Showing 39001 words to 42000 words out of 260321 words
Chapter 14 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
yashiga cikin abubuwa koya kika kuskure se kiga an samu akasi azo ana dana sani nidai a shawara ku haqura nasan kuma shina Bashir din baze bari ayi ba”. Dada ta sake fada ranta fal takaicin Addah.
“Wallahi se Anyi jikar tawa ta fari kuma takwarata kice bazanyi suna ma baqin ciki ma kikemun kenan ko”
“Wane irin baqin ciki kuma Addah nima ai jikata ce ko ban haifi Bashir ba”
“Toh in ma dai hada baki kukayi kedashi yace baza’ayi ba tun wuri ki gaya masa wallahi suna ba fashi ya lalo kudade ya bata da zatayi hidima in ba haka ba rai ya baci” tana gama fadar haka ta juya fuuu tayi ciki.
“Dan Allah Dada muje wallahi ko Yaya ya yarda bazasuyi sunan ba ai dai ni zece nabada kudin ko zamu gani” Naziru ya fada yana huci, haka suka shiga motar suna tafe shida Fainusa suna debewa Addah albarka Dada dai bata iya ce musu komai ba gaba daya ta tafi tunanin meke damun Addah a rayuwa ne. Su yanzu inda hankali ko cewa akayi suyi ai sace Aa amma har tana rantsuwar ae sunyi, to wannan karon zata ja itama bazata takurawa Bashir ba kuma ko sunyi galaba akan sa ya yarda seta hana, zata nuna mata bafa tsoro yasa take mata biyayya ba.
Allah dai ya mana maganin abinda yafi qarfin mu.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 16
Ranar Juma’a Bashir ya dawo Gombe kuma ranar aka sallamo baby Iman, Bashir da kansa ya dakkota bayan da ya dawo dan daman shi ya hana likitan sallamar su akan se yadawo saboda matsawar da Addah tai masa akan zancen shagalin suna.
Amiran bata daddara ba washe garin randa sukayi maganar seda ta sake kira ya kuwa yi mata tatas dan dama sunyi waya da Dada ta gaya masa yanda suka kwashe da Addahn dan haka ya qara tabbatar mata da wallahi ko sisin sa baze bayar ayi wani suna ba idan bata gode rai da lafiyar da Allah ya basu ita da yar ba ta godewa Azabarsa. Ai kuwa itama Addah batayi sanya ba ta karbe waya ta masa wankan tsaf ta kuma sake tabbatar masa fa taron sun ba fashi.
Shekara da shekaru tana rabar da kudin Barka da biki, haka auran Amiran kaman na munafukai basu barta tayi shagali ba yanzu ma a haifar mata jika suce Aa, to kuwa bazata sabu ba shidai ya mata shiru harta qaraci kumfar bakinta ta kashe ya kuwa rangadawa Amirah text din gargadi tunda ga ranar ma be sake kiranta ba idan ma ta kirashi baya dauka se yau Juma’a daya dawo garin suka hadu.
Yaso ma da ya tafi ya karbo yarinyar shi kadai sedai kuma ya tuna Amiran na buqatar a karanta mata yanda zata kula da yarinyar yasa yace ta shirya su tafi se gata ita da Hajia Addah aka shige mota.
Sau goma suka hada ido da Addah se sun jefi juna da harara ita da Bashir can dai da abin ya isheta tace “Bani kake harara ba Bashir Uwarka Nafi da Amadu su kake harara mara mutunchin kawai, kuma duk baqin cikinka suna ne se munyi se dai kayi bindiga ka mutu”.
Kici kanki be ce mata ba har suka je Asibitin, sosai likita yaja kunnensu akan kula da Iman, Banda wanka a tsundumata a ruwa, suna tsaye ya saka Nurse ta kwatanta musu yanda za’a ringa wanke mata jikin shima ba kullum ba musamman yanayin garin sanyi ya kankama.
Sannan ya dora musu da bayanin in so samu ne mamanta kadai zata ringa daukarta kar a jagwalgwalata su tabbatar kuma ko yaushe tana cikin dumi kar ake fitar da ita cikin iska ko sanyi a kula da kayan da za’a ringa saka mata kuma.
Sallama sukayi suka tafi bayan ya basu ranar da zasu dawo ganin likita.
Bashir be yadda ma an dauke ta a hannu ba cikin Baby carrier daya siyo tundaga lagos ya sakata ya dauka Addah ta hau salati da salallami wai ya saka ya a kwando to duk bala’in sa dai ko mayu ne su se ya basu yar in sunje gida tunda ba da ita ze ringa yawo ba,
shida be tankata ba. Seda ya ajiyeta dakyau ya maqala belt din ko ina sannan ya shige ya tada mota har sukaje gida kuwa Addah bata saduda ba se sababi takeyi.
A gidan ma suna zuwa da kansa ya bata feeder ta fara sha dan bottle feeding suke yi kafin ya bawa Amirah taci gaba da bata yana tsaye, seda ya tabbatar tasha yanda ya kamata ya dagata kamar kwan da baya so ya fashe ya sakata a kafada tayi gyatsa kafin ya kwantar da ita a dan gadonta. Seda ya dauketa hoto a wayar sa sannan ya juya.
Kallo daya yayiwa Amirah dake doka uban Murmushi saboda ganin irin tattali da kulawar da yake nunawa yarinyar, ta san yanzu ko Albarkacin Iman seta qara matsayi a zuciyarsa shi kuwa gogan tsaki ya buga ya fice daga dakin dan haushinta yake ji.
Yana fita Addah da jama’arta suka duru daki ganin Baby, kamar me tattaro kaya ta zura hannu zata cukumota Amirah kuwa tayi caraf ta riqe tana cewa “Haba Addah bakiji me likita yace bane shine zaki kawo mata wannan cafkar ai seki ballata”.
Suka kwashi salati ita da jama’arta kafin ta fara masifa tana cewa “Eh lallai yanzu na yarda ba iya Bashir ne tanbadaddenba harda ke, yo in banda tanbada ni uwarki zaki hana na dauketa har ni zaki gayawa kar a karya miki ya, to da ban haihu ba yau se nayi kuka kiji da jinki seda na haifi Goma na binne takwas gaku nan biyu a raye harke ma kinyi yar kanki zaki nunamun sanabe da iyayi”.
Inna Gaji ce ta ceci Amirah tace “Ba haka bane Fattu yanzu dai barta mu kalla daga haka dan Allah abunda in muna da tsahon rai watarana da qafarta zata taka ta hau jikin duk wanda take so” haka aka lallaba Addah kowa ya leqa yarinya dake baccinta masha Allah kyakykyawa da ita kowa se yace ta kwaso kaman nin yayan Ma’u.
Addah dai bata haqura ba seda ta daukota Amirah na kumbura baki tana komai,
“Oh ni Fatu wannan abu kamar yar kyanwa, kwanta karna manta Dan mutum ne nayi jifa dashi” ta fada tana maida yar cikin Gadonta kafin ta harari Amirah data cika baki da iska tayi qwafa ta fita daga dakin.
Bashir kuwa yana fita Part din Ma’u ya bude ya shiga, ya zuqi qamshin da a gurinta kadai ya sanshi dan gidanta na nan dana Lagos qanshi su daya duk kuwa da bata ciki ya rigada ya kama Gurin se a sannan ya tuna dakin masu jegon ma daya shiga kodan Air freshener beji ba bare Turaren wuta.
Wanka ya farayi ya yi sallar Isha da shafa’i da wuturi sannan ya shiga kitchen ko ze samu abinda ze ci tunda can basu bashi ba. ya yi sa’a kuwa cikin Freezer ya samu farfesun kayan ciki dama mutuminsa ne nan da nan ya dumma ya dauki bread ya hada tea ya fara ci. Seda ya kusa cinye wa naman suna ya fado masa a rai, kunsan mutuminku ko kura Albarka nan da nan ya qarasa cinyewa ya dauki waya ya dannawa Amirah kira dan baya so ya koma su hadu da Addah.
Amirah na cikin waya da Tailor data bawa dinki dan tuni ta kai musanyen lace din da aka sako mata na barka ta karbo wani ta bada dinki da sauran kayan da zatayi amfani dasu a lokacin ma tailor yana gaya mata ya gama ne gobe ze kawo ya karbi bakance din kudinsa, ganin kiran Bashir yasa ta cewa Tailor tana zuwa ta amsa wayar da fatan Allah sa Zancen sunan ze mata.
“Kizo ina son ganin ki, ki taho mun da nawa kason Naman” ya fada a taqaice. Seda cikinta ya bada qulululu dan bata taba zaton ze tambaya ba. Tas suka rabe naman nan ko gutsiren hanji beyi saura ba ita yanzu me zata ce masa?
Ai kuwa beci ta manta ba aduk sanda Anty Asma’u ta haihu kasawa yake ya tsare se an cire masa nasa kason, tana kuma yawan jin Asma’un na qorafin daga baya se ya biyo wanda aka aje mata ya cinye ta rasa wane irin so Bashir yakewa Nama a rayuwarsa dukda gashi yanzu ita sun hada sun lamushe.
Haka ta zari mayafin ta ta fita tana taraddadin me zata ce masa, a qofa taci karo da Addah ta dawo daga raka baqin ta.
“Ke kuma ina zaki fita a daren nan da danyen jego” ta fada tana kallon ta ganin ta da mayafi.
“Yaya Bashir ne yake kirana”
“Oh to se kin dawo” Addah ta fada tana rabeta zata wuce se Amirah ta ruqota tana rartaba ido.
“Ya akayi se wani qifta ido kike kamar an kama Kwarto?”
“Addah wai cewa yayi in taho masa da kason naman sa na suna” cewar Amirah.
“To se ki tafi ai” Addah ta fada tana son wucewa ciki.
“Kin manta Addah ya qare fa babu ko diddiga yanzu me zan ce masa”
“Ke dallah matsa ki ban guri se kice masa ya qare ko kice an hada an kaiwa Nafi bashi kenan ba”.
“Addah wace Dadan kuma kin manta itama fa baki basu ba wanda aka ware musu bashi kikace a bawa su Hajia Salamatu ba da suka Zo barka kika ce ta rabawa yan group dinku?”.
Se Addah tayi kasaqe tace “haka ne kuma fa, tab di amma fa mu ma munyi gwari wallahi to yanzu ya za’ayi?”
“Nima ban sani ba” Amirah ta fada tana marairaicewa. Ta tabbatar laifin cinye nasa kadan ne akan idan yaji ko su Dada ba’a aikawa dashi ba.
“Kinga yanzu kije kawai in ya tambaya kice kin manta, idan ya biyo sahu ni kuma zan ce masa Muzuru sun shigo sun cinye bamu sani ba se in nuna masa duddugar bashi kenan ba, shima ai yasan dangin ku da yawa ya wani se miki rago biyu ai yayi kadan” (😳) tana gama fada tayi ciki abinta, nama dai sun cinye ba kuma a isa ace su biya ba.
Amirah kuwa jiki a mace ta shiga palour, ga abinda yake a gabanta amma ta bige da kallon qurilla taga me aka chanza a ciki i lai kuwa taga sabuwar Kantamemiyar Cinema Tv bango guda da Asma’un ta saka kana ganin muatanen ciki kamar zasu fito, sannan ta chanza Dining dinta ba na da bane ga wasu hadaddun Kwanuka akai shikansa Turkish Centre carpet din ba wancan bane kamar.
Kallonta Bashir yake ba laifi ta sace amma bata gama dawowa daidai ba ga cikinta nan haryanzu da girman sa Allah dai yasa kar tayi tumbi dan a duniya ya tsani tumbi a jikin mace kuma da Allah ya taimakeshi Ma’un sa haihuwa Biyar amma har yau bata da tumbi ko dan tana kula da jikinta ne oho?
yanda yaga Amiarn tana kalle kalle yasa ya girgiza kai kawai kafin yace “Malama ko zauna mana kin tsaya mun akai. Zama tayi kan Kujerun da suka dade da tsole mata ido ta kuma quduri niyya itama fa se ya mata irin su yanzu ko ga qarin Dining ma da TV duk irinsu take so itama a siya mata.
Sake gaishe shi tayi ya amsa hankalin sa akan Tv, jin shiru bata miqo masa komai ba ya sakashi kallonta yace “Ina naman” dan fa shi har ya dakko a exotic drink coconut and pineapple dinsa da ze hada ya kora nama seta hau kame kame tana sosa kai tace “uhm uhm daman”
Idonsa akanta yace “malama daman me kin tsaya kina wani kwana kwana in ma wani abu zaki tambayeni bani dashi ki bani namana ki tafi daman kiran da na miki kenan”.
“Ai naman ne ya qare” ta zabi da ta fada masa gaskiya kawai komai ta fan jama fanjan.
“Ya qare?” Ya tambaye ta, se daga masa kai alamar Eh dan ta kasa kuma bude bakinta saboda kallon da yake mata.
Daurewa yayi ya danne bacin ransa kafin yace “ toh kun kai gidan Dada kun bawa Ma’una nata ko?”
“Ai se tafi da rikicewa, kai ta juya masa alamar Aa cikin tsawar da seda ta zabura yace “Malama ki bude baki kiyi mun magana ko”
Jiki na rawa tace “Ni wallahi ban sani ba kasan bani da lafiya su Addah ne suka raba ban san kota kai musu ba dan ni wallahi ko yanka daya banci naman ba”.
Ya tabbatar basu bawa ko daya daga ciki ba kenan, dan haka kawai yace ta tashi taje kafin ya jawo wayarsa ya danna kiran Dada yana saita fushinsa. Bayan ta daga suka gaisa, tambayarta yayi an kai musu naman suna kuwa tace Aa.
“Kar kace zakayi magana Bashir nama dai Allah na tuba kullum ai muna ci, ba wani Abu kasan yan gidan su nada yawa kowa ze so a qulla masa” Dada ta fada da son kwantar masa da hankali dan tasan Bashir da Nama.
Seda yayi kokawa da bacin ransa kafin yace “Amma Dada raguna har biyu manya ne fa ba wai qanana ba su soya su cinye ko yanka daya su kasa kai wa uwata idan ni da na siya banda mutunchin da zasu bani sannan ga Ma’u da yara gaba daya suna cikin gidan a soya duk su kasa basu”.
“Kadaiyi haquri” Dadan ta sake fada kafin su kayi sallama. Ransa a bace ya shiga dakinsa ya kwanta se kuma ya ja wayar ya kira Asma’u dan yau duk basuyi waya ba.
“Ran Alhaji Bashir Baban Ali ya dade” ta fada cike da nishadi dan hirar sa suke yi da Yaya Bilki ya kira. Murmushin da beyi niyya bane ya kwace masa kamar wanda ake watsawa ruwan sanyi yaji zuciyar sa na huce wa, muryarta kadai ta wanke masa bacin ran Naman suna seya gyara kwanciya yana cewa
“Ba wani nan bayan kunyi tafiyar ku ma kin manta dani inaga sena biyo ku sannan zaku dawo”
“Haba dai kwatakwata fa kwanan mu biyar yau cikin weekend muke saka ran dawowa ai” Asma’u ta fada.
“Shikenan ma kinga da kun dawo se mu wuce kawai, na gaji da zaman gwauranta kan nan”.
Dariya tayi kafin tace “oh kana Gombe kenan”
“Eh na shigo dazu, an sallamo Fatima yanzu tana gida”.
“Masha Allah Allah ya raya mata ya bata lafiya, ashe Addah aka saka”.
Da “Amin” ya amsa ya share tambayar ta ta. To me take so yace mata in dai ba son tada zaune tsaye kuma ba.
Yaran ya tambayeta tace sunyi bacci suka dan taba hira kafin sukayi sallama bayan sun gaisa da Yaya Bilkisu.
“Kinji mutuminki nace ashe Addah aka saka yayi kamar beji ba” Asma’u ta fada bayan ta ajiye wayar.
“Kema da neman magana kike wallahi me kike so to yace miki?” Cewar Yaya Bilki
“Me kuwa zece daman kinga ai ta ta uwar tafi tawa a gunsa shiyasa ya saka mata sunanta”.
“To da be saka ba dama Addini ne yace dole ayi ko kuwa da ze zama laifi” cewar Goggo da shigowarta kenan. Muqus Asma’u tayi, dan tasan idan ta tofa wata fada ne zata sha ita kam se taga kamar Goggo tafi son Bashir a kanta ma wani lokacin, bargo taja ta rufe har kanta hankali tacewa Yaya Bilki “idan ta fita ki gaya mun” jin Goggo ta ci gaba da magana.
Seda Goggon ta fita kuwa ta bude tana cewa “Ita Goggo bata san takaicin da ake qullawa mutum ba tayi ta rufeshi da fada, wai fa kinji ma cewa yake idan mun koma se mu bishi mu tafi ni nama fasa tafiya Sunday din sena tabbatar ya koma tukunna. Sati uku mukayi dashi munci biyu se na qarasa sati na wallahi dan har Bauchi nake so Naje wa Alawa sannan naje Jos ma”.
“Ai kuwa da ba kwana zakiyi a Bauchin ba nima da naje Alawiyya har tayi mitar ta gaji ban taba zuwa ba” inji Yaya Bilkisu
“Kai haba dai amma baki kyauta ba wallahi ina Gombe ina Bauch” cewar Asma’u
“Ba haka bane kinsan yawan ci abin zuwan haihuwa ce to kusan tare muke haihuwa kota rigani kona rigata amma daya baya Arba’in to sedai mu hadu a gida”.
“Eh to hakane”. Hira suka ci gaba dayi kafin sukayi bacci.
A Gombe kuwa washe gari Bashir ga haushin cinye masa nama gana tambayar kudi da Amirah tazo ta fara masa da sassafe, buyagin gaske yai mata ya faffada mata maganganu son ransa qarshe ta fita tana kuka da dana sanin zuwan daman Qawarta Husna ce ta tsara mata yanda zataje ta same shi gashi babu biyan buqata se baqin ciki ta kwaso tana shiga dakin ta kuma ta tarar da Addah ta cika baho da ruwan zafi ta tube Iman tana shirin tsumbulata tai mata wanka.
Da mugun gudu Amirah ta tare ta hannun ta ya shiga cikin ruwan da sauri ta cire jin zafin ruwan ta yayimi towel ta nade Iman tana kallon Addah data saki baki da Hanci tana kallonta itama.
“Dan ubanki saboda zan mata wanka shine kika buga wannan tsallen kamar wata yar ball kika kwace ta? So kike a bar ya mace ba wanka kusan sati biyu da haihuwa tayi warin qashi To wallahi ba da ni ba dole a wanke mata dattin mahaifa”.
Ita dai Amira bata kula ta ba, se jijjiga Iman da ke dan kukan da ko muryar ba’aji dakyau take dan ta firgita, jin Addah bazatayi shiri ba yasa tace “wai Addah baki ji me likita yace bane gaskiya idan ba zaki mata irin yanda yace ayi ba ki bar wankan kawai zan nunawa Inna Gaji ta ringa mata. Haka kawai idan wani abun ya sameta ai nice da Asara kuma ji ruwan da kika saka kamar wanda zaki fige kaza”.
Salati Addah ta debo ta dire kafin ta shiga auno mata ashar tana cewa “kiji mun yar banza ni kike shatawa layi akan wannan magen dan bazance mutum ba to kinyi da yar halak in na sake taba ta kice shegiya nake” ta mike tana gyara zani tana ci gaba da banbaminta.
Inna Gaji da shigowarta kenan ta tambayi ba’asi Amiran ta mayar mata seta dubi Addah tace
“Wallahi Fatu kin fiya tada zaune tsaye in