Showing 90001 words to 93000 words out of 260321 words
Chapter 31 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
yan kudade zaki fi qarfina, inaji har fada kikeyi kudi maganin wulaqanci idan mace ta gawurta miji zeyi shakkarta to bari kiji ko kin fi Dangwote kudi ina nan a matsayin mijin ki kuma baki isa na biki ba.
Daman tunda kika fara aikin nan naga halayenki da yawa sun chanza, saboda zan fita nema kema ki fita kina ganin kanmu daya ba? to ya zama dole zan dauki mataki, ki fara shirin ajiye aikin nan”.
Kamar sokuwa haka na ringa binsa da kallo har ya gama magana. Dan Allah meye laifina anan? Daga neman rancen kudi shine ze tado wadannan maganganun haka.
Sena sake matsawa kusa dashi ina cewa
“Yanzu saboda Allah Baban Ali rashin tambayar ka kudi da nakeyi ashe nan ma laifi nake ada da nake tambayar ka kuma cewa kayi ai na ishe ka da bani bani kai bakaga amfanin Kasuwancin da nake yi ba wai dan Allah me yasa ba’a maka gwaninta ne??
Kuma ni a yaushe kaji nace nafi qarfin ka ko ina so ka bini idan dai ba neman tada zaune tsaye ba daga ji mutum yana waya se kace dakai ake baka san hawa ba baka san sauka ba.
Maganar aiki ko kuma wani kudin daban da nake samu kasan idan da tarawa nakeyi da yanzu na kai inda nakai wallahi amma ko na samu jikinka suke komawa tunda kafin na amfani kaina da biyar na amfana wa yaranka da dari. Yaushe rabon da ka dauki sisinka ka bani da sunan wata hidima tawa kota yaran nan?
Siyowar da kakeyi da kanka ma tunda kaga idan ya qare inayi ka sakar mun se sanda ta raya maka sannan zaka siyo ko ka bada kudi a siyayyar.
Idan ba sallah ba na manta rabonda yau Baban Ali ka kawo dankunne kace gashi wannan naki ne kuma kullum kana ganina da sabon abu amma baka taba tambayata a ina na samu ba duk ba sauqin ka bane, idan da bani da abinyi ai duk nauyin a kanka suke”.
“Oh gori zakiyi mun kenan daman ni nace ki ringayi ko ke kika dorawa kanki?
To ki dena, daga yau karki sake saka silenki a hidimar gidana kota yayana ki gani idan bazan iya ba” Ya fada a fusace.
Haka kawai naji zuciyata ta karye wani kuka yana neman taho mun, wai me zanyi na burge Bashir a rayuwa ne? Duk abinda nayi aje a dawo wata rana se ya zama abin fitina, seda na dauke hawayen daya zubo mun akan fuskata kafin nace
“Ko baka fada ba nima bazan sakeyi ba idan yaso seka gani in abin kirki nake maka ko akasin haka” daga haka naja bakina nayi shiru ina goge hawayen da suke zuba daga ido na dan na kasa hana su fitowa.
Meyasa maza ba’a iya musu a rayuwa ne? Idan kika zauna baki nemi na kanki ba a goranta miki idan kin tashi kin nema shima baki tsira ba to ya ake so kayi?
Wayar sa ce ta katse mana shirun da mukayi se ya daga yace “zan kiraki” kafin ya kashe.
Ina lura da yanda yake satar kallona yana zuba tsaki se na dena goge hawayen na barsu kawai suna shata se ya miqe gaba daya ya bar mun dakin yana fita kuwa na fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa.
Bashir
Gaba daya jikinsa yai sanyi da ganin hawayen nata, shi da kansa yasan be kyauta sam Asma’u bata cancanci wani abu a gurinsa ba bayan kulawa da tattali amma dole tasa kashi yin koma menene dan a nasa ganin an fara dakko sare sarin da zata fi qarfin nasa saboda sam ada ai ba haka take ba.
Idan ya gaya mata magana tana ji amma yanzu abinda tasa a gaban ta kawai shi takeyi. Bata yij shawara dashi sedai kawai ta gaya masa zatayi abu kaza in aka ci gaba da haka ai wataran ma se tayi sannan ze sani dan haka ya quduri niyyar kawai ta aje aikin nan tunda shi yake sake bude mata ido tana hulda da manyab mutabe tana ganin rayuwa kala kala.
Kwana biyu a tsakanin gaba daya na dauke masa wuta na fita a sabgarsa na kuma qudurce a raina yar biyar dita Bashir baze sake ci ba. Dakansa ya sakko ya ringa neman shiri dayaga yanda na watsar dashi seda na gara shi kuwa sannan na haqura amma fa ba wai na chanza ra’ayi ba jira kawai nake wata yayi na fara tatike Aljihun Bashir.
Sati biyu tsakani wata ya qare kuma a satin nasan zeje Gombe, ina sane na zauna na rubuta uban list kai harda abinda muke dasu seda na rubuta na hada total dina kusan dubu dari da Ashirin, ana gobe ze tafi ina jinsa yana mitar an qara kudin jirgi seda ya gama na miqa masa takardar ina cewa
“Ga wannan karna manta ka tafi, na manta Gas din mu ya qare shima qaramar cylinder da tayi saura ita aka saka jiya sannan lemon yan makaranta da Biscuits suma babu na manta ban rubuta”.
Takardar ya karba ya duba se ya dago ya kalleni yace “Wannan kudin duk na menene haka kusan dubu dari da Ashirin?”
“Shi yasa fa na rubuta maka komai dalla dalla da kudinsa karma kace qari nayi maka ko wani abu” na fada ba tareda na kalle shi ba, seda yaja wata qwafa kafin naji yace
“Yanzu kudin zan baki kenan?”
“Ka siyo da kanka ma duk daya ne ai” nayi saurin katse shi. Beyi magana ba mintina kadan naji wayata tayi qara alamar shigowar message na jawo na duba Alert ne na dubu dari da Hamsin daga Bashir nayi murmushi nace
“Sun shigo harda qari ma muka samu toh mungode Allah ya qara budi”.
Washe gari ya tafi Gombe.
Weekend din a daddafe nayi shi dan gaba daya bana jin dadi, zazzabin dare ne yake damuna safiya nayi kuma naji garau na bari akan Monday idan be dena ba zanje Asibiti.
GOMBE
Wato wata Irin ladabi da biyyaya Amirah ta ara ta yafawa kanta wanda duk hudubar Sa’ada ce. Jikinta na bari Daman yanzu da yace zezo zataje ta qalqale gida a gyara ko ina dukda dai da taimakon Ummi harda Sa’adan ma suke zuwa wani lokacin sannan idan yazo tana iya qoqari tayi tsafta harya tafi a bangaren girki ne dai har yanzu da saura yana ci yana qorafi dan baya masa kamar na Ma’u.
Wannan zuwan da yayi sosai yaji dadinsa ga tarairaya yana samu da kula kamar wani jariri babu aikin office babu hayaniyar yara.
Butulci irin na dan Adam a yanzu se yake ganin Yafi samun yanda yake so a gurin Amirah musamman da yanzu ta dena masa qorafin da tambaye tambayen kudin da takeyi gashi a karan kanta ta canza sosai komai tana yi yanda yake so.
Suna zauna ana gobe ze tafi tana bare masa Ayaba yana ci ya kalleta yace “kina son zuwa Lagos?”
Sam Amirah bata kawo da ita yake ba dan a bazata maganar tazo mata har seda ya sake maimaitawa kafin tace “Meze hana mana Yaya ai kowacce mace zata so ta zauna kusada mijinta daman, wani gidan zaka samar min kenan”ta fada tana danne zumudin ta, lallai ta yarda kissa tafi Asiri tunda gashi yanzu hankali kwance tana samun abubuwan da suka wahala suka kashe kudinsu a banza akansu.
“Aa ina ganin zaku ringa karba karba ne dan baze yuwu na ajiye ku gaba daya acan ba”.
“Toh Anty fa ya zatayi da aikinta” ta fada tana gyara zama a ranta tana Addu’ar Allah yasa matsala suka samu daman ta lura tunda yazo bata ga sunyi waya ba.
Seda Bashir yasha ruwa kafin yace “Ina ganin zata ajiye aikin ne kawai idan yaso ta cigaba da kasuwancinta kema ya kamata ki samu wani abinyi zaman haka ya isa”.
Tamkar Amirah ta taka rawa haka taji amma ta dake, cikin kisisina tace “Toh yaran kuma fa su acan za’a barsu ko suma nan zasu dawo?”
“No su zasu zauna can saboda School”
“Amma Yaya indai makaranta ce anan ma fa akwai ko wacce iri kake so, ni ba wannan ba ma abinda yafi damuna Tarbiyyar su kasan fa yaran da suka tashi a Kudun nan duk zaka gansu se a hankali ko a gida ana musu tarbiyya tunda kullum suna fita su cakudu da yara kala kala se kaga anayi tana warwarewa. Ni da zakaji shawarata ka dawo dasu nan ga makarantu nan na kudi masu kyau a saka su”.
Shiru Bashir yayi yana tunani, baza’a hadama karantun boko nacan da na nan ba amma maganar tarbiyya tabbas tayi gaskiya abinda yasa ya hana Amna yin Jamb wannan shekarar kenan yace ta bari se next year saboda kafin nan ta dan qara girma da wayo yana tsoron turata Jami’a cikin Yayan Arnan nan.
Su kansu su Aliyun yasan badan Ma’un ma Jajirtacciya bace irin yaran da suke cakude dasu a makaranta da sun debi dabi’un da ba nasu ba.
“Haka ne kuma, shikenan zanyi magana da Ma’un se muga yanda za’ayi”.
Litinin ya koma Lagos da wannan qudurin a ransa. A daren ranar suna cin abinci bayan ya gama ya kalli Asma’u da tunda suka zauna ta kasa cin komai yace “Inason magana dake idan kun gama” ya wuce dakin sa.
ASMA’U
Yana tashi nima nabi bayansa gaba daya jikina baya mun dadi dan haka ina shiga na kwanta akan gado ina jiransa ya fito daga yin Brush.
“Daga Next month Amirah zata fara zuwa nan”.
“Wata sabuwa” na fada a raina, sena miqe zaune ina kallonsa nace “toh ni mene ne nawa a ciki idan Amirah zata zo ko a nan gidan zata sauka ne?”
“Ina nufin ke zaki tafi Gombe idan zata zo, then se ku tsara yanda kuke ganin lokacin da kowacce zata ringayi a nan din”. Ya fada yana zama a gefena.
Yanzu kam na gane inda ya nufa, wato tsohuwar magana ce ta taso kenan yaje ta sake masa fanfo akan tanaso ta dawo nan. Zaune na tashi na jingina bayana da Allon gadon nace “Toh Baban Ali ya zanyi da aiki na kuma? Sannan Yara suma ya za’ayi dasu?”
“Maganar aiki na gaya miki zaki ajiye daman yara kuma dasu zaku tafi duk wadda take Gombe se su zauna a gurinta”.
“Kan uban nan lallai ma” na fada ina kallonsa kafin naci gaba da cewa
“Yanzu saboda matarka tana so ta dawo nan shine zakace na ajiye aiki na amma kasan sam wannan ba adalci bane ko?”
“Ke zaki koyamun yanda zanyi adalci kenan, toh ki dauka duk yanda yayi miki amma na gama magana dole ki ajiye aikin ki Ma’u ki koma Gombe tunda haka na tsara” ya fada yana kallona.
Seda na qare masa kallo dan na tabbatar da gaskiyar abinda yake fada kafin na sassauta muryata ganin dagaske neman rigima yake nace
“Haba Baban Ali, ka manta wuyar dana sha kafin na samu aiki nan, mutum nawa ne suke nema Allah ya zabe ni akan su ya bani amma yanzu lokaci daya kace na ajiye. Da ace muna da Branch a Gombe da babu musu zan nemi transfer in koma can amma yanzu kawai dan kana so ka kawo wata ni kuma seka tauyeni kace na bar aiki na ai bakayi mun daidai ba.
Ni bani da matsala zaka iya dawo da ita ko a cikin gidan nan ne ka bata daki amma dan Allah kabar maganar aikina ina son sa ban kuma shirya barinsa a yanzu ba”.
“Shikenan tunda kina son aiki ki, seki zaba ko shi aikin ko kuma umarnina” yana fadar haka yaja bargo ya rufe har kansa nima sena fice nabar masa dakin.
Sam abin ma dariya ya bani lallai akwai match me zafi a gidan nan to Allah ya bawa me rabo sa’a.
Washe gari tsaf na shirya zan fita aiki, ina tsaye ina barwa Amna sallahun abinda zata girka ya fito muka kalli juna se cewa yayi
“Kiyi mun tuwo da miyar Kubewa da rana za’a zo a karba”
“Naman rago zaki sakawa Miyar Akwai soyayye ma a Freezer seki diba” na fada ina zuge jaka ta dan duk a zatona da Amna yake seda naji yace
“Dake nake ba ita ba, daga yau ma karta sake yimun girki kuma kullum za’a ringa kaimun lunch office” yana gama fada yasa kai ya fita na bishi da saurin. Sanda na fito yana tsaye a jikin motarsa.
“Ban fahimci abinda kake nufi da nayi maka lunch ba ka manta zanje aiki ne” na fada ina kallonsa, idan ya amsa ni to motar sa ma tayi magana, ya kunna mota ya bata wuta, harya taka ya leqo ta window yace
“Banyarda ki dara qofar gidan nan ba” ya qarawa motarsa wuta ya barni a tsaye.
Kamar mara laka haka naja qafafuna na koma cikin gidan, akan kujera na zube ina sauke numfashi, dagaske dai Bashir yake ya na so ya rabani da aikina kenan. Badan ina tsoron Allah da fita zanyi sedai duk abinda ze faru ya faru amma yau zan haqura idan yaso ya dawo naji me yake nufi dani tukunna.
Anty Suhaima na kira ina kuka na shaida mata komai tunda daman da ita muka fara maganar ai, haquri ta bani tace yanzu zata kira Alhaji qarami ta gaya masa duk yanda mukayi zanji ba’a rufa awa guda ba kuwa sega kiran Alhaji Qaramin.
Shima din nasiha yayi mun akan na kwantar da hankali na shedan ne kar mu bashi qofar da ze farraqamu ya tabbatar mun kuma ze kira Bashir din yayi masa magana.
Ban san yaya sukayi ba dan daya dawo be kulani ba fuskar nan dai kamar ta shanu haka muka kwana kamar abokan gaba. Washe gari dan na gwada Sa’a ta na shirya kuma akayi dace tafi kuma mutu be ce dani ba hakan yayi mun dadi alamu sun nuna sunyi magana da Alhaji Qarami kenan kuma ya barni naci gaba da zuwa aiki.
Haka muka cinye sati biyu cir ana wannan yanayin duk iyakar qoqari inayi gurin kyautata masa dayi masa duk abinda nasan yana so amma kallon banza ban ishi Bashir ba bare na arziqi haka idan zan kwana ina masa magana baze daga kai ya kalleni ba ko wani abin yake so sedai ya kira daya daga cikin yaran yayi masa.
Abinda na lura dashi shine harda zugar mutane a cikin abun nasa kuma daman na san Bashir halinsa ne daukar shawarar wasu indai ka gaya masa abinda yayi daidai da ra’ayinsa tofa shikenan.
Haka dai nake lallabawa ina taka tsantsan da duk abinda ze qara mun laifi a gurinsa ga zazzabin da yake damuna kullum qaruwa yake ga kuma sabuwar damuwar Bashir gaba daya na susuce har wata rama nayi,
A bakin Aliyu naji cewar Monday zuwa Laraba su Bashir bazasu yi aiki ba an basu hutu, nan da nan nima na rubuta letter akan bani da lafiya naci sa’a akayi mun approving da wuri dan daman duk wanda ya ganni yaga mara lafiya.
Nan da nan na shiga shirye shiryen yanda zamu gyarota da Bashir dan wannan zaman doya da manjan da mukeyi bayamun dadi kuma a zahiri na fishi cutuwa sedai nima qudurce a raina indai yana tunanin abinda yakeyi ne zesa na sakko na bi ra’ayin sa na ajiye aiki na na koma Gombe ya dakko wata Mata ya kawo nan to kuwa bazan chanza ba.
Idan da ace wani uzuri can na daban yasa ya yanke hakan zan iya karba amma wallahi indai akan Amirah ne a wannan gabar na shirya karbar komai.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 31
BASHIR
Ransa fes ya bar gidan ranar dan ya tabbatar da Ma’u bazata fita batareda izininsa ba. Zuciyarsa ta kasu biyu, wata tana gaya masa abinda yayi daidai ne inda wata take nuna masa kuskuren abinda yake shirin aikatawa kuma kamar rashin Adalci ne.
Shikansa ya tabbatar da aikin Ma’u rufin asirinsa ne kamar yanda ta fada kudin jikinsa yake komawa shida yayansa.
Haka yayita juya abun a ransa har ya isa office, Lokacin da suka fita break kiran Alhaji Qarami ya shiga wayarsa, yayi matuqar mamaki amma daya tuna abinda ake ciki seya goge mamakin.
A mutunce suka gaisa sannan Alhajin ya fara cewa
“Engineer yanzu Suhaima take gaya mun wata magana wai ko ka hana Ma’u zuwa aiki ne ko menene dai, nasan halinsu qilan wani laifin tayi maka koh?”
Kame kame Bashir ya shiga yi yama rasa abinda zece masa, se Alhajin yayi murmushi irin na manya. Yana sane yayi masa haka tunda Suhaimah ta fada masa komai harda dalilin daya saka yace tabar aikin amma yana so ne yaji gaskiyar komai a bakinsa hakan da yayi ya tabbatar masa da son kaine kawai irin nasu na maza ya saka shi aikata hakan.
Seda yayi gyaran murya kafin yaci ga da cewa “Koma mene dai yanzu ina roqa mata arziqin a barta taci gaba da aikinta, kuma koda gaba wani abu ya sake tasowa nine uban Asma’u ni ya kamata ka gayawa zan dauki mataki akai” daga haka dukayi sallama ya kashe wayar.
Sam hakan be yiwa Bashir dadi ba, akan me zata kai qarar sa gurin sa saboda tasan Alhaji Qarami yafi qarfin yayi jayayya dashi ko ya nemi alfarma a gurin sa yaqiyi, yanzu gashi saboda qanwar sa ya sauke kai yana roqonsa bayan ko shi aikin nasa da yake taqama dashi bazar Alhaji Qaramin ce.
Yana hanyar komawa gida suna waya da Amirah Yake gaya mata abinda ya faru
“Amma wallahi Yaya sun ma raina maka wayo, kaida gidanka amma ace dan ka yanke hukunci wani yazo ya warware shi kawai dan suna da kudi se su ringa zuba iko a duk inda suka ga dama, gaskiya seka tashi tsaye koda yake aikin gama ya gama ai tunda har ka bada qofar da zasu ringa yanke maka hukunci a gida kaga gaba baka isa ka sa ko ka hana ba se a kai qarar ka inda akasan bazaka musa ba” Amiran ta fada kafin taci gaba da yi masa fanfo
Da yake abinda yake so ne nan kuwa ya hau kai yayi daram akayi sa’a akayi Sa’a daya tuntubi Bala da maganar shima, da yake duk kanwar ja ce duk irin Abinda Amiran ta fada ya