Showing 21001 words to 24000 words out of 260321 words
Chapter 8 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
daga baya ne zama da Asma’u ya sa tadan chanza tareda koyar wasu abubuwan amma dukda haka tsaftar biri gareta. Zata yi wanka ta gyara jiki amma fa duk dattin guri haka zatayi zamanta.
Yana jefa qafa busassun ganyayen bishiyar da suka zube ne suka masa Maraba. Compound din ya hada uwar qura dama ga shi an fara Sanyi da Hazo a garin. Takaici ya qume shi danya tabbata bata dawo ba kenan.
Bangaren Asma’u ya nufa dan yasan yace zeje dakinsa na part din Amiran ma ransa ne ze qara baci. Seda ya kunna wutar bangaren sannan ya bude palour ya shiga da Bismillah. Komai na nan a kintse yanda ta barshi, cike da gajiya yake daga qafafunsa ya haye benen da ze kaishi dakinsa. Nan dinma fes dashi ya saka hannu ya yaye ledar da take shimfidawa akan Katifa bayan ta cire bedsheets din saboda qura sannan ya zube kayan daya shigo dasu.
Toilet ya fada ya dan daurayeshi yayi wanka tareda dauro Alwala ya fito. Harya idar da sallah beji alamar waniya shigo gidan ba ransa ya qara baci amma seya danne kawai ya janyo wayarsa ya kira Qaninsa Naziru ya kawo masa motarsa dayake amfani da ita anan. Bayan ya kashe se yayi dialing number Asma’u, deep down yanajin kaman dazu da safe be kyauta mata ba.
Har wayar ta qaraci ringing dinta bata daga ba, ya sake kira nan ma shiru se ya maida akalar kiran zuwa ga Amirah dan yaga alamar hankalinta ragaggene. Ai a qalla yaci ta kira taji yazo ko kuwa tunda tasan da zuwan nasa yau amma still itama bata dauki wayar ba.
Ajiye wayar yayi a kan gado cikinsa na cigaba da qugin yunwa shikadai se sakin qwafa yakeyi da ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah. Kusan minti 20 Naziru ya kirashi ya iso, se ya dauki wallet dinsa da keys ya saka a Aljihu ya fita. Naziru na ganin sa ya fito daga motar da niyyar bude get ya shigar masa da ita Bashir din ya dakatar dashi da cewa
“Muje ka kaini naci abinci yunwa nake ji”.
Suna tafe babu me cewa qala kowa da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa, Naziru ne ya datse shirun da tambayar Yayan nasa Su Aliyu yace suna lafiya. Wani restaurant ya kaishi be fita daga motar ba ya bawa Naziru ATM yace ya yiwo musu take away ya karba ya tafi a ransa yana mamakin meya faru Amira batayi masa girki ba, tunawa yayi da tana da ciki se yai zaton ko shi ya hanata girkin amma dai ko yaya ne mutum ya taho gari ya gari har Lagos ai ko Indomie ta daure ta girka masa shidai ya siyo abincin ya fito.
Bashir kuwa bayan Fitar Naziru wayarsa ya zaro ya duba ko wata daga cikinsu ta biyo missed call dinsa amma yaga wayam. Na Ma’u be dame shi sosai ba dan yafi gasgata bata kusa da wayar ya santa sarai ko fada suke bata qin daukar wayar sa sedai ta daga tayi shiru amma ita wannan yarinyar fa?
In tana da hankali ai ita ya kamata ta kirashi ko amma gashi haryanzu ana neman 8 na dare bata kira ba. Har qofar gida Naziru ya kaishi ya shiga da Motar kafin ya fito yai masa sallama da niyar wucewa ya tsaidashi yace su shiga ciki.
Har saman ya kaishi yace ya gyara masa dakin dan baze iya kwanciya a ciki haka ba Bashir akwai tsafta koya datti yake a guri baya so abinda yake qara Masa son Ma’u kenan tsabtar ta ciki da waje ya jinjija mata ta wannan fannin sosai.
Har palour seda Naziru ya gyara tsaf ya goge ransa fal mamaki dan ya tabbatar yanzu Amirah bata gida to ko bata san ya zo bane? Shidai ya gama tattara komai ya tsaya jiran yayan nasa daya shiga daki ya fito. Kudi ya bashi yace ya hau mota tareda ce masa idan yaje gida ya cewa Dada seda safe ze shigo ya bishi ya kulle qofar ya dawo.
Yana shiga palour Asma’u ta kirashi se ya qarasa kan kujera ya zauna dakyau yana amsa wayar.
Asma’u.
Lokacin da Bashir ya kirata wayar ta na hannunta tana chatting da Umaima yayarta ce da suke Uba daya amma ita take bi a cikin gidansu. Akwai shaquwa sosai tsakaninsu dan kusan bata da Aminiya ma sama da ita. Hira suke yi tana gaya mata tafiyar Bashir din Gombe da yanda suka rabu.
“Ma’u kenan nidai bazan gaji da ce miki ki qara haquri akan wanda kikeyi ba, zuwa yanzu inda sabo ma ai yaci ki saba da wannan mood swings din nasa, ki watsar lamarin sa idan yayi dariya kiyi in ya daure kema haka. Ki kuma ci gaba da addu’a idan ma wani ne yake shiga tsakaninki dashi Allah ya miki maganin sa” cewar Umaima.
Tana cikin yi mata reply kiransa ya shigo tacewa Umaiman “kinga ma yana kira”
“Ki daga kiji me zece”
“Barshi kawai bazan daga ba se zuwa anjima sun kwanta zan kirashi” cewar Ma’u. Dariya Umaima tayi tana cewa
“Haba ai kuma ba zaki biye mata ku taru ku zama daya ba tunda ke kinsan abinda ya kamata, ki daga kuma karki nuna masa wani bacin rai ko wani abu dukda nasan ki ma Ma’ulle akwai sanin ya kamata ai” tayi maganar cikin sigar tsokana. Da “toh” Asma’u ta amsa ta ta kashe Datan bawai dan zata amsa kiran ba dan ta qudurce a ranta seta koyawa yarinyar nan hankali taji idan abinda take mata da dadi yanda take kiransa duk sanda taga dama kamar ita kadai take dashi.
Yanzu nema ta rage ada bata tashi kiransa wataran se sha biyun dare sun kwanta bacci, farkon wannan cikin nata ma lokacin tana laulayi akwai ranar da suna tsaka da soyayyarsu wurin 2 na dare ta kirashi wai ta kasa bacci se Amai take shine ta kira shima ta tashe shi.
Baqin ciki kamar Asma’u ta fasa ihu har bata san sanda ta fizge wayar ta tuttura mata ashar ba kuma saboda rashin adalci irin na Bashir qarshe ita yaji haushi akan me zata zageta bata ga cewa lalura ce ta sakata kiransa ba ranar kwana tayi tana kukan baqin ciki ai kuwa seda tayi masa yajin kusan wata dakyar ya shawo kanta ta sakko.
Sedata mula dan kanta ta gama komai sannan ta shiga daki ta kirashi, a yanda ta lissafa yanzu dole suna zaune ne suna hutawa dan haka tayi niyyar jan hirar har se illa masha Allahu harda loda kati a wayarta saboda tsaro (Sorry Ma’u wrong timing 😂😂😂😂).
Lafewa ta sakeyi a cikin gado sanda ya amsa wayar ta gaishe shi da tambayar ya hanya ya amsa mata da lafiya lau.
Rai rai ta saki jiki suka ringa hirar da sun manta rabon da suyi irinta, shi mamakin yanda ta sake kamar ba abinda ya faru ita mamakin yanda yake amsata sosai kamar ba Bashir ba yau ba Miskilancin nan babu baqin rai. Yanda take masa shagwaba kamar wata sweet sixteen yana biyeta gaba daya tagama narkar dashi a zaune, Hira tayi dadi tama manta da batun wai dan ta musgunawa kishiya yasa ta kirashi sema kwantowa kansu ruwa da sukayi gaba daya ta rudashi da salon da take masa magana shima ya rudata da masa salon, dakyar suka rabu a wayar lokacin 12 harta gota shima Asma’u ce ta kashe ganin yana neman sakata a uku to ai shi ga matar sa nan itafa sedai ta kama pillow batasan Gogan har ya fita shiga tashin hankali ba.
Haka ta kwanta tana juyi Kafin bacci ya saceta ranta fes koba komai dai Ta qunsawa Amirah.
Bashir
Yana zaune bayan sun gama wayar se zufa yake sharewa duk da sanyin Ac daya karade palour dan gaba daya Asma’u ta warware masa notin kai. Dakyar ya miqe ya nufi fridge din daya kunna tun dazu ya dakko ruwan sanyi ya kwankwada yana sauke ajiyar zuciya Haushin Amirah na sake ninkuwa a Zuciyarsa har ya gama wayar nan beji shigowar kiranta ko message ba gashi yanzu dayan dare ta kusa idan banda bata da hankali ai yaci ta kira taji ko lafiya ya taho ko be taho ba amma ina da dai ya mata alqawarin kudi ne be cika ba da yanzu ta ishe shi da kira kamar yaci bashin ta. Kwafa yayi a ransa yana jin kaman gobe ya juya Lagos kawai tunda zuwan nasa beda muhimmanci tunda bata damu ba.
Haka ya daddafa ya kwanta kafin ya samu bacci ya daukeshi.
Gidan Addah
Wuni Addah tayi tana bankawa Amira jiqe jiqen yan bori da magungunan mata ko tsoron halin da take ciki kar wani abu ya sami babyn basayi, bata haquraba seda Amiran ta fara sheqa Amai tukunna aka koma cushe cushe dana hayaqi. Bayan maganin gurin Wizy ta tura an sake karbo mata wasu duk ta banka mata a cewarta gara a hada hannu da yawa ayi maza buqata ta biya.
Babu lissafin zuwa ta gyara gida bare aje ga batun yi masa girki sukayi zaman su na jira yazo da kansa yace su tafi tunda a kwanakin ta sami kansa suna abin arziqi dan kiran da tayi masa jiya da daddare ma kuka ta saka masa akan ita dai yazo tana missing nasa in ba haka ba zata hawo jirgi ta zo Lagos sedai Anty ta basu daki.
A lokacin yasha mamakinta dan shidai Rashin kunyar Amirah na daure masa kai ko kadan bata jin nauyinsa wanda sam ba haka Asma’u take ba. Ma’u bata masa irin wadannan maganganun gatsal ta dai san signs da signals da take amfani dasu wanda suke bala’in burge shi da qawata zuciyarsa dan kullum cikin qara masa sabon ilimi take amma ita wannan se zance a baki ba abinda ta sani idan an zo wajen.
Se bayan Magriba ta shirya taci uwar kwalliyarta dan tasan zuwa sannan ya sauka Gombe. Ita sam tunanin taje ta gyara gida be zo mata da daman duk sanda zezo shi yake tuna mata to jiya da be magana ba itama tunda tsaftar ba damunta tayi ba se bata je ba a ganinta ai befi sati uku da zuwansa na qarshe ba gidan beyi datti ba ai. Tana zaune Adda na qara karanta mata yanda za’a yi suna jiran zuwan Bashir shiru se ji sukayi ana rufe qofar gidan ta kalli agogo 12 saura.
Seda gabanta ya fadi sanda taga missed call dinsa tun wurin bakwai ya kirata. A yanda ta lissafa sunyi waya sanda ze taso yace mata yanzu zasu taho kenan lokacin da ya sake kira yana Gombe ai ita yaci ta kira taji ya sauka.
To yanzu ya zatayi ta kirashi ne ko Aa haka tayi ta wasi wasi bata ko iya tankawa Addah dake faman sababi naqin zuwan Bashir din ba har tana da safe zata je ta samu uwarsa taji dalili dan baze ja mata asara ba wallahi.
Ita dai Amira daki ta shige ta chanza kaya dan Addah tace karta kuskura tayi wanka ance se ya kwanta da ita tukunna saboda abubuwan da ta sassaka, haka ta kwanta tana zullumin haduwarsu dan dai ta haqura bazata kirashi yau ba gara ta bari da safe se taji duk yanda ake ciki tasan dai ta kwafsa tabbas dama yaya ana lallabawa ne kuma yanzu ta sake ballo musu ruwa.
Tunanin qaryar da zata yanka masa in sun hadu ta shigayi amma duk wadda ta hado seta ga ze dago ta qarshe ta fawwalawa Allah kawai ta kwanta duk yanda goben tayi shikenan.
Washe gari Bashir tun qarfe takwas ya nufi gidansu, tun daga waje yake jiyo tashin muryar Addah data taso Amirah a gaba suka taho gurin Dada dan jin ina Bashir ya maqale dan ita bata magana a hankali. Bacin ransa ne ya nunku wato har sunada kwarin guiwar kawo qarar sa kenan ko? Se kawai ya juya dan bama ya so ya shiga yayi abunda ran kowa seya baci dan haka se kawai ya juya da niyyar fita, ya rigada ya makara dan tuni Addah ta hango shi ai kuwa ta shiga taratsin kiran sunan sa akan ya dawo bashida zabi ya juyo jin Dada ta saka baki fuskar nan a dinke kamar wanda yaga mutuwarsa ya nemi guri ya zauna yana muzurai.
Kallo daya yai wa Amirah data duqar dakai kamar munafuka dan bata so suka hadu a gidan ba yanzu se yace ita ta kawo qarar bayan wallahi Addah ce, seda tace kar suzo amma taqi gashi yanzu ta ja matana jangwam.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 10
Kansa a duqe yana jin yanda Addah take surfa bala’i kamar wadda akayiwa wani abu magana daya biyu seta zagi Asma’u da ya rasa me ta tsare mata a rayuwa. Shifa Addah na bashi mamaki wallahi, idan ya tuna fuskar data zauna da Ma’u ada da kuma bayyananniyar fuskarta ta yanzu. Qiri qiri ta babbake ta hanashi magana bare ya yi nasa qirafin qarshe ma se suka dora masa laifin ai shi ya kamata ya biya ya dakkota tunda yasan halin da take ciki.
Baqin ciki kamar ya fashe lokacin da yaji Dada tana cewa Amirah ta tashi ta bishi su tafi yanzu se ya miqe yai waje fuu yayi waje ba tareda ya shiga ya gaisa da Mahifinsa da kuma Abokiyar zaman Dadan ba. Har suka dauki hanya be ko kalli Amirah data takure saboda tsoron abinda ze mata ba, ita dai bata so akace ta biyo shi ba dan su basusan Bashir bane shiyasa.
Tasan shirun sa ba Alkahiri bane dan haka ta saka ido tana jiran karbar hukunci har suka isa qofar gidan. A waje yai parking ya kashe motar ya fito yana gaba tana binsa a baya. Da key dinsa ya bude palour ta takaicin sa ya nunku ganin tarin datti a palour kamar wanda akayi biki dan robobin lemo ne da take away pack ko ina.
Waiwayowa yayi ya kalli Amirah da jikinta ya fara rawa dan ita se yanzu ta tuno da bridal shower din bikin Qawar ta da sukayi sati biyu daya wuce a nan din, kuma koda suka gama bata gyara ba ta bari akan se ze zo tazo ta share aam kuma ta manta. Nan da nan ta fara inda inda tana tattaro rantsuwa dason yi masa bayani ya katse ta
“Zan fita wallahi ko mutuwa zakiyi kafin na dawo ki tabbatar kin gyara gidan nan har compound ki fita ki share, in kin ga dama karkiyi ko kuma ki kira wani ya taya ki zaki gane wane ne Bashir shashasha da bata san ciwon kanta ba” yai maganar cikin fushin da har a muryar sa take ji kafin yasa kai ya fita.
Ita kam indai iya hukuncin kenan ma ai tazo da sauqi, tasan Yaya Bashir da qazanta ko yaya yanzu za’a ji kanku kuma shi in kayi masa laifi yayi magana abun nada sauqi amma idan muskilancin nan ya motsa se yafi shekara yana azabtar dakai ba duka ba zagi to ita gara yai mata hargagin ya bata horo shikenan tasan ya wuce.
Hijabin ta ayije ta debo kayan shara. 3 Bedroom ne a part dinta kowanne da toilet a ciki biyu nata se nasa daya, Madaidaicin palour,kitchen da store a ciki se Dining area. Nasa dakin ta fara gyarowa ta nutsu sosai dan gudun kuskure, ta share ko ina ta wanke toilet sannan tayi mopping. Bedsheet ta shimfida ta cire tsohon ta boye dan tasan ya gani se yayi magana ya hana ta barin Bedsheet a gado in bata nan amma taqi ji sedata kunna Ac ta tsaya tana maida numfashi, iya nan tayi amma harta gaji amma tasan idan batayi da kyau ba ma kanta ta jawa.
Har zuciyarta tace tabar dakunanta ta gyara palour kawai da Kitchen wata zuciyar ta ce mata ko sama sama ne tayi tasan yanda yake a kusan nan tsaf ze leqa ko ina.
Dakin baqi ta fara shiga Ba shara ba komai ta hau moping, toilet dinta ruwa ta watsa bata wanke ba taja ta rufe ta shiga Bedroom dinta. Yana nan a hargitsensa yanda ta tafi ta bari, kan gadon kayan gugar da aka kawo mata ne bata shiryasu a wardrobe ba, babu lokaci dan haka ta tattara ta watsasu duk gugar ta hargitse. Bedsheet din shima ta chanza ta hau moping bayan ta kwashe kufunan data sha wani lemo wani fura harda ledar balangun dataci ana gobe zata tafi ta manta bata dauke ba da sauran a ciki ya bushe.
Tana bude toilet dinta kuwa zarni da warin kayan wankin data tara suka bugota dan ita fa a qasa take tsula fitsarinta ga Tiles da kama zarni, kaya kuwa nan take watsar dasu har kuwa da inner wears dinta seta tara ta rasa na sakawa sannan zata wanke.
A farko tsabar wauta da rashin hankali ma harsu take hadawa a wanki se randa Allah yakai idon Bashir ya gani yai mata tatas tareda jan kunne me qarfi sannan ta fara wankewa daga baya kuma ya siyamata washing machine ta ringa wanke qananun abubuwa kayan sawa kuma suna da me wanki duk sati yake zuwa.
Sau daya ya taba bata singlets da Boxers dinsa ta wanke masa a injin ta hadasu a ruwan dattin kayanta qarshe dai se zubar dasu yayi daga nan kuma be sake bama sedai ya wanke da kansa.
Kayan ta tattara ta wanke bayin sama sama ta fito. Palour ma ta nutsu dai ta gyara kitchen kuwa da tasan ba shiga yake ba janyowa tayi ta kulle bayan ta kwashe kwanukan data bari da abinci a ciki duk sun rube kitchen din se doyin abinci yake seta watsasu a shara dan bazata iya wanke wa ba.
Tana tsaka da sharar compound ya shigo hannunsa dauke da ledoji daga gani abinci ne a ciki, seda gabanta ya fadi Allah yasa karya shiga kitchen neman plate dan ruwa da lemo a kwai a fridge din Dining. kallo daya ya mata ya shige palour abinsa.
Yafi babu sunan gyaran nata, centre table yaja ya dora abincin dan ko karyawa beyi ba ya fita dama ya zauna akan kujerun da suka fita hayyacin su kamar wanda suka shekara goma bayan ko cikakkiyar shekara beyi da