Showing 108001 words to 111000 words out of 260321 words
Chapter 37 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
kafin ya dawo sun tafi.
Tunda Amirah taga hanya kullum seta zo, abinda na lura shekara shida amma ba'a sakata a makaranta ba kuma duk sauran sa'anninta na gidansu suna zuwa. Dana tambayi Addah dalili tana dariya take cemun
"An kaita fa in gaya miki se tayi ta kuka wai bata son makaranta, ni kuma nace ina dalili tunda bata so yanzu a barta, in ta qara wayo dakanta ma zata ce a sakata".
Mamaki ya kashe ni, wai shekara shida se wani lokaci zatayi wayo ta zauna a makaranta? Abinda na lura dashi daman sam Addah ta sangarta yarinyar nan yanda kasan goyon gwarawa babu kwaba gata da shegiyar rashin kunya ga barna duk abinda ta gani seta lalata abinda yake hadani da ita kenan ma na fara gajiya da zuwan naya dan kullum tazo seta bata mun wani abun.
Akwai randa tazo inada wata yar Aku ta roba me magana, ina son Akun nan tun banfi shekara goma Hajjin su Anty Suhaima ta siyomun ita. A lokacin tace a kantin ita kadai ce tayi saura har Goggo tace baza'a siya ba dan rigima kawai zata zo ta hada a gida idan sauran suka gani amma Baffa yace se an siyowa Mamansa suka kuma yita nema ba'a samu wasu ba.
Tun sannan nake ta boyonta ko wasa bana fitowa da ita ayi kai in kana so kayi wasa da ita sedai mu shiga daki kuma ka biya ni kudi shekararta Tara yanzu na qudure har Yayana se sunyi wasa da ita.
Da yake babu wuta lokacin ni kuma ina Kitchen ina girki sena dakko mata na saka mata batir wai ta samu abin wasa.
Ina Kitchen ina jinta tana magana Akun na maimaitawa, se ji nayi tana qundumawa Akun zagi ita kuwa Aku ta maimaita.
"Yada wasan zagi Amirah ki dena babu kyau" na fada daga cikin Kitchen, se tace "Anty ita ce komai na fada se ita ma ta fadi irinsa" tana gamawa Akuma Ta maimaita.
"Bazaki dena kwaikwayata ba ko" Amiran ta fada caraf Aku ta sake fada itama, se abin ma ya bani dariya, ina shirin in leqo na gaya mata rikodin Akun takeyi duk abinda mutum ya fada itama seta maimaita se ji nayi Amiran nacewa
"Shegiya mahaukaciya wallahi kika sake kwaikwayona sena cire miki kai" ba kuwa ta rufe baki ba Aku ta dauka sena leqo ina cewa
"Ke Amirah bana hana ki zagi ba in banda shirmenki batiri ne da ita tana rikodin...." maganata ta maqale daidai sanda tayi wurgi da Akun nan da qarfin gaske ta daki bango take ta tarwatse komai ya kama gabansa.
Tsabar takaici kasa ko motsi nayi, yanzu Akun da har nagama tawa yarinyar ko kwarzane be sameta ba shine yanzu zata rada mun ita da qasa? A fusace na qarasa inda take na miqar da ita tsaye ina zare mata ido nace
"Amirah bakida hankali me yasa zaki fasa?"
Se kuwa ta wani murguda baki cike da fitsara tace "Na fasa din, ai seda na gaya mata ta dena kwaikwayona harda fa zagina take yi yanzu dana fasa se naga yanda zatayi".
Saboda haushi ban san sanda na kai mata ranqwashi ba, kamar zanyi haqaye nace "kin san shekarun Akun nan kuwa ta ma girmeki amma saboda shegen rashin jinki shine zaki fasa mun ai kuwa sena zane ki yau a gidan gobe ma ki sake yimun barna".
Fincikewa tayi ta nufi gurin Akun, injinta da shima ya cire ta hau tattakewa tana cewa "kika ranqwashe niΒ toh na fasa na fasa din ayi koma menene".
Lallai rashin kunyar yarinyar nan ta isa dole na koya mata tarbiyya tunda bata da ita ai kuwa na jata Kitchen na zari tsintiya na shiga tsula mata a jiki daman rigar ta me kamar Bea ce bata da hannu ai kuwa dukan ya shigeta tana tsalle tana ihu ina tsula mata ina cewa
"Gobe ki sake yiwa wani rashin kunya tunda ke fitsararriya ce". Seda na mata lilis kafin na saketa, ta kwasa da gudu tana kuka ko ta kan Takalminta da Hijab bata bi ba ta bar gidan ni kuwa ko a jikina na tattare fasashshiyar Akuna idona ya ciko da kwallar takaici ganin babu ta yanda za'ayi ta hadu, a kan Centre table na ajiye jin abincina na kamawa a Kitchen.
Ina kwashe abincin Bashir ya dawo, yasan yanda nake son Akun nan da mamaki ya kalli pisis din da suke ajiye ya kwalo mun kira na fito ina masa sannu da zuwa.
"Meya samu Akun taki? waya fasa ta haka?" ya tambayeni yana kallona, se ji nayi hawaye ya silalomin na bude baki da niyyar magana hargagin Addah ya katse ni.
A sukwane ta fado dakin tareda Amirah a bayanta da har sannan bata dena kuka ba tayi tumu tumu da ita qasa har cikin gashinta da naci wuya jiya na gyara mata shi tsaf da niyyar yau zamuyi kitso da gani birgima tayi a qasa.
Ke Asma'u me Amirah tayi miki zaki kama ta kiyi mata wannan dukan kamar kin samu jaka" Ta fada tana hura hanci.
"Ni ba abinda nayi mata Addah kawai dan na fasa waccen shegiyar Akun shine ta kama ta dokeni da zabori" Amirah ta fada cikin kuka kafin Addah tayi wani abu se ji mukayi
"Fuu" Bashir daya fi kusa da Amiran ya dauketa da mari ta kuwa kwala ihu dan marin ya shigeta da gaske.
"Zaki wuce daga nan ko sena tattakaki fitsararriyar banza da wofi, wato ke kika fasa har kina sake fada kuma an hukuntaki shine zakije ki kai qara toh zuwa kukayi a rama miki ko me" ya hayayyaqo mata kamar ze sake rufe ta da duka tayi bayan Addah tana hadiyar zuciya dan tuni kukan nata ya tsaya.
"Idan ita ba'a rama bata ba ai kai seka zo ka dakeni dan ubanka se insan ka isa ka tarewa matar ka fada" Addah ta fada kafin ta juyo kaina tace
"Ke kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake dukar mun Yarinyar idan ma ba cin zali ba akan ta fasa abin wasa kawai ki hau dukan ta to wallahi karki sake" ta juya fuu suka fice ni kuwa na rakata da ido.
"Maganin ki kenan ai da kike jawo yarinyar kece baki san halin ta ba amma Yanzu gashi ta fara nuna miki, mtsw" ya ja tsaki ya shige dakinsa ya barni a tsaye.
Daga wannan abu naja baya gaba daya da Addah dan ba'a fi kwana uku ba se gata da Amiran ta kawo su harda Ummi wai zataje unguwa akayi sa'a Bashir yana nan yace mata muma fita zamuyi ta ringa mita kuwa nidai suna fita na sakawa qofa muqulli to ina dalili yaro yayi maka ba daidai ba in ka hukuntashi a zo har gida a gabansa a ci maka mutunchi to ni banga ana haka a gidan mu ba.
Bata haqura ba dan ba'a rufa sati ba ta kuma zuwa wai tazo duba mu kamar ma ba'ayi komai ba, ranar nayi Farfesun kaji akan da daddare se na soya mana doya muci dashi. Bayan na kawo mata ruwa da lemo na koma Kitchen din, har ga Allah banyi niyyar zuba mata ba dan kadan nayi. Ina da dambun nama harda kilishi su nayi niyyar na kawo musu se ji nayi tana cewa
"Asma'u zubo mana farfesun mana idan da biredi ki hado mun".
Se nayi tsam a Kitchen, a raina nace "ikon Allah" na dai samu dan bowl na saka mata cinya daya da rabin qirji dan fa be kai gudar kaza bama wanda nayi nasan Bashir kadai se ya tashi dashi ma.
Ina ajiye mata ta kalli kwanon, se cewa tayi "meye wannan kika zubo haka, a gidan dan nawa a kawo mun wani abu kamar na roqa, matsa nan ki gani" ta miqe se gani nayi ta shige Kitchen abinta, ina tsaye ta dawo da kular naman dukka da biredin dana manta ban dakko mata ba ta zauna ta hau ci ta nayi mun hira.
Abinda yafi qarfin ka aka ce seka mayar dashi wasa, haka na zauna ina kallon ikon Allah ta cinye tas har tana cewa wai tayar mata da kwadayi kawai yayi. Da zata tafi babu kunya tace idan muna da danyan nama na bata, na shiga Kitchen zan debo mata se gata ta biyo bayana, ta debi kwai, taga kayan miya suma ta diba nidai na saka mata kaza daya a leda daga yanda ta karba nagane kamar ta raina ne nayi saurin tare ta da cewa
"Daga gidan gonar Baffan mu aka kawo mun, kinsan idan ya fitar da kaji yana rarraba mana da kwai" se tayi wata yar dariya tace
"Au uhm kunji dadin ku kuwa" mukayi sallama ta tafi. Ina sane na mata haka dan karma tayi zaton dan nata da take iqirari ne yake siyowa bare har tayi iko dasu, daga gidan mu aka akawomun dan har yau kayan miya kadai Bashir yake siyowa sedai idan munyi sha'awar jan nama ya siyo danye ko gasashshe saboda tunda muna da komai na cefane kamar ma bama taba kayan garar nan, sannan kaji basa yanke mun da kwai.
Idan na aika a siyomun a gidan gona Baba Idi Manager kyauta yake bani ko a bani ninkin na kudin dana bayar.
Da naci da komai Amirah ta dawo zuwa tun Bashir yana fada shima har ya haqura sauqin ta daya mun koma makaranta dan haka bana zama Asabar da lahadi ne kawai take zuwa shima daga baya na takurawa Bashir akan yaje ya samu babanta yayi masa magana akaita makaranta haka akayi kuwa aka sakata har Islamiyya ma shikenan muka samu sauqin abun.
Watan mu shida da aure ranar da safe ina zaune Yah Bilki ta kirani take cemun wai Goggo ta haihu, a kwance nake amma seda na miqe zaune nace "kinsan me kike fada kuwa haihuwa fa kika ce wace irin haihuwa ana zaune lafiya yaushe ma ta samu ciki?"
"Wallahi dagaske, ni kaina bakiji yanda nayi mamaki ba amma kuka fa nayi zargin haka dan zuwan da nayi na qarshe nidai naga cikin amma se nayi zaton ido nane wallahi yanzu Su Bilal suka zo suke gaya mun munyi Auta"
"Ikon Allah amma yanzu dan Allah wace irin haihuwa ce haka yaya nayi suma suyi gaskiya daga wannan an gama" na fada se Yah Bilki tasa dariya tace
"Se ki gayawa Baffan ki ai bani ba, nidai gobe zanje naga Baby kefa?"
"Nima in na taso makaranta inaga in biya goben yanzu dai ai bazata kori mutane ba ko daman abinda bata so a gani kenan yasa take kora ta in naje" na fada ina dariya, se tayi dariya itama tace
"Yo ai sanin hali, yanzu da kin sani har na America tuni da labari ya tarar dasu, shikenan se mun hadu goben" mukayi sallama.
Bashir na dawowa na gaya masa ina ta mita dan me Goggo zata haihu shida cikanki be qara ce mun ba tunda yace Allah ya raya.
Washe gari kuwa daga makaranta gida na wuce, abin Allah ina ganin yarinyar naji ta shiga raina, haka na tasa Goggo a gaba kamar wata kakata da zolaya data gaji ma daki ta shige ta barmu Baffa kuwa se nan nan yake da Yar Babyn me kyau da akayiwa Huduba da Aminatu muka yi mata laqabi da Amna.
Ranar a gidan muka wuni da yawa munje ga matan yayyen mu maza da muka tashi tafiya kowa ta kama hanyarta a motarta muka fito tareda Yaya Fati ina cewa "Bari na biki ki sauke ni a gida toh tunda kece yar hanyar mu" daidai mun qaraso inda Yayan mu na biyu a gidan Alhaji Yasir yake tsaye yana waya.
Muka gaishe shi har mun gota ya tsayar dani sena dawo.
Seda ya gama wayar ya kalleni yace "ke dawa zaki tafi"
"Yah Fati ce zata sauke ni a gida" na fada ina dan wasa da hannuna dan yafi Alhaji Qarami zafi daukar sa muke kamar shine babban Yayan,
"Ta tafi, kije Bello ya kaiki gida, ga wannan" ya fada yana miqo mun kudi da ban san ko nawa bane, sena karba nayi masa godiya na juya inda Yah Fati take jirana nace mata
"Ki tafi Kawai, Baban Sharifa yace naje Bello direbansa ya kaini, kinga har kudi nasa mu ma se jibin zaku zo dai ko?"
"wallahi kina sharafin ki yarinyar nan komai aka tashi ace ke wani tausayin ki ake ji a gidan nan bayan babu abinda kika rasa ta wani fannin ma kin fimu jin dadi dan dai ana ganin mu a qaton gida ne kawai, shikenan bari naje dare yana qarayi" muka yi sallama muka rabu.
Kwana biyu dayin haka da daddare muna zaune aka buga get, Bashir ne ya fita ya bude se gashi ya dawo wai gurina aka zo sena zura hijabi nabi bayansa.
Ina zuwa na ga Bello ne direban Alhaji Yasir daya dawo dani ranar nan da wata dalleliyar mota Toyota qirar shekarar baqa dukda dareni amma kana ganin yanda take qyalli.
Gaisawa mukayi nace da Bashir "Bello ne direban Alhaji Yasir fa" se yace "oh ai ban san shi ba.
Key da takaddu Bellon ya miqo mun yana cewa "Gashi Alhaji yace a kawo miki, tun jiya ma naso kawowa wallahi takaddun ne basu kammala ba se dazu, mota fa tayi kyau Hajia Allah ya sanya Alkahiri ya tsare ki da sharrin qarfe".
Tsabar murna bansan sanda na dane Bashir ina dariya ba nace "wayyo dadi munyi mota muma munyi mota"
shima dariyar yake ya riqeni ganin muna neman faduwa Bello ya juya ze tafi irin yaji kunyar nan na tsayar dashi na shiga gida da gudu cikin kudin da Alhaji Yasir din ya bani ranar nan na qirgo dubu biyar na bashi ya ringa kuwa zuba mun godiya ya tafi.
A daren na kira Alhaji YasirΒ nayi masa godiya "Ba komai, ki tabbatar idan kina buqatar wani abu ki ringa gaya mana" ya fada kawai ya kashe wayar.
Na kira Baffa na gaya masa shima yace "Inye yar gatan Yayanta kice se munzo dani" nayi dariya. Haka na ringa kiran yan gidan mu ina fada musu abin arziqi kowa ya taya ni murna, badan dare yayi ba ma ba abinda ze hana ni ta fiya gida yanzu na nuna musu, haka nayi bacci da ido daya, bini bini na daga labule na leqa motar nan Bashir se dariya yake mun.ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 35
ASMAβU
Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka akayi rabon gado yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa maβaikata barin aikinsu.
Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu wani aiki daya samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin yazo mana da sauqi saboda Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan abinda baβa rasa ba muke siya irin su kayan miya ko ganye da dai sauran masarrafi dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da suke hannuna na siyo mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun.
Duk sati Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga kuma na man mota da ake hadamun dashi yanzu.
Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan kaishi Asibiti suka tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi kenan dan da kudin akayi duk hidimar Asibitin sa.
Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na cefane gashi a gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana shekarar qarshe a Jamiβa, Afiya tana Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary daga Saβad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke.
Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa na tarar da Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a sannan shi aka zuba masa yaci. Abun ya balaβin daga mun hankali.
Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa biyu, taliya, macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba na hada sannan na tsaya a hanya na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan.
Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar mun da Bashir yana gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai na wuce gidan mu. A can na tarar da Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai nata be isa haihuwa ba ni se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba.
Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole ba kuma shima Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba gaba daya mun barwa Allah shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu muna.
A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe Yola yaje daurin auren Yar Baffa Samaβila.
βMamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida baβ ya fada bayan dana gaishe shi, sena marairaice fuska nace
βBaffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya koβ
βNa sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na sake leqa gidan, ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan Siga Allah ya tsare mu daiβ.
βAmin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwaβ na fada ina gyara zamana. Se ya kalleni yace
βGidan ku Maβu ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu ba wa kuke dashi a fadin duniyar nan