Showing 195001 words to 198000 words out of 260321 words

Chapter 66 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42732

in Allah ya kaimu tunda na fuskanci ciwon so ne yake damunka mu kuma bamu da maganinsa sedai mu baka shawarar yanda zaka sauqaqawa kanka indai ba kana so ka saka kanka a hatsarin kamuwa da ciwon zuciya ba".

Haka ya kwana yana juya maganganun Likita a ransa, qarfe goma na safe aka bashi sallama, kamar mara galihu haka ya tattara Samuel yazo ya dauke shi ya kaishi gida sanda ya isa yar gasken da alama ko tashi daga bacci ma batayi ba se ya wuce dakin sa shima ya kwanta akan gado yana ci gaba da saqe saqe.

Kiran Bala ne ya shigo wayarsa, kamar ya share sedai ya daga dan haushinsa yakeji tun ranar daya katse masa kira be biyo baya ba se yau.

"Allah ya taimaki Engineer Allahh sa ban katse maka aiki ba" Bala ya fada yana yar dariya.

Shiru ya masa be damu ba yaci gaba da cewa
"Gani a Lagos na shigo yanzu, idan anjima ka tashi aiki se na shigo nan ta gurin ku"

"Banje aiki ba ina gida yau" ya fada a cunkushe

"Oh dan Allah? Ta bari yanzu naje na kama daki idan na ajiye kayana se na shigo gidan, a sanarwa Madam dam ko Karyawa banyi ba na taho" Bala ya fada daga daya bangaren, se Bashir ya ajiye wayar yana cewa

"Seka iso toh".

Wa ze gayawa tayiwa wani girki ko ya manta da wacce take a gidan sa ne yanzu yake wannan maganar. Wanka ya shiga yayi, yaji dadin zuwan Balan dan yana da buqatar wanda zasu tattauna akan lamarin Ma'u, baya so ya sake yanke hukunci ba tareda shawara ba.

Se daya Bala ya iso gidan yaciyo uwar kwalloya kamar me zuwa daurin aure. A palour suka zauna Amirah ta kawo masa ruwa da lemo daga nan ta shige daki basu sake jin duriyarta ba.

"Mutumin wai Ina Ma'u ne banji labarinta a Gombe ba ko kun daidaita ban sani ba?" Bala ya tambaya yana shan Lemo.
Bashir yaja tsaki yace
"Tana gidanda yake kusa da namu, kasan wai har Ma'u ta manta dani ta fara sabuwar rayuwa tareda wani mutum daban bani ba" ya qarasa cikin jin zafin abinda ya ke fadar.

"Dagaske kai amma naji dadi" Bala ya fada cike da murna se kuma daga baya ya gano shirmen da yayi saboda yanda yaga Bashir ya zuba masa ido yana kallonsa se yayi saurin wayancewa yana cewa

"Ina nufin naji dadi da kace tana kusa daku kaga yanda zaku fi samun daidaito da wuri kenan"

"Bazata saurare ni ba Bala, idan ta ganni nunawa take kamar bamu taba hada komai a rayuwa ba Ka bani shawara ya zanyi na dawo da Ma'u rayuwata Bala kai kafi kowa sanin ina son Matata"

"Na sani Bashir amma yanzu yayi wuri da ka nuna karayarka, kafi kowa sanin irin son da Ma'u takeyi maka na tabbata bazata taba iya rayuwa da wani namiji idan ba kai ba. Ko kaganta da wani is sedai tayi dan ka gani rabka ya baci amma na tabbatar badan wai tana son sa ko akwai wani abu a tsakanin su ba.

Ka qara haquri mutumina karka manta fa laifi tayi maka ka hukuntata idan ka karaya yanzu ka bata qofar da a gaba zata taka ka yanda take so".

"Laifin me tayi mun Bala? Nifa nayi mata laifi na tirsasata yin abinda yake son raina saboda taqiyi na yanke hukunci ba tareda tunanin abinda hakan ze jawo mana ba.

Da bakina na saketa nace ta barmun gidana kana zaton zata manta wannan ta sake dawowa gareni? Bafa abinda tayi mun son zuciyata ne kawai ya kaini da dana sani" Bashir ya fada a matuqar karye.

Bala da yake faman antaya masa harara yayi saurin tareshi yana cewa

"A wata hudun shine har ka karaya haka kake nema ka zubarwa da kanka mutunchi haba Bashir, kai kana zaton Asma'u zata iya zaman aure da wani ba kai ba wallahi ko bayan shekara dari nasan kai zata zaba.

Kai duk duniya fa babu wanda besab irin son da take yi maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka mutumina, in banda kai ma yanzu ga yammata nan a gari birjik basu auruba se bazawara me yaya shida kake zaton daga rabuwarta dakai zata samu miji?

Ka saki jiki mutumina ka ci gaba da harkokin ka muna nan wallahi zata zo har cikin gidan nan ta nemi ka mayar da ita".

Kallonsa Bashir yake har ya gama magana. Ko kusa bega alamar abinda Bala ya fada a wannan karon me yuwu ba bane amma idan ya tuno tarin qaunar da takeyi masa a baya fa se yaga kamar hakan zata yuwu.

Amma ze gwada koda na wata dayane ya gani amma fa daga haka baze iya qara haquri ba, in har bata sakko ba to shi ze ajiye girman kanya nemi sulhu da ita kamar yanda likita ya bashi shawara.

A gidan Bala ya wuni har dare, abinci kuwa se siyowa sukayi dukda har sannan ba wai ya ji garau bane.

Haka ya qarasa cinye satin kafin ya koma aiki yayi iya qoqari gurin rage damuwarsa amma abin ya faskara akullum cikin tsoro da fargaba yake kwana da tunanin rasa Asma'u. Sam ya kasa samun kwarin guiwar da Bala yake ta nanata masa yana ganin lokaci yayi da zeje ya zube guiwoyinsa a gabanta ya roqesta koda kuwa zata sake koda masa marine indai hakan ze sakko da ita daga fushin da take dashi ya amince ta tsinko darbejiya ma ta dake shi son ranta.




Ayi manaji da wannan please na shiga hidimomi ne 🙏🙏🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 54

Washe garin ranar tun goman safe Bala ya sake zuwa, yau ma wuni sukayi dai suna ta tattaunawa duk dai akan Asma'un ne har kuma yamma Bala beyi shirin tafi ba seda Bashir da kansa ya tambayeshi wai ba yace aiki ne ya kawo shi ba yaushe ze fara.

Cikin kame kame Balan yake ce masa
"Eh daman aikin na kwana daya ne mun gama kawai dai ina so na huta ne. Ni na gaji da zaman gida ma mu fita waje mu sha iska kuma ita wannan matar daman haka take bata dafa abinci ne?"

Shiru Bashir yayi masa harya qaraci surutunda yayi shiru, be haqura ba bayan wani lokaci ya sake ce masa su fita waje dole ya takurawa Bashir din seda suka fita wajen suka saka kujeru suka zauna.

Basu jima a gurin ba motar makaranta ta sauke yara, gaba daya suka gaishe su, Bala ya kamo hannun Abdallah yana cewa

"Abdallahn Mami an dawo kenan. Ya naganku a school Bus ina Mamin taku?"
"Daman a school bus muke dawowa" Abdallah ya fada yana shigewa cikin gida yabi bayan yan uwansa.

"Wai mutumin ta dena dakko yara daga makarantar kenan?" Bala ya fada yana yar dariyar nan irin ta wanda yaso munafunci akayi sa'a ko kallonsa Bashir beyi ba hankalinsa yana kan wayarsa da yake dannawa.

Kusan minti talatin wata hadaddiyar mota Toyota latest model Baqa ta kunno kai cikin layin, daga Bashir har Balan da ido suka bita harta tsaya a daidai qofar gidan Ma'u, seda aka kwashi yan mintina kafin qofar ta bude ta zuro fararen qafafunta da suka sha Jan lalle sukayi shar dasu ga wasu hadaddun takalma na yan gayu masu tsinin dunduniya data saka.

Lokaci daya ta fito gaba dayanta, tana sanye da straight gown ta Ash din Leshi tayi daurin nan nata na tsokano sharia kunnenta saqale da AirPod tana murmushi da alama waya takeyi ba tareda ta kalli ko ina ba ta qarasa bakin qofa ta kwankwaso Amnah tazo ta bude tareda karbar jakar hannunta suka maida qofa suka rufe.

A tare Bashir da Bala suka sauke wata Ajiyar zuciya. Shi Bashir tashi ta ganin Asma'u ce ita kadai ta fito daga motar saboda yanzu har fargaba yake yaga sabuwar mota me kyau a layin tunda Asma'u ta fara kule kulen nan idan yaga mota ta shigo zuciyarsa ta ringa lugude kenan harse yaga wanda yake cikinta sannan hankalinsa yake kwnaciya.

Bala kuwa tsabar yanda Haduwar Ma'u ta tafi dashi ne se bude baki yake amma ya kasa cewa komai harta shige gidan se ya sauke ajiyar zuciya ya waiwaya yana kallon Bashir yace

"Kaga wata Arniyar mota Alaji ga kuma hadaddiyar mata ta fito daga ciki kai ina ma ace na samu irinta ai wallahi komai ma zan iya bayarwa indai zan mallaki wannan".

"Asma'u ce fa" Bashir ya fada yana jifansa da wani kallo, Bala kuwa ko a jikinsa sema tabe baki da yayi yace

"Ita dinfa, Allahna tuba ni ko Asma'u na samu ai da mugun gudu zan karbeta dan ni nasan darajar irinta. Ai wallahi ban taba sanin kai lusari bane se randa kace mun ka saki Ma'u, yo Allah na tuba ko yankar naman jikina zata ringayi ai zan jure kai in fita ma a kalleni ace ga irin matar da nake aure ma ai martaba ce".

Sakin baki kawai Bashir yayi yana kallon Bala daya dage yana rattabo magana, Lusari daya kira shi ma be dame shi ba kamar jingina kansa da Ma'u da yayi. A mugun fusace ya shaqo wuyansa jin yana ci gaba da maganarsa yace

"Idan ka sake hada kanka da Matata sena yanke maka harshe..."

"Malam tsohuwar matarka dai ko ka manta ka sake ta ne, kuma wallahi dan dai bazata saurareni bane amma duk da haka ma bari kaji sena gwada sa'a ta waya sani ko rabo na ne ya rantse Allah ya matse ka ka saketa" Bala ya fada yana banbare hannun Bashir daga wuyansa.

Tsabar mamaki Bashir daskarewa yayi a gurin be dawo hayyacinsa ba seda Bala ya kusa barin layin ko kafin ya yunqura ma ya bace masa.
Naushi ya kaiwa Iska cikin azababben kishi da fushin da suka turnuqeshi.

Kenan angiza me kantu Bala ya ringa yi masa yana nuna masa aibun ta yana qara kambama masa laifuffukanta har seda ya rabu da Ma'u shine yanzu ze zo yana cewa idan ya sameta shi baze rabu da ita ba. Wai ma ina hankalinsa yake da duk be taba lura da hakan ba se yanzu?

"Kaico na dana zama me daukar zugar was akan iyalina, kaicona ni Bashir da na fifita lalataccen Aboki akan masu gaya mun gaskiya" ya fada yana dafe kansa.

Cikin gidansa ya koma suka hadu da yan biyu zasu fita da gudu ya kauce musu yana binsu da kallo cike da tausayin kansa.

Haka kawai ya raba musu kai ya saka suna rayuwa tsakanin gidaje guda biyu. Shidai ya yarda da qaddara ce ta gifta data tilasta rabuwarsa da Ma'u kuma Allah kadai yasan hikimar sa tayin haka. Baze sare ba yanzu nema ze daura dambar gyaran kuskurensa ya kuma maido da Asma'u cikin rayuwarsa kota halin qaqa.

Dakinsa ya shiga ya tarar da Amirah tayi daidai akan gado tana sauke numfashi, fuskarta ya kalla kafin ya kalli qasan Tiles yaga amai ne a Gurin. A mugun fusace yace mata

"Ki tabbata kafin na shiga na fito kin gyara gurin nan yanda kika tarar dashi idan ba haka ba na lahira se ya fiki jin dadi yau a gidan nan" yana gama fada yayi gaba ze shige bandaki ya jiyota cikin kuka tana cewa

"Nifa bani da lafiya, zuwa ma nayi na gaya maka shine amai ya kamani gaskiya bazan iya tashi bama bare na gyara guri".

"Ko mutuwa kike kina tashi se kin gyara gurin nan, duk gidan nan nan gurin ne yayi miki kama da kizo ki zuba qazantarki? Amma karki kwashe ki jira na fito na tarar dashi a nan" ya shige Bandakin ya barta a gurin.

Yanayinsa da ta gani tasan tabbas ba tausaya mata zeyi ba idan ya fito din, haka ta tashi ta dakko tsintsiya da abin kwashe shara ta debe kafin ta debo ruwa da mopper ta gyara gurin se haki takeyi tana gamawa ta wuce dakinta ta ta fada kan gado kawai ta fashe da kuka.

Wannan masifa har ina? Ace kana da ciki amma banda hantara da kyara ba abinda yake shiga tsakaninka da uban cikin se baqin rai to ko ana so ko ba'a so seta haife cikin nan sedai baqin ciki ya kashe mutum.

Bashir kuwa yana shiga ruwa ya sakarwa kansa ba tareda ya cire kayan jikinsa ba. Kalaman Ba ne suke masa yawo a kwakwalwa suna barazanar fasa masa ita.

Shi Bala zece yana son matarsa? A yanda ya dauki Bala ya zata ko mutuwa yayi se inda qarfinsa ya qare gurin kare masa martabar gonarsa amma se gashi da ransa rabuwa kawai sukayi yana iqirarin idan zata so shi ze aure ta gaskiya dole ya koyawa Bala hankali ta yanda ba matarsa ba ko wata can a gari aka saka baze sake sha'awar cewa ze aureta ba.

Tsabar yanda kansa ya dauki zafi haka ya fito jikinsa na digar da ruwa ya manta da kaya a jikinsa seda ya kai tsakiyar dakin kafin ya ja tsaki ya koma ciki, wanka ya sakeyi ya fito.

A gurguje ya shirya, gidan Musa yake so yaje yanzu yana buqatar wanda ze fadawa abinda yake ransa ko zeji dadi.

Sanda ya fito bebi takan Amirah ba, a bakij qofa ya hadu da Jafar ya taho da paper bag a hannunsa suna zuwa kusa yaji qanshin Snack be bata lokaci ba ya miqawa Jafar din hannu ya kuwa bashi ya tsaya kawai yana kallonsa.

Meatpie ne guda uku manya a ciki, se ya zaro daya ya miqawa Jafar din Murya a cunkushe yace masa
"Dakko mun Exotic ne sanyi" Jafar ya kwasa da sauri ya wuce Kitchen kafin ya dawo har Bashir ya kunna mota yana bashi kuwa ya qara gaba.

Yana tafe yana cin Meat pie yana kora lemonsa can qasan zuciyarsa kuwa yama rasa wanne tunani ze kama yayi a haka ya qarasa gidan Musa ya tarar be taso daga aiki ba se ya kirashi a waya yace masa yana hanya ya kusa qarasowa dan haka ya jira shi.

Seda sukayi sallar Magriba sannan suka shiga gidan. Musa na tattare kayan da suke kan kujera yace
"Se haquri Engineer kasan gidan Gwauro ko ina ma zubarda kaya muke tunda bamu da masu tattare mana"

Bashir dai yaqe yayi har Musa ya gama ya dakko musu ruwa da Lemo da Abincin daya taho dashi ya zauna se ya kalli Bashir da yayi shiru ya zubawa guri daya ido yace

"Yadai Bash naga kayi shiru ko dai jikin ne har yanzu?"
Numfashi Bashir ya sauke yana gyara zama yace
"Musa akwai matsala ina jin kamar kaina ze fashe wallahi damuwa tayi mun yawa".

Musa daya debi abinci ya kai baki yayi saurin hadiyewa yana kallon Bashir ya gyara zama yace

"Wace irin Matsala kuma Bashir meya faru?"

Ba bata lokaci Bashir ya shiga lissafa masa abinda ya faru tun daga kan dalilin sakin Ma'u har zuwa yanayin da ake ciki a yanzu haka da maganar da Bala ya fada masa. Musa da tuni ya sume a zaune yana kallon Bashir seda ya kai aya kafin yaja numfashi ya dire yace

"Gaskiya Bashir ka tafka wauta qundumemiya ma kuwa kai wa yace maka ana rabuwa da matar fari, matar dakuka sha wahalar ku tare sannan yanzu ka saketa akan wata can da ka ganta rana tsaka Bashir ka rabu da matar ka uwar yayanka gaskiya ka bani kunya ka kuma bani mamaki tsahon lokacin nan ace baka tare da Asma'u amma baka gaya mun ba.

To ni yanzu me zanyi maka ma ai ka riga kwabarka tayi ruwa sedai na baka haquri kawai Allah ya kawo maka dangana amma duk macen dakayiwa haka ka sake ta akan yar uwarta mace gaskiya da wuya tayi haquri ta sake dawo maka dan ka rigada ka nuna mata iyakarka ka nuna mata cewar waccen ta fita martaba da mutunchi a gurinka to zaman me zata sakeyi da kai?"

"Haba Musa kaida nazo neman mafita a gurin ka ya zaka ringa magana haka?
Dan Allah ka taimakamun ka bani magita ina son matata bana so na rasata" Bashir ya fada kamar me shirin saka kuka.

Musa kuwa Ido ya saka masa yayi tagumi yana kallonsa har yayi ya gama sannan yace

"Kanaji ko shawarar da zan baka kawai ita ce ka tafi malam ka gwada sa'arka, wani girman kai duk ba naka bane yanzu dan ka rigada ka kwafsa yawwa kaje ka sauke kai qasa ko roqeta in Allah ya soka ta haqura ta dawo maka shikenan amma dai Asara kam ka tafka wallahi".

Haka suka rabu da Musa ya koma gida yana sake tunanin abinda ya gaya masa kuma ya tabbatar hakan shine mafita dole ya nemi yardar Asma'u dan baze tsaya yayiwa kansa salalan tsiya ba.

Ya tarar da Amirah na fama da kanta tayi amai ta galabaita kamar bazata kai ba, dole ya dauketa suka tafi Asibiti saboda yanayin jikin dole se gado aka bata. Seda ya biya duk abinda ya kamata kafin ya barta ya tafi gida da yaje be tarar da Yaran ba Aliyu ne kadai yace sauran suna gidan Mami. Be damu ba yayi kwanciyarsa, dan yanzu yafi samun kwanciyar hankali ma idan suna can saboda anan sun ringa tsokanar Amirah ita kuma tayi ta sababi tanazage zage.

Washe gari ya kamata ya koma aiki haka ya tattara ya fita seda ma ya kusa isa ya tuna da Amirah dake Asibiti be biya ya dubata ba bare ya kai mata abinda zata ci duk da dai Asibitin suna bada Abinci.

A waya yayi order abinci ya basu Adireshin Asibitin dan baze iya komawa ba, haka ya wuni sukuku a gurin aiki se sannu ake masa dan duk a zatonsu jikin nasa ne har sannan be gama warwarewa ba haka ya tashi kai tsaye ya wuce Asibitin dan duba halin da Amiran take ciki.

Da kuka haiqan ta tareshi tana masa qorafin baya sonta be damu da ita ba tunda ya banzatar da ita a Asibiti be sake bi ta kanta ba. Ganin mitar bame qarewa bace ya tafi ya barta dan abinda yake kansa ma a yanzu ya isheshi bayay buqatar qarin wani abun kuma.

Ya isa gida ya kasa tsaye ya kasa zaune. Tunanin yanda ze tunkari Ma'u yakeyi, meze ce mata? Ta yaya ze tunkareta?

Wayarsa data dauki qara ce ta katse masa tunani, shnan Dada da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login