Showing 210001 words to 213000 words out of 260321 words
Chapter 71 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
Shafa’i da wutri na nayi Addu’oi kafin na fito palour ina jin badan dare yayi ba da tabbas sena fita na siyo naman nan dan dai bazanci na hannun Bashir ba.
Turus nayi daga bakin qofa ina kallonsu yanda sukayi face face da naman sunaci wasu nacin shawarma.
“Yanzu Amnah me na gaya miki?” Na fada ina kallonta, se tayi saurin ajiye Naman hannunta tana zare ido tace
“Wallahi Mami shiya ce mu cinye kuma ma seda Addah da Anty Amirah suka diba da gaba daya ma suka qwace seda Abbi yayi ta masifa kafin suka bamu kuma Addah ta sake biyo mu ta dibar musu”
“Shikenan ai kun kyauta, idan kin gama ki dafa mun Indomie ki kawo mun” na fada ina komawa ciki.
Wayata na dauka, Ina so na kira Yusuf wata zuciyar kuma tana hanani. Saqo ne ya shigo wayata, Bashir ne na bude na fara karantawa bansan sanda na bushe da dariya ba saboda ganin irin abubuwan da ya rubuto wato kalaman soyayyane kala da kala a ciki gaba daya se naga abin wani banbarakwai.
Ina gama karantawa na goge shi ina tuno da wani saqo da Yusuf ya turo mun dazu da yamma se kawai na danna kiran lambar sa.
“Allah yasa muga Annabi” ya fada yana daga wayar, senayi murmushi me sauti nace
“Amin”.
“Amma Asmy batan lamba kikayi ko?”
“Me ka gani?”
“Babu komai, kawai dai nasan kina sane bazaki kirani a waya ba sedai tuntuben lamba kikayi”
“To shikenan bari na kashe tunda haka kace” na fada kamar zan kashe din se yayi saurin tare ni da cewa
“Aa bafa haka nake nufi ba, Allah ya taimaki Amaryar Yusufa barka da dare toh ya kike?”
“Barka dai Excellency ya aiki ya Jama’a?”
“Aiki Alhamdulillah kinsan kuwa yau wunin Site nayi na dawo duk na gaji wallahi Asmy, ya gida ya yara ya kuma kewata?”
“Ni na rasa irin son kudinka dai Yusuf, idan ba haka ba dan Allah ina kai ina Wani supervision na aiki? Dan Allah ka barwa sauran Jama’a suma su samu mana”
Dariya yayi yace
“Asmy kenan, nifa ko Inyamuri baze nunamun neman kudi ba, dazu naje wani qauye zamu siyo gyada muna zuwa suka lullube motata nace kai ku matsamun ni ba wannan ya kawo ni ba neman Halal na fito yau”.
Dariya sosai nayi, daga nan muka shiga hira har Amnah ta kawo mun Indomin, Allah Alah nake mu gama magana ba tareda ya taso mun da zancen dazu ba, seda zamuyi sallama kuwa yace
“Saura kwana shida, ina Addu’a Allah yasa naji Alkhairi”
“Amin Allah ya sa muga Alkahiri” nima na fada daga nan mukayi sallama.
Ban kwanta bacci ba se gurin uku da rabi na dare, sosai nayi sallolina da Addu’oi na rufe da sallar Istikara tareda kyakykyawan yaqinin samun haske a cikin al’amarina na kuma bude zuciyata ko Bashir, ko Yusuf ko ma wani ne daban Allah ya zaba mun zan karbe shi nayi fatan ya zame min siradin zuwa Aljannah.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 57
BASHIR
Iya bakin qoqarinsa yakeyi gurin aiwatar da abinda Musa ya gaya masa, duk yanda yasan ze shawo kan Ma’u yi yake amma kamar wadda yake qarawa wuta fetur daman baya samun ta a waya duk ubannin saqonnin da yake tura mata kuwa bata taba maido masa da ko guda daya ba.
Ya rasata ina ze sameta suyi maganata fahimta, baya son zuwa gidan ta tunda tace masa bata so amma dole ya zama me gadin qarfi da yaji, da wuri yanzu yake baro office yazo kanlayi ya kasa ya tsare amma ko sun hadu ma wani shashasha take mayar dashi dan daga gaisuwa bata ma bashi damar magana zata wuce abinta.
Abun na bala’in ci masa tuwo a qwarya, ga azumi yana gaba towa baya so suyi azumi a wannan yanayin. Gidansa daman tuni yafi qarfin sa in har yana son nutsuwa to fa sedaiya fita waje dan karadi da surutun Addah kadai ya ishe shi. Shi bata barshi ba ita Amiran da take fama da kanta itama bata tsira ba ga jaye jayen magana da take dakko masa haka kawai seta wanke qafa ta shiga gidan maqota kuma in dai taje seta takalo wani abun haka za’ayi ta tararsa ana kawo qararta sedai yai ta aikin bada haquri.
Kusan sati ana wannan yanayi ranar yana zaune da daddare a dakinsa haka kawai zuciyarsa ta ayyana masa kiran Goggon su Ma’u.
“Nasan tana sona da Ma’u kuma ita kadai ce zata fahimceni a yanzu in Allah ya taimaka seta shawo mun kanta a sanyi komai ya daidaita” ya fada a fili yana janyo waya cike da kwarin guiwa ya shiga kiran Goggo.
Seda ta dan jima tana ringin kafin ta daga da sallamarta suka gaisa yanda suka saba yana tambayarta jikin Baffa tace da sauqi kafin itama ta tambayeshi su Amirah da yara yace duk suna lafiya se sukayi shiru gaba daya.
“Lafiya dai ko Bashir naji kayi shiru” Goggon ta katse masa shiru, seda ya hadiyi wani yawu kafin ya gyara zaman sa ya sunkuyar da kai kamar yana gabanta yace
“Daman Goggo kira nayi in bada haquri, wallahi nauyi da kunyarki ta saka tun lokacin da abin ya faru na kasa kiranki se yanzu dai na daure nace bari na kira”.
“In banda abinka Bashir meye abin bada haquri kuma kamar wanda ya aikata wani laifi, shi zaman aure ai raine dashi idan lokacin mutuwar sa yayi kuma ba yanda aka iya ko da dalili ko babu haka ana so ba’a so za’a rabu, karka ji komai wallahi Allah yasa hakan shi yafi Alkahiri a gare mu baki daya” Goggo ta fada a sake babu damuwar komai tattare da ita.
Cike da qarfin guiwa Bashir ya shafa kai yace
“Hakane wallahi duk abinda ma ya faru Goggo laifi na ne kuma dai sharrin shaidan ne amma yanzu na gane kuskurena kuma in Allah ya yarda haka bazata sake faruwa ba”
“Ai ita rayuwa daman haquri akeyi amma babu komai ai koma dai laifin waye a cikin ku Ai abubya wuce Allah yayi wa kowa zabin Alkahiri a gaba”
“Ai Goggo Alkahiri dai yana nan tare damu dan in sha Allah zamu koma kuma babu abinda ze sake faruwa a gaba se Alkahiri, badan ma wancan tsautsayin daya faru ba ai da yanzu ma ta dawo dakinta qila tana shirin haihuwa koma ta haihu amma yanzun ma muna saka rai in Allah ya yarda kafin Azumi komai ze daidaita.” Bashir ya sake fada da qarfin guiwa.
“Toh haka da sauri har kun daidaita kenan?” Goggo ta tambaya cikin mamaki, se ya shafa kai kamar yana gabanta yace
“Aa dai tukunna, kinsan mutuniyar ne akwai rikici itama wani lokacin to har yanzu dai inata ban baki ne amma taqi ta bani dama amma nasan dai in aka ci gaba zata haqura shi yasa ma na kira yanzu ko za’a dan taimaka a saka baki tunda tana jin maganar ku qila tafi saurin sakkowa”.
Seda Goggo taja ajiyar zuciya tana jinjina qarfin halin Bashir kafin ta iya ce masa
“Eh to ai duk da na gari da yake so yaga daidai dole yaji maganar iyayensa. Zancen mu saka baki kuma ai bata taso ba Bashir dan a yanzu Addini da kansa ya bata damar zabar abinda take so dan ta wuce Budurwa bare ace za’a fada mata yanda zatayi.
Idan taga tana da sha’awar zama dakai mu masu yi muku Addu’ane idan kuma tace Aa shikenan se muce Allah zabawa kowa rabon Alkahiri”
Yanda kasanta saka guduma ta kwade masa guiwoyi haka yaji duk ya rikice har wata zufa ce ta tashin hankalo ta shiga zubo masa. Cikintawar murya yace
“Goggo a haqura kuma dan Allah a dai duba ko dan darajar yaran nan Goggo be kamata mu rabu ba”
“Yo Bashir mantawa kayi dasu sanda ka saketa ne? Kuma ina duk cikinsu babu me shan Nono. Daidai da Biyu sun isa su riqe kansu su zauna ba tareda uwarsu ba shekara Bakwai ai da yawa idan ma kuma kana ganin bazaka iya riqe su bane seka kawo mana daman kai ka damu da abaka yayanka amma mu muna so zamu riqe su Allah ya raya har zuwa sanda zasu mallaki hankulan kansu.
Sannan daman ina so na kiraka akan zancen Farida, kaga ita mace ce to na nemi alfarma ka barwa uwarta ta riqeta samarin kuma su zauna dakai shikenan. A gaida matar gidan Da yaran se anjima” tana gama fadar haka ta kashe wayar bata ma bashi damar sake wata magana ba.
Kamar wanda akawa mutuwa haka ya zabga tagumi tunda Goggo bata goyon bayansa toh ina ze kama??
ASMA’U
Sosaina dage da kai kukana da neman zabi zuwa ga sarkin sarakai. A wannan taqin tsakanin Yusuf din da Bashir har na rasa wanda yafi uzzurawa rayuwata dan yanzu Bashir ya dage saqon ban haquri da kalaman soyayya karo da karo seya turo mun Ashirin a rana haka kiran waya sedai nayi ta ganin missed calls dinsa tunda nayi blocking layin se kawai nayi murmushi na share.
Sauqin dana samu da Yusuf tafiyar gaggawa data same shi zuwa qasar Turkiyya zeyi wata daya dan se cikin azumi sannan ze dawo.
Yanzun kam Wasai nake jin zuciyata duk wannan qunci da takura da nake ji da wata makauniyar soyayya yanzu ya yaye, ina matsayin da zan iya karbar ko wanne irin al’amari hannu biyu bani da wata matsala tartibiya, rayuwata kawai nake a kullum kuma ina nanata Addu’ar neman zabin Allah a dukkan lamurana ba tare da na gajiya ba.
Shirye shiryen shigowar watan ramadan muka fara, ana saura kwanaki uku a dauki azumi ranar da wuri na taso daga aiki saboda ina so muje muyi siyayyar abubuwan da bamu dasu.
Seda mukayi sallar magriba kafin muka fita, na saka simple doguwar riga da hula se na yafa siririn mayafi a kaina muna tafe muna hira da Jafar dana dauka yamun rakiya. Ina ajiye mota ya juyo yana cemun
“Lah Mami ga motar Abbi, shima yazo siyayya daman dazu da safe naji yana cewa Anty Amirah tayi list tace wai sedai su taho tare..”
“Jafar na hanaka wannan shegen surutun amma baka ji tambayarka nayi ko yaya” na katse shi ina qoqarin fita daga motar. Biyo bayana yayi muka shiga supermarket din, kai tsaye Gurin buhun huna muka fara biyawa dan akwai Kunu da qosan sadaka da ake mana duk azumi sanda muna tareda Bashir, wannan karon ma bazan fasa ba. Dan har a Gombe ina so ayi dan sosai na samu rarar kudin hayata bana, an fitar da lissafin zakka da komai amma dukda haka na samu kudi har mamaki nake to wai da duk ina suke shigewa da bana gane lissafin ne.
Wake da Gero se pastar mai muka siya na bar musu tunda motata bazata dauka ba sa kawo mana gida se muka wuce cikin kantin muyi abinda ya kaimu, ina tafe ina amsa wayar da Goggo ta kirani. Saka Albarka ne da addu’ar fatan nasara da dacewa a duniya da lahira taketa zubamun dan se yau aka gaya mata batun Umarar dana biya mata.
“Idan naje zan dage da yi miki Addua Ma’u, Alah yasa da an sallace ki fitar da miji kiyi aure dan zama haka ba qimar mace bace sam” ta fada. Sena marairaice ina cewa
“Kai Goggo gaba daya wata nawa ba auran biyar fa shine har zaki fara maganar na sake wani, nidai ba yanzu ba danni makaranta ma zan koma na qaro karatu”.
“Sanda Mahaifinku ya mutu Allah ya jiqansa watan mu biyu da fita takaba na daura aure da Modibbo dukda shekaruna ba kuma nayi aure dan wata buqata ko jin dadi bane Aa nayi ne dan samun lada da cika wasiyyar mahaifinku seke yanzu da quruciyarki zakice bazakiyi aure ba.
Me kika dauki kanki ne Asma’u? Gaba daya fa shekarunki Talatin da shida ne a duniya dan kinyi aure da wuri kin tara Yaya ne yasa kike daukar kanki kamar wata uwar mata kome? A yanzu fa da akwai yammata Sa’anninki dama wanda suka girme miki da ko auran fari basuyi ba ballantana kice kin kai shekarun da maza bazasu so ki ba.
Ina da duk labarin wadanda suke sonki ai, ba’a rufa sati ba har nan Yayanku ya rako wannan yaron Yusuf ya gaishe ni sannan a nan ma Himu dan gurin Addah Sadiya (Yayar Goggo ce) yayiwa Yayanki Muslim magana shi ya dakatar dashi shi yasa ma bakiga yazo ko ya kiraki ba.
To ki tsayar da hankalinki wallahi daganan zuwa a sallace ko ki fitar da miji ko ki tattara ki koma can gidan ku ki zauna dan bazan lamunci zamanki a bariki ke kadai ba aure babu wani Muharrami, ke ko kunya ma bakyaji yanzu a fara sallama da Amina ke gaki uwarta babu aure wa ze dauke ku da muhimmanci ma”.
Baki na tura jin daga maganar arziqi ta koma fada kuma. Jifa kuma inda ta juya wace Amnan za’ayi sallama da ita yanzu fisabilillahi? Ni dana san ma wannan maganar zata tayar da tunda ta kira na bata uzurin ina waje idan naje gida na kirata.
Fadan ta taci gaba dayi dan itama fa Goggo akwai Mita in ta kama zance daya, daga qarshe ta rufe da zancen kwashe kayana na gidan Bashir na Gombe
“Ko da Bashir din kuka daidaita ne naga babu wanda yayi maganar kwashe kaya ko kuma kin bar masa ne ban sani ba? Daman cikin satin daya wuce ya kirani yana wasu soki burutsun banzansa nidai ban bashi fuska ba” ta fada.
Se a sannan ma tuna ma da inada wasu kaya a gidan Bashir na Gombe , cikin qaguwar karta kuka daddago wata maganar nace
“Za’a kwashe Goggo, kinga ai bamu zo gari ba muqullin kuma yana nan tare dani shiyasa, amma da munzo hutun sallah in Allah ya yarda za’a kwashe”
“To yadai fi dan karma naji wani zancen kome ko wani Abu indai ba kuma haka Allah ya qaddaro ba gara ayi addu’a Allah ya hada kowa da rabonsa na Alkahiri”.
Wani iri naji, wato duk yanda take son Bashir yau da kanta take cewa babu zancen kome gidan sa lallai Bashir ya bata rawar sa da tsalle.
Sallama mukayi, jafar ya dauki qatuwar Trolly muka fara zuba kayan da muka zo siya. Can gurin da ake ajiye su nama muka ci karo da Bashir da Aliyu daga uban har dan kowa ya kalli gefe ya tura baki sama kome suke jira oho ga dai trollyn da suka fara zuba kaya nan a gabansu.
Kallo daya nayi musu na mayar da hankali na kan Freezer na fara ciro abinda nake da buqata ina sakawa a cikin Trolly, gaba daya hankali na ya tafi a abinda nakeyi se jin magana nayi daidai kunnena har seda na tsorata na dago da sauri muka hada ido da Bashir dake tsaye dab dani.
“Meye haka zaka tsoratani” na fada ina harararaa qasa qasa, se ya marairaice kamar wani yaro yace
“Ma’u me yasa bakya amsa kirana? Idan na turo miki saqo ma bakya bani amsa me nayi miki dan Allah?”
Kallonsa nayi tareda jan gajeran tsaki se kawai na juya ina cewa Jafar
“Muje, in suka bar gurin se mu dawo”
“Kiyi hauwa dan Allah ki tsaya, kinga muma shopping muka zo gaba daya na manta abubuwan da kike siyo wa na taho da Aliyu yace shima be sani ba” Bashir ya fada yana shan gaba na.
Se na tsaya ina kallonsa a raina nace
“Tunda ba kai kake siyowa ba ai daman bazaka sani ba”
“Dan Allah Ma’u” ya katse mun tunani kamar ze durqusa mun tsabar yanda yake kwantar da murya. Ni mamaki ma yake bani wai Bashir dai me kamar Boss shine yake karya murya haka yana roqona ashe daman ya iya ikon Allah.
Ba tareda na kalle shi ba nace
“Me dame zaku siya”
“Duk abinda ya kamata na girki saboda Azumi banda kayan abinci da mai” yayi saurin bani amsa.
Tare muka ringa zagayawa, ina da list dina a kai dan haka komai na dauka se Aliyu ya daukar musu ina kallonsa se bata rai yake haka tunda ya gaishe ni be sake magana ba kamar wanda akayiwa dolen zuwa.
Siyayya mukayi da yawan gaske dan daman ni abinda ya kawoni kenan cefanen mu yayi qasa sosai, da mukaje gurin biyan kudi na zaro ATM dina zan bayar yayi saurin tarewa ya miqa nasa ban ja ba na maida abuna Aljihu ai daman tare zamu ci da Yayansa.
Seda aka loda mana kayan mu tsaf a mota na kalleshi fuska a sake nace
“Baban Ali se da safe toh a gaida Iyali mun gode” na kama murfin motata zan shiga ya riqe yana cewa
“Dan Allah ki unblocking dina, kuma koda wani layin na kira bata shiga ki taimaka ina so muyi magana ne tunda kin ce bakya so nazo gida”
“To shikenan zanyi” na fada bawai dan zanyi da gasken ba Aa dan kawai ya qyale ni na tafi. A tare muka jera ina gaba yana bayan mu har gida.
Ina shiga na tarar da an kawo mana kayan dinkinmu na sallah. Seda muka gama jera siyayyar da mukayi kafin na fito da kayayyakin nawa ne dana Amnah da Farida ina dubawa nace
“Yaushe aka kawo kayan?”
“Kuna fita yazo, yace nasu Aliyu se wani satin za’a kawo wai Be gama wadanda aka kai daga baya ba”.
Wani shegen Lace na daga ina dubawa da mamaki dan dai nasan babu shi a kayan dana bayar dinkin sena kalli Amnah nace
“Wannan kamar ba namu ba inaga Hassan ya rikice ya sako mana kayan wasu, miqo mun wayata na kirashi naji”
Wayar ta bani na shiga kiran Hassan Tailor, seda muka gaisa yake cemun nayi haquri fa be hado dana mazan ba ya bari ne a gama dukka saboda na baya da Alhaji ya kai sune ba’a qarasa ba.
“Wane kaya aka sake kawowa kuma Hassan? Sanan naga qari akan namu ma inaga na wasu ne ka hado dasu fa”
“Aa Hajia dukka Alhaji ne ya kawo su wancan satin ai” ya bani amsa.
Sallama mukayi ina ta mamakin wai Bashir ne ya kai, ashe yasan shagon Telan kai abubuwan mamakin nasa dai suna da yawa.
An kama Azumi Ramadana, yanda nake fita aiki na dawo a nutse har na kama wasu ayyukan gida yana bani mamaki. Sena tuna Azumin da suka wuce tun