Showing 99001 words to 102000 words out of 260321 words

Chapter 34 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42719

na murguda masa baki kafin na shige dan sam bana son Balan nan saboda yana shan Taba nasha ganinsa yanayi ni ban ma san me yasa su Yaya suke kula shi ba.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa muna hira yanda muka saba nake bashi labarin abun da ya faru
“Wani sabon abokin Yaya Abubakar ne yace na dena kuka amma su da duk se dariya ma sukeyi mun” na fada cikin shagwabar da idan ina gaban Baffana jina nakeyi kamar wata yar jaririya zuba tabara nake son raina idan akayi sa’a Goggo na kusa ta make ni.

“Banda dai tsiwa irin ta Mamana ya zaki mari mutum kawai dan yace yana sonki, ki kiyaye kar a sake kuma gobe kuje har gida dasu Alawiyya ki bawa Ibrahim din haquri kinji ko” Baffan ya fada. Sena marairai ce nace “toh Baffa bazan kuma ba.

Washe Gari Alhamis kuwa bayan mun taso boko da yamma babu Islamiyya mukaje har gidan su Ibbah na bashi haquri, da yake yana da sauqin kai yace shi harya manta ma Maman sa se nan nan take dani wai yarinya me kyau da hausarta wata iri ta hado mana kayan dadi muka tafi muna gulmarta wai su a dole turawa.

Muna zuwa qofar gidan mu muka ci karo dasu Yaya Abubakar yau ma su na zaune, gaishe mukayi ina ta satar kallon na jiyan nan daya maida hankali yana danna waya so nake naga ko zeyi mun magana amma har muka shige gida be ko dago ya kalle mu ba.

Baki na tunzura nayi wucewata dakinmu, inajin su Alawa suna cewa nazo mu raba kayan da Maman au Ibbah ta bamu nace bana ci nayi kwanciyata ina jin haushin da ban san koma mene ne ba.

Da daddare Yaya Abu yace na dafa musu Indomie, ina gamawa na juye a flask na bawa Khadija ta kai musu ina zaune a palour Hajia Umma se gata wai naje inji Yayan yana kirana.

Suna zaune a tsakar gida daga gefen inda akayi kujeru na sumunti da tebura, su hudun dai kamar kullum ga kular Indomin a tsakiya an cinye tas Yaya Aliyu ya kalleni yana cewa “wai Bashir ne yace ne yadda ke kikayi girkin nan ba shine muka kiraki ki gaya masa da kanki”

“Wai daman Yaya Bashir kaine” na fada da mamaki ina kallon wanda aka kira da Bashir din. Se yanzu kuma nagane fuskarsa Bashir din gidan Baba me Mota ne, rabon dana ganshi har na manta tunda su ka fara zuwa Jami’a shi aka ce A Zaria ban sake ganinsa ba kusan shekara shida yanzu.

“Daman Fainusa tace Yayansu ya zama dan gayu ashe dagaske take “na fada ina zama a gefen Yaya Abubakar, se Bashir ya dago ya kalle ni yana murmushi yace “dagaske? Har nakai ki gayu?”

Rufe fuska nayi da mayafina irin naji kunyar nan, sosai na ringayi masa tambayoyi meyasa na dena ganinsa yace makaranta ce tasa saboda nisa baya zuwa gida se qarshen shekara, duk sanda yake zuwa mu kuma bama nan munyi tafiya. Haka na shantake seda Goggo ta aiko kirana sannan na tafi.

Tundaga wannan ranar kullum da daddare idan na dafa musu indomi zanje na zauna ina taya su hira kuma duk saboda Bashir dan haka kawai nake jin ina son yin magana dashi, haka ko a cikin gida banida labari se na Bashir yayi Bashir yace kaza ana haka muka fara shirin qualifying exam daga ita zamu shiga SS3.

Bashir ne yake tayani karatu yana ganar dani inda ya shige mun duhu, wannan kusancin da muka qara samu ya saka Shaquwa sosai ta shiga tsakaninmu dan idan na wuni ban ganshi ha har ji nakeyi kamar bani da lafiya gashi lokacin sun fara Service dan ma anan Gombe yakeyin nasa.

Banfarga cewa nayi nisa a soyayyar Bashir ba saboda ban ma san menene so ba, abu daya dana yarda Ya zama wani bangare na jikina haka ina bala’in jin haushin na ganshi yana magana da wata mace ranar haka zan wuni ina qunci.

Yaya Bilkisu ce ta fara haska mun cewa son Bashir nakeyi, nayi futu futu nace qaryane ni ba wani so kawai dai Allah ne ya hada jinin mu amma a qasan raina ina jin dama hakan ta kasance yace yana sona dana ji dadina kuwa.

Mun shiga SS3 kamar anyiwa Samari bushara da zuwa gurina sukayi mun caaa saboda yanda kyau da surata suka sake bayyana sosai, ban kuma canza hali ba ina nan ina tatawa duk wanda yace yana sona rashin mutunchi a qasan raina kuma ina cike da damuwa da takaicin me yasa shi Yaya Bashir baze ce yana sona ba se wannan banzan Balan ne ranar ya wani ce wai yana so na se kace nayi masa kalar budurwar yan shaye shaye.

Muna second term aka fara Registration na Jamb, duk su Alawiyya sunyi ni kuwa ranar da za’a kaisu siyi qin zuwa nayi nace banida lafiya, washe gari da yamma Su Yaya sun shigo gida ake hirar, Ina ji Bashir na tambayar kowa course din daya cike nayi banza dasu sanda yazo kaina har seda Junaidiyya ta tabo ni sena tura baki nace
“Ni ba zanyi ba”.

Kafe ni yayi da idanunsa masu sakani a wani irin yanayi da bansan na menene ba yace
“Me yasa bazakiyi ba?”
“Haka kawai” na fada ba tareda na kalleshi ba, se ya miqe yace na biyo shi muka fita can tsakar gida inda muke zama muna hira.

Idonsa akaina na sunkuyar da kai ina wasa da yatsun hannuna yace mun “me yasa bazakiyi Jamb ba”
“Ni babu komai kawai bana so nayi” na fada ba tareda na kalle shi ba.
“Toh aure kike so kenan?”

Sena dago da sauri na kalleshi, ganin ni yake kallo se na sauke idona ina tura baki nace
“Ni ban ce haka ba”.

“Toh idan ba aure kike so ba me yasa bazaki ci gaba da karatu ba bayan ma ko saurayin baki dashi wa zaki aura ma”.

Harara qasan ido nayi masa kafin nace “Allah ze kawo ne Idan lokacin yayi”

“Idan kuma yanzu ya kawo fa” ya fada cikin qasa da murya, se na daga kai na kalleshi.
“Allah kasa yace yana sona” na fada a raina tamkar kuwa Bashir yaji ni se ji nayi yace

“Idan kuma ni ne mijin naki fa Ma’una zaki aure ni?”

Abunku da ba kwaila tsabar murna se kawai na tashi nabar gurin da gudu ina dariya ina jinsa shima yana mun dariya abinda ba kasafai ya fiya yi ba.

Kan gado na na hau na ringa tsalle ina ihun murna, Yaya Fati Dake kwance akan Nata gadon ban sani ba ta tashi ta rufeni da fadan wane irin shirme ne zanzo ina wa mutane tsalle a gado kamar wata yarinya. Sena fada kanta ina cewa
“Tsallen murna ne Yah Fati ki barni nayi”.

“Murnar me kikeyi” ta tambayeni bayan data daga ni daga jikinta.

“Bazaki gane ba Yah Fati kawai kedai se lokaci yayi” tashi nayi na shige Toilet nayo alwala, inajinta tana cewa Allah ya shirye ni nidai na tayar na ringa jero sallolin godiya ga Allah daya sa Bashir yace yana sona.

Washe gari dakansa ya tasani a gaba mukaje nayi register Jamb, Law na ciki muka gama komai muka koma gida.

A hankali soyayyar mu ta bayyan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina da Bashir. Da yawa gani sukeyi kawai shirme nane haka shima a bangaren Bashir lokacin daya gayawa Aliyu halin da muke ciki se yace masa

“Anya Bashir kana ganin abin nan me yuwuwane?”

“Me yasa kace haka Aliyu” Bashir din ya tambaye shi, se ya ci gaba da cewa

“Kawai gani nayi kamar akwai tazara me yawa tsakanin mu dasu, ka ture abotar mu da Abubakar wannan ba wani abu bane amma ka fahimceni da wuya kaga mace ta fito daga gidan Attajiri ta auri na qasa da ita sedai shi namiji me kudi ya auri diyar talaka, sannan idan ka dubi irin mazajen da yaran gidan su suke auri babu qaramin mutum a ciki ita kanta Ma’u a kalar da Allah yayi mata Bashir ko a gidan talauci ta fito ba matar qaramin mutum me fafutukar neman abinda ze rufawa kansa asiri irin mu bace ba”.

Shiru Bashir yayi dan tabbas Aliyun yayi gaskiya. Shidin ba dan kowa bane Babansa me rufin asiri ne kawai Ma’aikacin gwamnati me da yake dab dayin ritaya kuma ba wani babbaba kusan yanzu shi ake saka ran ya zama jigo a cikin gidan su tunda shine Namiji Babba yayar sa daya da qanne biyar,

a yanzu ne ma ya gama makaranta yake bautar qasa kafin ya fara fafutukar neman aikin yi kuma.

Amma tabbas yana son Asma’u kuma itama ya yarda tana sonsa ba kuma ya fatan ace ya rasa ta.

“Haka ne Aliyu, ka taya ni da Addu’a Allah ya zaba mana abinda yafi Alkahiri toh”

“In sha Allahu, Allah ya sadamu da akhairan mu” Aliyun ya fada.

Wannan maganar da sukayi da Aliyu seta sa ya dan fara ja baya da Ma’u musamman yanda a yanzu kullum yaje gidan ze tarar da zaratan samari yayan masu qunbar susa a manyan motoci sunzo gurin Ma’un duk da bata fitowa amma hakan se yake ganin kamar wata rana zata iya chanza ra’ayi ta zabi wani daya fishi dan haka se yayi baya da zuwa gidan.

Da yake itama suna shirin fara SSCE se bata damu ba dukda indai sun hadu se tayi masa qorafin me yasa yanzu baya zuwa gidan sosai se yace mata aiki ne ya masa yawa dan yanzu ya samu temporary aiki a wani company yana zuwa.

Cikin dan lokaci su Ma’u suka gama Jarabawar su, kamar kuma yanda Alhaji ya saba a shekarar ya kaisu gaba daya suka sauke Farali tafiyar da sukayi kusan rabi da kwatan tsarabar da tayiwo ta Bashir ce harda yan gidansu. Randa suka dawo bata jira yazo ba ta hada akwati guda ta kai masa har gida tayi sa’a ta same su gaba daya yan gidan suna nan harda Alhajinsu dan haka bata zauna ba suna gaisawa ta tafi.

Bayan tafiyarta Su Fainusa suka bude akwatin suna zaro kayan ciki, sosai mamaki ya kama su ganin uban tsarabar se Dada ta kasa haquri tana kallonsa tace “Bashir ni meke tsakanin ka da yarinyar nan haka irin wannan uwar tsaraba data kawo mana?”

Fainusa ce tayi caraf tace “Dada soyayya sukeyi, ina jin a Islamiyya ma Ma’un Bashir ake ce mata”. Se Bashir ya harareta yace “ke waya tambaye ki? Tashi a nan kona mammake ki”.

“Ikon Allah, Anya bata fi qarfinka ba Bashir kaida zaka dauko daidai”

“Daman mace tana fin qarfin namiji ne Nafi?” Alhaji Amadu ya katseta, seta girgiza kai tace

“Gani nayi Alhaji idan ka kallemu ka duba gidan data fito kar ace son zuciya ne yasa ya nemi auranta”.

“To ai Annabi ma yace ana auran mace dan Asali da kuma dukiyarta kinga in hakan yayi ma ba laifi bane ballantana nasan ma ba hakan bane, idan matarsa cea se kiga Allah ya qulla abun, kiyi masa fatan Alkahiri kawai” cewar Alhaji Amadu.

“Hakane Allah ya tabbatar da Alkahiri toh ai Asma’u yarinyar kirki ce”. Daga haka suka ci gana da hirarrakin su.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 33

ASMA’U
Mun rubuta jarabawar Jamb cikin Nasara kuma ko wannen mu ya samu isashshen makin da ze samar masa gurbin karatu a fannin daya zaba yanzu se jiran sakamakon SSCE mukeyi.

A dan tsakanin Baffa ya taramu, daman munsan maganar bazata wuce ta aure ba dan haka tun kafin ranar kowa ta fitar da zabin ranta dan dukkan mu wannan karon yan Aure ne maci gaba da karatun a can.

Da Daddare muna zaune a palour Baffa ni, Alawiyya, Yaya Fati, Yaya Bilkisu se Junaidiyya mune yan candyn Bana, cikin sakin fuskar da Baffa yake da ita a cikin iyalansa muka dan taba hira kafin ya gabatar mana da maqasudin kiran namu.

“Na kiraku ne dan naji ra’ayinku dukda dukkan ku nasan kunyi jarabawar shiga Jami’a me kuka zaba aure ko kuma Bokon za’a ci gaba?”

Seda muka kalli juna muka qara sunkuyar da kawuna kafin muka hada baki gurin cewa “dukka gaba daya muka zaba Baffa”.

Alhaji Qarami da yake gurin ne ya shiga tsokanar mu da cewa “wato gaku cinye du ko zaku ce wani dukka kuka zaba to baze yuwu ba sedai ku dauki daya” se Baffa ya katse shi yace

“Aa bana so karka takuramun yara, shiyasa bana saka iyayenku mata a cikin magana ta dan karma wata ta tilasta su fadar abinda ba ra’ayinsu ba shine kai yanzu zaka zo kana tsokanarsu ko, gasunan se su gaya maka su waye surukan naka idan yaso se ka ci gaba da bincike muga abinda hali zeyi”.

Da daddaya kowa ta fadi sunan rabin ranta, nice ta qarshe harda gyara zamana na bude baki zanyi magana Alhaji Qarami ya tare ni da cewa
“Ai ke nasani Amaryar ta Excellency ko?” (Yusuf kusan abokin Alhaji Qarami ne dukda a shekaru Alhaji Qaramin ya girme masa sosai, yaro ne a cikin manya da Allah yayi masa nasibi sosai a rayuwa, Asalinsa dan Bauchi ne kuma guri daya suke aiki da Alhaji qarami a Abuja tunda yaga Ma’u yace a duniya nan shi yaga mata haka kuwa take garashi kamar kwallo amma be sare ba kullum yana kan binta.
Yanzu haka ya shiga siyasa ne ya tsaya takarar Dan Majalissar Taraiya dan yace se ya kai har shugaban qasa in Allah ya yarda shiyasa suke kiransa da Excellency).

Lokaci daya na hade fuskata kamar ban taba murmushi ba ina kallonsa nace “Ni Bashi bane Alhaji Qarami ai na gaya masa ni ina da wanda nake so”.

“Haba Ma’u yanzu kice bakyason Yusuf duk yanda yake bala’in sonki kullum cikin hidimar ki yake yana hanyar zuwa gidan nan” Alhajin ya fada, sena tunzura baki gaba kaina a qasa nace

“To ni nace yayi mun ne ai tun ranar da ya fara zuwa na gaya masa nacin sa ne yasa kashi ci gaba da zuwan ai”.

Ze sake magana Baffa ya tare shi da cewa “ya isa Muhammadu barta ta fadi zabinta babu dole a al’amarin aure”.

Karkacewa nayi ina murmushi nace “Ni Baffa Yaya Bashir nake so”.

Se Baffa ya kalli Alhaji Qaramin da son qarin bayani, cikin takaicin qin zabar Abokinsa da banyi ba yace “Wai wannan yaron Bashir Abokin Abubakar dan gidan Alhaji Ahmad na qasan layin nan take nufi”.

“Toh toh na gane dan waje Amadu me Mota kenan toh ai babu laifi se aje a cigaba da addu’a Allah ya tabbatar mana da Alkahiri gaba daya”(Inkiyar Baban su Bashir ce saboda ya tabayin Direban Babbar mota yana saurayi tun sannan ake kiransa haka)”.

Godiya mukayi wa Baffa kafin muka fice kowa ranta qal.
“Amma Ma’u baki kyauta ba tayaya Babban Yaya ze miki magana ki musa masa” Bilkisu ta fada bayan da muka yi gaba nida ita, sena kalleta nace “kiji ki Yah Bilki da wata magana, so kike nayi shiru haka kawai a cuceni yanda yake so na auri abokin nan nasa tsaf ze iya zuga Baffa, yanzu kuwa dana fada a gabansa kinga ai nayi maganin abun”.

“Dukda haka da kin sani bari kikayi ki same shi ke dashi ki gaya masa, kuma ni wallahi nafi miki sha’awar Yusuf din ma gashi Kyakykyawa dan gaye ga Kudi”.

“Ai se kije ke ki aure shi nidai bana so” na fada ina harararta, Alawiyya data qaraso gurin mu
Tayi caraf tace “ga ma Uncle Fahad banza duk samarinta na arziqi ta rasa wa zata zaba se wannan me girman kan tsiyar da ita kadai yake yiwa murmushi a gidan nan”.

Hayayyaqo mata nayi ina cewa “Eh shidin na zaba ba’a son Fahad din saboda dan uwanku ne baza’a aureshin ba sedai haushi ya kashe ku, Nida Yaya Bashir kuwa nan gani nan Bari yan baqin ciki sedai su mutu”

“Allah ya baki haquri ni ba da wata manufa na fada ba ta Bashir” Alawiyya ta fada dan ita baiwar Allah ba ruwanta bata iya wa fitinata. Banza na musu nayi shigewata daki ban qara kula kowa ba inajinsu suna ta maimaita zancen kowa aka gayawa se yayi mita na rasa me yasa basa son Bashir.

Idan ma lissafin su bekai sauran manemana Arziqi ba ni wannan baya gaba na dan Arziqi da rashinsa duk nufine na Allah, zaka iya auran mutum yana dashi ya tsiyace ko kuma ka aure shi bashi da komai daga baya ya samu wadatar nidai kwanciyar hankali nake nema kuma a gurin wanda kake so yake son ka kadai zaka same shi.

Dan haka inason Bashir ko a bukkar kara ze ajiye ni na yarda zan rayu dashi har qarshen rayuwa indai akwai so da qauna ba matsala.

Cikin dan lokaci maganar auran mu ta taso kuma a daidai lokacin makarantu suka fara sakin Admission, Alawiyyah da daman ATBU ta saka saboda daman saurayinta dan Sarkin Bauchi ne lokacin har ina tsokanarta nace Allah yasa se ta samu Admission acan kuma yaqi auranta toh Allah ya taimaketa ta samu ga batun aure ma har an kawo kayan nagani inaso na alfarma abinka da gidan sarauta.

Ni, da Yah Fati da Yah Bilkisu harda Junaidiyya duk GSU muka cike su ukun dukka sunansu ya fito a first Batch kowa ta samu course din da take so amma ni har aka saki second batch babu sunana bayan kuma gaba daya ma makina ya fi nasu a Jamb din.

Har aka fara Registration Admission dina be fito ba qarshe har makarantar seda akaje amma wai babu sunana sukace wai sedai a sakani a yan Alfarma a bani wani course din daban nace bana so abarni kawai inda rabo badi sena sake Jamb haka kuwa akayi se Alhaji Qarami yace bazan zauna ba ko Diploma ce naje nayi kafin wata shekarar nan da nan kuwa aka samomun diploma a Computer Science na fara.

An kawo goron Yah, Fati da Yah Bilki suma anan cikin Gombe ne suka samu nasu mazajen duk yayan Babban gida nida Junaidiyya ne ba’a rigada an kawo ba ita dai anzo tambaya Dan Abuja ta samo yaron wani Minister abinda ya dakatar da kawo kudin ma wai Babansa ne yayi tafiya se qarshen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login