Showing 30001 words to 33000 words out of 260321 words
Chapter 11 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
work load dina qaruwa yakeyi maimakon ya ragu”.
“Sannu, ki tashi kiyi sallar isha kici abinci ina jiranki” yasa kai ya fice daga dakin
“Aifa Allah ya kawo mu” ta fada tana miqewa ta shiga toilet. Seda tayi sallar sannan ta fita neman abinda zata ci, kadan ta dibi abinci ta dora da fruit salad kafin ta tattare sauran ta gyara komai.
Dakinta ta kima tayi brush ta chanza kayan ta sannan taja qofar ta tafi gurin Bashir. Yana kwance a kan gado ya zubawa pop dakin ido ta shigo, be motsa ba harta ajiye kayan da ta dakko su zata saka da safe tana zama akan gadon wayar sa dake kan mirror ta hau ringing.
Bata motsa ba dan tasan me kiran shima kuma bece ta dakko masa ba dan haushin Amiran yake ji wato se yanzu ta raya mata ta kirashi kenan, jin kiran na yankewa wani na shigowa ya sakashi sakin tsaki ya tashi zaune tare da dakko wayar a fusa ce ya daga da niyyar balbaleta da fada amma kukan ta da kururuwar ta shiga uku da takeyi ya dakatar dashi.
“Ki nutsu malama kimun magana meya faru” ya fada cike da gundura da kukan nata, Amira kuwa dakyar taja fasali ta tsagaita kukaj kafin ta shiga kora masa bayani tana cewa
“Daman Addah ce tun da safe ta tafi gidan Umma Balaraba toh bata dawo ba se dazu bayan La’asar aka kira mu wai tana FMC wasu sun tsinceta a hanya a sume shine suka kaita can” Sabon kuka ta rushe dashi bayan data gama kora masa jawabin kafin qit ta kashe wayar kuma.
Dafe kai yayi yana maimaita Innalillahi, a garin yaya toh meya sameta kuma?
Asma’u data ga yanayin da ya shiga ce cikin damuwa ta shiga tambayarsa meya faru ya gaya mata ita hankalinta ya tashi sosai. Tasan baze wuce a garin shegen yawon qauyukan da take zuwa gurin malamai bane Allah dai yasa ba wani mugun abun ta hadu dashi ba.
Haka suka hadu sukayita jimami bayan Bashir ya kira Naziru shima dai yace masa besan meya faru ba yana zaune Dada tace suje ya kaita Asibitin, kuma dai har yanzu suna zaune Addah bata farfado ba dukda Dr yace babu wata matsala sun dan mata allurar bacci ne ta huta kamar wani abu ne ya firgitata ta shiga tashin hankali.
Sudai sunfi tunanin ko yan kwace ta hadu dasu suka zare mata wuqa tunda ba’a sameta da komai nata ba wayarta ma da aka kira aka fadi tana Asibitin ba’a san waye ya kira ba an kuma bi kiran wayar a kashe.
Haka dai suka kwanta kowa rai babu dadi.
Da safe ma tunda suka tashi yake bige bigen wayar jin yayi jikin nata, ance ta farka tun cikin dare se ihu take tana Allah ya isan kudinta abunda ya qara tabbatar musu da zargin kwace aka mata kenan todai seda aka sakeyi mata Allurar bacci kafin aka samu sa’ida.
Be kira Amira ba seda ya isa office ya dan babbata baki kafin ya sukayi sallama yace ze turawa Naziru kudi koda zasu buqaci wani abun.
Asma’u ma ta kira Dada tayi mata yame jiki ta kuma kira Ummi, shawarar ta kira Amirah ta shigayi da zuciyar ta ko karta kira dan ita ta manta rabon ma da suyi waya tana ga tun lokacin da Amiran kwanta a Asibiti bayan haihuwarta ta farko lokacin tana Adamawa taje gurin Goggonsu se a waya tayi mata sannu dan tacan ta wuto Lagos. Dama ta dade da blocking dinta a whatsapp saboda irin abubuwan rashin mutunchin da take dorawa a status dan Asma’u ta gani, yanke shawarar kiran tayi ko ba komai Ai rashin lafiya na gaba da komai.
Seda wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga murya a dashe tace “Hello” tayi shiru, Ma’u tayi qarfin halin cewa
“Amirah ina kwana yame jiki kuma?” Jin bata da niyyar magana.
Seda na mula sannan kamar wadda akayiwa dole tace “Lafiya da sauqi kuma zata warware insha Allahu se an kammala abinda aka fara idan ma turen wani mugun abun akai mata sedai ya komawa mutum kansa ehe” ta ja tsaki tareda murguda baki kamar tana gaban Asma’un kafin ta kashe waya.
Mamaki ne ya nemi kashe Asma’u a zaune, ita sam bata ma gane kan zancen da takeyi ba illah zallar rashin kunya da taji a muryar Amiran ga kuma kashe mata waya da tayi, daga abin arziqi shine zata mata wannan diban Albarkar?
Koda yake ita ta kai kanta ai da bata kirata ba ai bazata mata ba gobe ma ta sake.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 13
Addah, abinda ya faru waccen ranar.
Kuka riris Addah ta shigayi bayan data tabbatar da cewa Malamin nan dan damfarane, qarin tabbacin data samu tana tsaye wata da ta yankawa kanta kazar wahala ita ma ta zo neman malam Wizy anan suka samu daya daga cikin Almajiran ya fede musu abinda yake faruwa.
Wato dama shi ance aikinsa kenan kuma takamaimai basu san dan wacce unguwa bane. Haka yakeyi duk sanda suka tashi zasu je inda ba’a sansu ba su kama guri idan sun gama cin kasuwarsu ta watse ba zaka san ina sukayi ba.
Haka suka dauki hanya da me Adaidaita tana faman rusa masa kuka batayi aune ba taga yayi kwana da ita wata hanya daban, da taso tayi masa ihu ya zare mata wuqar dake boye a qugunsa dole Addah tayi shiru se yan idanu tana hawaye haka tana ji tana gani seda sukaje inda babu mutane ya kwace jakarta data zubo kudin raguna biyu ga kuma wadanda Hajia Balaraba ta bata na nata aikin duk ya kwamushe harda wayar ta sannan ya buga mata abu akai ta suma kafin ya kwasota ya kawota Asibiti ya tsere abinsa.
Seda ta kwana 4 a Asibitin sannan aka samu kanta ta dena iface ifacen kudinta da takeyi shima se bayan da Alhaji Murtala yayi mata horror sannan ta dauki dangana a fili a zuciya kuwa baqin ciki kamar zeyi ajalinta. Abu goma da ashirin gashi babu damar ta raba baqin cikin da wani ayi mata Allah shi qara dan ko Amirah bata jin zata gayawa bare tsautsayi yasa wani yaji zancen.
Amma fa wallahi an cuceta, Dubunta fa har dari da sittin dan iskan yaron nan ya lashe ga Hamsin din Balaraba. Wai ma wace toshewar basira ce ta same su kai wannan ibtila’i da yawa yake, amma bazata haqura ba wallahi insha Allahu seta nemo wanda ze mata aikin da Wizy ze kawo kansa da kansa ya biyata kudin ta (baki daddara ba ashe 😂😂).
Haka dai tace a sallame ta ta warke suka koma gida taci gaba da jinyar zuciyarta.
Dama damanta ma yanda Bashir yake ta rawar jiki akan ciwon nata, kamar yanda yace ya turowa da Naziru dubu dari yace ayi hidimar Asibiti dan ko babu auran Amirah ai Addah uwa take a gurinsa ze kula da ita kamar yanda zeyiwa Dadansa dan ma dai Addar se a hankali dai, already kuma Alhajin ya biya komai dan haka Nazirun ya danqawa Amirah kudin yace ko zasu buqaci wani abu inji Bashir. Wadan nan kudi ta qudure a ranta da taji dama dama zata kaisu a shaqo mata wuyan wizy kuma (Ai me rabon shan duka baya jin bari dama 😂).
Ganin yanda Bashir din yake ta tasu dan kullum sau biyun nan Safe da Dare se ya kira yaji ya jikinta yasa taga dama ta samu na yadda zata tura Amirah gurinsa, (wai nikam dole ne 😂😂 Allah sa dai ba rabon wahala ke kiran Amirah ba itama). Tunda sun gwada wacceb hanyar bata yuwu ba dan haka suka sake wata.
Sun san yanda Bashir yake da son yara ya kuka kwallafa rai akan cikin jikinta dan haka yanzu shine target dinsu, Addah batayi sanya ba ta karanta mata duk yanda zatayi, da Bashir din ya kira waya zata langwabe yau tace kanta anjima cikin ta, Aa jiri ne yake damu ta shidai se yace mata taje Asibiti ta kuma rage yawan zurga zurga saboda halin da take ciki. Ganin an kwashe sati biyu ana haka be ce ze zo ba ko ita ta tafin yasa suka shirya sabon plan.
Ranar Juma’a data kama Sati biyu kenan rabonsa da Gombe da daddare suna cikin waya tace bari tayi fitsari, bata kashe wayar ba ta ajiyeta akan sink ta dauki hand shower tana tsiyayar da ruwa kaman me fitsari se kawai ta fasa ihu.
Bashir da acan bangare yana riqe da waya yana jiran ta gama ya miqe a sukwane jin ihunta har yana tunkude cup din da Asma’u ta cika masa da Kunun Aya ya tuntsure a qasa take kuwa ya fashe.
“Lafiya meya sameki” ya tambayeta a kidime, seta fashe masa da kukan qarya tana cewa “Jini, jini ne yake zubomun” ta ci gaba da kukan.
Sosai hankalin Bashir ya tashi, idan be manta ba wancan karan da haka ta fara zubar da jini kafin Wani lokaci jaririn ya mutu a cikinta se inducing dinta sukayi ta haihu dan haka yake taka tsan tsan da abinda ze sake janyo faruwar hakan.
“Subhanallahi a garin yaya toh ko kinyi wani abun ne daya fi qarfin jikinki?” Ya tambaye ta
“Nima ban sani ba kuma ni banyi komai ba, dama ba tun yau ba ya fara kawai gaya maka ne banyi ba bana so hankalin ka ya tashi” Amirah ta fada tana sheshshekar kuka, a ranta Addu’a takeyi Allah yasa yace zezo dan wallahi qafarsa qafarta itama se taje an ci uwar da ake ci acan tare da ita.
“Kin gane ki gyara bari na kira Naziru yazo ya kaiki Asibiti yanzu” maganar sa ta katse mata tunani, se ta dan diririce dan bata zaci zece aje Asibitin ba amma kuma idan taqi tasan wata matsalar zata kwantowa kanta in kuma sukaje akaga ba haka ba nan ma ba tsira zatayi ba, daurewa tayi tace masa
“Aa karbar shi dare yayi yanzu kuma bada yawa bane ai da nayi tsarki ma ya dena zuwa, sannan Anty Ramle tana gida (Amaryar babansu Nurse ce) koda wani abu ya taso zata iya taimaka min kafin muje Asibiti”.
Sallama sukayi ya kashe wayar Badan ya gamsu da maganarta ba dai ya qyaleta tunda yasan Anty Ramle tasan aikinta sosai zata kula da ita amma koma menene zuwa safiya dole taje Asibiti dan baze dauki ganganci ba, kai qila gobe ya tafi ma dakansa ya kaita gara in ma wani abune a shawo kan matsalar da wuri.
Tsakin daya sakeyi a karo na ba adadi ya saka Ma’u daga kai ta kalleshi, tunda ya barar da kunun Ayan ta kwashe kwalaben tareda goge Gurin kawai ba tareda ta tankashi ba dan taji duk maganar da sukeyi. A ranta tadan tausayawa Amiran in da gaske takeyi dan dai duk mace tasan wahalar ciki da haihuwa dole in kaga wani dashi ka tausaya masa.
Bata tambaye shi abinda ya faru ba shima kuma be gaya mata ba har sukaje kwanciya, juyi daya biyu ya saki tsaki kai har abin ya fara bawa Asma’u haushi amma ta jure bata tanka masa ba sema danna kanta da tayi cikin pillow ta tilastawa kanta yin bacci. Wai kuma ashe shirun data yi laifine se jinsa tayi yana cewa
“Wai dan wulaqanci kina jina amma bazaki iya tambayata meya faru ba ko?”
“Ikon Allah” ta fada a ranta, a fili kuwa daga kai tayi ta kalleshi sau daya ta juya ta rufe idonta ba tareda tace masa komai ba, ai bashi kadai ya iya miskilancin ba.
Bashir kuwa jin ta masa shiru ya qara tunzurashi, kwafa yayi yana sake zabga tsaki kamar ze katse harshensa, ga damuwar halin da Amiran take ciki ga share shin da Ma’u tayi ta juya masa baya. Wayar sa ya dauka ya shiga duba jirgin Lagos to Gombe a gobe Asabar amma babu dolensa ya haqura, Haka yai ta juye juyensa har shima baccin ya dauke shi.
Asubar fari ya dannawa Amirah kira, tana can tana sharar baccinta har wayar ta qaraci ringing bata ji ba, seda ya kira sau biyu ana uku ta daga cikin magagin bacci.
A tsaitsaye suk gaisa ta tabbatar masa da komai lafiya babu abinda yake damunta yanzu sannan sukayi sallama yana jaddada mata ta shirya anjima Naziru ze zo ya kaita Asibiti ta amsa shi da toh bawai dan zata je din ba to me yake damunta ma.
Suna gama wayar ya maida akalar kiran kan Naziru, gaya masa yayi yaje ya kaita Asibitin duk abinda ake ciki ya sanar dashi sukayi sallama.
Asma’u tana kwance akan gado duk tana jinsa, mamaki take yanda gaba daya ya rikice, ganin yana neman ya hanata baccinta yasa ta miqe ta bar masa dakin ta koma nata ta kwanta.
Har yamma bata san ya aka qare da jikin Amirah ba, ita bata tambayeshi ba shima be mata maganar ba dan wani shareta ma ya shiga yi a dole wai haushin ta yake ji ita abun ma se ya bata dariya. Da yamma ma kudi ya bawa Ahmad yace ya kai mata su fita su siyo abinda suke so shi bazashi ba ta kuwa karbe su ta zuba a jaka suka shige kitchen da yara suka hau yin shawarma suka gasa kaza da zasuci da daren se smoothy na Ayaba daya ji madara.
Ta bayan kitchen dinsu akwai fili da suka gyara ya zama kaman wani garden wurin suka shirya abincinsu, kowa yayi wanka yasha kwalliya kamar masu zuwa wani guri suka haucin abincu ba tareda anyiwa Bashir daya hakince a palour tayi ba. Tunda suka fara gasa kazar qamshin ya fito dashi ya zauna yana jiran a gama a kawo masa amma yaga sun tattare sun tafi baya. Ganin da gaske fa zasu cinye yaja zaune yana jiyo dariyar su cikin nishadi se ya miqe ya tafi gurin ya tsaya a kansu yana muzurai.
Gaba daya suka kwashe da dariya, sunsan dama ba ze iya dauke kai ba Bashir da Nama kamar kura in ya gani se ya ci haka kuwa ya zauna yana zare ido aka ci dashi tas suka dauka pictures kafin kiran magriba ya tayar dasu.
Seda suka zo kwanciya Asma’u take tambayarsa yaya jikin Amiran yace mata da sauqi tayi masa fatan samun lafiya shikenan kuma fushin ya wuce aka shiga sabgogi.
Lafiya lau suka cinye satin, yara sun fara exam ta third term zasu samu hutu me tsaho nan da sati biyu da wannan damar Asma’u take so tayi amfani ta dauki leave ita ma dan ta kwana biyu bata je Gombe ba, sannan tana son zuwa yola ta duba Maman ta da jikinta yake yawan motsawa kwana biyun nan.
Ranar Wednesday daya rage saura kwana biyu kenan yaran suyi hutu, already ta rubuta takardar hutunta har anyi approving tana so ne a ranar friday su wuce Gombe dan babu jirgin Saturday. Da daddare bayan sun gama dinner suna zaune a palour ita da Bashir yaran na dakunan su suna Karatu Muhammmad da Ahmad kuwa sunyi bacci dan su sun gama tasu exam din.
Kallon Bashir dake duba wasu takaddu tayi tace “Baban Ali kayi mana booking flight din kuwa mufa mun gama hada kayan mu”
Ba tareda ya dago ba ya bata amsa da cewa
“Waini saurin me kikeyi ku tafi ku barni ni kadai”
Murmushi tayi kafin tace “ba haka bane, kaga na dade rabona da gida inaso mu dan kwana biyu na zaga dangi ga kuma tafiyar Yola ma gara mu je da wuri ai”
“Hakane” ya fada ya ci gaba da aikin sa.
Gombe
Daga ciwon qarya Amirah ta fara na gaske, haka nan se taji kanta ya sara mata ko in tana tsaye ta fara jin dumm kamar jiri ze kayar da ita idonta ya ringa mata dundumi bata gani da kyau amma Saboda rashin sanin ciwon kai sam bata bawa abin muhimmanci ba ta cigaba da sabgoginta idan ta gayawa Bashir yace taje Asibiti ma bata zuwa Sedai ta karbi kudin a hannun Naziru ta kashe.
A hankali kuma se ta fara kumburi, farko qafarta ce ta fara Se Addah tace mata alamu ne na ciki ya tsufa babu komai ta dai ringa dan tattakawa haka, sau biyu Antu Ramle na mata magana akan kumburin tace ta shirya suje Asibiti amma taqi qarshe ma tace ta dameta ita a rabu da ita ana haka kuwa ta ci gaba da hawa kafin kace me tayi himm ga ciki shima ya qara girma.
Safiyar Friday dakyar dama ta tashi daga kan gado, Addah data shigo dakin take gayawa bata jin dadi tace mata ta daure tayi wanka ta shirya to se suje Asibiti haka ta yunqura ta shiga bayin, wai dan daurewar da jikinta yayi ya warware ta sakarwa kanta ruwa masu zafi gaba daya bayin ya turare kan kace me numfashinta ya fara sama sama yana neman daukewa ba shiri ta yunquro ta fito cikin tsautsayi tana fitowa ta yanke jiki ta fadi cikin tashin hankali suka kwasheta zuwa Asibitin da take Awo.
Lagos
Ranar Friday da zasu tafin yaran basu je makaranta ba dan babu abinda zasuyi takardar hutu kawai za’a basu kuma already an turo musu ta email daman, jirgin qarfe 6pm zasu bi zuwa Gombe amma tun kafin la’asar sun gama komai hatta jakunkunan su sun loda a mota. Se murna sukeyi kamar suyi tsuntsuwa su gansu a Gombe haka suke ji.
Qarfe biyar sukaji tsayuwar motar Bashir dan daman yace ze dawo da wuri ya kaisu Airport sedai daga yanayin daya shigo gidan tasan ba lafiya ba.
“Kuje Mota ina zuwa” ya fada yana shigewa dakinsa, yaran suka fita amma ita se tabi bayan sa. Sanda ta shiga yana waya gaba daya ya birkoto wata shelf daya ke ajiye files dinsa na office da alama wani abu yake nema.
“Ayi duk abinda ya kamata kafin nazo yanzu zamu taho insha Allah” taji ya fada kafin ya kashe wayar ya shiga diban wasu daga cikin filea din daya zubar. Ita ya miqawa yace “Joseph na waje please ki bashi zamu yi waya”
Karba tayi ta fita a ranta tana tunanin meyake faruwa ne toh, haka ta miqawa Joseph files din tana shirin kowa se gashi ya fito bayan ya kulle gidan gurin wutar gidan ya nufa ya kasheta gaba daya, seta kalleshi tana cewa “akwai