri ce.

Kaga dai a yana yin da kukayi aure gashi a hankali abubuwa suna ta warwarewa bata nuna gazawarta ba ni kuwa kana kallo yarinyar nan Momy ba yar kowa ba amma ta dauki buri ta dorawa kanta wai fa dana kaita taga gida na rainawa tayi wai ban dora bene ba, ta shiga kawo mun wasu tsare tsaren banzanta, Ni fa in ba’ayi wasa ba auran ma fasawa zanyi.
Idan da rabo nayi a Aljanna, ashe bamu sani ba tafiyar ma tazo gangara” se ga hawaye ya zubo ta gefen idonsa.

Jikina ya qara macewa dakyar na iya cewa “ Allah ya sa muyi kyakykyawan qarshe, waya sani ko nika mutuwar zanyi”

“Karki sake fadan haka In sha Allahu lafiya lau zaki haihu” ya fada yana kama hannuna.

Wannan rasuwar ta rage kaifin shagalin bikin su Fainusa dan duk wani makusancin Bashir yasan Su su hudun nan tare suka tashi, Ranar Asabar data kama kwana shida da rasuwar Aliyi aka daura auran a ranar kuma kowa aka kaita gidanta. Daman Banje kai Amare ba dan gidan mu ma na tafi da hayaniyar yan biki ta fara yawa se dare Bashir yaje muka tafi gida.

Kamar ciwo na jira kuwa yana yin parking nayi wani ciwon baya da mara lokaci daya sunyi mun sallama, se Bashir ya shiga ya dakko mun Akwatina muka kama hanyar Asibiti. Tsabar takaici ina cikin azabar ciwon da nakehi kamar haihuwar ta taho gab ne wai Bashir tambayata yakeyi yanzu ya za’ayi idan haihuwa ce bamu siyi kayan Baby ba bansan sanda na qunduma masa zagi shiga kayan babyn ba nace ya mun shiru ko ya sauka a motar,

Haka muka qarasa aka shiga filin daga, zo kuga idon Ma’u a labor room ashe aka ce wasa Farin girki wannan ciwo sallama ne, haka dai akayi ta gumurzu har Asuba, cikin ikon Allah Ana kwada kiran Assalatu na santalo qaton Baby na me kama da Bashir sak kamar an tsaga kara hasken Fata ta kawai ya dakko.

Murna a gurin Bashir kamar ya taka rawa, kafin Gari ya gama haske Asibiti ya fara cika da dangi na harda nasa, Hajia Babba da Hajia Umma ne suka zo, a kunne na radawa Hajia Umman akan tace gida zasu wuce dani dan tun farko farko danayiwa Bashir maganar wankan gida yace ba wannan maganar ban sake ba.

zuwa rana kuwa da likita ya tabbatar babu wata matsala aka bamu sallama Hajia Umma tace gida aka yi dani, ze musa Addah ta tace muje babu komai daman sunyi niyyar kawo nin, saboda haushi ko sallama Bashir beyi mana ba ya kama hanya ya tafi.

Oho nidai muma mukayi tafiyar mu gida, daman na dade da hada kayan tafiya wankan muna zuwa aka tura su Khadija gidan suka dakko mun ina ta Addu’ar Allah yasa kar a tambayi ina kayan wanka da sauran abubuwan da ake siya ilai kuwa kafin ma mu qaraso Hajia Anjin saka su Baba Jummai sun shirya mun dakin da zan zauna duk wani abun buqata na zaman jego an tana da.

Seda muka kwana muka wuni sannan Bashir yazo shi ala dole fushi yake yi, ko a jikina jegona kawai nakeyi ingantacce haka yarona Aliyu da tun a Asibiti yayi masa Huduba shima yana samun kula sosai.

Kwanan mu biyar aka kawo kayan barka daga gidan su Bashir tareda ragon suna. Yan rigunan su ba laifi da turamen Atamfa uku nawa, haka aka taresu cikin karamci suka tafi yan barkar da suka tarar yan uwan mu nata yan qananan maganganu dan kowa yayi zaton yanda yanzu ya samu budi babu laifi zeyi abinda yafi haka ni kuwa ko a jikina dan dama ba jiran abinda zasu kawo nake ba, ko sanda na masa magana kawai dan haqqinsa ne ya kamata yayi.

Ranar suna munsha shagalin mu, na ringa shiga ina fita ta Alfarma. Amirah da tun kwana biyar da suka zo tana gurina da yake anyi hutun makaranta daman nayi mata dinku na duk inda na shiga tana nan yan gidan mu suyita tsokanarta ana yar Anty tayi dariya.

Zaryar da Bashir ya ringayi ta saka aka tattara ni satin mu uku muka koma se na tafi tareda Baba Jummai da zata qarasa mun Arba’in.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 36

Shekarar Aliyu daya na samu cikin Jafar, nasha kuka sosai saboda ba qaramar wuyar raino nake ci da karatu ba sannan yanzu kuma ga wani sabon cikin har rigima se da mukayi da Bashir ya kuma tabbatar mun se ya bata mun rai in har wani abu ya samu cikin nan bisa gangancina.

Haka na hada ciki da raino ga karatu da lokacin ina Level 3 ga hidimar gida idan na fita makaranta duk yammar da zanyi haka zan dawo nayi girki da abubuwan dana fita banyi ba kuma Bashir babu ruwansa ko yaya na kuskure ya ringa mita kenan.

Ganin Aliyun yana cin abinci sosai yasa na tambayi Bashir ko zan ringa barinsa a gurin Addah idan zanje makaranta, da farko qi yayi seda na tasa shi da kuka sannan ya yarda washe gari kuwa da zan fita na hada masa duk abinda nasan ze buqata na kaishi gidan.

Faran faran ta karbe shi musamman daman na hada dan ihisani na kaimata, na tafi makaranta ta hankali kwance tunda nasan za’a kulamun dashi.

Ranar qarfe biyu na taso, tun daga Get din gidan nake jiyo kukan Aliyu gabana ya yanke ya fadi na qara sauri ina shiga na tarar dasu a tsatstsaye akan Aliyu da yayi faca faca da ruwan kwata yana ta tsanyara kuka abin tausayi.

Da sauri na qarasa na daga shi, a bakin Mama Binta Kishiyar Addah nake ji wai Amirah ce ta dauke shi suka fita waje wasa shine wai ta ajiye shi ya tsallaka kwata ya fada ciki, ita Addah bama ta gidan tuni ta fice, haka na dauke shi muka tafi gida raina duk a bace.

Idan ba wulaqanci ba taya za’a barta ta fita dashi har ya fada kwata. Seda ina masa wanka naga inda ya kuje a jikinsa, haka na lallabashi yayi shiru bayan na bashi abinci da paracetamol na ruwa dan jikinsa yayi duki kafin na goya shi na shiga aiki ina tunano irin tijarar da Bashir zeyi mun idan ya samu labari.

Ilai kuwa yana dawowa ya fara dudduba yaron kamar yasan me ya faru se ji nayi yana kwala mun kira, haka muka kwana yana masifa ya kuma ce karna sake kai masa yaro ko ina nima din daman ba sake kai shi zanyi ba.

Haka na ci gaba da karatu da raino cikina wanda yana wata takwas Bashir ya sake rasa aikinsa sakamakon korar ma’aikata da Banki sukayi haka suddan kuma ta rutsa har dashi.

Sosai muka shiga tashin hankali musamman yanda korar tazo musu ba tareda tsammani ba gashi a lokacin shekara ta qare lokacin biyan kudin Hayar mu yayi ga shirin haihuwa ta shi kansa Bashir din a sannan ya koma Mesters kuma kowa yasan yanda Masters yake da cin kudi.

Haka nayi ta qoqarin kwantar masa da hankali da nuna masa In Allah ya yarda komai ze zo da sauqi mu ci gaba da Addu’a kawai Allah ze kawo mafita.

Hidimar yanzu data farkon Auran mu ba daya ba, a wancan lokacin muna da ajiyayyun kayan abinci wanda sune jigo sannan sauran buqatun mu ba wasu masu yawa bane yanzu kuwa shi yake siyan kayan abinci ga qaruwar Yaro da shima akwai nasa buqatun na yau da kullum da dole suna buqatar kudi chanjin rayuwar da muka samu se nan da nan ta nuna a jikina musamman saboda yanayin da nake ciki ga tsohon ciki ga karatu da yazo mana gangara.

Haka muka ci gaba da malejin rayuwa kullum cikin saka ran samun budi daga qofofin ubangiji, da dan abinda nake samu daga kasuwancin da nakeyi nake riqe damu dan sam Bashir beyi wani tanadi ba ba kuma zan dorawa yan uwana nauyin da Allah ya sauke musu ba dan iya zumunchi sunyi mun ya kamata ace yanzu kuma shima ya jajirce ya riqe gidan sa.

A sanda yana aikin Babu yanda banyi da Bashir ba akan ya ringa cire wani abu a Albashin sa duk wata yana saving amma yaqi. Shi irin mutanen nan ne da a rayuwarsa idan ya samu kudi kawai a biya buqatar da take a lokacin baya ajiyewa saboda buqatar kota kwana.

Nayi nacin har na gaji akan bayan aikin yaje ya samu Baffa suyi maganar kasuwar ya ringa gwada wata sana’ar ko babu komai ya zama mutum yana da wata madafar bayan albashi saboda gudun bacin rana akwai sanda har magana ya gaya mun wai ko fata nake masa ya rasa aiki ya ringa fushi yana jin haushi na daga nan nace bazan sake masa magana akan yin wata sana’a ba.

Abinda na lura dashi wannan a halin mazan Bauchi da Gombe yake sunbada amanna da aikin Gomnati, kadan daga ciki ne suka yarda da kasuwa, Nidai dana tashi gidan mu naga ba’a zaman banza zan ci gaba da saida saidena dan bazan dogara da se abinda miji ya dakko ya bani ba.

A wannan yanayin na haifi Jafar, wannan karon a gida na na zauna daman kuma ban saka rai da samun komai a gurin Bashir ba kodan halin da muke ciki ma da yaya ya biya kudin haya haka dai akayi suna na kuma samu Alkahiri sosai daga yan uwana.

Bayan haihuwar Jafar abubuwan da suka faru ba masu dadi bane dan sosai muka shiga matsin rayuwa, tun muna iya siyan kayan abincin wata a ajiye har seda takai mun koma awo a kullum na abinda za’a dafa kuma duk nice qarfin riqon gidan a abinda nake samu zan bashi yayi a haka har seda muka cinye jarin nawa duk ma abinda zan samu a haka yake qarewa tunda komai da shi mukeyi babu wani abu da yake shigowa Bashir daidai da ci gaban karatunsa da tallafi na yake yi seda takai har mota ta na siyar na bashi kudin akan ya kama wata sana’ar sedai wane tudu wani gangare kudin suka narke, Bala ya bawa akan ze saro masa kaya daga Lagos wai yan Fashi suka tare su suka karbe sukayi masa dukan tsiya dan seda yayi kusan wata a kwance yana jinya.

Haka muka ci gaba kullum ina hanyar zuwa gida karbar kudi seda ta kai ni da kaina na fara jin kunyar hakan na dena zuwa, aiki kuwa kullum ina tafe, ina Teaching ga wasu training centers dana ke koyarwa suma duk dan dai mu rufawa kan mu asiri seda ya zama wata rana idan mun samu abinda zamu ci da rana sedai ni dashi mu haqura da na dare yara suci nakan kwana ina kuka wani lokacin idan na tuna yanzu fa akwai wadanda tunda suka somi rayuwa cikin irin wannan qunci da matsin suka tashi ko?

Idan kaga yanda na koma sena baka tausayi yanda kasan nice Mijin ba Bashir ba dan shi yana zaune a gida zan fita aiki na dawo kuma na dafa abinda ya samu muci wannan abun yana bala’in baqanta ran yan uwana kuma yana daga dalilin daya sa duk suka zuba mun ido suga gudun ruwana ni kuwa ko a jikina, Ina son Bashir bana jin duk abinda zanyi masa na fadi kuma ko banyi dan shi ba zanyi dan yayana dan haka ban taba jin haushin kaina akan abinda nake yi ba.

Abin takaici daya lokacin qannen sa da sukayi aure Allah ya taimake su gaba daya sun samu gidan hutu dan haka yanzu gidan su basu da wata matsala ko wacce na iya qoqarin ta se kuma ya zamana sun ware Bashir domin ko gidana yanzu babu wadda take zuwa tunda bani da abinda zan basu.

Ita kanta Dadan yanzu wani gani gani takeyi mun idan munje gidan babu wannan sakin Fuskar irin nada wanda duk cikin zugar Addah ne, a cewarta baqin ciki da kyashi ne ya hana nasa a bawa Bashir kudi a gidan mu na gwammace mu zauna cikin talauchi ni da shi din saboda wai ina baqin cikin yana wahaltawa yan uwansa sama dani, a raina nace ashe sun san da yana da shi din ma su ya ringa wahaltawa bani ba dan kafin ya mun abu daya ya musu goma sannan wane baqin ciki zanyi da har zan zabi zama cikin

Daidai da Addah se in manta rabonda na sakata a ido ko su Aliyu na kai gidan ba’a minti Ashirin se a dawo mun dasu tace fita zatayi, Amirah kanta yanzu ta rage zuwa idan nace mata me yasa se tace Addah ce take hana ta rayuwa kenan se kana dashi mutane suke yi da kai a duniya.

Ana cikin haka wata rana Bashir ya shigo gida cikin tsananin murna yake nuna mun saqon gayyatar da wani wani kamfani suka aiko masa daga Lagos, a cikin ayyukan da Alhaji Qarami ya ke ta fafutukar nema masa se yanzu Allah yasa daya suka gayyace shi, a yanda yake gaya mun mutum biyu za’a dauka kuma su biyar aka gayyata Jarabawar gwajin nan da kwana uku ze tafi.

Tun daga ranar na fara Azumi ina Yiwa Bashir Addu’ar nema sa’a. Gogan kuwa se shiri yake ya binciko tsofaffin littattafan sa yana ta karatu. Ana gobe ze tafi da daddare har wurin daya yaha zaune yana fama da takaddu na kalleshi nace

“Baban Ali da ka ajiye karatun nan haka ka huta Addu’a ya kamata muyi tayi dan a irij wannan abun fa sa’a ake nema ba wai karatu ba”.

“Ma’u kenan, a irin karatun da nayi na tabbatar da duk tambayar da sukayi mun sena amsata sannan duk wata kwarewar aiki da zasu nema ina da ita, kedai kawai ki fara shiri dan har na hango mu a Lagos” ya fada yana ci gaba da bude littafinsa, se na ja numfashi na gyara kwanciyata nace
“Toh Allah ya tabbatar da Alkahiri”.

Washe gari ya hau mota se Lagos, kwanan sa biyu ya juyo bayan sunyi Jarabawar ya dawo da tabbacin kamar ma ya samu aikin dan har yana ce mun “ko mutum daya zasu dauka nasan nine, bakiga yanda su kansu masu Jarabawar suka ringa jinjina qoqari na ba”
Ni kuwa nace masa

“Kadai ce In sha Allahu, kuma muci gaba da Addu’a idan rabo ne za’a samu”.

Sati daya sakamakon ya fito amma babu sunan Bashir wasu mutum biyu daban ne dan daya ma babu shi a wadanda sukayi Jarabawar tare, ina jin abokin da yayi yana gaya masa wai dan wani Minister ne aka aiko da sunan sa dole aka cire mutum daya aka saka shi.

Haka Bashir ya ringa qunci da bacin rai akan rashin samuwar aikin, duk yanda naso na nuna masa komai na rayuwa rabo ne idan Allah be tsaga da naka ba duk wuya haka zaka haqura bazaka samu ba amma yaqi fahimta qarshe ma abin ya zamar mana rigima har yana gaya mun magana akan niyyar samar masa aiki ne kawai ba’a yi ba aka wahalar dashi idan ba haka ba duk hanyar da muke da ita ace an rasa ta inda za’a samar masa aiki me yasa su yan gidan mu mata da maza da sun gama makaranta suke samun aiki ga Abubakar tuni ya samu chanjin aiki daga inda yake a Kano zuwa NNPC.

Ganin fa yana neman ya raina mun hankali yasa nima na horance masa, nayi masa tatas na gaya masa ai ba haqqi na bane na samar masa aiki dan haka idan ze tashi ya nema tun wuri ya nema kuma na cire hannuna daga duk abinda ya shafi sabgarsa, idan har ya aureni ne saboda ya samu kudi toh ya sawwaqe mun kawai.

Wannan abun ya bala’in dagawa Bashir hankali se gashi har yana bina yana bani haquri akan sharrin shaidan ne shi ba abinda yake nufi kenan ba, haka muka ci gaba da jalan ta rayuwa yau fari gobe baqi a haka na kammala karatuna na fara hidimar qasa.

Ranar wata Talata da bazan manta da ita ba, muna zaune da yamma nida Jafar dan a lokacin Aliyu ya fara zuwa Islamiyyar da take cikin layin mu. Shekarun sa uku a sannan tuni bakinsa ya bude sosai dan haka nake hadashi da Amirah suna tafiya kuma sosai yake karatun dan in aka dawo ya ringa tilawa Bacci kadai yake saka shi yayi shiru.

Lokacin zafine kuma babu wuta dan haka na shimfida mana tabarma a tsakar gidan muka zauna Jafar nata wasa da Yar motarsa me Batiri ni kuma ina duba takaddun Test da nayiwa dalibai na a makaranta Aka bugo Get, Hijab na na saka na leqa, Alhaji Buba ne me gidan da muke haya shida wani mutum da wani saurayi me kama dashi daga gani dan sa ne.

Seda gabana ya fadi da ganinsu dan nasan zancen baze wuce na kudin haya ba amma ai da sauran kusan wata biyu nan gaba haka muka gaisa nace musu Bashir din baya nan.

“Eh ba wurinsa muka zo ba munzo ne mu duba gidan daman mun riga mun gama magana dashi” Alhaji Buban ya fada. Sena kalleshi da mamaki dan ban gane su duba gida ba,

“Wani abu aka ce ya samu gidan Alhaji” na fada ina kallonsa, se ya girgiza kai yace “Shi Bashir

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login