Showing 159001 words to 162000 words out of 260321 words

Chapter 54 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42668

jikin ki be fada miki ba toh kiyi a hankali idan ba haka ba kuwa sena ladabtar dake tunda naga ke baki da hankali ba kuma ki da tunani, abinci kuwa a gidan ubansu suke ko suci ko kar suci dole ki dafa ki ajeye musu idan kuma kinqi kinsan sauran base na gaya miki ba, wuce ki fita tun ban lakada miki na jaki ba anan” na qarasa ina nuna mata qofa, nazata zata sake magana se naga ta juya tana qunquni ta fita a fili na fuskar ta

“Mara kunyar banza, ai da kin tsaya na koya miki hankali. Ku kuka (na juya kan yaran) daga yau ku ringa tsayawa a gidan ku kuna cin abinci idan baqu qoshi ba se kuzo nan ku qara kunji ko”.

“Wallahi Mami bata iya abinci ba, jiya fa data saka wani kifi a spaghetti har yanzu ina jin qayarsa a wuyana qarshe fa a bola ta juye abincin kowa yaqi ci” Jafar ya fada kafin nayi magana Faridah tayi caraf tace

“Waifa doyar da bamu ci da safe ba ta dumamawa Abbi shine ya ringa mata masifa, yanzu ma yana daki a kwance Kamar Bashida lafiya ina ga kuma yunwa yake ji, Mami ki bamu abinci mu kai masa dan Allah”.

Tsayawa nayi ina kallonta, dagaske Bashir bashida lafiya to me ya same shi? Na san dai yunwa tana iya kwantar dashi dan sam bashida jimirinta toh amma ni ina ruwana meye nawa a ciki shida ya dakko yar gwal ai seta dafa ta bashi.

Da zasu tafi Faridah da shegen naci seda ta dibar wa Bashir Friedrice da pepper chicken din da Amna tayi ga hadin kosulo abin dai ba’a magana na qara musu da zobo roba biyu sadaka nace ta kai masa.

BASHIR

Gaba daya haka ya wuni a office ya rasa me yaje masa dadi, ga damuwar rabuwarsa da Ma’u da se yanzu abin ya fara dukansa daya tabbatar da ta kufce masa se yayi da mugun gaske kafin ta sake dawowa hannunsa.

Ya rasa wa ze gayawa damuwarsa, a wannan karon be karbi shawar Bala ba gani yake kamar bazata fiddashi ba, amma wani lokacin idan ya tuna irin son da Ma’u takeyi masa se yaga kamar duk buyagin iska kawai takeyi na dan lokaci zata sakko su koma zaman su.

Wai ma shi me yayi mata ne? A iya saninsa laifi ta masa ta qi bin unarninsa kuskure daya da yayi shine daukar matakin saki a cikin fushi kuma har biyu, daya sani hutu ya bata na lokaci ya fita sabgrta har se ita da kanta ta dawo ta nemi shiri ta kuma yarda da sharadin daya bata kafin su daidaita amma yanzu ya lalata komai, ya bi rudin shedan ya rabu da Ma’unsa.

Ita wadda Shedab din yayi masa kururuwa akanta gashi nan ya dakko ta idan bada gasha shi babu abinda take yi ko iya horon yunwar da take masa aka barsu na shekara daya yasan dakyar idan bazatayi ajalinsa ba wai shi wannan wane irin bala’ine yake tun karar rayuwarsa.

Wayarsa ya dauka ya shiga neman Number Amiru qaninsa da tun ranar da zancen sakin Ma’u yaje Gombe ya kirashi dan yaji menene gaskiyar zancen ya kuma tabbatar masa da anyi daga ranar basu sake magana ba.

Ya kirashi sau ba Adadi amma Amirun baya dagawa daga baya ma blocking dinsa yayi, haka Naziru ma baya amsa wayarsa to yan uwansa ma kenan kuma shi bashi da sauran wani shaqiqij Abokin da ze tattauna wannan matsalar in banda Balan se Abubakar da ko giyar wake yasha be isa ya tun kare shi a yanzu ba.

Abdulkarimu ne ya fado masa a rai, ba bata lokaci ya danna masa kira kuwa akayi sa’a ta shiga seda ta kusan tsinkewa kafin ya daga wayar

“Alhaji Bashir yaushe rabon da ka nemeni tunda giwa tayi lafiya ka samu kan Madam shikenan ka watsar dani” Abdulkarim ya fada bayan da suka gaisa. Seda Bashir yaja numfashi kafin yace

“Abdulkarim ina cikin Bala’i na rasa yanda zanyi wallahi ka taimaka mun”

“Allah yayi mana maganin abinda ya damemu, lafiya dai Bashir meya sameka haka kake dangana kanka da Bala’i?”

“Abdulkarim hau ce ta hauni, nabi dokin zuciya na saki Ma’u gashi yanzu harta gama iddah ban mayar da ita ba na rasa inda zan kama ji nakeyi kamar zan haukace, yanzu har ta fara kula wasu Mazan sau biyu ina ganin ta a motar Maza Abdul” ya qarasa maganar kamar ze fashe da kuka saboda yanda yakejin zafi a duk sanda ya tuna ganin da yayiwa Ma’u na jiya dana yau din.

Salallami Abdulkarim ya ringayi yana cewa
“Ka saki Ma’u Bashir wace irin hau ce kai kuwa take binka haka ka rasa matar da zaka saka a rayuwa se Asma’u, Asma’u fa Bashir toh wallahi babu ruwana, abu daya zan iya maka inyi maka Addu’ar Allah ya taqaita maka wahala na kuam roqeshi karya maido maka da Asma’u rayuwarka dan baka san darajarta ba”

“Idan Allahn naka ne seka roqeshi karya dawo mun da ita din, na kiraka ka bani mafita shine zaka zageni kayi mun fatan tsiya ko? Daman nasan ba qaunar zama na da ita kake yiba, to dakai da duk sauran masu jin dadin abinda ya faru kuna kallo Ma’u zata dawo mun sedai baqij ciki ya kashe ku ku mutu”.

“Allah ya yafe maka Bashir” Abdulkarim ya fada kafin ya kashe wayarsa.

Bashir kuwa hada kansa yayi da teburin gabansa yana sauke numfashi, babu abinda yake cizon zuciyarsa irin idan ya tuna ganin da yayiwa Ma’u da wasu, Matarsa Ma’u da wasu qartin maza da sunan zawarci.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allah ka kawo mun dauki, Allah karka barni da iyawata” ya fada a fili yana sake wawurar wayarsa, dole ya ajiye duk wani abu a gefe ya kira Baba, ko ze zageshi kai idan ma ta kama yaje ya tsugunna a samowa Baban bulala ya zane shi duk ya yarda indai ze saka baki Asma’u ta haqura ta dawo masa dan yasan a yanzu dai su biyu ne zasu iya shawo masa kanta babu musu ta yarda daga Baban se Goggonta, shi kuwa dai rashin kunyar tasa bata kai ya tunkari Goggo a yanzu ba dan yaci ace kafin ya saki Ma’u ya tuno da karamcin matar amma duk ya hada ya take to wai shi me tayi masa ne ma??

Sallamar da Baba yake ta faman kodawa ce ta dawo dashi hankalin sa ashe wayar ta shiga tuntuni yana can zurfin tunani be sani ba.

“Barka da rana Baba, ya qarfin jikin?”
“Barka dai Bashari, jiki Ahamdulillah idon ka kenan se yau zaka kirani ko da yake kaida kake da Amarya ai dole ayi maka uzuri” Baban ya fada babu wata damuwa a muryar sa.

“Ayi haquri Baba” Bashir ya fada yana gyara zama, yanda yaji Baban a sake ya qara masa kwarij guiwar fadar abinda yake ransa.

“Ba komai ai nima ban ce kayi laifi ba, ya iyalan naka gaba daya da yaran kuna lafiya dai ko?”

“Lafiya lau Baba sedai Ma’u ce dai..” se kuma yayi shiru ya kasa ci gaba da magana, Alhajin da yaji yayi shiru yace

“Me Ma’un tayi kuma? Lafiya dai ko wata matsalar ce ta sake tashi?”

“Daman Baba naje ne jiya da niyyar mu sasanta na mayar da ita dakibta, shine take gaya mun wai tayi bari bayan mun rabu dan haka iddarta ta cika tuntuni babu kome tsakanin mu”

“Kai masha Allah barka barka abu yayi dadi gaskiya, ai kuwa na kirata da mun gama wayar nan tunda nima laifinka ya shafe ni kwana biyu ta dena kirana” Baba ya fada cikin murna kamar be ji abinda Bashir din ya fada ba.

“Baba kamar baka gane me nake cewa ba” Bashir ya fada a rarrabe, se baban yayi murmushi yace

“Nagane Bashir, kace Ma’u tayi bari ko iddarta ta cika. Murna nake tayata da Allah ya dubi kyakykyawar zuciyarta ya rabata Mijin da besan darajarta ba butulu irinka, wannan kadai ya isheka ishara ka gane cewa Allah yana arawa mutum dama ne a rayuwa idan yayi wasa ta subuce masa shikenan sedai ya mutu yana nadama da dana sani, yanzu daka kirani me kame so nayi maka?”

Kwata kwata kalaman Baba basu dami Bashir ba dan ya tsammaci fiye da haka ma, shidai fatansa Baban yayi iya fadan da zeyi ya haqura tunda dai ai bazece yafi son farin cikin Ma’u akan nasa ba.

Seda ya sake marairaicewa sosai kafin yace
“Na karbi kuskurena Baba duk abinda ka fada gaskiya ne kuma na yarda, zan chanza hali wallahi zan dena duk abinda kasan inayi na rashin kyautawa kasa baki Ma’u tayi haquri ta koma dakin ta”.

“Toh fa da wuri haka Malam Bashir kuma ni wannan lissafin ai bani zaka yiwa ba ita wacce kayiwa laifi can zaka samu ka bawa haquri ka gaya mata ka chanza ko kuwa kayi shawara dani sanda kayi sakin”

“Ko naje Baba bazata saurareni ba tace ta gama aurena dan girman Allah Baba kaji tausayina ka saka baki nasan kai kadai ne zaka saka baki ta haqura ” Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka

“Amma Allah yayiwa Asma’u Albarka, in gaya maka gaskiya Bashir indai da shawara ta ne bazan taba barin Asma’u ta koma gidanka ba zan kuma ci gaba dayi mata Addu’ar Allah saka mata ladan haqurin da tayi dakai ya bata mijin da ze yasan mutunchinta, Idan Wannan ya sa ka kirani to se anjima kar kuma ka sake kiran wayata indai akan wannan shirmen ne” kafin Bashir ya sake cewa wani abu Baba ya kashe wayarsa.

Ji yayi zazzabi na neman rufeshi, ya hade kansa da guiwa yana jan Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un a zuciyarsa abinda yake dauka ze zo masa da sauqi gashi se komai yana sake rincabewa, ya zeyi? Waze kama? Ta ina ze fara? Duk be sani ba.

Haka ya qarasa wunin ba tareda ya saka ko ruwa a cikinsa ba ya kamo hanyar gida dan bashida wata nutsuwa, se a sannan ma ya ji daya sani Azumi yayi da wannan wunin yunwar yana shiga ya tarar da Amirah tana masifa Ahmad ya zubar da Lemo akan carpet tanayi masa magana ya gudu waje,

Tun kafin tayi masa magana ya tareta da cewa
“Bana jij dadi, ki barni dan Allah karki qara mun damuwa akan wacce nake ciki, ki hada abinci na ki kawo mun daki” ya shige ciki ya barta.

Yana wanka ta shiga da Try ta zubo doyar dazu da safe a plate se Sauce din Hanta da Albasa da ta dan qarayi saboda doyar tayi Armashi ga Lemo me sanyi na Exotic da ruwa duk ta ajiye masa.

Yana fitowa ana kiran sallah dan haka ya zura jallabiyya ya tafi masallaci seda ya dawo ya tsaya a Kitchen ya fara hada shayi kafin ya wuce dakin dan gaba daya hanjinsa sun qulle, yana bude farantin ya fara kwala mata kira, Amirah na can ta sake wanka tana kwalliya ta jiyo kiran nasa, seta zura hijab ta fito tana mitar

“Haka kawai daga dawowarka shikenan kuma mutum baze huta ba zaka fara kiransa kamar wani saboj makaho” da wannan mitar ta tura qofar ta shiga babu ko sallama.

“Meye wannan kika kawo mun” ya fada yana nuna doyar, seda ta harare shi ta qasan ido kafin tace

“Doya ce, naga da safe baku ci ba kuma kar ayi almubazzarancinta shiyasa na ajiye na dumamata yanzu, gashinan har sauce fa nayi maka dan kaji dadin ci”.

“Tunda kike kin taba ganin an maimaita mun abinci a gidan nan, bama wannan ba ke kike siyan abincin da bazaki dafamun abinda nake so ba ko kuwa” ya fada a nutse dan bama shi da qarfin yin masifar a sannan.

“Ni fa na gaji da wannan abun, duk abinda nayi ban iya ba a gidan nan, ance bana girki idan kuma nayi a qi ci akan me wallahi daga yau idan na dafa in za’a kwana goma ba’a cinye ba shi zanyita maimaita wa ba ruwana ai ni ba yar aiki aka dakko ba balle ace...” bata san tasowarsa ba se saukar tagwayen mari dataji akan fuskarta, kafin ya angizata waje, ya sake komawa ya kwashi try din abincin ya watsa mata sannan ya kullo qofarsa.

Dafe qirjinsa da yayi masa nauyi yayi ya fada kan gado da baya, beyi aune ba sejin wasu hawaye masu dumi yayi suna gangarawa zuwa cikin kennensa a maimakon ya hana kansa se kawai ya bude baki kamar qaramin yaro ya shiga rera kuka irin na wanda duniya tayiwa daurin Goro.


Ayi haquri dab Allah 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 47

Kuka me sunan kuka Bashir yayi tamkar wanda aka cewa Dada ta mutu, seda yaji wani kaso na damuwarsa ya kafin ya shiga bandaki ya wanko fuskarsa ya dawo ya zauna tareda rafka uban tagumi ga Yunwa se sakadar ciki aa takeyi dan takaici shayin da ya hado ma be sha ba harya huce.

Yana zaune a gurin seda yaji hajijiya na neman kadashi kafin ya miqe da kyar dan dole ya gita ya nemi abinda zeci kafin yunwa ta kashe shi, yana bude qofar ya ga Faridah a tsaye, da Alama kwankwasawa zatayi.

"Abbi kaga Anty Amirah ko, dan kawai na tambayeta kai shine ta zage ni" Faridah ta fada tana hararar Amirah dake zaune can kan kujera tana kada qafa. Komawa ciki yayi Faridah ta bishi ta kwandon Abinci ta ajiye tana cewa

"Abbi ga Abinci, a gurin Mami na karbo maka kaga harda zobo ta ce a kawo maka sadaka".

"Sadaka, Almajiri na zama kenan lallai Ma'u" ya raya a ransa kafin ya hadiye wani tsinkakken yawu sanda qamshin shinkafar ya dake shi, ga Kaza mutuniyarsa.

Faridah na shirin Zuba masa a plate ya karbe kular gaba daya ya saka cokali ya shiga cin abincin kamar wanda ya shekara yana Azumi seta miqe ta koma kan kujerar dake dakin ta zauna tana kallonsa.

Cikin dan lokaci Bashir ya tashi abincin nan tas Ya shanye Zobo Faridah dai se kallonsa takeyi, seda yayi gyatsa tareda hamdala kafin ya kalli Faridan ya miqa mata hannu alamar taje. A jikinsa ya dorata ya sumbaci goshinta kafin yace

"Nagode Faridah ta kamar kin san Abbinki Yana kewar Abincin Mami".

"Abbi yah Amna ce tayi ai, kuma Abbi tunda Anty Amirah bata girki kaima ka ringa zuwa gidan Mami kana ci mana kaga mu a can muke cin abincin mu me dadi" Faridah ta fada tana marairaice masa, murmushi yayi yace

"Ai ba laifina bane Mami ce bazata bari ba, amma ki gaya mata da kanki ki roqeta ta dawo nan gidan ko ni na ringa zuwa can se mu ringa cin abinci tare duka yanda muka saba ko?"

"Toh Abbi amma bakaine ka koreta daga nan gidan ba ai nasan bazata sake dawowa ba sedai kai ka ringa zuwa can, gobe da safe zan gaya mata tunda yanzu dare yayi"

"Shikenan, dauke kwanukan kije ki kwanta Allah ya yi miki Albarka"

"Amin Abbi" ta fada tana hada kayan a kwando ta fice taja masa qofar.

Wani irin sanyi da nutsuwa Bashir yaji a zuciyarsa, to kodai maganar Bala gaskiya ce da yace ya bata guri idan aka kwana biyu zata huce su daidaita tunda gashi kuwa yaga alama.

Idan har Asma'u zata aiko masa da abinci to kuwa in yayi haquri yana zaune zata neme shi su shirya, daman ya sani duk abinda zata fada iya fatar baki ne be kai zuciyarta ba. Ya sani Ma'u tana sonsa kowa kuma ya shaida hakan shima yana sonta amma ya rasa me yasa mutane suke da tantama akan son da yakeyiwa Ma'unsa.

Tashi yayi yaje yayi brush ya dawo kan gadon ya kwanta gaba daya jikinsa ya mutu tunda ciki ya dauka bacci kawai yake da buqata, wayarsa ya jawo ya rubutawa Ma'u text

"Nagode Ma'una, uwargida na har a Aljanna" yana turawa ya saka wayar a silent ya ajiye zuciyarsa qal ya kwanta tareda jan bargo dan gani yake kamar ma har sun shirya da Ma'u ai, hannunsa ya miqa ze kashe makunnin filtila ya jiyo kamar Muryar Faridah tana kuka, se ya miqe ya fita palour yana zuwa kuwa ya tarar da Amirah ta cukumeta kamar me danbe da sa'arta tana cewa

"Ni za'a nunawa Bariki, a zubo abinci daga wani guri a baki ki kawowa mijina ko to wallahi duk abinda aka zuba bazeyi tasiri ba, zama na daram a gidan nan babu yanda aka iya dani ke kuma sena miki dukan tsiya ta yanda gobe bazaki sake karbo abu ki kawo masa ba" Ta kaiwa Faridan Mari ya tareta a fusace ya tunkudeta gefe yana cewa

"Wai ke wace irin shedaniya ce da baki taba so a zauna lafiya, saboda dazu na barki shine yanzu zaki kama mun yarinya kina duka akan me?"

"Akan me ma kake tambayata? Da kasan kana son abincin uwar tata me yasa ka koreta daga gidan ai da seka barta ta zauna tayi ta girka maka kana ci dan haka yanzu wallahi baka isa a ringa shigo maka da abinci daga wani guri kaci ba, kodai kaci wanda na dafa ko kuma ka zauna da yunwa idan ka fita can waje ka siya kaci ehe" Amirah ta fada tana girgiza jiki a gabansa,

Tsabar mamaki Bashir ya gagagara cewa komai, yanzu shi take tsayawa a gabansa tana gaya masa be isa yayi abu ba a cikin gidansa ba bata jin tsoron bare shakkar gaya masa duk abinda taga dama lallai Amirah.

Jan hannun Faridah yayi zuwa dakinsa kafin su qarasa kuwa Amirah ta tare qofa tana cewa "Ai wallahi bazata sake kwana a dakin nan ba idan banda rainin hankali ni ina matar gida ka koreni daga dakinka sannan ka bar yarka ta kwana a ciki baze yuwu ba".

"Amirah ki matsa mun daga hanya bana cikin yanayin da zan biye miki yanzu" ya fada yana kokawa da bacin ransa, Amirah kuwa ko a jikinta sema qara babbake hanya da tayi tana murguda baki tasan dai qarqari yace ze mareta ko to kuwa ta dena tsayawa ya daketa kamar wata jakarsa.

Ganin da yayi ta kafe a qofar bata da alamar matsawa ga shi sauran yaran duk sun fito suna kallo yasa ya sassauta murya yace da Faridah
"Wuce dakin Antyn ku ki kwanta, ke kuma shiga ciki muyi magana"

"Nifa na gaji tun wuri ka nemar mata Gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login