Showing 258001 words to 260321 words out of 260321 words
Chapter 87 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
ne?
Sati daya mukayi muna cin Amarci da tsinke, koda yaushe muna tare sallah kadai take fitar da Yusuf waje dai dai da wayoyinsa ya kashe su komai tare mukeyi, ayyukan gida, wanka bacci koda yaushe ina zaune a jikinta ko muna wasanni kamar wasu qananan yara dan har wasan guje guje muke yi idan mun rasa abinyi sosai shaquwa ta shiga tsakanin mu da soyayyar da ban taba zata zan sake yiwa wani kalarta ba.
Satin mu biyu da aure muka tafi honeymoon, seda muka shafe wata biyu muna zagaya duniya kafin muka yada zango a America yayi wa matarsa sati daya dan ni a hotel nace ya ajiyeni dukda ma bacci kadai yake mayar dashi gidan kusan kullum da ya dakko Ma'u qarama ze taho da ita gurina se dare zasu koma gida har muka cika kwana bakwai kafin muka dawo Nigeria. Cikin kwana uku muka huta aa duk wani shiri da zamuyi, Naje Gombe nayi kwana daya mukayi sallama dasu muka tattara muka wuce Abuja inda muka kafa sabuwar rayuwar mu me cike da Aminci da yarda da juna.
Watanni uku da suka biyo baya bayan Fitowar sakamakon jarabawar su Aliyu Yusuf ya sama musu Scholarship na gwamnatin tarayya shida Amnah suka tafi America inda ze karanci Fasahar Zane zane (Architecture) Amnah kuma Pharmacy, ba'a samu wata tangarda daga Bashir ba dan a gurin Anty Suhaima zasu zauna shiyasa ni kaina lokacin da Yusuf din ya kawo mun maganar fitarsu waje ban damu ba.
Babu dadewa Bashir ya samu izinin tafiya qaro qaratu daga gurin aikin su zuwa qasar Faransa, wannan dalilin ya dawo da riqon Faridah da Jafar hannuna wanda da Goggo ta kafe akan itama sedai a barta a gidan ubanta. Suka tafi tareda Abdallah da yan biyu saboda A lokacin Jafar yana Aji biyar ne a sakandire yace baze bisu ba ze zauna ya qarasa karatunsa a nan dukda rabin zaman nasu gidan Alhaji Qarami ne duk tsarin Goggo ne wai bazasu je agolanci ba.
BAYAN SHEKARA GOMa
ALHAMDULILLAH shine abinda a kullum bana gajiya da maimaitawa tabbas na yarda ba komai da kake so a rayuwa yake zamar maka Alkahiri ba kamar dai Soyayya ta da Bashir, haka abinda kaqi a qarshe idan ka bashi dama yakan zamo wannan Alkahiri da kake ta wahalar neman sa baka samu ba.
Rayuwar aurena da Bashir, shigowar Amirah rayuwar har zuwa rabuwar mu da kumaaurena da Yusuf su kadai sun isa su zame mun izina a rayuwa. A cikin shakaru shida da auren mu da Yusuf ko nace His Excellency Governor YUSUF WUNTI mun samu qaruwar Yaya uku, na farko nayi yan biyu mace da Namiji da suka ci sunan Umar da Ruqayya se Autana Sulaiman da muke kira da Junior.
A tsahon shekarun nan a kullum tsakanina da Yusuf se godiya da sam barka dan ya isa Miji kuma uba da duk mace zata bugi qirji ta nuna shi a matsayin mijinta. Bance babu qalubale a zaman auran mu ba amma fahimtar da muke da ita ta taka muhimmiyar rawa gurin kawo daidaito a tsakanin mu dan koda wasa Yusuf be taba kwana da fushina a zuciyar sa ba haka nima.
Tuni nabar aiki ba tareda wani ya bani shawara ba, dan abin shirita ya zamar mun dole na rubuta resigning na tsayar da hankali na akan gidana na qara bunqasa kasuwanci na dan yanzu kasuwa kam se Hamdala, tuni na sake bude qaton shago a cikin Abuja na zuba kayan yara, da aka kwana biyu na sake bude Salon qaton gaske na zuba ma'aikata duk wani gayar da kwalliya na mata munayi a Gurin kuma Alhamdulillahi komai ya samu karbuwa dan Yusuf da kansa yake sake tallata ni duk abinda nake siyarwa da yaji wani yana nema ko ana zancen za'a siyo a wata qasa zece matarsa tana siyarwa, har tsokanar sa abokanan sa suke idan ana son abu ace
"Wunti Madam na siyar da kaza?"
Duk sanda dayan mu ya batawa dan uwansa, ya koya mun dabi'ar fitowa na fadi abinda yake zuciyata. Idan nayi masa laifi ze zaunar dani ya gaya mun, idan na yin fada ne ze yi mun ya nuna mun kuskure na daga nan gurin maganar ta wuce har Abada zamu koma daidai kamar babu abinda ya taba faruwa a tsakanin mu.
Haka tsakanina da Yan uwansa se sambarka, har bayan rasuwar Hajiyar su shekaru biyu da suka gabata sanadiyyar Hadarin mota daya rutsa da ita sun ci gaba da daukata a matsin Yar uwa da suka bani. Suna girmamani a matsayina na matar Yayansu nima kuma naja su a jiki ina tafiyar da kowa a yanda ya kamata.
Hajiya Intee kuwa lokaci da yawa ma ni mantawa nake ina da kishiya dan a rayuwa idan kuna jin ace mutum Zero tension to Intee kenan, ita dai barta da kallon wulaqanci wanda na lura da cewar dabi'arta ce idan aka zo batun Miji ita auro ni da akayi ma qara mata wani Yanci yayi dan ta sakar mun ragamar komai ban fi shakara ba ta tattaro Ma'u qarama aka dawo da ita Nigeria, shi kansa Mijin se ya shekara beje mata ba se randa ta bushi iska ta kirashi ko ita tazo sannan fa badan ma Allah yasaka Adali bane dana tabbata zuwa yanzu idanbe rabu da ita ba toh tabbas ita da babu zasu zama basu da banbanci a gurinsa.
Bazan gaji da buga misali da Rayuwar Yayana ba wadda a koda yaushe na daga hannu na bana sauke shi ba tareda na roqa musu kariya da shiriya a gurin Allah ba wanda Alhamdulillahi dan ubangiji ya dafamun, ya shirya mun su da shiriyar sa da kuma jajircewa irin ta mahaifinsu dan dole na Jinjinawa Bashir ta yanda abubuwan da suka faru suka zamar masa darasi babba da yayi sanadiyyar daidaituwar rayuwar sa.
Amnah tayi aure ta Auri Naziru qanin Bashir tun taba shekara ta uku a karatun ta yanzu haka suna Can American inda shima ya samu aiki harda qaruwar dansu guda daya Ahmad.
Aliyu ya gama karatunsa ya dawo dukda seda ya hada harda Masters yanzu yana ayyukan kwangila wanda Yusuf yake sakar masa sosai yake nemo masa kwangila daga ko ina dan yanzu sun dinke baka jin kansu, wani lokacin ma zezo Bauchi bazan sani ba sedai kawai Na ganshi yace Dady ne ya kirashi zeyi wani aiki.
Jafar nedai na hannun damana kuma sirikina dan fa hadin nan dagaske zamuyi shi da takwarata data zama budurwa itama yanzu saboda tana da girman jiki, shekaru sha shida idan ka ganta zaka dauka tayi Ashirin dan haka ma Babanta yace da Faridah ta qarasa karatunta ze hadasu yayi musu aure idan yaso ita Ma'u ta cigaba a gidanta.
Yan biyu na dai da Babana sun zama yayan Amarya sedai lokaci lokaci idan sun samu hutu suzo mana, Bashir ya qara aure tun banfi shekara uku da yin aure ba auri Sa'idah Bayerabiya ce yar wani babban Malami a garin Lagos macen kirki data rungumi yayana ta riqe da amana tamkar ita ta haife su.
Fadar irin tashin da sukayi da Amirah ma bata lokaci ne dan har seda tayi sanadiyyar mutuwar auranta tayi zaman shekara daya a gida dan daman akayi sa'a ta dawo Nigeria lokacin haihuwar Yarinyar da Bashir yayi mun takwara da ita wadda daga kanta har yanzu bata qara ba, dan haka koda aka fara dauki ba dadi akan zancen auran nasa a yanda na samu labari har cikin gidan su taje ta ambaci sunan uwarsa da ubansa tace idan ya haifu a cikinsu ya sake ta babu bata lokaci kuwa Dada ta kirashi a waya tace ya saketa Alhaji yace a ta fau baza'ayi haka ba.
Qarshe gidansa na Gombe ta cinnawa wuta ya qone qurmus ko tsinke ba'a fitar ba babu Arziqi ya aiko mata da saki biyu ya kuma saka aka kwace yarinyar bayan daura auransa da Amaryar sa ta wuce da ita Faransa suka ci gaba da rayuwarsu.
Seda taji jiki zawarci shekara shida kafin ya mayar da ita ya barta anan Nigeria cikin gidan su ya gyara mata bangaren Alhajinsu bayan ya rasu take zaune ana gara rayuwa babu dadi babu wahala dan taji jiki shiyasa ta yarda da duk yanda yace dan ko banza bazata taba hada zaman da irin zawarcinda tayi a gidan su ba bata da maraba da boyi boyi, kudin da zata siyi omon wanki ma gagarar ta ya ringa yi gashi ita ba wata sana'a ta iya ba babu kuma wanda yazo koda wasan yace yana sonta saboda yanda labarin abinda ta aikata ya karade ko ina harya gama zawarcin.
Addah kanta da take tsaya mata tayi duk abinda taga dama ta kanta take yi dan ta gamu da wanda ya fita iskanci, malamin daya ce tayi auran kisan wuta zeyi mata aikin da Ahaji Murtala ze mayar da ita dashi sukayi auran akan sati biyu zatayi ya saketa se gashi yanzu ana lissafin shekara kusan Tara kenan harma ta haqura rayuwa ta bida ita tana can wani surquqin qauye ya kafeta ga kishiyoyi uku shegun qauye sun tasata a gaba rayuwar ta kam yanzu ta zama abin tausayi mutum dai kawai ya tsoraci Allah a rayuwa.
Ummi qanwar Amirah tana zaune lafiya a gidan mijinta cikin rufin asirin Allah sun rungumi junansu sun zauna tamkar babu wani abu daya taba faruwa a baya. Hatta da mutanen gari tamkar an shafe musu tarihin abin a zuciyar su babu wanda yake tunawa harta haifi yayanta guda uku yanzu.
Ban manta da Maqociya Aminiyar kwarai Anty Halima ba, itama tuni sun bar Lagos bayan da Baba yayi ritaya sun koma Zamfara da yayanta hufu yanzu dan a jere a jere tayi su tunda Allah ya bude mata hanya, hakan be saka mun yanke zumunchi ba kullum muna cikin waya ko chatting tana sake bani sirrika tana aiko mun da makaman yaqi nima kuma Alkahiri na be taba yanke mata ba, duk wani abu daya tashi na romon damakaradiyya sena sakata a ciki, ga connection da nayi mata da matan abokanan siyasar Yusuf suna siyan kayan Arziqi a gurinta duk wadda ta siya kuwa seta koma sanna ta qara kawo mata wasu shi yasa takance dani
"Ma'u haduwa ta dake ta zame min Alkahiri", na kance d ita
"Anty duk abotar da aka qullata domin Allah daman tana zama Alkahiri me girma fatana zumunchin mu ya dore har gidan Aljanna".
MURFI
Ina cikin Sujjada naji an bude qofar dakina an shigo, nasan Yusuf ne, Dan duk daren duniya ko qarfe nawa ze kai suna Meeting idan sun gama a gida ze kwana, akansa na qaryata cewar da ake yan siyasa basu da lokacin iyalansu dan nidai nawa Mijin yasha banban da sauran.
Kafin yara su fara makaranta ko wata qasar ze tafi qafata qafarsa, har kuma Yanzu indai tafiya bata wuce sati ba sedai na barsu a gida mu tafi balle kuma ace yana gida Nigeria ya kwana a wani guri da ba cikin gida ba gaskiya da wuya.
Seda na sallame na Shafa addu'a kafin na kalle shi ina murmushi nace
"Sannu Excellency se yanzu"
"Kinganni fa Asmy, mutanen nan sun huramun wuta da yawa, ni kuma ina kan bakana bazan yarda da duk wani sharadi mara tushe ba sedai idan zasu kwace tikitin takarar su su karba amma bazanyi abinda zanje gaban Allah na kasa kare kainaba, wai har party chairman ne yake munbarazana, nace masa duk aikin banza ne babu abinda zasu iya wanda Allah beyi ba".
Kusada shi na koma na kama hannunsa nace
"Babu komai ka tsaya akan gaskiyarka, ba abinda ze same ka da izinin Allah kuma seka cika burinka tunda dai kaine akan gaskiya su kuma qarya kuma a koda Yaushe Gaskiya ita take Nasara akan qarya".
"Shiyasa nake qara sonki Asmy ta saboda a duk sanda na rasa qarfin guiwa kina dawo mun dashi, Allah ya gafartawa Hajiya, maraicina kadan ne tunda ina da mace ta gari da bata mantawa dani a cikin Addu'ar ta"
"Amin yah rabbi, ni yaushe za'a bude mun ofishin First Lady ne na qaddamar da campaign dan dai kasan wannan karon baza'a barni a baya ba, First Lady lamba daya ba wasa ba kai wayaga Ma'u a Villa" na fada cikin wasa ian wani buda kafada irin yanda zan ringa tafiya a Villa.
"Ga babban office dinki nan, ai kici gaba da Sallah kina taya mu da Addu'oi dan ina ganin hasken su amma darajarki ai tafi qarfin ki fita yawan campaign dan zan iya zagewa mu daku da duk wanda yace ze daga miki yatsa, yanzu dai kawo mun Baqin Lipton kizo kiji wani abu, ni naga wani qyallin go shi ma kike kodai mun samu qaruwane?" Ya fad yana shafa goshi na, sena miqe ina dariya nace
"Rufa ni ka sayani, meya rage ban haifa ba ni kuwa da zan haifo shi Yanzu?"
"Bashir, ba kiyiwa Bashir takwara ba" ya fada har yanadaga murya dan na kusa fita daga dakin. Se nayi turusna wai wayo, wani abu naji ya motsamun a zuciya kai Allah karya kawo abinda baze wuce ba sena kalle shi ina murmushi nace
"Ai ka rigada kayi jana'izar Bashir a zuciyata dan haka bani da sauran qwan da zan haifa na saka masa sunansa, idan kuma jinjiri kake so to sedai mu haifi Yusuf Junior a Villah idan Allah ya kaimu".
TAMMAT BI HAMDILLAH
SAQON GAISUWA GA DAUKACIN MASOYAN LITTAFIN WATA KISHIYAR A DUK INDA KUKE A FADIN DUNIYA ALKAHIRIN ALLAH YA KAI MUKU 🙏🙏🙏
NA GODE DA JUMURIN BIBIYA DAGA FARKO HAR ZUWA QARSHEN LITTAFIN NAN ALLAH YA HADAMU A LADAN ABINDA MUKA KARANTA NA QARUWA YA YAFE MANA KURAKUREN DA MUKA AIKATA A CIKI
MASU KIRANA A WAYA DA MASU TUROMUN SAQO NAGODE, MASU NEMANA A DUK SANDA SUKA JINI SHIRU KWANA BIYU DAN TABBATAR DA LAFIYATA INA GODIYA SUNAYEN KU BAZASU RUBUTU BA AMMA DUK WADDA TA GANI TASAN DA ITA NAKE KUMA NA GODE KWARAI ALLAHYA SAKA DA MAFIFICIN ALKAHIRI
NAGODE ONE LOVE 🥰🥰😍😍
SE MUN SAKE HADUWA A LITTAFINA ME ZUWA 🙏🙏🙏.
MEENA VIP GROUP HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on
+234 7014979567
WhatsApp ONLY