Showing 6001 words to 9000 words out of 260321 words
Chapter 3 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
drawer dan Nurse tace karsuyi motsi me girma daze farkar da ita ya qarasa gefen gadon yana kallonta tayi wani fresh tana bacci kaman bame ciwo ba se ya rankwafa kanta tareda kissing goshinta, under his breath yace “get well soon my Ma’u, I’m sorry for hurting you”.
Zaman kurame sukayi shida yaran kowa na tunanin abinda ya dame shi basu Ankara ba se jin kiran sallar Magriba sukayi se a sannan ya tuna ai ko La’asar beyi ba. Shida Aliyu suka tafi masallaci har suka dawo kuma bata farka ba dan haka cikin damuwa ya koma gurin likita yana gaya masa.
“Babu damuwa mun mata Alluran bacci ne dan ta samu ta huta sosai jinin ya sauka zata farka amma se zuwa cikin dare, kaje kawai kayi settling bills babu buqatan me jinya Nurses din mu zasu kula da ita”.
Jiki a sabule ya koma dakin, Gurin da Su Aliyu suke ya kalla yace su tashi su tafi gida
“Abbi ni zan kwana a nan” cewar Amna
“Aa baa barin me jinya mu tafi da safe kafin ku tafi school se mu biyo ku dubata”. Dakyar suka tafi har shi kansa ji yake kaman ya sake zama sedai tuna sun bar sauran yaran yasa dole suka tafi bayan ya biya kudin duk abinda ya kamata ace ya biya din.
ASMA’U
Basufi awa uku da tafiya ba na bude ido lokacin qarfe tara na dare harta dan gota, jinina yana da qarfi sosai ba kasafai Allurar bacci take daukata na dade ba. Sakayau na tashi kaman an zare mun qaya dukda bansan ainihin abinda ya same ni ba amma babu ciwon kan babu jiri se kawai kasala da nake ji da kuma bakina da sam ba dadi. Ina qoqarin miqewa Nurse ta shigo tana ganina ido biyu ta fada da fara’a tana cewa “Sannu patient har kin farka lallai kina da qarfin jini muda muke tunanin se kin kai gobe ma”
“Murmushin na mayar mata cikin muryar marasa lafiya nace “gashi har na tashi kam amma naji dadin jikin ma sosai ai”
“Karki tashi Bari na sake duba Bp na gani” ta fada ganin ina qoqarin miqewa daga gadon, zama na koma nayi ita kuma ta dauko Abun auna BP, seda ta gama ta kalleni still tana murmushin tace “kinga kuwa yayi normal bari na hada miki ruwa to ki wanke jikinki dukda naga bakiyi staining bama se kici abinci”
Kallon rashin fahimta na bita dashi fahimtar haka ya sakata Dafani tace “I’m sorry kin samu miscarriage saboda faduwan da kikayi”
“Miscarriage kuma? Cikine dani daman?”
“Eh almost 3 months ma baki sani ba?” Ta jefin tata tambayan, se lokacin na gane a fili nayi magana. Sena qaqalo murmushin dole to ban ma san me zance ba dadi zanji ko rashin dadi ma oho nan ta barni ta shiga toilet din, mintina kadan ta fito bayan ta tara mun ruwan. Ita ta rakani har toilet din kafin ta baroni na fara wankan.
Sosai naji dadin ruwan bayan na gama nayi brush da sabon tooth brush din data ajiye mun na saka pant da pad da duk a nan na gansu sannan na daura sabon towel babba na rufo kaina da qarami na fito ina jina wata sakayau a raina ina yaba tsarin Asibitin komai nasu tsaf kamar A Turai.
Turus na tsaya kofar toilet din ganin Mutum a zaune bakin gadon dana tashi wanda da alama an kuma chanza bedsheet din kai, haka kawai na tsinci kaina da daure fuska abinda yai ma yara da safe yana dawomun se kawai na juya da niyyar komawa cikin toilet din yai zuruf ya miqe tare da biyo ni kafin na samu damar rufe qofar ya turo ta ya shigo ciki bani da zabi kawai na durqushe a qasa na fashe masa da kukan da ban san nima na menene ba.https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 4
Zama yayi shima a qasan tareda janyoni jikinsa ya rungume yana bubbuga bayana a hankali, cikin qaramar murya yake cewa “I’m sorry Ma’una I’m sorry” ni kuwa kaman yana cemun ki qara volume ne. Kuka nake dagaske kukan takaicin daya dade yana shaqamun, qara tuno wasu abubuwan nake ina qarawa kukan nawa Armashi nasan Bashir baze hanani ba zebarni nayi iya yina ne a cewarsa kuka rahma ne idan yayi yawa ne yake zama matsala.
A duk sanda irin haka ta faru ko yayi mun wani abu da har takaini da zubda hawaye dama shi ba Namiji bane me bada haquri duk kuwa girman laifin da yayi zedai saurare ki da kunne duk irin mita da qorafin da zakiyi se kinci babbar Sa’a ne zece miki “Uhmm” in ta kai maqura daya san shi yake da laifi shine ze rungume ni a jikinsa nayi kukan iya yina yana bubbuga baya na har nayi shiru dan kaina to yau an Auna arziqi har na samu arziqin sorry, Miskili kenan aka ce kafi mahaukaci ban haushi.
Se ya tunamun da lokacin rasuwar mahaifin mu kamar haka ya riqeni nai kuka a jikinsa har seda naji wani kaso na radadin zuciyata ya ragu sannan ya rabu dani ya koma gurin karbar gaisuwa.
Nurse ce ta dawo dakin, sheshshekar kukana da ta jiyo daga toilet ya sakata bude kofar da sauri a zatonta ko wani abun ne ya same ni amma se ta tarar damu
“Haba Alhaji ya zaka barta tana kuka bayan kasan condition dinta please patient taso ki zo ki saka kaya a jikinki kar sanyi ya kamaki”. Fincikewa nayi daga jikinsa na fito ina ci gaba da sheqa kukana, kamar qaramar yarinya haka ina saka kayan baccin data ajiyemun ina kuka har na gama na dauki Mug din tea data hadamun na hausha ina kurba ina kuka kai abun ma abun dariya. Tsayawa tayi kawai tana kallon ikon Allah dan Bashir dai ba sabon abu bane a gurinsa indai Rigimar Ma’u ce, ganin dai dagaske nake ya saka Nurse fita ta kirawo Dr Bolaji.
Tare suka shigo, kallona yayi ya nufi inda Bashir ya tsaya wanda kallo daya zaka masa ka hango tashin hankali da damuwar da fuskar sa ta kasa boyewa, ban san me yace masa ba naga sun fita waje se Nurse din ta juyo wurinata miqa mun magunguna data ballo tana cewa “kiyi shiru kishanye tunda ya tafi se ki kwanta na mayar miki da drip din”
Shirun nayi ina jan majina da ajiyar zuciya hancina kuwa yayi jajir kamar me mura na hadiye kwayoyin tare da gyara kwanciyata raina Fes, a zuciyata nace “Wallahi kadan ka gani yanda zanyi kwanan Asibiti dalilinka kaima bazaka runtsa da dadi ba, ko minti goma ban qara ba bacci ya sure ni ga gajiyar kuka ga allurar baccin data qara a ruwan ko na samu na huta.
Daga ita har Dr Bolaji daya dawo kallona kawai suke Dr yai murmushi ya nufi qofa yana cewa “This Madam na correct trouble maker”
Nurse ta saka dariya kawai tabi bayansa dan dakko abubuwan da zata buqata ita zata kwana dani.
BASHIR
Tuqi kawai yake gaba daya baa nutse ba kansa in banda sarawa babu abinda yakeyi, a duniya babu abinda yake rudashi da hargitsashi irin Asma’u. Matar nan Tasan duk wani lungu da saqo da zata shiga ta tado masa da hankali (kuji fa) in banda fitina irin tata shi yanzu ai ta lafiyarta yake yi amma yaga alama ita neman tada zaune tsayene kawai a gabanta yanzu. Yana tafiya yana jin yadda wayarsa take ta faman vibrating Daidai ya faka motar kira ya sake shigo masa, a mugun fusace ya daga dan yasan Amira ce.
Tun dazun ya gaya mata yana da uzuri idan ya gama ze kirata amma shine take zabga masa kira kamar ta na binsa bashi a qalla ta masa missed calls sunfi 100. Yana daga wayar ta fara magana cikin Son kwaikwayon salon da Asma’u take magana dashi tace
“Yayana ina ta kiranka tun dazun baka answer ba kafasan duk yau banji muryar ka ba ga baby ma yana ta misss.....” tsabar takaici be bari ta qarasa ba ya daka mata tsawar da seda cikinta ya juya sannan ya cigaba
“Ke wacce irin wawuya daqiqiyar yarinya ce, kin kirani nace in na gama abinda nake zan kira ki amma shi ne kika ci gaba da kira kamar kina bina bashi ko? Shiyasa Ma’u ta fiki dan ita bata da shishshigi da wannan mugun takurar, Stupid ki sake kiran wayata wallahi in bani na kiraki ba zakiga hukuncin da zan dauka akanki” qit ya kashe wayar.
Wani huci yake fitarwa kaman kumurci, gaba daya yaji bala’in haushinta yake ji dan itace ummul aba’insin ta komai dayake faruwa. Dukda bata shigo rayuwarsa ba da bata juya masa daddadar rayuwar da suka gino me cike da so, qauna da sadaukarwa ba shida Ma’un sa.
Yafi minti 30 a cikin motar yama rasa tunanin me zeyi se sannan yaran suka fado masa a rai ba shiri ya fito daga motar ya shiga gidan. Gaba daya suna zaune a palour sunyi zuru zuru alamun sun sha kuka sun qoshi har yan biyu basuyi bacci ba, suna ganinsa suka nufe shi gaba daya tareda sake fashe masa da sabon kuka daya sa gaba daya yaji dama shima yayi kukan ko zeji sauqin abinda yake ji a ransa.
Dakyar ya samu sukayi shiru, Amna ya tambaya sunci abinci tace Aa, dare ya rigada yayi dan 12 harta gota dan haka yace ta hada musu cornflake kawai su sha. A qaton bowl ta hado shi suka hadu kowa da spoon suna sha yana kallonsu dan bayajin ko ruwa ze iya bita maqoshinsa. “Kai anya ze iya rayuwa babu Asma’u kuwa?” Ya tambayi kansa
“Idan ta mutu fa” wata zuciyar ta qara tambayarsa
“Kai ina insha Allahu ma sena rigata mutuwa” ya fada a fili ba tareda yasan a fili yake maganar ba da Alama Ma’u na dab da zarar dashi 😂😂
Bayan sun gama yace suje su kwanta amma qememe Suka qi yana tashi suka bishi Amna Farida da Aliyu ne kawai suka zauna a palour, ba yadda ya iya haka ya jera su akan gadon ya shiga toilet ya dauro alwala ya fara sallah dan yasan bama ze iya bacci ba yau, haka yai ta jera salloli in ya gaji ya huta har bacci barawo yai nasarar sace shi.
HAJIA AMIRAH
Sororo tabi wayar da kallo hawaye na kwace mata ta kalli Mamanta Adda Fatu da har tafi Amirah kidima dan a hands free ta saka wayar, ita dama bata so ta sake kiransa ba tunda yace ze kirata amma Adda Fatu ta sata a gaba dan a yau take so ya aikowa da Amirah kudaden da sukayi qaryar zatayi siyayya saboda tafiyarta Lagos amma wani uzurin daban take so tayi dasu.
“Adda kin gani ko bamu samu biyan buqata ba yanzu mun ballo matsala Allah kadai yasan yanzu hukuncin da zeyi mun” ta fada tana share hawaye.
“Ke dalla can ba abinda zeyi miki qarshe ma kiga ya kira ki yanzu ya baki haquri ta yuwu wani ya bata masa rai kika taka sahun barawo” bata qarasa rufe baki ba sukaji alamar shigowar message wayarta, baki washe Adda tace “kingani ko duba muga ko kudin ya sako”
Ita dai Amirah jikinta be bata ba dan tasan waye Bashir a tsorace ta bude message din ashe MTN ne suke gaya mata zata iya aron kati dan nata ya kusa qarewa. Wata muguwar dariya Ummi qanwar ta ta sheqe da ita tana tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace
“Wai ke kin yarda Yaya Bashir ne ze kiraki ya baki haquri to sannu uwarsa, ai wallahi ki shirya ma Allah kadai yasan abunda ze biyo baya dan kinsan sarai fadansa kamar na kurma yake baya mutuwa”
“To se kijie ki saka shi ya dauki matakin ai dan uwarki shegiya me baqar fuska” Amirah ta fada tana hayayyaqo mata
“Gata nan a zaune ai uwar tawa baqar fuska kuma na gode keme farar ai gaki nan kin zama Bora a gurin miji, Allah dai ya rabamu da auran cin Amana” Ummin ta mayar mata dan itama ba baya bace gurin fitsara. Nanda nan fada ya kaure a tsakaninsu seda Adda Fatu ta zuzzunduma musu Ashar sannan suka yi shiru kowa tana harar yar uwarta.
“Shegu kuda baku gudun abun magana a daren nan kunsan an kasa kunne a jiyo zancen mu a yada shine zaku min tijara kishiyoyi naji ni kubarni nayi tunanin mafita ma kun hanani” ta fada tana hararar su duka. Yunqurawa Amira tayi dan cikinta yayi girma sosai ta shiga daki har tana takewa Ummi qafa da gangan
“Salon na taba ki wani abu ya same ki ko to bazan kula kiba aniyarki ta biki” Ummi ta fada.
“Tashi ki shige kafin na rade ki yar kwal uba” Adda Fatu ta fada tana neman madoki, setayi saurin barin wurin dan tasan tsaf zata sha dukan kuwa.
Tunani ta shiga yi ta yanda zata samu kudi kafin wayewar gari, bashi ne tun na lokacin Auran Amirah har yau bata gama biyaba kusan shekara biyu dan a zatonta zasu samu a hannun Bashir din ganin yanda Ma’u take wadaqa sedai tunda akayi auran ita dai bata ga kyautar dunkulalliyar dubu dari yayiwa Amiran ba, ze dai aje mata komai na buqata amma baze bata kudi ba.
Ganin ba mafita kuma ta tabbatar kaman yanda matar tace da safe zata biyo kadin kudinta ko kudi ko kayan kudi tofa rashin mutunchi zata mata dole ta nemi mafita qarshe ta yanke shaqarar zuwa gidan su Bashir din gurin Nafi ai ita Uwarsa ce idan ta kira shi baze qi dagawa ba, da wannan shawara ta kwanta akan asubanci zatayi kafin matar tazo insha Allahu ta dawo.
LAGOS
Malam Bashir kuwa dakyar ya iya farkawa da Asuba kansa kaman an dora masa Dala tsabar ciwon da yake masa, basu iya fita masallaci ba a gida sukayi sallah suka hau shirin makaranta dan zasu fara biyawa Asibiti su duba Mami.
Tea suka dafa suka soya kwai suka karya, basu daukar mata komai ba se kaya kala daya wanda zata saka idan An sallameta tunda Asibitin nada uniform na marasa lafiya baa buqatar kaya haka abinci ma a can ake basu..
A hankali ya tura qofar hadi da sallama, a nutse ta dago ta kalleshi tareda amsa sallmar, fuskarta dauke da wani kyakykyawan murmushi. Magana take yi da yaranta kowa na gaya mata yanda yayi missing nata.
Qara shigowa yayi idanunsa akanta yana qarewa kyakykyawar fuskarta me cike da kalama kallo ganin yanda Omo blue din Uniform din Asibitin ya amshi fatar ta matuqa kamar wasu kayan kwalliya. Aliyu ne ya bashi kujerar da yake zaune akai still idanunsa akan ta yaja ya zauna dukda daqi sake dagowa ballantana ma su hada idanu da ita.
Shigowar Nurse da taje kawo mata breakfast yasa ta daga kanta Yaran suka shiga gaida Nurse din tana amsa musu da kulawa, Dan gyaran murya yayi tareda kallon yaran yace “kuje mota ku jirani kar mu makara idan mun taso se mu sake biyowa aga Mami ko? Basu musa ba da daddaya suka fice bayan sun mata Addu’ar samun sauqi itama Nurse aje kayan tayi ta gaishe shi kafin tayi waje abunta.
Cikin sanyi jiki ya miqe zuwa gefenta da tun kafin ya qaraso ta dauke fuskarta zuwa dayan side din, be haqura ba ya bita, can qasan maqoshinya furta “How are you feeling now? Ina ne yake miki ciwo?”
“Oh really ka damu ne daman da lafiyata toh Alhamdulillah Yanda kaso be samu ba jinina ya sauka ya dawo dadai”. Be kula maganar taba ya sake matsarta yana cewa “Why? Me yasa baki gayamun that you are pregnant ba??”
Ita se a yanzu ma ta gane dalilin wannan fake concern din wato saboda cikin da ya zube, murmushi tayi me kama da yaqe tana tashi zaune sosai tace
“Baban Ai kenan, to ina ruwanka da ina da ciki ko bani da shi naga yanzu ai baka damu dani da yaya nane bako? Ko da yake dama ai bazaka damu ba tunda qaddarace tasaka kuka hada Zuri’a dani
Yanzu ai gashi za’a haifar maka jininka yayan dangi na meye zaka damu akan wanda Allah ya taqaita samuwarsa bare yazo shima a barshi a titi a bula masa qura ko yaje makaranta ko kar yaje duk ba matsalar ka bace.
Wallahi Baban Ali kayi nasarar doramun Hawan jini amma ina tabbatar maka bazan bari ka nakastamun rayuwa ba idan kuwa haka ta faru sedai muyi mutuwar Kasko”.
Kaman wanda aka dasa haka ya bude ido da baki yana Kallon ta, kai wannan Mata wai ita bata yafiya ne a ko yaushe burinta ta ringa hukuntaka da kuskuren da ka aikata? To in ba haka ba meye na dawo da wadannan maganganun marasa dadi? Yana shirin maida mata da martani wayarsa ta dauki qara, hadiye bisashshan yawu yayi kafij ya zaro wayar yana tattara kalaman da ze bata amsa dasuba zuciyarsa.
Sunan “DADA da ya gani ya saka shi saurin daga wayar ya kai kunnensa. Cikin harshen fulatanci ya shiga gaisheta ta Amsa tana tambayarsa Asma’u da yara.
“Bashir Meya sami wayarka Amirah tace tun jiya tana kira baka dagawa” ta fada bayan sun gama gaisuwar.
“Qarata ta kai kenan, ai kuwa seta gane bata da wayo” ya ayyana a ransa a fili kuwa se yace
“Dada Ma’una ce bata da lafiya tayi Bari muna Asibiti tun jiyan”
“Subhanallahi a garin yaya” ta tambaya muryarta na nuna Alhini se ya sake narkewa abin tausayi yace
“Nima ban sani ba ina office aka kirani wai ta yanke jiki ta fadi ina zuwa muka hato Asibiti” ya yanko maganar da shi besan gaskiya ya fada ba ko qarya. Asma’u dai kallonsa kawai takeyi tana qara mamakin Bashir a ranta, miqo mata wayar yayi seta tsaya kamar bazata karba ba kome ta tuna kuma ta karba.
Sama sama ta gaida Dadan tareda amsa ya jikin da take mata dan itakam ai sun shata ta warke abinda mutanen nan suka mata ta yaya zata manta dashi?
Kallonta Bashir yake a ransa baya jin dadin yanda alaqar Dada da Ma’u ta lalace be kuma san ta yanda ze gyarata ba, yasan sun mata laifi amma Ma’u ma akwai ruqo da kafiya ai.
Miqo masa wayar tayi ya karba sukayi sallama da Dadan sannan ya