Showing 189001 words to 192000 words out of 260321 words

Chapter 64 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42726

haka se kace wata kashi daga nazo kusada kai zaka tashi sannan ka dena cin abincina gaba daya mun zama kaman wasu yan haya a gidan nan kowa sabgar gabansa yake yi"

"Malama ki wuce kije kiyi wanka kuma karki sake zuwa kina mun magana da yawu a bakinki. Sannan na miki magana akan ki ringa suturta jikinki kin qi ko? Shikenan" Bashir ya fada yana miqewa ya shige bandaki ya barta tana banbamin fadab bazatayi wankan ba ai jikinta ne ba nasa ba.

Sanda ya fito bata dakin, shiryawa ya shigayi, yasan tunda ta fara wannan neman rigimar to idan ya zauna gidan dole se ta saka shi yayi hayagaga shi kuwa yanzu ciwon kan da yake fama dashi kullum ma ya ishe shi ba se ya qara wani ba.

Yana tsaye yana warming mota kamar ance ya kalli qofar gidan Ma'u yaga wasu lafiyayyun motoci guda biyu a ajiye ga Bouncers hudu majiya qarfi se fareti suke a qofar gidan.

A farko tunaninsa Alkasim ne yazo, yayan au Ma'u ne babban dan sandan farin kaya ne yasha shine me yawo da wadan nan mutanen ko a Gombe idan yana gida haka Zasuyita zagaye unguwar.

Harya shiga motarsa ze tafi ta mudubi ya hango ana fito da kwanukan abinci, cike da mamaki ya dakata ai kuwa idonsa sukayi mummunan gani da mutumin daya fi tsana a Yanzu ya fito daga gidan yana zuba murmushi kamar wanda akayiwa Albishir da Aljanna.

Be gama cika da mamaki ba seda yaga Ana ta fitowa da yara akwatuna suna dauka, yana nan tsaye suka wuce shi kamar da gayya ma har wani quuu suka taka motar suka fice da gidu Bashir ya bisu da ido zuciyarsa na tafasa saboda bacin rai.

Kashe motarsa yayi ya nufi gidan, a bakin qofa suka hadu da Aliyu daya fito fuskar nan kinini kamar wanda aka daka sukayi wa juna kallon kallo kamar wasu zakaru kafin Aliyun ya rabe shi ze wuce se yayi saurin ruqoshi yana cewa

"Waye ya fita daga gidan nan yanzu?"

"Saurayin Mami ne, Uncle Yusuf" Aliyun ya bashi amsa kai tsaye kafin ya janye hannunsa ya yayi gaba.

Seda Bashir ya dage bango kafin ya iya tsayawa da qafarsa. "Saurayin Ma'u?" Ya maimaita maganar a fili yana bin bayan Aliyu da ya tafi ya barshi da kallo.

Dagaske Ma'u ta bawa wani damar shiga rayuwarta bayan shi? Wannan irin kata'i ne yake taso masa daga qirji yana shaqe masa wuya kalamar saurayi da Aliyu ya gaya masa tayi masa zafin da gara ace wuta ya fi masa sauqi akan jin wannan mummunar maganar.

Fasa shiga gidan yayi ya juya dan tsoro yakeji, idan ya shiga ya samu tabbacin maganar da Aliyu ya gaya masa daga bakin Ma'u ya tabbatar zuciyarsa kawai bugawa zatayi a take ya mutu dan baze iya dauka.

Yana dafe da qirjinsa dakyar ya iya kwasar qafarsa ya koma jikin motarsa yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun 10KM. Gaba daya jinsa yake shi ba a sama ba ba a qasa ba, qafafunsa kansu rawa sukeyi beyi aune ba se ganinsa yayi dirshen ya zauna akan kwaltar da take qofar gidan kawai se ya mayar da kansa ya hade da guiwa yana jan numfashi.

"Lafiya Engineer kake zaune a qasa meya faru?"yaji muryar da be tantance ko ta waye akan sa ba, dakyar ya dago yana nuna masa kansa da qirjinsa daga nan be sake sanin abinda ya faru ba se farkawa yayi ya ganshi kwance a gadon Asibiti.

Dafe kansa da yayi masa nauyi yayi ya tashi zaune yana qarewa dakin kallo, "me ya same shi? Waya kawo shi Asibiti?" Qoqarin cire qarin ruwan da aka saka masa ya shigayi, Shigowar da likita yayi tareda wata Nurse a bayansa ya dakatar shi.

"Kai kai Engineer ya zaka cire bayan be qare ba" likita ya fada fuskarsa dauke da murmushi ya shiga gyara masa ruwan. Dakansa ya saka masa abin duba Blood pressure ya gama karantawa yana fadawa Nurse din ta rubuta ya sake saka abin gwada zafin jiki nan ma ta rubuta kafin ya kalleshi yana ci gaba da murmushin yace

"Mun gode Allah jininka ya sauka zafin jikin ma babu yanzu akwai inda yake maka ciwo ne?"

Kansa ya nuna masa, da alama dai likitan akwai Fara'a dan murmushinsa ya qara fadadawa yana cewa
"Ze dena amma sekayi qoqari kaima ka cire duk wata damuwa daga ranka, a shekarunka dai baka buqatar na tsaya ina gaya maka abinda ya kamata kayi ko karkayi, abu daya dai shine lafiya tana gaba da komai.

Bansan menene damuwarka ba amma koma yayane ka daure ka rageta dan jininka ya hau sosai, sannan akwai Yunwa a tattare dakai abinda yake qara maka qarfin ciwon kan kenan da kuma rashin bacci, indai zaka kiayaye yawan tunani ka kuma ringa cin abinci me kyau in sha Allah komai ze daidaita".

Kallonsa kawai Bashir yakeyi harya gama bayaninsa yana murmushin dai yacewa Nurse ta hada masa shayi yasha se ta bashi magani. Ruwan ya cire masa saboda ya samu ya shiga bandaki ko yana da uzuri, jiki ba kwari Bashir ya wuce Bandakin, tunanin da aka hanashi ya shigayi lokacin da Asma'u ta hadu da Hawan jini sanadiyyar auran Amirah da yayi ashe shima nasa rabon yana tafe sanadin rabuwa da ita.

Brush yayi ya dauro Alwala dan besan awa nawa yayi a kwance ba. Nurse din ya tambaya waya kawo shi kuma tun yaushe tace bata san wanene ba amma tun jiya da rana ne yanzu kuma qarfe goma na safe harya gota.

Buda ido yayi sosai yana kallonta, kwana yayi a sume kenan?

Sallah ya tayar harya fara a tsaye yaji baze iya ba seya koma ya zauna. Seda ya biya duka bashin sallolin da suke kansa kafin Nurse ta miqa masa shayin data saisaita ta shiga bude wasu kuloli daya gani a ajiye ta shiga zuba masa soyayyan dankali da kwai se farfesun kayan ciki da shaqa daya yayi wa qamshin su ya gane daga ina suka fito.

"Waya kawo abincin nan?" Ya tambayi Nurse din. Seda ta ajiye masa kafin tace
"Yaranka ne suka kawo, jiya da dare ma sun kawo abinci baka farka ba aka bayar dashi wannan da zasu tafi makaranta suka kawo".

"Su kadai suka zo ban da mamansu?" Ya sake tambayar ta.
Tana tattara kayan aikinta tace
"Bansani ba gaskiya su kadai dai suka shigo nan Maza biyu da mata biyu" tana gama fada ta yi gaba se ya dakatar da ita akan ta dauke ragowar abincin ta fita dasu tana masa godiya.

Kamar wasa se gashi ya tashi da abincin tas har yana jin dama bece ta fita da sauran ba, bayan shayin data hada masa seda ya sake hada kofi daya ya qara nan da nan yaji ya farfado se ya shiga neman wayarsa yayi sa'a kuwa ya ganta an ajiye masa akan durowa so yake ya kira office dinsu ya bada uzuri yana dannawa hotonsu tareda Ma'u da yake kan screen din yayi masa sallama nan take zuciyarsa ta buga dum

"Saurayin Mami ne" maganar ta shiga yi masa yawo a kwakwalwa.
Jifa yayi da wayar ta daki bango ta tarwatse, ya dafe kansa da hannu biyu yana jijjigawa saboda yanda ya taso masa da ciwo lokaci daya cikin sauri aka turo qofar dakin, likitan ne tareda Nurse din dazu dan dukka dakunan Asibitin da akwai CCTV a ciki suna lura da halin da halin da mara lafiya yake ciki.

Allura Likitan yayi masa nan da nan bacci ya dauke shi, ya kalli Nurse din da damuwa yace
"Har na fara tunanin bashi sallama saboda yanda Komai nasa yayi normal kinga kuma lokaci daya komai ya birkice, ina tunanin akwai wani abu da yake tunawa da yake tayar masa da hankali kunyi magana dashi ne dazu?"

"Bamuyi magana ba, kawai ya tambayeni waya kawo shi Asibiti nace ban sani ba, se ya tambayi abinci fa na gaya masa yaransa ne suka kawo amma banda mamansu shi kenan".

"Kuma kinsan abin da mamaki, wanda ya kawo shi makwafcinsa ne, sannan yaransa sunzo amma babu matarsa amma dazu da safe Maceceta kawo su sedai baya shigo ba, a mota ta jirasu suka wuce.

Ki zauna ki kula dashi, zanje zagaye duk abinda yake da akwai ki sanar dani" daga haka ya fita yabar Nurse tana gadin Bashir.

ASMA'U

Ina kwance a dakina gama wayarmu kenan da Yusuf daya kira yana tayi mun santin abinci ina masa dariya se ga Aliyu ya shigo gaba dayansa a birkice dan ko Knocking beyi ba ya fado dakin.

"Meye haka Aliyu, wane irin iskanci ne zaka shigo mun daki babu sallama" na fada ina tashi zaune.

"Mami, Abbi ne bashi da lafiya" ya fada kamar zeyi kuka. Sena yatsina fuska nace

"Allah ya bashi lafiya, ko kuwa ni likita ce da zaka zo ka gaya mun? Idan jikin yayi zafi da yawa ku tafi Asibiti mana ai zaka iya tuqashi ko ya kira Samuel ya kaishi".

"Mami Faduwa fa yayi a qofar gidan, Dadyn su Sa'id ne ya tafi kaishi Asibiti shida Mr Uche" Aliyun ya sake fada se na waiwaya na kalleshi,

"Faduwa kuma? A garin yaya?"
"Nima ban sani ba, a qofar gidan nan na barshi na shiga can gidan se kawai Malam Sani ya leqo ya gaya mun wai ya fadi yanzu an tafi kaishi Asibiti".

"Allah ya bashi lafiya" na fada a sanyaye.
"Mami zanje na ganshi"
"To seka dawo, kayi masa sannu" na fada ba tareda na kalle shi ba.

"Mami ke bazaki je ba?" Aliyun ya sake fada yana kallon qasa, harara na banka masa nace

"Fitar mun a daki, sannan idan zaka je ka nemi motar haya dan idan ka dauki mota ka tafi VIO suka kama ka karka ce ka sanni".

Ina jinsa yana qunquni ya fita, ban iya yin baccin da nayi niyya ba na shiga tunanin to me ya janyowa Bashir faduwa tuntube yayi kome tunda bema shigo mana nan ba dai dan da zanji yara sun fada kuma yaushe rabon Bashir da gidan nan ma tun zuwan sa na qarshe wanda har na mareshi.

Da zasu dora abincin dare Amnah tace mun zasu dafa harda Abbi su kai masa nace musu toh, ganin dare yayi kuma babu me kai su yasa muka tafi tare, a waje na tsaya suka shiga da abincin basu jima ba suka dawo wai bacci yakeyi, muka kamo hanyar gida duk jikinsu a sanyaye se naji nima na damu dukda banganshi ba amma yanayin da fuskarsu ta nuna ya tabbatar mun bashi da lafiya dagaske kai ni tunda nake da Bashir ma zan iya irga sau nawa ciwo ya kaishi Asibiti.

Muna shiga gida Yusuf ya kirani, ban daga ba seda na gama sallamar yaran muka rage aikin gobe da safe tunda Monday ce duk zamu fita kuma dukkan su a gidan suka ce zasu kwana. Seda nayi wanka na shirya kafin na dauki wayar.

Agogo na kalla naga har sha daya saura dare yayi, sena mayar da ita na ajiye kawai idan Allah ya kaimu da safe na kirashi kawai ina ajiyeta kuwa ta fara qara alamar kira, sena dauka Yusuf din ne nayi murmushi na daga na saka a kunnena.

"Ina fatan ban katse miki abinda kike yi ha dan nasan dai yanzu bakiyi bacci ba" Yusuf ya fada.

"Aa yanzu naga missed call dinka ma se kuma naga dare yayi nace da safe na kira se kuma ga kirankabya shigo" na fada ina kashe fitila me haske na koma kan gadon na zauna.

"To ai ke zaki iya bacci bakiyi magana dani ba, ni kuwa kinga ko bazan iya ba, shiyasa na baki isashshen lokaci kafin na sake kira".

"Uhm" na fada ina kaiwa kwance amma maganar sa ta dakar dani na tashi zaune dakyau ina zare ido

"Na kasa daure wa Asmy, jan rai da jan ajin naki yayi yawa. Tun tuni nake jira ki gaya mun da bakinki auranki ya mutu amma kinqi, nayi haquri a lissafina yanzu kin gama iddah na kasa jurewa dan naga alamar baki da tausayi idan na biye miki haka zakiyi ta gara zuciyata.

Yanzu dai nasan na riga kowa saka Number wallahi dan haka karka kice zaki kawo mun uzuri, nidai gani na sake dawowa a karo na biyu da qoqon barar soyayyarki Asmy, ina roqon ki amince dani ki bani dama na shiga rayuwarki mu rayu a qarqashin inuwa daya a matsayin ma'aurata".

Miyau kawai nake hadiyewa qut qut ina zate ido ni kadai a daki har ya gama maganar sa ban iya cewa komai ba. Seda muka kwashi kusan minti goma ba magana kafin ya yanke shirun da cewa

"Kinyi shiru Asmy kice wani abu dan Allah, bance ki soni dole ba dan kin dade da gaya mun bakya sona ba kuma zaki taba sona ba na yarda, ni ina sonki kuma na tabbata qarfin son da nake miki ya isa ya riqe auran mu base kin taimaka da komai ta bangarenki ba.

Nidai kawai ki bani dama na shiga rayuwar ki, idan Allah ya yarda bazakiyi dana sani ba.
Zan baki abinda ya dace dake, zan shayar dake madarar soyayyar da ko a mafarki baki tafa hasaso irinta ba nidai kawai ki amsa mun ki bani dama" ya qarasa da qaramin sauti kamar me shirin yin kuka.

Se gani harda jan bargo na rufe qafata da sukayi sanyi, inda yasan yanda kalamansa suka qulle mun baki da jijiyoyi gaba daya da yayi shiru amma ina sema qara wuta da yayi yana zayyano mun kalaman da suke kassaramun jiki.

Irin Kalaman da a kullum nake mafarkin jinsu daga Bakin Bashir se gashi har na qaraci zamana dashi be taba ko kwatanta gaya mun irinsu ba.

Yusuf be kyaleni ba seda yayi mun lilis da kalaman da suke bayyanar da tarin qaunar sa gareni dan wannan ya wuce a kirashi da so. Haka mukayi sallama ba tareda na iya bashi amsar komai ba dan zama nayi kamar wata farin shiga a lamarin.

Wai kuka zuciya da jaye jaye seta ringa rayamun dama ace Bashir ne yake gayamun maganganun nan da lashakka sena narke a gurin nan sedai a sakani a ruwan qanqara na hade.

Haka nayi baccina cikin nishadi cike da mafarkai masu dadi wai gani nida wani da ban gane fuskarsa ba muna tsinkar furan soyayaa wani lambu me cike da Ni'ima harda yan dagwai dagwai din yara mata guda biyu masu kyau da gani ma yan biyu ne.

Washe gari haka na tashi cikin nishadi muka hada abin kari harda Bashir aka zubawa muka biya suka sake shiga su kadai suka ajiye kafin muka wuce na kaisu makaranta. A hanya suke gaya mun har sannan bacci yakeyi se abin ya fara bani tsoro na qudure idan mun dawo da daddare se mu sake zuw amu duba shi tunda abin na gaske ne ko babu komai Uban yayana ne ba kuma shida wasu dangi a garin bayan mu, to wai ina matar sa ma take? Na tambayi kaina daidai sanda nake ajiye mota ta a inda aka tanada danyin fakin.

Sanda na shiga office na tarar da wasu clients guda uku masu son zuba hannun Jari, nan da nan na shiga hidima dasu nan da nan kuwa muka qulla yarjejeniyar.

Da kaina na hada musu coffee muka sha kafin kafij suka saka hannu a takardu muka basu wanda zasu tafi dasu na ajiye namu, na rakosu bakij office na juya ciki kenana daya daga cikinsu wanda kana ganinsa kasan Bahaushe ne ya dawo da baya da murmushi

Nima murmushin nayi nace "yaya dai?"
"Mantuwa nayi" ya bani Amsa yana zaro wayarsa daga Aljihu ya miqa mun
"Na manta ban karbi numbar Hajiya ba saboda ko akwai wani abu se na kiraki".

"Ai da akwai Number a jikin Letter headed dinmu, idan kana da wani enquiry seka kira" na fada ina zama akan kujerata, se ya ja kujera shima yana cewa

"Ki dai bani da kanki bata kamfani ba lambar wayarki nake so tunda dake muka qulla kasuwanci".

Irin masu tsinannen nacin nan ne, daya tasani gaba seda na bashi lamba sannan ya sarara mun, sema daya gwada kira yaga ta shiga wayata dake ajiye tayi qara sannan ya haqura ya tafi yace mun sunansa Hayatuddin.

Mamaki na ringayi me yasa yanzu Maza suke tunkarata suce na basu lambar waya wai tayaya suke gane banida aure yanzu tunda nidai babu abinda na chanza daga yanayin shigata ko mu'amala amma yanzu ranaku daddaya ne zan fita ba tareda wani ya tare ni ba, baga masu aure ba saboda tsaurin ido harda samari dan akwai ranar da na shiga Shoprite seda nayiwa wani dan banza tatas a gurin wai yazo ze biya mun kudin kayan dana siya.

Kafin na koma gida har Amnah ta shirya abincin da zasu kaiwa Bashir sanda na isa har sunyi wanka suna zaman jirana. Ina shiga suka fara sintirin zuwa tambayar yaushe zamu tafi yaushe zamu tafi dana ga zasu dame ni nace inaka sake tambayata an fasa zuwa shine na samu sa'idah, seda mukayi sallar Isha, ina cikin yafa mayafin Abayar dana saka kalar Maroon data karbi fatata kamar ka sace ni ka gudu Kiraj Yusuf ya shigo wayata.

Haka kawai naji murmushi ya kwace mun, wayar mu ta jiya da daddare na tuna dan duk yau bamuyi magana ba ya dai yi mun wani mugun text da safe dan seda muka fita break din rana ma na gani ina karantawa kuwa na goge dan ji nayi yana neman ya tsaga mun zuciya biyu bayan na rigada na saka zaran kirtani na dinketa tsaf ta yanda babu abinda ze sake hudata ya shiga.

"Ran gimbiya ya dade" ya fada cikin sakakkiyar muryar sa.
"Tareda naka" na bashi amsa ina fesa turare.

"Ki saka kadan dan Allah, bana so wasu su ringa jiye mub qamshin ki baki san irin yanda nake kishinki ba ko?" Ya fada daga cikin wayar,

Seda na janye na duba naga ko video call ne amma naga normal kirane, mamaki ya kamani ya akayi yasan me nakeyi se ji nayi yace

"Mamaki kikeyi ya akayi na sani ko, ruhina da naki a hade suke, duk abinda kike yi ina ji a jikina"

"Hakane" na bashi Amsa se ya fashe da dariya yace

"Gani a qofar gida nazo zance"
"Se dai ka daki gurbi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login