Showing 105001 words to 108000 words out of 260321 words

Chapter 36 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42720

iri daya da Asma’u ba dan tasan Bashir bashida gidan da za’a zuba su, seda Hajia Babba tayi mata kaca kaca tace kuam karta kuskura ko cokali abanbanta in yaso idan an rasa inda za’a zuba a bawa Ma’un kayanta ko siyarwa ne tayi tasan dai an mata yanda akayiwa yan uwanta.

Ita dai Goggo nata Ido, ko Suhaima data kira tayi qorafi cewa tayi babu ruwanta matar mutum kabarinsa kuma ita bata ga aibun Bashir ba da za’a ce baza’a aure shi ba.

Washe gari sukaje da ita da Bashir din da Aliyu se Alawiyya yar uwa ta rai da rai. Ita kam gidan ma ya mata a haka, bandaki ne matsalar dan duk ya dafe nan take a cikin kudaden data karba ta ware ta bawa Bashir din dakyar ya karba tace a canza kayan bandaki har tiles din qasa dana bangon a cire, ya hada da abinda yake hannunsa ayi sauran gyare gyare da fenti idan yaso dakunan se a saka carpet kawai a ciki,

Haka kuwa akayi a cikin kwana biyu se ga gida ya dawo sabo dan gyara aka masa gangariya kai bakace tsohon gidan nan bane, ana i gobe kamu kuwa aka je aka jera mata kayan ta sega gida ya fito shar yaji kaya yan order. Gadajenta biyu Yan Turkey masu kyau da tsada ga kujeru na alfarma da kayan kallo kai duk wani abu da ake siyawa yar gata an sakawa Asma’u haka kayan Kitchen sosai Goggo ta gwangwaje su da kuloli tunda duk Baffa ne yake siyan Electronics iyaye mata su saka abinda babu ai kuwa tayi qoqari kai baka ce auran Yaya uku take ba.

Tsaf aka shirya gida har yan jere na cewa wai daman qaramin guri yafi kyan kwalliya se suka ga kamar jerenta na neman yafi na masu manyan gidajen kyau.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 34

Ranar Juma'a aka daura aure na da Bashir, Juma'ar data shiga cikin jerin rana kun tarihin rayuwata na farin ciki da bazan taba mantawa da su ba. A qa'ida ranar da aka daura aure a gidan mu ake kai Amare amma mu ba'ayi haka ba saboda Dinner da manyan Yayyenmu suka shirya zasuyi a daren ranar sauran Yayyen mu mata se tsiya sukeyi wai an fi son mu su kuwa kamar ana jira da an daura ake kwashe su.

Da yake tun ana sati daya da biki muka san da shirin Dinner, nasan dole sauran Angwaye zasu gwangwaje suyi shiga ta alfarma tunda suna dashi dukda Bashir ma nasan ze yi iya qoqarinsa amma baze iya kamo su ba saboda tattalin arziqinsu ba daya bane su duk masu dashi ne.

Haka na samu Baffan mu na tasa shi da naci seda ya bani shadda yadi goma cikin irin wadanda yake dinkawa ni kaina bansan kudinta ba kawai dai nasan suna da kyau kuma ko cikin Mutane ina dadewa banga wanda ya saka irinta ba sefa manyan irinsa.

A gurin Yah Mustapha  na samu hula harda takalmi daya siya dan daurin aure saboda duk gidan mu ya fisu gayu, dakyar ya bani wai order su yayiwo takanas seda mukayi ma zan biya kudin rabi nidai dana samu suka zo hannuna nace a gudunmawar sa, yana ji yana gani na masa fin qarfinsu se na bawa Yah Abubakar shaddar nace ya kaiwa Bashir dinki tunda abokinsa ne yasan Size dinsa na roqeshi dan Allah karya gaya masa ina so na bashi mamaki ne.

"Ma'u kenan, yanda kike son Bashir kike tattalin sa Allah yasa kar wata rana yayi miki halin mu na maza" abinda Yah Abubakar ya gaya mun kenan a lokacin da se naji jikina yayi sanyi.

Gaba daya daman na lura dashi kamar hadi na da Bashir beyi masa ba na rasa dalili dan har tambayarsa na tabayi yace mun babu komai, da yake daman shi ba mutum ne me yawan magana ba se na bar maganar kawai nasan idan da Bashir nada wani mugun abu baze barni na aure shi ba.

Tsaf na hade kayan nan bayan an dawo daga daurin aure angwaye sun shigo aka dauki hotuna, masha Allah gaba dayan mu munyi kyau kuma ko wacce ta dace da zabin ta se fatan Alkahiri dangi da abokan arziqi suke yi mana. Suna shirin ta fiya nayiwa Sadiya qawata rada dan daman ita na bawa ajiyar Kayan tayi maza taje ta dakko su, seda suka fita tabi bayan Bashir din ta bashi.

Muna zaune a bangaren da qawayen mu anan ta hira irin wadda ko wanne qawayen Amarya sukeyi idan ana biki, hayani ya na tashi wayata dake hannuna tayi qara, Bashir ne daman zaman jiran kiransa nakeyi sena miqe da sauri na shige bandaki na kullo qofar ko naji maganar sa dakyau.

"Ma'una kayan menene wadannan, ina kika samo shadda me bala'in tsada haka?" ya tambayeni bayan dana gaishe shi.

"Kamanta an jima akwai Dinner da za'ayi, kalar kayan da zan saka ne zamuyi Anko".

"Ina sane har ma nayi dinki nima, mantawa nayi sam ban ma gaya miki kalar nawa kayan ba ai" ya fada daga daya bangaren, sena marairaice nace

"Se ka ajiye su gobe ka saka idan za'ayi budar kai nidai yau wannan nake so na gani a jikinka".

"Shikenan an gama Amaryata, na tabbatar yau ke kadai ce zaki fini yin kyau a gurin nan"

"Haka nake so Angona yafi na kowa, se anjiman idan kunzo, kar dai ku bata lokaci qarfe takwas zuwa Goma Baffa yace za'a tashi" daga haka mukayi sallama na kashe wayar.

A filin tsakar gidan mu aka shirya za'ayi dinner, tun la'asar masu decorashan din da aka dakko suka katange iya inda suke buqata suka fara aikin su, kafin magriba sun gyara guri tsaf se ka rantse wani babban dakin taro ne.

Seda mukayi sallar magriba sannan aka fara shirya amare, munyi kyau har mun gaji cikin dinkin riga da skirt na wani hadadden material da akayi mana kowa da kalar nata da ze dace da shigar Angonta, munsha daurin goggoron mu me kyau dan fa fashion designer guda aka dakko ta shirya mu dukda a sannan ba'a fara kwalliya me fente fenten nan ba amma ta tsatso mana kyau da iya abinda ake amfani dasu a sannan.

Har mun saka kayan sarqoqin mu Hajia Umma tace mu cire, saitin sarqa, awarwaro da zubuna ta kawo mana na gwal qirar dubai wanda sallama ce Baffa yake bawa Iyayen mu mata kudi su siya mana idan za'a kaiki dakin ki saka shi ta bawa kowacce nata ta saka nan da nan kwalliyar mu ta qara qawatuwa se walwali mukeyi ta ko ina.

Seda mukayi sallar Isha'i sannan muka fita babban palour inda kafatanin yan gidan mu mu a lokacin mu talatin da tara ne muka hallara ga Baffa da Matansa Hudu aka shiga daukar hotunan family.

Lokaci daya hawaye suka balle mun kamar sauran na jira kuwa muka dauki kuka wiwi wanda nasan na zallar murna ne Baffa kansa seda ya kauda kai gefe ya goge kwalla ganin irin wannan arziqi da ubangiji yayi masa.

A ko da yaushe kalmar godiya ga Allah bata taba barin bakinsa, ya bashi lafiya, ya bashi arziqin mata, dukiya da Tarin Yaya ya kuma shirya masa su, sannan be jarabce shi da wani babban Alkaba'i daya dame shi a rayuwa ba banda qananun abubuwan da kowanne mumuni ba'a gaza jarabtar su dashi to shi kuwa me zeyi idan be godewa Allah ba da kuma Addu'ar neman cikawa da Imani dan abinda ya rage masa kenan a yanzu.

Bayan mun gama hoto da yan gida Angwaye ma suka shigo, kowa yayi kyau amma wallahi Bashir dina ya fisu dan se ya zama tamkar wani wata a cikin taurari kamar yanda na zama Zara cikin yan uwa na, haka muka sha hotuna musamman da iyaye da manyan yayye suka fita aka bamu guri nan muka baje kojin mu aka dauki hotuna kala kala kafin muka dunguma zuwa gurin dinner.

Taro ne akayi shi a tsare harda Baffa duk fulatancinsa seda Yayyen mu suka tilasta shi ya dan zauna a teburin da aka shirya masa da Aminan sa da be ma san an gayyato su ba, ganin su ya sa ya saki jiki haka iyayen mu mata Goggo ce dai seda aka kai ruwa rana dan seda muka yi mata hawaye nida Yah Bilki sannan ta fito se wani jan mayafi take tana rufe fuska yanda kasan ita kadai ce bafulatana a gurin.

Cikin Awa biyun nan akayi komai aka tashi, anci an sha abinci na alfarma qarshen dai yan gayun Yan Abujan ma sun yaba gashi komai a tsare babu kida balle ayi rawa irin slow music din nan aka saka kawai aka ci abinci aka dauki hotunan tarihi seda aka fara watse wa nema qannen mu suka dage se an saka musu kida ai kuwa waqa biyu aka saka Baffa na hango yanda aka hade mata da Maza ana rawa yace a kashe kowa ya tafi haka muka kwana ana ta hirar taron nan dan babu qarya munji dadin sa.

Washe gari da wuri aka miqa mu. Munsha kukan rabuwa, Junaidiyya aka fara tafiya da ita dan jirgi sukabi qarfe goman safe suna tafiya yan Bauchi ma suka dauki Amaryar su, kafin qarfe biyu an tafi kai Yah Bilki da Yah Fati ni kadai nayi saura tunda kusa da gida ne.

Seda aka dawo daga kai su aka baro wadanda zasu tsaya musu budar kai kamar yabda kowa yasan Al'adar mu ta Gombawa, anayin sallar La'asar nima aka kwashe ni se gidan su BShir inda za'ayi budar kai na.

Seda aka damqani a hannunsu, ga kayan garar da kashi biyu akayiwa ko waccen mu, ta gidan su miji daban tamu daman tun da akai jere kowa an kai mata gidan ta sannan ga turame da kwanuka harda Saitin Gado da akeyiwa Uwar miji seda akayiwa kowacce babban Gado dan Dubai haka aka kai musu.

Bayan sun biya kudin budar kai da Turmin zani da tabarma nan qanne da abokan wasan Bashir suka fara zuwa kowa ta ajiye kudinta se ta fadi sunan da ta sakamun, wannan yar farar yarinyar da muka gani randa muka zo gurin Bashir ta taho da gudunta da naira goma a hannunta.

A inda taga ana ajiye kudin ta ajiye kafin ta kama mayafina cike da rashin ji har tana neman ture mun daurin dankwali ta bude fuskata tana cewa "Na saka mata ANTY" mata suka dauki guda kowa ya yaba da ganin kyakykyawar Amaryar Bashir, hannunta na kama na zaunar da ita nace "Yaya sunanki?"

"AMIRAH" ta fada tana yar dariyar yarinta, nan da nan naji ta shiga raina saboda ina da son yara daman gata yar fara kyakykyawa da ita.

Anyi Budar kai lafiya seda aka kira sallah aka tashi, yan uwana sun mun kara dan ba qaramin kudi suka zuba mun ba haka dangin Bashir ma ba laifi sun mun liqi sosai bayan an gama qawayena suka tattare mana kudin mu muka koma dakin Bashir inda nan aka gyara aka sauke mu.

Anan muka kwana se washe gari muka tafi gidan mu daga ni se Bashir dan daman ba'a raka amarya mu iya kacin su gidan su miji se ku qarasa keda shi kawai.

Soyayya me tsafta suka shimfida a cikin gidan auran mu, ban qara tabbatar da Bashir yana qaunata ba se a yanzu dan a aikace yake nuna mun duk abinda bakinsa baya iya furtawa.

Cikin sati daya da mukayi wata irin shaquwa me qarfi ta sake shiga tsakanin mu dan kullum muna manne da juna babu inda yake zuwa se masallaci da yayi sallah kuma ze dawo gida kuma har zuwa sannan babu wanda yazo mana kullum gidan mu a kulle muna ciki muna kashe juna da soyayya.

Matsalata daya da Bashir dan irin taya aikin nan da naji ana cewa Angwaye na taya Amaren su shi bayayi, yana zaune zanyi komai na sedai na kawo masa idan muka ci abinci yana zaune zan tattare kwanuka naje na wanke qarqari ya zo Kitchen din ya tsaya ina aiki muna dan hira idan yan maganar na kansa kenan dan Bashir be fiya magana ba, miskiline seta raya masa sannan ni kuma gani da dan banzan surutu dole da qarfi da yaji tasa yake biye mun wani lokacin kuma na qaraci maganata idan na ishe shi ya jani ya kashe bakin maganar da Zazzafan Kiss shikenan.

Seda muka kwana goma sannan muka fita, da yamma Aliyu yazo da yar motarsa one door daya siya dan shima ya samu aiki tuni kuma da yake bashida wani nauyi akansa shiyasa har ya iya siyan mota.

Muna tafe yana tsokanata wai me nake bawa Bashir a dan lokaci haka yayi kumatu ya yi haske shima ze zo a ringa samma sa miyar Amarya ko ze dan farfado nidai murmushi kawai nakeyi irin najin kunyar nan har muka je gidan su Bashir.

Cikin farin ciki Dada ta karbe mu harda Anty Amina Babbar yayarsu da bata koma Bauchi ba tunda tazo biki. Haka sukayi ta jana dan saki jiki nidai ina ta sunkuyar da kai, da Dada taga haka se ta tashi ta barmu ai kuwa na dan sake dasu dan basu da duhun kai nan da nan muka saba mukayita hira. Dab da Magriba Alhajin su ya dawo, seda sukayi sallah kafin Anty Amina ta rakani muka gaisa se saka mun Albarka yakeyi.

A gidan mukaci abincin dare sannan Aliyu ya dawo muka tafi bayan na ajiye musu tsarabar da na kawo na manta ta a motar Aliyun ina jin Dada na Tambayar Bashir mun shiga gidan su Addah kuwa yace Aa, tace yayi qoqari ya kaini mugaisa.

Da muka fita a zatona zamu shiga gidan mu dan tun tuni a qagare nake, saura qiris ma na dauki Fainusa dazu muje amma dai na danne .
Ganin da nayi Mun dau hanya har mun wuce gidan yasa na tabo Bashir nace

"Baza muje mu gaida su Baffa bane naga mun wuce gidan?"

Be tareda ya waiwayo ya kalleni ba yace "Ai ni munje dasu Aliyu ranar nan mun gaishe su, ke kuma ba yanzu ba. Se kinyi wata sannan zamuje" ya maida kai suka ci gaba da maganar su da Aliyu. Tsabar takaici bansan sanda kuka yazo mun ba. Muzo har unguwar ina kallon kofar gidan na mu yace wani bazan shiga ba se nayi wata amma ai shi munje nasu gidan idan Adalci ne me yasa be bari duk maje lokaci daya ba.

Sakin kuka na nayi ya fito fili, Yah Aliyu ya shiga bani haquri yana cewa Bashir "muje mana ko a tsaitsayene ta gansu" amma mutumin nan mirsisi yaqi magana har muka isa gida Aliyu ya ajiye mu na shige na barsu a waje yana wa Bashir din mitar be kyauta ba.

Ranar haka na share shi, bayan mun kwanta ina jinsa yana wani shafani nai masa banza qarshe yaja tsaki ya juya ya kwanta nima na gyara kwanciyata a raina nace "kaima kaji yanda naji idan da dadi ai".

Haka na tashi washe gari babu walwala, nayi duk abinda na saba na koma daki na kwanta, ina kallonsa se zarya yakeyi yana kallona amma dan baqin hali ya gagara bude baki yayi mun magana haka muka wani har dare dadai yaga abin nawa bana qare bane se jinsa nayi a cunkushe yana cewa

"Dan bamu shiga gida jiya bane wai kike ta wannan Fushin to shikenan wani satin se kije" nayi masa banza kuwa tunda shi baze iya bani haquri ya rarrashe ni ba ai shikenan. Dakyar ya samu na sakko shima seda ya yarda randa na cika sati biyu ze kai ni nan da kwana uku kenan sannan na haqura, washe garin ranar da yamma yace na shirya zamu je gidan Addah ashe ma unguwar mu daya suna ta bayan layin mu ne.

Sam Addah ta kasa zaune ta kasa tsaye sanda mukaje, haka ta ringa kawo mun Abubuwa se sannu da zuwa take mun kamar wadda tazo daga China ina kallon Bashir se hada fuska yake da gani abin be masa ba yaran Abokanan zamanta da yaransu suka ringa shigowa muna gaisawa da yake akwai yammata da yawa Sa'annina a cikinsu dama wadanda suka girme ni nan da nan muka saba.

A nan Bashir ya tafi ya barni yace ze dawo da magriba, Amirah na naniqe dani qaramar Ummi ce me dan qyuya bata sakewa da mutane  Addah kuwa ta ringa bani labarai kala kala anan nake jin ashe su kadai ita da Dada iyayensu suka haifa anyiwa Addah aure ba dadewa suka rasu dan haka Nafi(Dada ta koma gurinta har tayi mata aure).

Na zata tana da wasu yayan bayan su Amirah a cikin hirar da muke  naji su kadai ne yayanta tace dai ta haihu duk basu tsaya ba dan Babban Danta ma ya girmi Amina yayar Bashir.

Da zamu tafi haka ta hada mun kayan yaji su citta da kanumfari da daddawa dasu kuka harda Barkono se kuma tace bari abarshi a daka se a kawo mun daga baya, Amirah harda kukanta da zan tafi wai seta bimu seda Bashir yayi mata jan ido sannan ta koma muka rabu da alqawarin zasu zo daman sun barmu mu dan huta ne tukunna.

Kwana biyu naje gidan mu, wannan tun safe na tafi ai kuwa nasha Fada gurin Goggo kamar tayi me wai tunda nake wa na taba gani tazo gida sati biyu da aure sena tattara na tafi bazan zauna ba aikuwa na ringa kuka dakyar Baffa ya bata baki ta haqura na kuwa bar mata dakin ta na koma gurin Hajia Babba har dare seda zan tafi naje mukayi sallama tana sake buga mun warning din karta sake ganin qafata idan ba wani abu ake a gidan ba, a hanya Bashir yayi ta tsokana ta wai gashinan, da yace bazan zo ba ai harda daukar fushi dashi yanzu gashi naje din an koroni.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa. Su Addah da kishiyoyinta uku masu kirki suma duk sunzo haka yaran gidan suna zuwar mun musamman da yanzu Bashir ya koma aiki in ya fita se gidan duk kadaici ya isheni in suka zo musha hirar mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login