Showing 93001 words to 96000 words out of 260321 words

Chapter 32 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42724

dora nasa akai, wannan dalili da hujjojin da suka kafa masa na cewa daga inda wasu suka fara shiga cikin hukuncinsa tsakaninsa da Ma’u toh raini yazo dan tasan duk sanda ya fada mata abinda be mata ba tana da inda zata kai a tilasta shi ya chanza, wannan yasa shi ya kasa ganin kyautatawa da duk qoqarin da Ma’u ta ringa yi na son ganin ta wanke kanta.

Se yake ganin duk ihu ne bayan hari, ta rigada tayi abinda tayi dan tayi ta nuna wa duniya be isa ba shi kuwa yayi Alqawarin bazata ga gazawarsa ba dan haka su zuba su gani da kanta zata haqura tace ta bar aikin nan dan babu gudu babu ja da baya.

ASMA’U

Ranar Litinin da wuri na tafi Asibiti dan daren jiya kasa bacci nayi ga zazzabi ga wani ciwon mara dakyar naga safiya. Ina zuwa bayan likita tayi mun tambayoyi kai tsaye ta turani lab inda suka dauki jini na da fitsari suka ce na jira a waje. Minti 30 tsakani Nurse ta kirani dan har an kaiwa Dr result.

Ba qaramin mamaki nayi ba jin wai ciki ne dani dan ko kadan ban kawo hakan ba har likitan tana tsokana ta wai haihuwa Biyar amma na kasa gane alamun ciki. Seda tayi mun scanning, cikin sati 9, magunguna ta rubutamun da zasu taimaka mun da zazzabi da kasalar da nake fama dasu na karba a pharmacy kafin na wuce gida raina qal kamar an mun bushara da Aljanna.

Ada na ce na gama amma yanzu damun cikin nan naji dadinsa sosai dan nasan shine ze zama silar daidata tsakanina da Bashir.

Sanda na koma gidan ya fita daman Amnah yareda sauran yara suka fita taje makarantar ana neman su dan suna shirye shiryen yi musu graduation party.

Ban zauna ba saboda murna duk se naji na warke ma, dakin Bashir na shiga na gyaro shi tsaf na wanke Toilet na saka qamshi, kafin na nemi guri me kyau na ajiye takardar test din Asibitin inda nasan hankalinsa ze kai.

Dakina na koma nima na sake wanka na sheqa kwalliya sosai dana san dole na burge Bashir, Dumamen tuwon da mukayi jiya naci da baqin tea kafin na sakeyin brush na dawo palour na zauna zaman jiransa.

Se gurin sha biyun rana ya shigo, na miqe fuskata dauke da murmushi na nufe shi amma kafin na qarasa ya dakatar dani ta hanyar daga mun hannu se na tsaya din kuwa ina kallonsa ya wuce ni ya zauna akan kujera.

Jiki a sanyaye nima na koma na zauna, idonsa akaina yace “Weekend din nan zaki Tafi Ita kuma Amirah tazo”.

“Wai dan Allah Baban Ali me yasa kake da son tada zaune tsaye? Ina mun gama da wannan maganar ko. Nagaya maka ni bani da matsala da zaman Amirah amma banga dalilin da zesa ni a takurani ace na koma wani waje ba saboda ita, tazo mana kowa ba zaman ta zatayi ba namene se an shiga haqqina wai” na fada ina yatsina fuska dan harga Allah na gaji da maimaita abu guda.
Kullum daga ya zauna zancen kenan Amirah zata zo toh ko Addah ce tazo mana ina ruwan wani.

“Oh hakane, wato kina ganin kin isa kenan a zaton ki dan kin kai qarata ze sa na chanza ra’ayina ne? Ni ba irin namijin da ze zauna yan uwan matarsa suna tsara masa yanda zeyi bane kin kuma fi kowa sanin idan nayi niyyar yin abu babu uban da ya isa ya saka ni ko ya hanani”. Bashir ya fada yana kallon cikin ido na, sena miqe tsaye nima ina kallon sa nace

“Duk abinda zakayi ya tsaya kaina ni kadai karka ce zaka zagar mun Yaya dan ni nasan mutunchinsa kuma ko banza wallahi Alhaji Qarami yafi qarfin raini a gurin ka dan yayi maka abinda duk duniya babu wanda yayi maka shi, ko gani kayi za’a zage shi kamata yayi ace se inda qarfin ka ya qare”

“Ni kike gayawa haka Ma’u ni kike gorantawa cewa Yayanki yayi mun abinda babu wanda yayi mun shi ko?”

Shiru nayi masa dan idan na bude baki nasan bazan fadi abu me dadi ba dan gaskiya Bashir ya qure ni na tabbatar so yake sena zazzage masa galan din rashin mutunchi daga nan se ya juya duk wani laifi zuwa kaina tunda daman neman sanadi yakeyi, ina jinsa yana ci gaba da fadar maganganu son ransa ban tanka shi ba qarshe ma nayi wucewa ta dakina na ina shiga ya biyo baya na yana cewa

“Wato ga mahaukaci ina miki magana kin tafi kin barni a tsaye ko lallai Ma’u kina so kiga asalin kala ta kenan”.

A fusace na juya nace “wace kalar taka ce tayi saura da ban gani ba Bashir, ai duk wata fuska ta ka ka rigada ka gama bayyana mun ita na gani na kuma san da wanda nake zaune dan tsahon shekarun da mukayi a baya Kura ce da fatar Akuya nake zaune da kai. Daman mutane sunyi gaskiya da suka ce baka tantance halin namiji se randa ya qara aure.

Wallahi ka bani mamaki Bashir ban taba tsammanin ka a cikin layin maza masuyiwa matansu butulci ba a lokacin da suka samu wasu.

Dame na rage ka, ta ina na gaza? Dame ita wacce kake fifitawar ta fini?
kullum hanqorona na burge ka nayi maka abinda zaka ji dadi amma a koda yaushe sakamakona baya zama me kyau anya ka taba sona kuwa?

Karkasa na yarda da cewa ka aure ni ne kawai dan biyan buqatar kanka yanzu da kake ganin ka samu yanda kake so kake neman ka mayar dani bolar da zaka juye sharar ka duk a sanda ka debo ta idan ba haka ba meye laifi na? Ko kuma ni ban cika mace ba nata matancin yafi nawa da yasa kake take nawa haqqoqin dan biyan tata buqatar.

Wallahi Bashir idan baka yi a hankali ba zaka tashi cikin jerin mazan da zasu je lahira da shanyayyen jiki saboda ka gaza Adalci a tsakanin matanka, idan ma kana tunanin idan kayi mun abu zan yafe ko ban kaiwa Allah qarar ka ba Bashir yana kallo kuma se yayi mana hisabi nida ku” nayi maganar cikin muryar da take nuna qololuwar bacin raina dan gaskiya nakai bango na kuma shirya tarar ko menene tunda naga alamar Bashir ya fara daukar kawaicina a matsayin sakarci shiyasa yake kawo mun duk shirmen da yaga dama.

“Ni kikewa fatan na tashi da shanyayyen jiki Ma’u saboda nabaki umarni a matsayina na mijinki kinqi bi?” ya fada muryarsa na rawa idonsa ya kada yayi jajir har wasu jijiyoyine suka fito a cikinsu, banji ko dar ba a raina ba na gyara tsayuwata ina kallonsa ido cikin ido. Se ya girgiza kai yayi kwafa kafin yace

"ASMA'U, ASMA'U, ASMA'U sau nawa nawa na kira sunanki?
Dukda yanda Asma’un daya kirani ya dake ni dan na manta rabon da Bashir ya kira ainihin sunana amma se na dake, hannu biyu na saka na riqe quguna nace

"Sau uku ENGINEER BASHIR AHMAD" dan ni ma fa ba baya bace a fagen iya fitsara, kawai dai shekaru da yanayin rayuwa suka sa nayi sanyi amma a wannan gabar dole na fito masa a ainihin MA'UN BAFFAH ta wadda ya sani shekaru goma sha shida da suka gabata bawai ASMA'U matar Bashir uwar Aliyu, Jafar, Farida, Abdallah, Ahmad da Muhammmad ba.

Qara gyara tsayuwata nayi ina kallonsa ganin yanda yake bina da kallon dana tabbatar na zallar mamaki ne jin yanda ni na kira nasa sunan gaba daya ma Gatsal bako Sakayawa,

Sena saki wani guntun murmushin takaici, lallai Bashir ya manta dawa yake magana, a zatonsa nayi tibis ne ko? be san har yau da saurana ba sedai ba’a tabo ni ba.

Kansa ya girgiza yana qoqarin kokawa da hukuncin da zuciyarsa take ayyana masa, wani sashe na ingizashi akan  yayi inda dayan ke kwabarsa da nuna masa zafa ta iya kwabewa amma idan ya ja da baya ai ma zata raina shi kuma yabi abinda take so kenan.

Kai ba wannan ba raini biyu ma tunda itama ma AMIRAN zata qara tabbatar wa duniya be isa da ASMA'U ba tunda gashi ya bata umarni taqi tabi. Se ya gyara tsayuwarsa tareda qara tsuke fuskarsa da dama can bata da fara'a sam, wani kallo yake jifanta dashi da yasan yana ladabtar da koma waye amma banda wannan kangararriyar Matar. Cikin kaushin murya yace

"For the last time ASMA'U ina baki umarnin kiyi resigning daga aikin ki ki tattara yara ku koma Gombe d....."

"Na gaya maka wallahi Bashir bazan bar aiki na na koma Gombe ba saboda zaka kawo Matarka Lagos" nayi saurin katse shi.

"Shikenan, Se ki zaba ko auranki ko kuma aikinki" ya fada cikin sautin dake nuna qololuwar bacin rai yana harde hannu biyu a qirji yana bina da kallo, daga inda nake ina iya jin yanda yake sauke numfashi kamar wanda ya hadiyi kunama.

Qara jinjina qarfin hali da rainin wayon Bashir nayi a raina, wato ni nice rumfa sha shirgi ko ga Uwar garke wai na tattara yara mu koma Gombe, to kuwa yau na shirya ganin qarshen rainin hankali da duk abinda Bashir yake taqama dashi dan haka nace

"Idan har saboda MATAR KA kake so nabar aikina to na zabe shi BASHIR".

"Haka kika ce"

"Eh Haka na fada”.

Seda ya hadiye wasu qulalai da suka tokare masa maqogaro, kaso tamanin na zuciyarsa yana kwabarsa amma kashi Ashirin ya rinjayi harshen sa

"Kije na SAKE KI SAKI DAYA idan yaso se ki zauna da aikin naki".

Wani irin dummm naji kunnena ya dauka, wallahi wannan kalmar itace mafi munin ji a rayuwata gaba daya, wannan rana tafi kowacce duhu a tarihin rayuwata.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Bashir kasan me ka fada kuwa? dagaske kake" na fada cikin yanayin da ni kaina bazan iya fasaltawa ba

"Oh baki yarda ba? To kije na qara miki DAYA, badan babu kyau ba Asma’u da sena cike miki ukun ki kinga se kiji dadin yin aikin ki dakyau ba tareda nayi miki rashin Adalci ba" ya fada daidai sanda yake ficewa daga dakin.

Wani jari ne ya kwashe ni ya yar akan dake, Allah ne ya rufa min asiri na fada kan gadon da yake baya na. A yanda nake na tabbata in a qasa na fadi babu abinda ze hana barin jikina shanyewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirnifimusinati wa'allifni khairan minha" cikin ikon Allah kalaman da bakina ya shiga maimaitawa kenan jikina yana wani irin rawa tamkar wadda aka jona mun shocking.

Duk yanda naso kwakwalwa ta tayi tunani na kasa dan ji nayi tamkar an saka super glue an liqeta, se zufa ce take ketomun ta ko ina kaina yai dum kafin kace meye numfashina ya fara sama sama ba shiri na fara laluben inda Inhaler ta take wadda sabuwa ce daman dazu dana fita na siyo, dakyar na samota bayan dana zazzage jakar dana fita da ita a qasa saboda yanda nake a rikice jikina yana rawa.

Seda na zuqa sosai sannan numfashina ya fara dawowa daidai amma fa kwakwalwar na nan a toshe. Kai ido na fa ya soye bama alamar Hawaye zasu fito, to kukan maganin me ma zeyi mun?

Ni? ni Asma'u yau Bashir ya saka? Wallahi ko a mafarki naga Bashir ya sake ni nasan shedan ne amma gashi kamar a zahiri hakan ta faru.

Ina cikin wannan yanayin aka sake turo qofar dakin, nasan yarana dukka suna makaranta kuma lokacin tashinsu beyi ba.

Nima dai rabon ganin wannan baqar rana ya saka ni daukar Excuse din rashin lafiya wai dan na huta na zauna da Habibina mu sasanta sabanin da muketa samu a dan tsakanin nan ashe ashe....

"Zaman me kikeyi? Ki tashi kisan inda dare ya miki dan gobe nake so azo a sakawa AMIRAH sabon kaya Zuwa Weekend ita dana isa da ita zata dawo dan haka na baki grace of today ki hada ya naki ya naki kinga yanzu komawa Gombe dole"

kalaman Bashir kenan da suka fi dafin maciji a wurina haka ya juyawa yabarni ni bame rai ba ni ba sumammiya ba.

Dakyar na iya miqewa na rarumi hijabi na, dole na nemi inda zan tsugunna kafin qarewar yau nida yarana. To tunda BASHIR ya iya sakina Allah na tuba watsi dani akan titi kuma ai shi yafi komai sauqi a waje sa.

Kofar gidan na fito ina tunanin ina zan nufa? Flat din da yake jikin namu ido na ya fada, idan ban manta ba Abokin aikin Bashir ne a ciki wanda tsautsayi ya fada masa a ka koreshi daga aiki dole ya saki gidan tunda dama Office ne suke basu dan haka yanzu babu kowa a ciki.

Gidan Baba na shiga dan nasan yana gida kaman yanda Bashir yake nan tunda Office dinsu daya, haka na ringa danna door bell ba saurarawa.

Banyi zaton nayi sallama ba lokacin da Anty ta budemun qofa na nausa kai ciki kawai dan fa bazan iya cewa wallahi ga abinda nakeyi ba ni kaina cikin Sa'a kuwa na tarar da Baban na zaune a palour yana Kallon News, se kawai na isa gabansa na durqusa.

"Hajia Ma'un Bashir" ya fada yana murmushi. haka suke tsokanata kai kowa na Estate din ma haka yake kirana kadan suka sanni da Maman Aliyu wasu kuma suce Maman twins.

"Meya faru" Baban ya sake fada dan se sannan ya lura da yanayin fuskata. Banyi kuka ba amma kallo daya zakamun ka hango zallar tashin hankalin da nake ciki, se kawai na tsinci kaina da cewa

"Baba Flat din Maman Boda zakamun hanya a bani haya na shiga yau dan Allah".

"Bangane ba? Me ya samu gidan naku? Ina Bashir din?" Duk ya jero mun wadan nan tambayoyi da daya kadai nake jin zan iya amsawa dan haka na bude baki dakyar nace masa

"Baba BASHIR ya SA KE NI SAKI BIYU kuma yace na tattara kaya na a yau nabar masa gida kafin ya dawo" na qarasa ina Rushewa da kukan da se yanzu na samu damar yinsa. Kuka nake tamkar raina ze fita inda Baba da Anty keta faman zabga salati suna qarwa.

"Asma'u ya sake ki fa kika ce? Me kikayi masa har haka?” Baba Ya fada bayan daya tashi tsaye ya goya hannunsa a baya, sena dago cikin matsanan cin kukan da nake dan har kamar zan shide nace

“Wallahi Baba banyi masa komai ba, kawai saboda yace na ajiye aiki na saboda Amirah nace bazanyi ba shikenan yace se naje na zauna da aikin nawa”.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, meya ke damun Bashir da ze yanke wannan danyan hukuncin ba tare da shawara ba? Wacece ma Amiran?” Baban ya fada yana kallon Anty da tayi mutuwar tsaye jin musabbabin sakin, cikin tsananin bacin rai tace

“Amma Wallahi Bashir ya isa Asararre yanzu akan wannan tanbadaddiyar yarinyar me zubin Aljanu ya sake ki lallai Namiji se a barshi”.

“Wai wace yarinya ce ina tambayarki” Cewar Baba, se Anty ta kalle shi tace

“Wacece kuwa idan banda wannan yar iskar maci Amanar yarinyar da yayi mata kishiya da ita, shine cin Amanar be ishe su ba yanzu seda suka raba ta da auranta. In sha Allahu se Allah ya saka miki kima dena kuka Alfarmar Annabi se yayi nadamar da bazata amfane shi ba a rayuwa tunda dai shi wawa ne”.

“Ya isa haka Halima wannan wace irin magana ce, ka mata kuje ciki bari naje na ga Bashir din ni” Baba ya katse ta, se ya dauki Glass dinsa na qara qarfin gani da wayar sa ya fita Anty ta zauna akan kujera tana sake tsinewa Bashir da Amirah nidai in banda aikin kuka babu abinda nakeyi.

Sanda Baba ya fita rashin ganin motar Badhir ya tabbatar masa yafita dan haka ya kirashi a waya itama seda ta kusa katsewa sannan ya daga.

“Bashir kana ina ne nazo gida baka nan” Baba ya fada bayan da Badhir ya daga wayar.

“Na dan fita ne” Bashir ya fada murya a cunkushe kamar wanda aka yiwa duren dusa.

“Idan ka dawo kazo ina son ganinka” Baban ya sake fada kafin ya kashe wayar ya koma cikin gida. A inda ya bar mu nan ya tarar damu ina ci gaba da rusa kuka Anty na faman debewa Bashir Albarka.

“Yanzu Halima a maimakon ki tausheta shine zaki zauna kina fadar maganganu kina sake daga mata hankali ko kin kyauta, ki samo mata ruwa tasha, Asma’u kiyi shiru haka, na kira Bashir din yanzu ze zo”. Baba ya fada bayan daya zauna akan kujera.

Sassauta kukan nayi na shiga jan rai ina ajiyar numfashi kamar zan shide, dakyar na dan zuqi ruwan da Anty ta bani dan jinsu nayi sun min daci a baki, na hade kai da guiwa ina ci gaba da hawayen da na kasa tsaida su, wai ni yau aka saka? Ni Bashir ya saka saboda Amirah.

Kusan mintina 30 aka buga gidan, Anty Baban ya kalla kafin ma yayi magana tace “wallahi yallabai bazan bude masa ba, ni gara ka fita can ka same shi a waje dan idan ya shigo zan iya duddura masa Ashar ma”. Se Baban ya girgiza kai kafin ya miqe yaje ya bude qofar da kansa.

Tare suka shigo da Bashir da kallo daya zaka masa kasan ba’a cikakken hayyacinaa yake ba. Idanunsa sunyi jajir sun koma ciki ga jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu. Guri ya samu ya zauna ba tareda ya kalli ko gefen da nake ba, nima sau daya na kalle shi na mayar dakai ina ci gaba da share hawaye na dukkan mu munyi shiru se Baba ya katse shirun da cewa

“Bashir me ya hada ka da Asma’u har ta kai ga yanke irin wannan hukunci mara dadi, koda yake abinda ya faru ya faru dawo dashi bashida amfani dan haka koma menene haquri shine maganinsa dakai da ita duk kuyi haquri ka maida ita dakinta tunda da sauran zama bama se wani ya san Abinda ya faru ba”

Luguden duka qirjina ya shigayi na dago na kalli Bashir ina jiran naji amsar da ze bawa Baban, ina ma ace yace daman wasa yake yimun ba dagaske bane ba. “Daman ana saki da wasa ne” zuciyata ta raya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login