Showing 102001 words to 105000 words out of 260321 words

Chapter 35 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42665

watan da muke ciki zasu zo.

Ganin duk anyi maganar su amma nida Bashir shiru yasa hankali na ya fara tashi. Sau biyu ina sake masa magana bayan da aka bashi damar ya turo amma se yace na qara masa lokaci akwai abinda yake jira gashi kuma a kwanakin gaba daya ma ya janye da zuwa gidan mu musamman da Yaya Abubakar baya nan, daman shi a Kano yayi service se Allah ya taimake shi gurin suka riqeshi.

Seda muka ci sati kusan biyu Bashir yana mun wala wala har takai Baffa ya sakeyi mun akan yaji shiru saboda yana so a hada gaba daya a aikawa da gidajen mazan sa rana shiyasa yake so yasan shirin Bashir din.

Ranar dana gaji da zilliyar tasa takanas na kama hanya muka tafi gidansu tareda Alawiyya wadda da dakyar ta yarda zata rakani, muna tafiya tana zagina wai in banda asara ga Maza da suka amsa sunansu suna bina amma na nace se wani Bashir gashinan yana wulaqantani kuma tsabar rashin zuciya na dauki jiki zan je gidansu. Nidai ban kulata ba har muka shiga gidan.

Kai tsaye Dakin Dada muka shiga, da yake daman na saba zuwa gaishetan se hakan be zama wani abun mamaki na daban ba. Mun sameta tareda Yayarta wadda naji suna cewa Addah da yaranta guda biyu babbar bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba se qaramar itama zatayi hudu haka.

Matar nada matuqar kirki ga faran faran da Jama’a nan da nan ta shiga hidima damu musamman da taji ance budurwar Bashir ce bakinta har kunne take tambayar wacce daga ciki aka nuna mata ni.

“Wai wai zuqi masha Allah, ashe yanda Bashir yake sunkuyar dakai har ya iya zabo mace haka kai Allah ya nuna mana lokaci musha biki, sannunku sannunku” haka tayi tayi dauke wannan ajiye wannan nidai kaina yana qasa ina ta Addu’ar Allah yasa ya shigo amma har mukayi kusan minti talatin shiru bayan kuma sanda muka shigo na ga qofar dakinsa a bude alamar yana gidan.

Naziru qaramin qaninsu ne ya shigo, ya qaraso inda nake da dan gudunsa ya zauna yana gaishe ni da yake muna shiri dashi sosai, seya miqe da gudun sa yace “bari naje na gayawa Yaya ga Anty Ma’u tazo” be dade ba se gashi sun dawo tareda Bashir din muna hada ido na tabo Alawiyya nace mu tafi daman jiran da nake kenan nasan dole ai ze bimu.

Mukayi musu sallama bayan mun ajiyewa Dada ledar dana zubo turarukan fesawa dana wuta da sababbin kudi yan hamsin hamsin na dubu biyu Addah ta dauke ledar tana zuba mana godiya kamar ita aka bawa mudai muka tafi.

Seda muka danyi nisa da gidan sannan Bashir ya biyo mu, sama sama suka gaisa da Alawiyya tayi gaba ta barmu, se ya kalleni yana cewa “Jiya munyi waya amma baki gayamun zaki zo ba”

“Me yasa zan gaya maka tunda baka son mu hadu yanzu, daman zuwa nayi in gaya maka dan karka ji a gari, tunda dai ka gagara turowa zan bawa wadanda suka shirya dama. Na kuma gode da batamun lokaci da kayi da duk alqawarirrikan qaryar da kayi mun akan zamu rayu tare” ina gama fadar haka nayi gaba na barshi a tsaye ina jinsa yana kwala mun kira nayi banza dashi.

A zatona ze biyo mu amma har muka je gida babu ko sahunsa, abinda ya qara qona mun rai ya tabbatar mun dagaske kenan daman Bashir yaudarata kawai yayi ba aurena zeyi ba yasa na gama fadawa a soyayyarsa sannan yanzu ze gudu ya barni. Ranar haka na kwana ina kuka, gashi ko a waya be kirani ba, babu wanda yabi ta kaina a gidan,

Hajia Anjij cema da safe da ta ga yanda idona ya kumbura ta jani tanayi mun nasiha da nayi haquri, lokaci da yawa abinda muke so be zama lallai shine Alkahiri a gare mu ba dan haka na fawwalawa Allah, idan Bashir mijina ne se munyi aure idan kuma Allah be yi ba duk nacin mu sedai mu haqura.

BASHIR

Tun lokacin da Asma’u ta gaya masa zancen an ce ya turo gida se maganar ta rabe masa biyu, bangare daya na farin cikin ya kusa mallakar Ma’unsa se kuma daya bangaren tashin hankalin da me ze aureta?

Har yanzu bashida komai be kuma bawa wani ajiya ba, dan aikin da yakeyi dubu goma ce ake biyansa a wata wadda dawainiyat karan kansa ma ba isar sa takeyi ba ga qannensa suma da qananun buqatunsu tunda Babansu yayi ritaya, kudin garatutinsa suya har hada yake dan juyawa ana samun abinda za’ayi cefane a gidan yanzu gaba daya duk burinsu akansa suke na ya samu aiki toh ta ina kuma ze fara daddago maganar aure.

Kullum da wannan zulumin yake kwana yake tashi ya kuma rasa dawa zeyi shawara baze iya tunkarar Abubakar ba, Aliyu kuwa tun tuni daman ya gaya masa ya rabu da Asma’u dan tafi qarfinsa toh se a yanzu ya ga gaskiyar abinda yake fada din amma kuma baya jin ze iya rabuwa da ita saboda sonta ya riga yayi masa irin shigar da fitar rai ce kadai zata iya raba shi da shi wannan dalilin ya sa yake zille mata dan ganinta ma kullum qara rura wutar sonta yake a zuciyarsa sannan ya rasa ta yanda ze fahimtar da ita halin da ake ciki.

Maganar data gaya masa dazun ba qaramin tayar masa da hankali tayi ba, gaskiya bazata sabu ba. Dole ya nemi mafita dan yana ji yana gani baze iya zuba ido wani ya raba shi da Ma’u ba ya rusa duk wani tsari da mafarkin sa akanta.

Jiki a sabule ya koma cikin gidan, palour Dada ya shiga ya tarar dasu ta zazzage turarukan tana ta santinsu gaba daya ta kwashe se kwalli daya ta barwa Dadan wai ai kullum ana kawo mata na yau rabonta ne kudin ma seda ta raba biyu ta dauka, ganin yanda Bashir ya shigo kamar kazar da tasha ruwa yasa suka dakata suna kallonsa.

“Lafiya Bashir ka shigo kamar wanda aka zarewa qashi” Addan ta fada tana kallonsa, se ya ja guntuntsaki yana kallon Dada yace “Dada maganar da mukayi dake akan sunce mu tura ne, kinsan tare ake so a hada dana sauran toh shine yanzu tayi fushi har tana cewa kawai zata bawa wasu dama tunda ban shirya ba”.

“Me zanji haka magana babu dadin ji, kai yanzu Allah ya kashe ya baka shine ka tsaya salubanci da sunce ka tura din amma ba’a je ba to uwar me kake jira?” Addah ta fada tana gyara zama.

Shiru Bashir ya mata, dan shi kwata kwata baya so tana shiga sabgarsa ma, Dada ce tace
“Toh Addah kin manta har yanzu be samu aiki bane, aure ai baze yuwu ba babu abinyi dame ze riqe matar?”

“Sannu Nafi, kai Allah Nagode maka da Halin Nafi. Wane irin aiki kuma kuke magana mutumin da Allah ya kawo masa hanyar arziqi, yanzu in banda rashin tunanin irin naki har kwa tsaya kuna zancen wani aiki ga babban aiki ya samu.

Ka samu yarinya irin wannan daga babban gida tana sonka kuma iyayenta sun yarda zasu baka qarewar aiki harda gida da mota se an hada maka nasan kai dai kawai ka tura ayi magana asan dagaske kake seka gaya musu baka da aikin yin Aradu zasu samo maka tunda yarsu tana sonka.

Kai ashe Nafi kina dab da ja mana Asara kai Jama’a Allah kayi magani”.

Kallon ta kawai suke har ta gama hayagagarta, se Bashir ya miqe ya fice a ransa ya na qudurce kawai ze gayawa Alhajin su aje, idan yaso su abar maganar nasu bikin zuwa sanda Allah ze sa ya samu madafa tunda ya rarraba CV dinsa a gurare yanzu jiran tsammani kawai yake yi. Kasa zama yayi a gidan ya fice, yana so ya kira Ma’u kuma yana tsoron abinda zata sake gaya masa Allah Allah kawai Yake Alhaji ya dawo ayi wacce za’ayi kawai.

Addah kuwa ci gaba tayi da surutan ta har tana cewa Dadan idan ma maganar kudi ce se a nemo Bashi ayi komai da an gama biki abinda ya samu a tattara a biya.

“Kiji ki Addah wane irin bashi ana zaune qalau dan Allah, babu komai idan Allah ya nufa matarsa ce to se kiga Allah ya kawo hanyar da za’ayi komai cikin rufin asiri. Haka suka rabu dai Addah na sake jaddada aje ayi maganar nan kar su bari damar nan ta wuce su.

Bashir kuwa Alhajin su na dawowa da yamma ya shaida masa, ba tareda wani ja inja ba kuwa ya amince shima abinda yace Allahn daya taso da maganar ze hore yanda za’ayi komai cikin rufin asiri, tun a daren ranar ya tashi qaninsa ya aikashi gurin Baffan su Asma’u akan a basu dama zasu kawo goron gaisuwa, a take kuwa yace duk sanda suka shirya suzo, washe gari kuwa suka hadu da Qannensa guda biyu da Amininsa daya sukaje aka kai gaisuwa.

Tarba me kyau suka samu daga gurin Baffan da yayyen Ma’u biyu manya, nan da nan aka qulla magana sedai sun nemi alfarmar a qara musu lokaci akan wata shida da Baffa yace ya yanke ranar auren.

“Kasan haryanzu Alhaji be samu wani aiki na gaske ba, yar buga buga ce kawai akeyi ana dai saka ran samun aikin nan kusa, abinda yasa muka zo din ma saboda kaga kar aga kamar wasa ne abun” Aminin Baban su Bashir Malam Salisu ya fada.

Se Baffa yayi murmushi yace “Babu komai Malam Salisu in sha Allahu babu abinda ze gagara, kuje kuyi shirinku iya abinda ya zama dole sadakine se ya nemi muhallin da ze ajiyeta duk abinda ya kakare masa yazo ya sameni babu komai” suka yi sallama suna ta godiya, haka suka koma gida suna ta yabon dattako da karamci irin na Baffa, dan lokacin da sukaje gidan daya daga qannen Baban su Bashir din har yana cewa anya za’a barsu su shiga kuwa shi Bashir me ya kaishi dakko abinda yafi qarfinsa.

ASMA’U

Ina kwance ina ta baqin raina tun jiya har yanzu ban ware ba, gaba daya na rasa ya ma zanyi dan bazan iya hasaso rayuwa da wani namiji da ba Bashir ba. Addu’ata kawai Allah ya mantar da Baffa karya kuma tado mun da maganar har zuwa sanda zamu samu mafita.

Ina cikin wannan tunanin Baba Jummai shugabar masu aikin gidan mu ta shigo dakin ta sakar mun guda a tsakiyar kai, da saurin gaske na toshe kunne ina zare ido ita kuwa se sake rangada abarta take ragowar na taya ta.

“Uwar dakina ta zama amarya mun shaida mun tauna goro da alawa Allah ya nuna mana randa zamu sha taushen daurin aure” ta fada kafin ta sake kwasar wata gudar.

Wani mugun bugawa qirjina yayi, waye ya kawo goro na? Na shiga uku kardai fa Baffa ya amsa wa wani daga cikin manemana magana.

Dafe qirji nayi na qara fito ta idanu waje nace “Baba Jummai gorona aka kawo dawa?”

“Wato Uwar dakina kina nan da halin ki na tsokana, baki ma san waya kawo goron ba kenan, to wannan Me gidan da baya dariya ne Engineer kike ce masa kowa” Baba Jummai ta fada.

Se naji kamar an kwararamun ruwan qanqara a tsakiyar kaina, wata wawuyar ajiyar zuciya nayi kafin na koma na kwanta ina yiwa Allah tasbihi. Gaskiya Bashir ya shammaceni.

Waya ta ce ta dauki qara, a jikina na ji cewa Bashir ne, seda na tura baki kamar yana gabana kafin na daga wayar.

“Amaryata” ya fada cikin qaramin sauti, shiru na masa ina ta faman juya baki kamar yana gaba na ina jinsa yayi murmushi yace “Fushi ake yi dani ko Ma’una ayi mun afuwa. Gani a qofar gida nazo bada haquri”.

“Ni bazan fito ba” na fada cikin muryar shagwaba, se ya marairaice shima yace

“Haba mana Amaryata so kike yi na kasa bacci dan Allah ki fito na ganki mana kafin nan da wata shida na dauke ki gaba daya ki zama tawa”.

Rufe fuska ta nayi ina murmushi nace “Dagake bazan fito ba, nima ai jiya banyi baccin ba kaga mun yi 1-1 kenan ka tafi se bayan sati uku zaka sake ganina”.

“Kice kawai sena zare sannan, ki taimaka mun nidai ki fito na ganki ko minti daya ne ki koma na yarda”.

Seda naja masa rai kafin na zura dogon hijabina har qasa na fita, a palour na tarar da Goggo da su Nasir suna kallo naja hannun Mimi yar dakin Hajia Umma ce muka fita.

Bashir na tsaye daga bakin Get gurin masu gadi, har wurin naje nace masa”A nan ka tsaya maimakon ka zauna, muqarasa toh”.

“Aa Gimbiya daman zuwa nayi naga kyakykyawar fuskar ki sannan na kawo miki wannan(ya miqo mun wata farar leda da kwali dan kwali qarami a ciki) ina so na kwanta da wuri gobe zanje wata Interview kiyi mun Addu’a Allah yasa a dace”.

Karba nayi ina cewa “In sha Allah za’a dace, Alah ya bada nasara”.
“Amin” ya amsa mukayi sallama ya tafi ina juyowa mukayi kicibus da Fahad sun taho shida Anwar yayan Alawiyya da take bi.

Fahad qanin Hajia Anjin ne shine auta a gidansu, Fari kyakykyawan saurayi me qirar larabawa ga iya soyayya dan da ace da Fahad na fara haduwa kafin Bashir inaga da yayi nasara akaina saboda iya tsara zancensa.

Hararar sa nayi ta gefe ganin irin kallon da yake mun yana murmushi kafin nace “Uncle Fahad ina wuni”

“Karma ki wani ce mun Uncle, yau dai naganshi daman akan wannan Kika qi ni Asma’u gaskiya kin fado da yawa, har naji sauqin radadin da nake ji tunda nafi wanda ya kasanin sau dari wallahi kuma har yanzu ban cire rai akanki indai ba gani nayi an daura miki aure ba bazan cire ran zaki zama mallakina ba” Fahad ya fada yana kafeni da idanunsa masu kama dana mage, sena fizgi hannun Mimi nayi gaba ina cewa

“Se kayi ta saka ran ai kar Allah yasa ka cire, wai ace ba’a san mutum amma su kamar mayu sun nace kuma ahakan dai shi yayi mun baku ba”

“Indai akanki ne ki kirani sarkin Mayu ma qarewa kenan Asma’u dan sena cinye ki hankalina ze kwanta”.

“Daga murya nayi yanda ze jini nace “sedai ka ci kanka dan kurwa ta daci ne da ita” na murguda masa baki harda fari da ido kafin na shige inajinsu da Yah Anwar suna mun dariya.

Haka kawai duk wanda yaga Bashir seya kushe mun abuna, su kyau da kudi yake a gabansu ni ba matsala ta bace ba.

Sannu sannu watanni naya shidewa harya rage saura wata daya bikin mu kuma a daidai lokacin muka gama jarabawar semistar farko a ND1 zamu shiga hutu.

Sosia hankalina ya kwanta tunda zancen auren mu da Bashir ya kankama nayi fresh abina na qara kyau da haske musamman ga gyaran jiki da tuni Hajia Umma ta fara tsuma nan da nan jikina ya sake mudewa ko ina ya cika bazaka taba iya mun kallo daya ka dauke ido ba se ka qara.

Bashir kansa wani lokacin idan ya kalleni yakan ce “anya Ma’u banyi zari ba kuwa ki kalli kanki ki kalleni ai se ace dan aiken ki ne ni” in ya fadi haka se nayi dariya nace
“Kai dai ka godewa Allah kadai dan shi yake yiwa bawa kyauta irin wadda beyi zato ba.

Ana biki saura sati uku aka kawo Lefen Junaidiyya daga Birnin Tarayya Akwati na dukan Akwai saiti hudu masu shida shida. Kaya kam sedai ace masha Allah dan komai yaji harda danqareriyar sarqar gwal dinta yar dubai ga kudin da suka doro akai dubu dari haka dangi a ka dauka ana ta murna yarinya tayi Goshi sati daya zagayo aka kawo na Yah Fati da Yah Bilki rana daya suma bangaren kowanne sunyi Bajinta akwatinan su Dozen Dozen da dubu hamsin hamsin akai.

Na Alawaiyya ne qarshe ana saura Sati daya suma suka dunguma masu algaita nayi maroqa nayi aka kawo sha tara ta arziqi kai komai dai se sambarka mutane anata yabawa kowa fadi yake saura Na Ma’u kowa naso yaga Lefeen ama’u yasan ba qaramin Miji na fallo ba nidai a raina nace kwaji dashi idan ma gulma ce ta qare muku dan ni banji komai ba da ganin Lefen su na taya su murna kuma ban damu ba dan tuni Baffa ya gaya mun yacewa Bashir ba se yayi lefe ba ya nemi gidan da ze sakani kawai, dan haka ma ya bayar da kudi masu yawan gaske yace aje Kano a hado mun duk abinda Amarya zata buqata sannan duk wata hidima zanyi ta biki Alhaji Qarami yace na gaya masa ze bani kudin to me ze dame ni kuwa.

Har satin biki Bashir nata fafutukar neman gida, duk yan gidaje masu kyau idan ya tambaya se yaji kudin ya shallake Aljihunsa gashi kuma a qalla dai yana so ya samarwa Ma’u muhalli me kyau kodan halaccin da akayi masa a zamanin nan adauki Mace kamarta daga irin gidansu a bashi babu lefe ai wallahi an gama masa komai.

Dakyar ya samu wani gida anan unguwar su babu nisa sosai, gidan dukda tsoho ne amma fasalinsa nada kyau 2 bedroom flat ne se babban palour harda Gurin Dining ga Kitchen da dan qaramin store sannan daga waje akwai wani dan palour haka qarami ga bandakin baqi a tsakar gidan se dan fili da ze ci mota daya.

Da yake ginin tsohone sunyi dakunan manya a wadace duk girman gado zasu iya dauka kuma da akwai bandaki a kowanne daki matsalar da babu tiles sumuntine a dakunan palour kadai suka sakawa tiles din.

Tareda Aliyu suka sha buga bugar neman gidan, bayan sun samu bayan ya biya Aliyun yace masa ya kamata ya gayawa Ma’u tunda tun wancan satin take masa maganar gidan dan tuni anje anga na sauran har ma jiya an tafi kafin Abuja da Bauchi na su na cikin Gomben ne yayi saura, da za’a siyo kaya ma da farko Anty Saratu Babbar Yayarsu Mace itace akan yin order kayan daman tafi kowa jin takaicin auran Bashir da za’ayi cewa tayi baza’a siya musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login