Showing 183001 words to 186000 words out of 260321 words
Chapter 62 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
tsuntsuwa na bace a gurin saboda yanda kalamansa suke rugurguza mun jiki da zuciya.
Dariya yayi yana kallona yace
“Wai daman ke raguwa ce ban sani ba? To kuwa ki shirya, magana ta kadai tana firgitaki ranar da kika zama mallakina kuma se yaya karfa ki bani kunya Ma’u”.
Wannan karon ban san sanda na miqe ba se gani na nayi na kusa kaiwa daki Yusuf kuwa yace me zeyi idan ba dariya ba ya samu guri ya ringa kyalkyalata son ransa nidai na shige daki na zauna bakin gado ina sauke numfashi kamar wadda tayi tsere.
Wasu Butterflies nake ji kamar suna mun yawo a kwakwalwa, Allah ya sani ina son soyayya, ina son a tarairayeni a nuna mun duniya babu yani koda kuwa qarya mutum yakeyi amma abinda na rasa kenan a rayuwar aurena da Bashir.
Bansan Miji yana gayawa matarsa kalaman soyayya ba, bansan me ake kira da tarairaya ba ko kalmar I love you se na shekara ban jita a bakin Bashir ba, ba qaramin gigicewa bace ta ke sakashi yayi magana idan muna mu’amala a sannan ne kadai bakinsa yake bin qarfin zuciyarsa ya furta abinda beyi niyya ba qila shi yasa yanzu yan wadan nan kalaman na Yusuf suke neman au rikita mun yar kwakwlawata.
Qarar da wayat tayi ne ya mayar dani hayyacina,
“Ki dawo nayi alqawari bazan sake cewa komai ba gaisawa kawai zamuyi na tafi dan a gajiye nake sosai wallahi” Yusuf ya fada bayan dana amsa wayar.
Kamar me zuwa gaban suruki haka na tafi idona a qasa na sake samun can gefen kujera na rabe ina jinsa yana mun dariya qasa qasa amma naqi dagowa balle na bashi damar da zamu hada ido.
“Bari na tafi Asmy, na gaji sosai wata irin tafiya daga Washington amma se kace wanda ya taho daga China”
Se na daga kai na kalle shi nace
“Wai ba daga Bauchi kake ba daman? Na zata ai kace kaje ganin su takwara ne”
“Suna America ai, ke dai kiyi ta tayani da Addu’a nima a wannan karon Allah ya datar da ni na samu mace ta gari, na gaji da wannan gantalallen auran wanda dashi kusan gara babu ni ina wata duniya matata tana can wani guri itama” ya fada fuskarsa na nuna rashin jin dadin abinda yake fada din.
“Ikon Allah kaji wata gantalewa kuma” na fada ba tareda nasan a fili nayi maganar ba seda naji yace
“Kinsan sunan da Hajiya ta sakawa auran kenan wai auran Gantali” ya qarasa yana dariya. Murmushi nima nayi nace
“Allah to ya rufa Asiri” ya miqe yana cewa
“Amin”.
“Har zaka tafi ko ruwa baka sha ba sannan ga abinci kuma na yi maka fa” na fada nima ina miqewa tsayen, se ya waiwayo muka hada ido yace
“Dagaske? Kai amma na gode yau nima zanci girkin Asmy daman tunda na shigo nake jin qamshi shiru kawai nayi kar kice na fiya kwadayi, amma sedai na tafi dashi dan so nakeyi naje na yi wanka na chanza kayan nan”.
A manyan Aluminum take away na juye masa hadin potato salad wani kuma Pepper chicken, na hada masa da Flask din da na zuba hadaddiyar party Jallop rice dan dai nasan babu wanda baya cin shinkafa indai dan Arewa ne dayan kuma Stit fry Egg noodles da taji shrimp.
Harda Lemo da Ruwan duk na tarkada yara suka ringa fit dasu se gani nayi suna shigowa da wasu irin qananan Akwatuna masu Kyau irin na yan gayu kowa da guda daya Jafar ne ya shigo janye da guda biyu shi kuma.
“Mami tsaraba UncleYusuf ya kawo mana, ga wannan na Yaya Aliyu ne” ya fada yana miqo mun guda daya.
“Bana so kudai da kuke kwadayayyu se kuyita karba ai” Aliyu da bansan yana gidan ba ya fito daga dakin su Amnah yana maganar, hararar sa nayi ya kalleni ya dauke kai, kamar ze zauna se kawai ma ya kada kansa ya fice daga gidan gaba daya ni kuwa na bishi da ido kafin na mayar da hankali na kan sauran da suke faman bude bude akwatunan su.
Kaya ne kowa kala biyu da takalmi harda Agogo da turare, bana buqatar a gaya mun masu tsada ne dab Designers ne nagaske da kana kallonsu kasan sunci kudi.
Wayata na dauka na wuce daki ina kiran lambar Yusuf din
“Wannan kayan fa hidimar tayi yawa ai kuma ace ko wanne se da aka siya masa gaskiya sunyi yawa” na fada bayan daya daga wayar.
“Akwai wani abu naki a ciki ne?” Ya tambayeni, sena girgiza kai kamar yana gabana nace
“Aa” na bashi amsa
“To qorafin me kikeyi? Yarana na siyowa bake ba, idan ma kishi kike saboda ban yi miki tsaraba ba toh sedai kiyi haquri bandake” ya bani amsa yana murmushi.
Murmushi nima nayi nace
“Mungode, Allah ya qara budi”
“Karki sake gode mun dan kinfi qarfin duk wani abu a gurina. Zan iyayin komai saboda Farin cikin ki Asmy, zamuyi magana idan na qarasa masauki in naci abinci sannan se nayi tunanin idan kin cancanci tukuici”
Da haka mukayi sallama ni kadai na ringa murmushi ina kallon wayar hannuna bayan da na kashe, wato soyaya tayi a rayuwa malam.
ENGINEER BASHIR
*SODA COMMUNICATION📱💻📱
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*💃🏽💃🏽 with the validity of 30days at affordable price we are available 24/7 08137145294
*MTN DATA*
1GB@280✅
2GB@550✅
3GB@850✅
4GB@1150✅
5GB@ *1400* ✅
10GB@2800✅
*AIRTEL DATA*
1gb@320✅
2gb@640✅
3gb@950✅
5gb@1600✅
*Pay through👇🏽👇🏽*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*🥰🥰🥰we are always there at ur service. WhatsApp/Call📞08137145294🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 52
Seda ta tabbatar da Mama ta shiga bandakin tajiyo qarar ruwa alamar ta fara uzurin daya shigar da ita kafin ta sauke qafafunta qasa dakyar saboda yanda gaba daya jikinta yayi mata nauyi.
A yanda take bazaka taba zaton zata iya motsawa ba amma da yake ita ta saka kanta se gashi cikin abinda be wuce minti biyu ba cikin sanda ta fice daga dakin ta taki sa'a kuwa harta salallaba ta bar ward din bata hadu da kowa ba saboda dare ya rigada ya tsala Asuba ma ta fara kawo kai daga Marasa lafiyar har ma'aikatan da yawa sun samu bacci se masu jiran kiran kota kwana acan dakin su.
Qarfin hali kawai take tana daga qafa har ta fice daga get din Asibitin, zuciyarta ta qeqashe babu alamar tsoro ko fargabar wani abu musamman a irin yanayin da ake ciki na rashin tsaro da garkuwa da mutane haka Umaimah ta ringa tafiya a cikin daren nan a matuqar galabaice ga tsohon ciki seda ta kwashe kusan minti Arba'in kafin ta kai layin gidan nata zuwa sannan ikon Allah ne kawai yake tafiya da ita dan tamkar zata mutu haka ta zube a bakin Get din layin tana bugawa.
Masu gadi ne suka taso da dalleliyar fitilar su suna tambayar waye, Sammani me gadin Gidan su ya gane ta, da sauri ya bude mata Get din yana mata sannu qasan zuciyarsa fal mamakin ya akayi ta taho daga Asibiti a wannan yanayin?
Dazu fa da sukaje ko motsi batayi kai shi tunda uwarsa ta haifeshi be taba ganin mace tamkar Aljana irin Hajia Umaimah ba, haka ya ringa binta da sannu har ya rakata cikin gidan, daga bakin qofar palour ya tsaya ta shige ya jawo qofar, a ransa yana Addu'ar Allah yasa a kwashe lafiya.
Kai me ma ya kaishi barinta ta shiga gidan be fara sanar da Alhajin ko ya kira Hajia Babba ba? Tunanin abinda kaje ka dawo ya sakashi tuntumawa da gudu ya nufi bangaren Hajia Babba beyi la'akari da cewa dare bane ya ringa buga musu qofa jikinsa har rawa yakeyi dan se a sannan ya gane qatuwar wautar daya tafka kuma duk abinda ya faru yanzu shi za'a fara ganin laifi.
Ganin yana ta bugu ba'a bude ba ya sakashi zagayawa ta baya inda window dakin Halifa yake ya zuge Net ya shiga kwala masa kira yana cewa
"Halifa, Halifa ka tashi ga Hajia Umaimah can ta dawo ka tashi dan Allah kar ayi kisan kai a gidan nan ace da sa hannuna".
Halifa daya farka da niyyar qundumawa duk uban da yake buga qofa Ashar da sauri ya wantsalo daga gado yana raba ido, Anty Umaimah kuma matar da suka baro a Asibiti bata hayyacinta waya dawo da ita gida toh?
Da gudu ya fice daga dakin ya nufi Sama gurin Hajia, a matattakala suka hadu tana shirin saukowa Habiba na biye da ita a baya kana ganinsu kasan hankalin su a tashe yake.
"Yawwa Halifa kaima kaji bugun kenan, muje mu duba wanene a wannan lokacin Allah dai yasa lafiya" ta fada tana qarasa sakkowa.
"Hajia Sammani ne wai Anty Umaimah ce ta dawo gata can ta shiga gida" Halifa ya fada yana yin gaba se Hajia ta dafe qirji tana cewa
"Umaimah? Umaimah kuma yaushe ta dawo ita aa bata da lafiya waya dawo da ita gida? Kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wannan bala'in har ina Umaimah bazaki kashe ni da raina ba" da wannan surutan suka dunguma bangaren Bayero sedai suna zuwa suka tarar da qofar palour a datse.
Sammani ya saka muqullin hannunsa amma yaqi buduwa alamar an rufe qofar ta ciki kenan.
Halifa ne ya koma cikin gida da gudu ya dakko wayarsa ya shiga kiran Yayan nasa, Hajia na tsaye ta kasa cewa komai, Addua kawai takeyi Allah ya tsare mata Dan nata da Marainiyar Alah.
CIKIN GIDAN
Humairah tana kwance lamo akan gado idan ka kalleta zaka dauka bacci take yi amma idonta biyu, ita kadai na san abinda take ji a jikinta bisa sabon al'amarin daya sameta. Sam Yaya Khalil be tausaya mata ko ya dubi qarancin shekarunta ba seda ya gurjeta son ransa tamkar me biyan bashi kafin ta samu kanta a hannunsa.
Yanzun haka da tana da qarfin tashi da barin masa dakin za tayi dan bata san abinda ze biyo baya ba idan ya fito daga wankan da yakeyi, bata tunanin ze barta ta huta duba da yanda dakyar da sidin goshi ya barta ta fito daga bandakin kafin ya shiga yin nasa wankan.
Idanuwanta da sukayi laushi tubus suka qanqance saboda kuka ta lumshe tana jin wani bacci bacci yana fizgarta amma bata so tayi tunda asuba ta kawo kai gara idan sukayi sallah se tayi baccin amma in Yaya Khalil ya bata dama kenan.
Juyawa tayi daga rufda cikin da take zuwa rigingine wanda yayi daidai da bugun da akayiwa qofar dakin da take cikin wani irin tashin hankali kamar za'a balla qofar idan ba kunnenta bama harda kururuwa take jiyowa daga wajen.
A firgice ta yunqura tana cije baki ta miqe zaune, jitayi bugun yana qara qarf, ta waiwaya ta kalli qofar bandakin a daidai sanda Khalil ya fito daure da babban towel fari a qugunsa yana goge fuskarsa da wani qarami yana cewa
"Badai bacci kikayi ba yarinya dan yanzu ma aka fara..." se maganar sa ta maqale saboda bugun daya jiyo anayi tareda hargagin daya tabbatar na Umaimah ne ba shiri ya wurgar da towel din hannunsa ya nufi Humaira data dora hannu biyu aka hawaye suka balle mata, zatayi magana ya dora hannunsa a kan lebe alamar tayi shiru seta shiga girgiza masa kai.
Seda yaja numfashi ya ajiye zuciyarsa na tsalle saboda tsoro kafin ya nufi bakin qofar ba shiri Humaira ta kwasa da gudu ta shige gurin walk in closet dinsa ta fara neman gurin buya. Ita dai tana ga ajali ne yasa ta auri Yaya Khalil dan dai bata ga alamar tana da rabon komai a cikin zama dashi ba sena wahala.
Ta tabbata ko Umaimah bata kashe ta da hannunta ba kamar yanda ta dade tan iqirari to kuwa tabbas fargaba da tsoratarwar da take mata zasu saka zuciyarta tayi bindiga.
Khalil kuwa seda ya gyara muryar sa kafin a shaqe kamar wanda ya tashi daga bacci ya ce
"Waye wannan yake bugamun qofa a daren nan Sammani wane irin rashin hankali ne me ya faru zakazo kana mun bugu yanzu?"
"Kutumar bura ubanka ce ta faru Khalil, ka bude mun qofar idan ba haka ba wallahi har kaje lahira kana dana sanin abinda zan aikata maka Maci amana Macuci" Umaimah ta fada cikin hargagi.
An rigada an kai gabar da bayajin komai dan Umaimah ta zageshi, a yanzu tashin hankalin sa daya ne, idan ya bude qofar ta shigo taga Humaira besan me zata aikata ba haka idan yaqi budewar nan ma besan me zata yi ba waima ta yaya akayi ta farka har aka sallameta daga Asibiti tsakar daren nan wannan wane irin bala'i ne haka.
"Khalil bazaka bude bako? Shikenan ka zauna a ciki kaida Yar iskar Karuwar da ka dakko amma ka jirani na dawo zakaga abinda zanyi" Umaimah ta sake fada kafin ta juya dakyar take daqa qafa ta sauka qasa. Tana jin ana buga qofar kuma ta tabbatar da Sammani ne ze taso yan cikin gidan amma bata kukasu ba ta wuce.
Kitchen ta nufa, zuciyarta ta rigada ta gama qeqashewa abinda ta ayyana mata tayi kawai shi zatayi kota mutu ko ta rayu wannan duk ba damuwarta bace amma dole ta koyawa Khalil hankali na cin Amarta da yayi.
ASIBITI
A nutse Mama ta fito daga bandaki bayan data dauro alwala taja qofar ta rufe a hankali gudun karta tashi Umaimah. Kai tsaye idonta ya sauka akan gadon da Umaimah take kwance se taga babu kowa, da mamaki ta qarasa Gurin ta daga bargon dai dagaske bata nan.
Hijabin ta ta zura ta leqa waje ta tambayo ko Ma'aikatan ne suka dauki Umaiman tunda daman sunce akwai gwajin da za'a mata amma ta dauka ai seda safe.
Bacci sosai ta tarar da Nurses din sunayi abinsu, seta qarasa kusada wadda take kula da Umaimah ta shiga tashin ta, Nurse Halima ta farka bakinta dauke da salati ganin Mama a tsaye yasakata wartsakewa tana cewa
"Aa Mama badai jikin Umaiman bane? Muje na dubata mu gani se a taso likita"
"Ba ku kuka dauketa ba ne Nurse? Na shiga alwala na fito yanzu banganta a dakin ba" Mama ta fada cikin firgicin jin maganar Nurse, to ina Umaimah zata tafi a daren nan ita da ba lafiya ba?
Kafin kace me Asibiti ya hargitse ana neman Umaimah daki daki, da yake ba wani girma ne dashi ba cikin dan lokaci suka bincike ko ina amma babu Umaimah babu me kamar ta har Get an tambayi masu gadi sukace basuga fitar kowa ba zuwa sannan tuni Mama ta fara kuka, wayarta ta dakko ta shiga kiran Abba ta gaya masa halin da ake ciki seda ta kira sau biyar kafin ya daga wayar.
GIDAN ALHAJI SABO
A daidai sanda Mama take kira Anty Saratu ta farka yin fitsari, da yake wayar a vibration take bata ji ba, seda ta yiwo fitsarin ta dawo, dakyar take bude ido saboda bala'in baccin da take ji to kusan kwana biyar kenan a jere baccin su ragagge ne ko yau din se gurin qarfe daya suka dawo gida daga Asibitin kafin ta kwanta biyu tayi.
Hasken data hango wayar Abba tayi ya saka ta miqa hannu tana hamma ta jawota dan tasan qila Alarm din nasa na fama ne ze fara kadawa ya hana mutane bacci, sunan Maman Yara da ta gani ya saka fara tashin Abban ya yi juyi yana cewa
"Ohni Saratu wai me kuma kike so dan Allah ki barni na huta mana idan dai ba so kuke ku qarasani na mutu kawai ba"
"Alhaji Maman ce take kiran ka a waya, ina ga jikin Umaimah ne fa" ta fada tana miqa masa wayar, seya karba da sauri ya saka a kunne, Mama ta fashe da kuka tana cewa
"Alhaji An sace Umaimah, daga na shiga Bandaki nayi Alwala na fito babu ita a dakin gashi mun duba ko ina amma ba'a ganta ba".
"Kamar yaya ba'aga Umaimah ba? Ita Umaiman Allura ce ko me da za'ace ta bata wannan ma ai zancen banza ne, jira gani nan zuwa" Alhaji Sabo ya fada yana miqewa tsaye, jiri ne ya jashi ya koma dabas ya zauna da sauri Anty Saratu ta taro shi tana cewa
"yi a hankali Alhaji kasan kaima fa ba lafiyar ce dakai ba"
"Ba'a ga Umaimah ba Saratu, wannan abu har ina daga wannan tashin hankali se wannan kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miqomun riga ta muje Asibitin mu gani".
"Ba'a ganta ba kodai wani gurin ta shiga taya za'a ce baa ga mutum ba a Asibiti Ahaji sudai duba dakyau ko bayan gida ta zaga" Anty Saratu ta fada tana miqa masa jallabiyya se ya karba ya hau kici kicin sakawa amma ya gagara saboda yanda jikinsa yake rawa.
"Saratu bane babbar riga ki gani na dora zata fi mun sauqi" ya fada yana zama a bakij gadon ya dafe kansa da hannue biyu, al'amarin Umaimah nema take yi ta kashe su kawai ta huta dan ya tabbatar yanzun da kanta ta tashi daga Asibitin wannan kadan ne daga aikin ta.
Tareda Salmanu suka fito daga gidan, Salmanun ne yake jan motar. Seda suka hau titi ya kalli Abban yana cewa
"Abba an sanar da Yaya Khalil toh ya kamata fa yasan halij da ake ciki?"
"Be sani ba gaskiya, a kyake shi kawai muje mu gani idan ba'a sameta ba sannan se mu sanar musu" Abba ya fada yana tufe baki wayar Salmanu da take gefensa ta fara qara, seya cirota yana duba.
"Lah Abba kaga Yaya Khalil din nema qila toh yasan abinda yake faruwa" Salmanu ya fada yana daga wayar ya sakata a speaker.
"Salman ku taimaka mana, ga Umaimah nan tazo ban san me zatayi ba tace na bude qofar dakin da muke ciki idan ba haka ba se tayi abinda har naje lahira ina dana sani. Tsoro nake ji karna bude tayi mana wani abun kuma idan ban bude din ba bansan me zata aikata ba" Khalil ya fada cikin rawar murya dan dagaske ya gama karaya da lamarin Umaimah. Ya shaida yar daba ce ta gaske za kuma ta iya aikata masa duk abinda zuciyarta ta raya mata tunda ai ba yau ta fara ba.
"Muje gidan, bari na kira Maman ku na gaya mata, yanzu ita wannan yarinyar bazata bar rayukan mutane su huta ba ko? Ai Shikenan" Abba ya fada yana latsa waya.
Sanda suka isa sun tarar dasu Hajiar su Khalil a tsaye har sannan Sammani da Halifa na qoqarin buge qofar amma abu ya gagara