Showing 180001 words to 183000 words out of 260321 words
Chapter 61 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
da niyyar barin gurin seta dakata ganin Mijinta ya dage rigarsa yana lalubo kudi daga Aljihun wando.
“Kan bala’i, ba yanzu na tambayeka kudin kacemun baka dasu ba shine zaka dauka ka bawa wannan matar yanzu? To duk munafunci da kitimurmurar da kuke qullawa kai dasu na sani kuma wadda kake rawar qafar akanta cikin shege tayi se naga ta tsiya” Sa’adah ta fada tana kama qugu.
Be saurareta ba ya qirga dubu Ashirin cif ya bawa Addah ta kuwa karba ta hau godiya kamar zata durqusa masa, be saurari zage zageb da Sa’adah takeyi ba yaja motarsa ya bar gidan.
Addah kuwa me Napep ta tare bata tsaya ko ina ba se Asibitin da sukaje jiya dan tana so ta karbo dubu Talatin da biyar dinta data bada kafin Alqalami.
Tsayar da me Napep din tayi, da yake Nurse din ta gane ta tana shiga kai tsaye tace ta ciki na fitowa ta shiga ofoshin likitan haka kuwa akayi tana shiga likita ya dago da murmushi a fuskar sa yana mata sannu da zuwa.
Gaisawa sukayi, ta gyara zamanta tace
“Likita se kaji mu shiru jiya ko? Chanza shawara mukayi abinda ya kawo ni yanzu ma kenan na karbi dubu talatin din dana baka ka riqe biyar din kan ma ladan ajiya”.
Tunda Addah ta fara magana litita ya gintse murmushin da yakeyi, se da ta kai aya kafin ya kalleta yace
“Wane kudi kike magana Hajia? Yaushe kika zo nan kuma kudin ma kika bani” ya fada fuskar sa hade kamar da gaske. Se Addah tayi yar dariya tace
“Lallai likita aiki ya sha maka kai, baka gane ni ba nice fa nazo da yarinyata jiya za’a cire mata ciki kace na bada dubu dari biyu na bada talatin da biyar akan zan taho da cikon idan zamu can inda kace mu same ka din”.
“Inaga dai kinyi makuwa Hajiya, sannan maganar zubar da ciki fa naji kinayi ni ba aiki na bane dan haka ki tashi maza ki nemi wanda kika bawa kudinki tunda wuri ma kafin lokaci ya qure miki”
Ganin fa dagaske yana neman raina mata hankali yasa Addah ta fara daga murya tana bala’i, Nurse din da take bada kayi ce ta shigo da sauri tana tambayar ba’asi likita ya rufeta da fadan akan me zasu ringa barin masu tabin kwakwalwa suna shigo masa, haka ta iza qeyar Addah suka fito tana ji tana gani aka korata waje ta ringa Allah ya isan kudinta har suka je gidan Dada inda tace me Napep ya kaita.
Dada na zaune a tsakar gida abin duniya ya taru ya mata karo, Gaba daya bata jin dadin zaman gidan saboda yanda Alhaji ya dauke mata wuta. Naziru da Sa’adu daman tuni sun dena wunin gidan bacci kadai yake dawo dasu ga Fainusan da suke dan harkoki tare itama ciwo ya lafketa tun jiya da akayi maganar fasa auranta take kuka seda zazzabi yayi mata ligib sannan ta haqura.
Zaman da tayi a tsakar gidan ma wayar Bashir da ta manta rabon da suyi magana take ta kira amma baya dagawa. Sababin da Addah ta shigo tana yi ne ya sakata janye tagumin tana kallon qofar shigowa.
A kurar kusada Dadan ta zauna tana tsinewa me Napep din daya dakkota akan wai ya tsuga mata kudi ita bataga zaman jiran da yayi mata a Asibiti ba.
Kallonta kawai Dada takeyi da akwatunanta data ga dai mitar bazata qare ba taja Numfashi tace mata
“Ina zaki haka da Akwati niqi niqi Addah?”
Kamar wadda aka tunawa se kuwa Addah ta fashe da kuka tana cewa
“Dole ki ganni da Akwatu Nafi, Murtala ya sake ni sannan ya koroni. Dakansa ya shiga ya hadomun kayana Nafi saboda tsabar wulaqanci” se kuka.
Salati Dada ta ringayi tana tafa hannu tace
“Yanzu shi Babansu Amirah me yayi zafi haka? Akayi haqurin kusan shekaru hamsin ma se na dan taqin da yayi saura kai amma wannan abu beyi dadi ba, Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri”
“Wane Alkahiri ne acikin saki Nafi? Nidai yanzu idan Amadu yana ciki ki masa magana ya roqar mun arziqi Alhaji yayi haquri ya mayar dani dan gaskiya ba zan saku ba, tsofai tsofai dani naje ina nace ansake ni? Da can banyi zawarci da jajayen sawu ba se yanzu da girma ya cimmani bani da sauran mamora wallahi baze yuwu ba”.
Nan suka shiga Daki Dada ta hau hada mata abin kari kafin Alhaji Amadun ya dawo. Se gurin sha biyu ya shigo daga dubiyar da be samu sunje jiya da Sa’ad dinba, tun daga tsakar gida yake jiyo maganar Addah ya girgiza kai a ransa yace
“Tazo kenan, koda wace fitinar take tafe yau kuma se Allah” ya shige dakinsa ba tareda ya keqa su ba. Ba jimawa Dada ta shiga, bayanin dalilin zuwan Addah tayi masa, cike da jimamin abun yace ta kirawo Addan tana zuwa ta zube a gabansa ta shiga rusa sabon kuka, abin nata kamar tashin iska, tun dazu take warkajamin ta ta manta da an sake ta se yanzu da taga Alhajin ta tuna.
A wayarsa ya kira Alhaji Murtala suka gaisa a mutunce kafin yace masa
“Idan babu damuwa Alhaji akwai maganar da nake so mu tattauna ne ko zuwa dare zan iya zuwa gida na same ka”.
“Indai maganar Fattu ce Alhaji muyita yanzu dan babu buqatar zuwan ka ka sameni” Alhaji Murtaa ya fada.
Se Alhaji Amadu yace “toh idan kace hakan, zan roqar mata arziqi kayi haquri ka mayar da ita dakinta, mata haquri akeyi dasu Alhaji sannan aka iya share shekarun da suka wuce ana haquri se da aka zo gangara tukunna dan darajar Allah kayi haquri taci arziqin zuri’ar da take tsakani”.
“Wato Alhaji bana buqatar na gaya masa wacece Fattu dan sharrin ta har cikin gidan ka ya iso, tunda na aureta kamar qaddara ban taba kwanan farin ciki a rayuwata ba a kullum daga wannan bala’i se wannan zata kwaso mun, yanzu kana gani kaf dangi da zuri’ar mu babu wanda irin wannan qaddara ta taba fadawa se ni a sanadin Fattu kuma to ni kuwa naci gaba da zama da Fattu saboda me indai ba kuma so nakeyi wata rana ta janyo mun Ajalina har gida ba” Alhaji Murtala ya fada, daga muryarsa zaka karanci irin dacin abinda da yake ji a zuciyarsa.
Alhaji Amadu yaja fasali cikin jimami shima yace
“Na sani Alhaji ni kaina shaida ne amma abinda ya faru kaida kanka yanzu ka kirashi da qaddara, kaga kuwa kota sanadin Fattu ko bata sanadin ta ba abinda Allah ya hukunta faruwarsa seya faru da haka ina dai sake roqar mata arziqi, kayi haquri ka maidata dakinta Allah yasa hakanya zamar muku kaffara”.
“Daga yanda ka dage kana roqona na tabbatar bata gaya maka saki nawa nayi mata ba ko? To saki biyu ne. Kasan dama akwai daya tun shekarar dana auro Binta shekaru Ashirin da biyar kenan yanzu na cikashe mata biyu ya zama uku kenan babu kome, taje Allah ya hadata da daidai ita a gaba ni kam Allah ya yaye mun” Cewar Alhaji Murtala.
Se Alhaji Amadu ya juya ya kalli su Dada da suka zauna kamar masu daukar karatu har sun fara jin dadi ko Allah ze sa a dace yace
“Kayi haquri Alhaji, wallahi ban sani ba badan haka ba me ze kaini neman sulhu? Shikenan Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri” ya amsa masa da Amin tun be kashe wayar ba ya fara sauke musu kwandon bala’i ita da Dadangaba daya a kan me zasu mayar dashi mutumin banza bayan sun san saki uku ne.
Hawaye Dada ta fara yi tana rantse rantsen itama bata sani ba ya hadasu yayi musu tatas suka fito daga dakin ko wacce fuska da Hawaye.
A wayar Dada ta sake kiran Alhaji Murtala ya daga cikin masifa yake ce mata
“Ina ganin mutunchinki Nafi karki sake kirana indai akan abinda ya shafi Fattu ne wallahi idan ba haka ba zaku sha mamakina “
“Nice Baban Amirah dan girman Allah kayi haquri, ni ko bazaka mayar dani ba to ka barni naje nayi zaman Yayana” Addah ta fada cikin kuka.
“Wadanne Yayan zakiyi zaman su? Amirah dake gidan mijinta ko kuma Ummi dana Tura Katsina itama data haihu zan daura mata aure dashi uban cikin nata, tsakanina dake Fattu Allah ya isa bazan taba yafe miki ba kin cuce ni ki bata mun zuri’a amma kije dan kanki” yana gama fadar haka ya kashe wayarsa, tana sake kira aka saka mata line busy alamar ya toshe layin ma gaba daya.
Kwananta biyu a gidan Dada sukayi uwar watse ta kama gabanta, Alhaji Amadu kuwa daman ido ya saka musu koda Dadan ta roqeshi akan Addah zata zauna a gidan be hana ba dan ko ba komai Fattu jininta ce babu yanda za’ayi ya raba su amma ya saka musu ido yasan halin su ze raba gashi kuwa tun ba’aje ko ina ba gayyar ta watse.
Gidan Anty talatun dai ta sake komawa, nan din ma bata rufa sati ba sukayi fada qarshe dai har kasuwa tabi Baban su Amirah tana kuka akan ya rufa mata Asiri ya barta tayi zaman Yayanta baqin ciki da takaici kamar ya kashe shi saboda irin wulaqanci da tayi masa har cikin kasuwa fa.
Wani daga cikin abokansa ne ya saka baki akan ya taimaka ya bata gurin zama, dakyar da taimakon Allah ya bata daki daya da bandaki a wani gidan Hayarsa ya kuma ce ze ci gaba da bata ribarta duk wata tunda kudinta ne, taje ta kwashe kayan dakinta tas ta siyar katifa kadai ta bati da yan kayan amfani ta koma gidan.
Haka dai da dadi babu aka kafa zaman zaman take tana ciyar da kanta, ba ta dai haqura ba, tana nan tana tanadi zata nemi duk yanda za’ayi a shawo mata kan Alhaji Murtala ta koma dakinta dan bazata iya wannan zaman ba dan ci uku ba wasa ba.
BAYAN WATA UKU
LAGOS NIGERIA
A cikin watanni ukun nan abubuwa da yawa sun faru na dadi da na rashin sa. A bangaren Ma’u dai Abin dadi ne ya sameta na qarin matsayi data samu a gurin aiki domin yanzu itace babbar manaja gaba daya a sashim su na siye da siyarwa ga kyautar danaareriyar mota da akayi mata da kuma kudin haya da kamfani ya dauke mata banda sauran Alawus kala kala da take samu.
Zuwa yanzu ta rigada ta saduda da komai rayuwarta takeyi ta jin dadi idan ka ganta bazaka iya mata kallo daya ka dauke ido ba saboda yanda hutu da jin dadi suka ratsa ta ta sake zama wata hadaddiyar Mace me aji bazaka taba mata kallon wadda ta haihu har biyar ba tafi kama da irin manyan Yammatan Abujan nan da suka kwana biyu basuyi aure ba.
A yanzu bata da wata damuwa a gabanta idan ba aikinta ba. Tana da isashshan lokacin kanta ta je duk inda take so a sanda taso dan wani lokacin Ranar Juma’a zatayi musu booking jirgi ita da Amnah su tafi Abuja ko Gombe suyi weekend su dawo, tun yaranta na damuwa har zuwa yanzu sun rigada sun saba da rayuwar gida biyu.
Idan tana nan zasuje mata idan bata nan kuwa basa damuwa zasu zauna a gidan su ne kawai tareda Abbinsu daya dawo kamar wata matar kulle daga gida se Office, dan yanzu se anyi dagaske ne zakaga Bashir a qofar gida ma bare ya tafi wani guri.
ASMA’U
Yau ta kama Lahadi na tashi da shirye shiryen tarbar Yusuf daya ce mun ze zo, zuwa yanzu na saddaqar da Yusuf yasan aurena ya mutu dukda be fada mun ba amma yana yin yanda yake kirana a waya dukda ba ko yaushe ba se muyi sati biyu uku kafin ya kirani, amma a duk snada ya kira se ya gaya mun wasu kalamai da zasu saka na rasa nutsuwata na tsahon lokacin da zamu dauka kafin mu sake yin waya.
Tun safe na tashi nake ta shirya abinci, nasan Yusuf a wancan lokacin shima irin Bashir ne suna da son abinci dan haka na tsaya na shirya masa kafiyayyun abinci dukda bansan meya fi so ba amma nasan dole zasu burge shi.
Ina jera abincin akan Dining Bashir ya fado mun a rai, se nayi murmushi kawai a fili na furta
“Rayuwa kenan, sekaga abu ya faru ya wuce kamar ba’ayi ba”.
mamaki nakeyi yanda gaba daya Bashir ya fita daga zuciya kamar wanda aka wanke da ruwa dan idan ba ganinsa nayi ba ko kuma yara sun ambaci sunan sa wallahi mantawa nakeyi da shi a lissafin rayuwata gaba daya.
Ba kuma dan na dena sonsa ba, Aa wannan abune da Allah ya halicci zuciyata dashi kuma na yarda Son Bashir shine Jarabtata amma nayi qoqari na saka kwado na qulle babin sa a zuciyata na kuma dage da kaiwa Allah kukana akan in har Rabuwata dashi Alkahiri ya kawo mun dangana gata kuwa na gani dan yanzu babu wani abu nasa da yayi saura da nake ji a tattare dani.
Saurin kawar da tunanin nayi daga raina daidai lokacin da yaran suka shigo daga sabuwar Islamiyyar da aka sake bude a cikin Estate din Asabar da Lahadi da safe sauran ranakun sati bayan sallar Magriba zuwa Isha.
daman anayi daga baya suka dakatar da ita shine yanzu aka sake ginin sabuwa harda bangaren matan aure dan nima ina shirye shiryen shiga.
Ina ganin sun bar baje a palour na qara sa ina cewa
“Aa ku tashi karku bata mun guri, kodai ku shiga can qaramin palour ko ku fita da kujeru waje dan baqi zanyi bana so gurin ya baci”.
Daya daga cikin daku nan dana mayar musu qaramin palour suka shige Jafar Acici ya shiga Kitchen ya hau bude bude yana cewa
“Mami tun daga farkon Layi fa nake jin qamshin abincinki yawuna duk ya tsinke kuma nasan da kanki kikayi yau ba Yah Amnah bace”.
“To su Acici ai seka shanye yawun naka tunda ya tsinke dan bazan sammaka abincina ba” na fada ina janye Babar kukar dana zuba musu nasu abincin a ciki, magiya ya shiga yi mun da farantinsa a hannu ina dariya wayata tayi qara se na ajiye masa kular ganin Yusuf ne yake kirana na fice daga Kitchen din.
“Badai har ka iso ba” na fada bayan dana amsa wayar,
“Na iso mana gani a qofar gida” ya fada cikin zolaya se nayi dariya nace
“Toh shigo mana, ka tsaya kuma daga waje?”
“Lallai yau dan gata nake har cikin gida aka gayyace ni? To me aka shirya mana ina fatan dai Wannan mutumin baze fasa mun kai ba”
“Kana ina yanzu?” Na tambaye shi ba tareda na amsa masa maganar sa ba dan na rasa dalilin da yasa yake son sako zancen Bashir idan muna magana.
“Yanzu zan fito daga Airport kuma kai tsaye gurinki zan wuto dan ba qaramin kewar Wannan kyakykyawar fuskar taki nayi ba”
“Allah ya kawo ka lafiya” na fada kafin na kashe wayar. Wanka nayi saurin Fadawa, a gurguje na shirya.
Riga da skirt na saka na Atamfa da ya zauna a jikina sosai nayi daurin daya dace da fuskata kafin na bi jikina da sanyayyan turare, ina cikin daura Agogo kiransa ya sake shigowa ban daga ba saboda naji dirar mota alamar ya iso kenan se kawai na dauki gyalen daya dace da kayana na yafa har saman kaina na fito.
Seda nazo tsakiyar palour nayi turus ni kadai, yanzu fa Bazawari na ne yazo kenan zan fita na taro shi ko ikon Allah rayuwa kenan kana taka Allah yana tsara maka yanda yaso.
Fitowa Aliyu yayi daga palour da suke na waiwaya na kalle shi,
“Mami fita zakiyi?” Ya fada yana kallona.
Gaba daya Aliyu ya rikide ya koma Bashir, tsahonsa, tafiyarsa kamanni sa haske kawia ya dara Bashir dan dukda gaba dayansu ba farare bane tas amma suna da haske Farida ce kadai Fara a cikin su kuma ita kadai ce take kama dani amma hatta da muryar su gaba daya iri daya ce haline akullum nake Addu’ar Allah ya banbanta musu.
“Mami” ya sake kirana se nayi firgigit na kalle shi nace “Eh baqo nayi yana waje”
“Baqo kuma Mami? Wane irin Baqo?” Ya tambayeni yana tsatstsare ni da ido.
Sena hada rai ina kallon sa nima nace
“Kaje ka shigo dashi, Uncle Yusuf ne” se na juya na shige dakina ina jin yanda ya bini da kallo.
Ban dade da shiga ba naji an buga qofa, Aliyun ne ya leqo fuskarsa ba yabo ba falla sa yace
“Ya shigo gashi a palour” ya juya abinsa.
Seda na dan ja lokaci kafin na fito, suna zaune gaba daya yaran Banda Aliyu, yanda suke hira ana dariya seka zata sun shaqu ne ko sun dade da sanin sa.
Tunda na fito Yusuf ya zuba mun ido yana kallona har na qarasa kujerar da take kallon wadda ya kai Ahmad ya tashi na zauna kaina a qasa ba tareda na bari mun hada ido ba.
“Mami wai bezo da Little ba” Jafar ya fada kamar zeyi kuka, Dariya Yusuf ya saka masa yana cewa
“Tana can har a bacci kiran Yah Jafar takeyi, sun koma makaranta amma da da ita zan taho daman dan itama tana so tazo gurinka, amma na maka alqawarin da kunyi hutu indai Abban ku ya yarda zan tafi da kai gurin ta idan zan koma”
Murna Jafar ya shigayi yaja qannensa suka nar gurin. Ni mamaki ma ya bani, se kace wanda be taba zuwa Bauchi ba ko kuma duk murnar ganin Little din ne oho.
“Gimbiya Asma’u” Yusuf ya katse mun tunanina, ban san sanda na saki wani lallausan murmushi ba kamar Gimbiyar kuwa ina qara sunkuyar da kai.
“Kinsan irin haka kike fitowa idan nazo zance shekarun baya, banbancin kawai waccen Ma’u kwaila ce kuma tazo tana tunzura mun baki tana hararata wannan kuma babbar macece tanayi mun murmushin da ze qarasa kassara zuciyata” Yusuf ya fada cikin wani irin sauti, se nayi saurin rufe fuskata da tafukan hannayena inajin yanda zuciyata take bugawa kamar zata fito.
“Ya zaki rufe dan Allah ki bude mun naci gaba da kallon kyakykyawar fuskarki kin san kuwa yanda nayi kewarta” Yusuf ya sake fada ya ilahi ji nayi kamar kawai nayi