Showing 3001 words to 6000 words out of 260321 words

Chapter 2 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42715

idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv.

Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya (Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen 🤣🤣😂😂🤣🤣😂)

Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido, yasan Ma'u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace "Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu" na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko da nata.

Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za'ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa'azi.


"Wallahi Asma'u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah ba, duk ina karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur'ani tsaf kin haddace da fassara amma kina nema ki kasa aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara sedai ko in baze iya adalci ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai kinsan wadda za'a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida tunda Ai Amirah kusan tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa'azi har na sauketa kan layin gidanta mukayi sallama na wuce a raina ina Addu'ar insha Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk wanda ya bani haquri se na masa Addu'a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana karbuwa kuwa 🤣🤣).

Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci gaba da kunnata kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na jcewa qila dani aka hada baki nace oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks , wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a gurin har wurin 12 sannan yara suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye weekend din ba dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na debo su amma yau bayan mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban mota ya dakatar dashu da cewa "kuje Maminku ce zata kaiku"

Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan dama mitarsu kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma daya sa na dawo ina dakkosu ke nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu amma dukda haka ni seda nayi latti dan school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while shi kuma yana gaba da school din dole seya wuceta zeje nasa office din.
Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya kyauta.

A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo traffic ya fara haduwa, abun takaicin wani sa'in zamu hadu a hanya har Horn ze mun in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan dai duk sare sarin neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin magana 😎).


Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu, abunda ya ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban samu nayi ba danayi sannan Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka once in a month zamu hada picnic muje beach a dan warware takaicin Namiji 😂😂 mu shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a gida na fita na barsu ma muka dawo kusan lokaci daya.

Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da buqata ina jinsa ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi haquri ta kusa dawowa kusada shi ai, wani lokacin naji haushi wani sa'in nayi mamaki kai Namiji dai a barshi kawai.
A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne amma daga sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan dakatar da ita dan tabbas Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane (Inji Asma'u fa 😁).

Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado har Bashir ya fita masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado na nade har ya dawo ya fara shirye shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba abinda yai matuqar qona mun rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi zafi ne?

Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni
"Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara" yasa kai ya fice daga dakin. Wasu hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso kusa da ni yana cewa

"Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?" Cikin muryata da kuka ya fara dishewa nace mace
"Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya"
Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace "sorry Mami kinsha magani toh?
Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?"

Dole na qirqiro murmushin dole nace "it is not that serious Jafar Kaina ne yake ciwo nasan stress ne dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don't tell your brothers ku wuce Makaranta kawai Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me amfani" na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da "Amin Mami Allah ya baki lafiya, Bye love you" ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani gane kan Abbin suke ba.

Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu,
Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan Tea ya fita yama kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da baqin miskilancinsa yace " yadai kunzo kun mun layi a gaba?"

"Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya" cewar Jafar.
Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma'u ba abune me sauqi ba, irin mutanen nan ce da suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace musu bata da lafiya dan Asma'u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude qofar sa ya shiga yana cewa "kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late"

"Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi" Farida ta fada dan ita yar gaba gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara gaba se suka rakashi da idanu gaba daya kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me jarabar son yaya da tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne?????https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM

Page 3


A salube suka shigo gidan gaba daya suka zauna A palour banda Abdallah daya zarto dakin da nake, yana ganina ya wullar da school bag dinsa ya taho da gudu jikina se ya sa kuka, nasan kukan me yake Abdallah akwai son karatu indai ba ciwon gaske ba baya Missing school.

Bubbuga bayansa nake da sigar rarrashi ina qoqarin hana nawa hawayen fitowa.
“Mami kinga Abbi ya tafi ya barmu kuma Yah Jafar ya gaya masa bakida lafiya amma ya tafi” ya fada in between tears, se na jashi zuwa gefen gadon dan jin kaina yana dada sarawa ga zazzabin na sake ruruwa.

“Ka dena kuka, sauri yakeyi yana da meeting ne shiyasa”
“Mami bafa yanzu bane se 10 naji yana waya da Uncle Samuel ai”
“Abdallah bana hana ka ba, idan babba ya fada maka magana ka dena jayayya”

“Amma Mami...”
“Shiii ya isa kirawo mun Amna se na kira muku Uber ya kaiku” na katse shi dan bana son aja maganar, fita yayi ba jimawa Amna ta shigo itama fuskarta da damuwa.

“Ki dauko wayata kiyi muku order Uber bazan iya driving ba bana jin dadi” na fada mata ina kaiwa Kwance jin jiri na dibana.
“Mami ko mun tafi ma kafin muje mun makara bazaa bude mana get ba sedai kiyi waya ki fada bazamu zo ba”.
Agogo na kalla tabbas kafin a samu uber su tafi lokaci ya qure dan haka na miqa mata hannu ta bani wayar, Number da suka tanada dan wani uzuri nayi dialing dakyar ina ringing kadan suka amsa, cikin muryata dake nuna halin da nake ciki nayiwa receptionist din bayanin Bazasau samu zuwa ba bani da lafiya Abbinsu kuma yayi tafiya, fatan samun sauqi tayimun tareda cewa idan gobe ma babu me kawo ayi musu Registration na school bus tunda tana zuwa har nan estate din namu, shaf na manta da zancen ma school bus se yanzu dan haka ba bata lokaci nace tayi kawai.

Har na gama Amna na tsaye bayan na aje wayar tace “Mami in kawo miki ko tea kisha se kisha Paracetamol kafin Abbi ya dawo kuje Asibiti?”
Kai na daga mata ta fita ba dadewa se gata da try ta doro tea se toast bread da kuma paracetamol da ruwan roba. Da daddaya suka shigo suka mun sannu har sannan Amna na tsaye seda na shanye ta ballomun maganin nasha nakwanta sannan ta fita.

Koda na farka bayan Azahar na danji dadin jikina dan zazzabin ya sauka sefa ciwon kan da sauran jiri da nake ji, wanka na lallaba nayi na dauro Alwala a raina ina qara mamakin Baban Ali da haryanzu ko waya beyo yaji sun tafi ko basu tafi ba. Agunda nai sallah na zauna naji anyi knocking, izinin shigowa na bada Aliyu ya shigo da Sallama hannunsa dauke da Babban try da suka dora abinci.

“Mami kin tashi tun dazu muke leqowa kina bacci”
“Na tashi Yaya (haka nake kiransa saboda qannensa su saba) ina su Ahmad naji shiru?” Na tambaye shi
“Bacci suka kwanta bayan mun dawo daga masallaci, Maman Ruth ta shigo muka ce mata kina bacci(Maman Ruth maqociyarmu ce)”

“Lallai an samu yanda ake so bacci yanzu, me kuka dafa ne” na fada ina jawo try din gabana.

“Irish porridge Yah Amna ta miki mu kuma Rice and Beans muka ci da fish”.
Kwanon na bude faten se tururi yake da qamshi kai kace Wata babbar chef ce tayi girkin. A plate na zuba wanda zanci muna dan hira da Aliyu har na gama ya kwashe kayan ya fita se nima na fito palour dukda dauriya kawai nakeyi amma kaina yana ciwo sosai, ban idasa zama akan kujera ba wani irin jiri ya kwashe ni daga nan ban sake gane komai ba nidai na farka kawai Na ganni kwance a gadon dana tabbata na Asibiti.

BASHIR
Tunda ya bar gidan hankalinsa ya kasa kwanciya, har ya kai get din estate din ya juyo da niyar daukansu se kuma Shedaniyar zuciyar da take ingizashi ta sake yi masa fanfo. Har ya kai office yana tunanin sun taho ko basu taho ba lokaci lokaci yana duba Mirrow koda ze hango su a bayansa amma shiru harya wuce makarantar tasu. Yana shiga Office be zauna ba ya kira layin makarantar ya tambaya ko sunzo nan matar ta sanar dashi Madam ta kira ta bada excuse ai haka ya aje wayar jiki a sanyaye jin dagaske dai ashe bata da lafiyar ba lambo tayi ba kaman yanda yayi tunani, duk haka ya shiga aiki sukuku babu kuzari har sanda ya shiga Meeting kafin su shigama yana Kallon kiran Amira amma yaqi dagawa dan se yaji yana jin haushin ta ita ce ummul Aba’isin ta komai da yake faruwa ai.

Tun yana sallar Azahar da be samu yi ba se qarfe uku bayan sun fito daga dogon meeting din da suka share awoyi sunayi wayar sa take ta qara dan ya manta be sakata a silent ba, yana sallamewa wani kiran ya sake shigo wa ya zarota a fusace dan ya ayyana Amira ce kadai zata iya masa irin wannan kiran mahaukatan sedai ya cika da mamaki ganin Number Asma’u da yayi saving da MA’UNA akan screen. Be kai ga dagawa ba ta yanke kafin ya yi wani abu aka sake kira se yai saurin dannawa dan tabbas yasan ba lafiya ba.

Muryar Aliyu ce cikin kuka yake ce masa “Abbi kazo Mami ta yanke jiki ta fadi tun dazu bata motsi” ai se yaji tamkar a saka guduma an bugi kwakwalwarsa Asma’u ta fadi meya sameta? Innalillahi.

Ikon Allah ne ya kawo shi gidan kawai yana shiga ya tarar dasu a zagaye da ita suna kuka kamar wadanda aka cewa ta mutu se ya matsa da sauri ya dagota yana jijjigata “Asma’u Asma’u ya shiga kiran sunanta. Danshin da yaji a hannunsa daya tallafo qasan ta ya saka shi duba wurin Jini ya gani wanda duk basu lura ba se yanzu ai kuwa yaran suka sake rudewa da Kuka kamar me shikansa dauriya yayi ya dagata tareda cewa Amna da Aliyu su fito suje Asibitin sauran Yaran kuma yace su Shiga gidan Maman Ruth kafin su dawo dan Anty(Amaryar Ogan sa ta take flat din dake kallon nasu) ta tafi Zamfara garinsu bikin qanwarta.

Bashi da Nutsuwar da ze ja mota dan haka yau Amna da kullum yaga Asma’u ta bata driving se yayi bala’i to gashi yau ta masa rana, ita kanta jikinta rawa yake cikin ikon Allah dai suka qarasa asibitin dan basu da nisa sosai.

Emergency a ka karbe ta, bayan kusan Hour daya Dr Bolaji ya fito daga dakin da suka shiga da Asma’un. Alama yayi wa Bashir daya biyo shi office
Se ya kalli Amna da Aliyu da fuskokinsu suka kode saboda kukan da suka sha,
“Ku jirani a nan ina zuwa” ya fada tareda bin bayan Dr Bolaji.

Bayan ya nutsu a office din Dr Bolaji ya kalle shi tareda turo masa takardar daya gama rubutu.

“Strees da damuwa suka hadar mata har ya jawo jininta ya hau sosai shine kuma yai sanadiyyar fitar cikin jikinta, ga wannan kaje ka kai Pharmacy zasu baka bill na kayan da akayi amfani dasu se ka karbo wadannan magungunan kuma, Allah ya taqaita abun amma ku kiyaye faduwa irin wannan ko a gaba ze iya jawo mata Paralyze bama dai fatan hakan” Dr Bolaji ya fada cikin harsheb turanci yana maida kai ga takaddun dake gabansa, kamar kazar data sha ruwan zafi haka Bashir ya miqe ya nufi Pharmacy din dan karbo magunguna.

Sanda ya dawo ya tarar da Nurse ta fito daga dakin da Bedsheet a hannunta daya baci da jini da kuma kayan jikin Asma’u da suka kawota dasu. Tambayan ta yanda zaayi da maganin yayi tace ya shiga dasu ya ajiye zata dawo yanzu seya tura qofar dakin a hankali ya shiga.

A ciki ya tarar da Aliyu da Amna kowannensu na share hawaye nan da nan yaji shima hawaye da be zata ba sun sakko masa, shikenan ya rasa Babyn da be masan dashi ba. Allah ya dorawa Bashir jarabar son Yara a rayuwarsa, ya kance shi beqi ya haifi yara Ashirin bama in ya fadi haka Asma’u se tayi dariya tace

“Haba se kace Akuya in dai ba kuma mata hudu zakayi ba”. A lokacin ya kan ce mata ke zaki zama Akuyar kuwa kiyi ta zubo su dan kinsan nidai babu gurbin wata mace bayan ke a cikin rayuwata. ko bayan data haifi Yan biyu Asma’un taso tayi planing acewarta yaran sun isa haka amma ya fitittike yace idan tayi koda be sani ba be yafe ba dan shi yana son yaga ya tara zuri’a masu yawa kuma Alhamdulillah yanzu Allah ya hore masa yana da yanda zeyi ya kula dasu, yasan bazatayi ba shi yasa dadewar da tayi bayan Yan biyu be dame shi ba yasan daga Allah ne bayan haka dama ance in shekaru suka fara ja haihuwar na ja baya ita ma kuma Asma’un na kusan shekaru 33 ne yanzu.

A hankali ya ajiye ledar kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login