Showing 213001 words to 216000 words out of 260321 words

Chapter 72 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42721

bayan dana fara aiki haka nake fita hayyacina kafin sallah kuwa sena zabga uwar rama saboda aikin gida dana office ga Bashir da tsurfa kala kala haka zan dawo nayita dora tukwane ina saukewa wannan karon kuwa Allah ya hutar dani, ga Amnah a gida ga Baba Harira.

Ita take zuwa duk azumi take tayamu da aikin kunu da qosan sadaka yar uwar mijin Anty ce anan Lagos suke ta hadani da ita. Wannan karon ma tun ana saura sati daya na kirata randa za’a dauki azumi kuwa se gata tazo, daman haka take zuwa se zamu tafi Gombe sallah kafin ta tafi shiyasa nake samun hutu dan kafin na tashi aiki na koma gida ma sun gama hada mana komai na shan ruwa.

Ranar Talata an kai azumi na goma sha daya, an shiga goma ta wuya in ji hausawa aikuwa dai ranar naji wuyar gashi akayi sa’a ranar naci uban aiki a office se kusan qarfe biyar da rabi na kama hanyar gida qarshe ina shiga ana kwada kiran sallar magriba.

Na samu har an fitar da abincin sadaka can masallacin da ake kaiwa ga kayan shan ruwa nan da suka hada sun shimfida babbar ledar cin abinci a qasa dukka yaran suna gidan harda Aliyu yau dan shima wani baqin rai yake ji dashi idan yazo sau dayan nan muka gaisa bana sake ganinsa yana can gidan su yana neman fitinar kakarsu.

Muna shan ruwa Yusuf ya kirani, bamu jima muna magana ba mukayi sallama yana jaddada mun cewar duk buda bakin da zeyi seya kai sunana gurin Allah ina dariya. Mun je sallar Asham muna dawowa na hadu da Bashir daya coge a qofar gidan mu da gani gudowa yayi daga masallaci dan ana idarwa muka taho kafin maza su fara fitowa.

“Ma’u dan Allah ki saurara zamuyi magana” ya fada yana matsowa inda nake.

“Baban Ali an sha ruwa lafiya?” Na fada fuska a sake ina harde hannu a qirji, seya shafa kansa yana cewa

“Ba lafiya ba, a taqaice ma ni ban sha ruwa ba. Amirah bata da lafiya sosai jikinta ya sake tashi, Addah kuma kinsan bata iya irin abincin da nake ci ba, ni duk ba wannan bama Ma’u dan girman Allah, dan darajar watan nan da muke ciki kiyi haquri mu komawa auran mu.

Wallahi nayi madamar duk abinda na aikata kiyi haquri kuskurene kuma bazan sake ba. Gaba daya rayuwata da sukurkuce babu abinda nake ganewa Ma’u.

Tunda kika tafi rabon da nayi bacci me dadi, a kullum cikin Yunwa nake wuni daidai da dakina sedai idan na gaji da kaina na gyara gaba daya gidan ma ya hargitse babu gyara babu qamshin ki Ma’u.

Gaba daya Azumin nan da akayi dore nakeyi kuma idan an sha ruwa ma dakyar nake samun abinda zan iyaci wani lokacin ma se yara sun tafi da abinci daga wurinki nake samun wanda zan karya Azumi na Ma’u, amma ki dubi Allah ki duba yaran mu kiga irin rayuwar da suke tsakanin gidaje biyu bayan muna da damar da zamu zauna taredasu a inuwa daya, na gaji da watangaliliya Ma’u ina buqatarki a kusa dani ki dawo ki tallafi rayuwata”.

Baki na bude kawai ina kallonsa, shifa Bashir bama shi da kunya wallahi wai na tallafi rayuwarsa.

“Wai ni Baban Ali me kake nema dani dan Allah? Saki na fa kayi akan matarka saboda naqi nabar aiki na koma gida ita ta dawo kusa da kai kace naje na zauna da aikin ko ba haka mukayi ba?

Me yasa baka duba yayan ba a lokacin da ka bani kwana daya rak akan in bar maka gida zaka zubawa Amaryarka sababbin kaya?

Meyasa baka duba makomar su ba lokacin daka zo har cikin gidana kaci mun mutunchi nida Yan uwana ka kwace yayanka duk a sannan baka san zasu ringa yawo tsakanin gidaje ba se yanzu da ka sheqa kaga babu riba sannan zaka zo kace mun wai kayi nadama inyi haquri na koma gidanka?

Bari kaji nasan me kake nufi, ba wai kana bani haquri bane saboda ka yarda kayi kuskure Aa kanayi me saboda ka gaza samun yanda kake so a gidanka. Dama kai ai babbar matsalarka a rayuwa cikinka ne koda iya wannan aka barka dole ka shiga garari wato ga Asma’u girkau ko in dawo in ci gaba da dafa maka kana ci tunda matarka bata yi.

Ba rashin gyara ba Allah yasa bola gidan ka ya zama wannan ku ta shafa bani ba kuma daga yau zan ja wa masu kawo maka abincin kunne wallahi ko yunwa zata kashe ka sedai ka mutu amma badai ni in dawo gidan ka in dafa maka abinci ba.

Kai bari kaji Bashir daga rana irin tayau kar na sake ganin qafarka a qofar gidan nan idan ba haka ba na rantse da Allah sena maka rashin mutunchin da ko a hanya muka hadu bazaka mun kallo biyu ba.


“Ma’u fata kike mun na mutu? Ke da kanki yau kike kira mun mutuwa?” ya fada cikin mamaki har yana kama baki, na galla masa harara dan da gaske na harzuqa da wannan rainin hankali na Bashir nace

“To ka mutu mana ina ruwan wani ni ina da Asara ne? Meye hadina da kai Ina Yaya ne to Allah baze hana ni yanda zan riqe su ba in ka mutu matar ka da yan uwan ka ne sukayi Asara bani ba.

Ka fita a harkata aure ne dakai na gama bazan koma ba ka fita a rayuwata malam idan kuma dan kana ganina a kusada gidanka yasa ka samu damar uzzurawa rayuwata toh se in tashi dan kasan gurin zama a Lagos ba wahala ze mun ba” ina gama fadar haka na wuce ciki na barshi a tsaye kamar an dasa shi.

Ina shiga na hau kan yaran da fada.
“Wallahi duk wanda ya sake diban abinci ya kai gidansu sena ci ubansa kuma sedai ya koma can ya ringa ci” na fada ina nuna su gaba daya.

“Toh Mami na sahur fa muke tafiya dashi” Jafar ya fada, daman nasan shi yake diba ai kuwa na hayayyaqo masa ina cewa

“Tunda ubanka ne ya siyo ya ajiye mun dole ka ringa guzuri kana kai masa ai, to bari kuji na shan ruwan ya isa can kuci na sahur a gidan ku idan ba haka ba wannan din ma wallahi zaku jawo in hana kai gaba daya ma se ku tattara ku koma gidan ku kar wanda ya sake zuwa ya takura mun anan”

“Yanzu Mami saboda kawai an kaiwa Babanmu abinci shine kike fada naga wasu can ma zuwa suke ki dafa musu su tafi dashi shine mu Babanmu zaki hana mu bashi” Aliyu ya fada yana ture kwanan gabansa.

Sena juya kansa a fusace nace

“Na hana idan kuma ka isa ka diba ka kai masa kaga yanda zanyi maganin duk wata fitsara da kakeji a ita, saboda kaga na qyaleka kwana biyu kana iskancin dakaga dama ko shi yasa to mu zuba ni dakai ai ka sanni ba kuma chanzawa nayi ba”

Miqewa yayi fuskar nan kamar ze fashe tsabar fushi ya nufi qofa

“In na sake ganin qafarka ma a gidan nan ma sena bata maka rai uban yan baqin zuciya kawai, baza’a bawa uban naka abincin ba idan kunyi zuciya ku auro masa wadda zata zo ta ringa dafa masa” na fada ina wucewa dakina.

Duk sukayi tsuru suna bina da kallo ganin yanda na horance musu. Ina ciki aka qwanqwasa na bada izini aka shiga.

Baba Harira ce ta samu kan kujerar dake dakin ta zauna tana cewa

“Kiyi haquri Uwardakina shi yaro ba’a masa haka. Be kamata ki ringa musu haka akan ubansu ba se su qullace ki bayan su bazasu gane abinda yake tsakanin ku ba.

Kinga ban tsawaita da son jin dalilin mutuwar auranku ba duk da nayi jimami kwarai amma shi aure ana zaune lafiya ma in Allah ya kawo se kinga an rabu amma dan Allah koma menene ki dena nunawa a gaban su. Zancen abinci kuma uwata ai sadaka ce idan an bashi ba’a fadi ba”.

“Baba Harira ki qyale wannan mutumin kawai ai bashi kadai bane da matarsa a gidan da surukarsa me yasa baza su dafa su bashi acan ba shine dan bashi da kunya har ze tareni yana gaya mun se an kai daga nan yake ci to wallahi kar ki sake bari su fita da abinci, in dole se sunyi sahur din su fito da Asubar suzo suci anan”.

Ganin da tayi dagaske raina a bace yake yasa ta tashi ta tafi tana qara nanatamun da nayi haquri. Tsaki na ringa saki ni kadai, nama rasa takamaiman bacin ran nawa na menene? Cewar da yayi na koma gidansa ne ko kuwa wani abu daban?

Anci sati biyu cikin Azumi yara suka fara jarabawar term, randa aka kai azumi na Ashirin da shida suka gama daman tun ana saura kwana biyu su qare na turawa da Bashir saqon cewar zamu tafi Gombe da yaran dan qila shi ba zuwa zasuyi ba idan ma zasuje ina so ni na tafi tareda yaran saboda akwai bikin qanne na maza biyu da za’ayi sati daya da sallah.

Ina tura saqon ya maido mun da amsar ya yarda daman ta ina ze hana shida yake neman hanyar shiri dani yanzu kam shishshigigi da cusa kai ba irin wanda baya yi mun. Ana ibi zamu tafi sega Hotunan tikiti ya turamun ta whatsapp, na budesu na duba na zuwa ne kawai yana tambayar yaushe zamu dawo ban amsa ba na kashe Datar na sauka a raina nace

“Kudina sun huta tunda ba roqar ka mukayi ba”. Kiran Yusuf ne ya shigo mun na daga muka gaisa yana mun qorafin qarin kwanakin da suka samu dan tun satindaya wuce ya kamata su dawo amma yanzu se ranar sallah.

“Yaushe ne tafiyar taku zan saka ayi muku booking jirgi yanzu” ya fada

“Ai an hutashsheka ma, kaga babansu ya rigada ya siya yanzu naga ya turo mun dasu” na bashi amsa.

“Bazaku hau ba, qarfe daya gobe za azo a kai ku Airport” ya fada ta sigar bada umarni kana ji kasan kishi ne cunkushe a qasan ransa.

“Ranka ya dade ya rigada ya siya, a daga mana qafa daman iya na zuwa ne idan zamu dawo se mu hau naka”.

Shiru ya mun be amsa ba seda na sake magana kafin ciki ciki yace mun
“Shikenan, Amma Asmy bana son wata alaqa tsakanin ki dashi dan Allah, nasan ze ringa fakewa da Yaransa idan na abinda ya zama dole ba babu ke babu shiga sabgarsa kinji?”

“Naji baza’a kuma ba, to ka saki ran mana se wani magana kake kamar Boss” na fada cikin sigar tsokana a qasan raina kuwa nace

“Ji mutum se kace ka aure ni irin wannan doka haka”.

“Baki san yanda nake kishin ki ba ko? Ki bari se randa Allah ya mallaka mun ke, ranar zaki san yanda ake tattala abinda ake qauna daga lokacin duk wani namiji da zeyi magana dake to ina tsakani” ya fada

Dariya nayi ina cewa “Allah ko to sannu sarkin kishi”

“Asmy se ana sonka ake kishin ka ai ko baki san haka ba? Ke daida bakya sona daman bazakiyi kishi na ba in kuma kin sona to ki fada yanzu naji

“Shikenan dai, yanzu zan kwanta saboda mu tashi da wuri dan bamu gama hada kayan mu ba” na fada ba tareda na bashi amsar tambayarsa ba.

“Yawwa gara dana tuna, idan kun isa Gombe za’a kawo kayan sallar su Abdallah. A Kano na bada dinkin da suka gama kuma kaitsaye Abuja suka tura se kawai nace a kaiwa Alhaji Tukur qilan ma ya riga ku isa yanzu”

“Kayan sallah kuma kaida kake da hidimomi da yawa ina kai ina qarawa kanka wasu?”

“Bana jin dadin abinda kike mun duk sanda nayiwa yaran nan abu. Qiri qiri kike nuna bakya sona Asmy da ina da zuciya nima da tuni na haqura dake amma na kasa, tunda dai bake nayiwa ba se ki barsu su karba in kuma bazasu saka ba to ki zubar kawai” ya fada a dan fusace.

“Ni fa sam ba haka nake nufi ba gani nayi kwata kwata yaushe ka kawo musu waccan tsarabar duk basu saka bama suna nan daman sallah muka barwa amma kayi haquri bazan sake ba, sun gode Allah ya qara budi” na fada cikin sigar lallashi.

“Da nayi niyar yi miki tsarabar Dogayen riguna tunda naga kina son su, yanzu nake so na fita na siya muku keda Intee amma kin jawowa kanki na fasa nata kadai zan siya”

“Haba mana na fa ce kayi haquri, kasan fa daman ina ta so na baka sautu kuma ina tsoron kar kace na mai dakai dan aike shi yasa nayi shiru amma a siyo mun mana ayi mun afuwa” na fada cikin shagwabar da ban san nima inayi ba.

“Dagaske hukuncin bata mun ran da kikayi kenan, badai wannan karon ba ko zan siyo miki sedai wani lokaci” ya bani amsa

“Shikenan toh Allah ya kaimu wani lokacin”

“Fushi kikayi?” Ya tambaye ni, se na yi murmushi nace

“Aa ba fushi nayi ba”.

“Karki damu zanyo miki tsaraba saura itama idan na kawo kice bakyaso, ki turamun da size na takalmin ki”.
Hira kadan muka sakeyi kafin mukayi sallama na kwanta dan ina so na tashi da wuri.


Wai dan Allah ni kadai nake fama da matsalar network if yes to to ya kamata a san yanda za’ayi dani 😭😭🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 58

BASHIR

Beyi niyyar zuwa sallah Gombe ba amma saboda karya shiga haqqin Amirah yasa ya tuntubeta ko zasuje. Suna zaune ita da Addah a palour ya fito daga dakinsa da ya mayar dimun da iman yana ciki indai yana gidan.

Ledar kayan sallar ta daya karbo dazu ya dauka ya fito palour,
Suna zaune Tayi daddaya a qasa taba cin Gyada dafaffiya ga cikinta nan daya fara girma a waje saboda Half vest ce a jikinta kawai ta daura zani kanta babu dankwali wai zafi take ji dukda akwai wuta sun kunna Ac suna hira da Addah da tayi shar abinta duk rama da baqin da tazo dasu babu to aci me kyau a kwana a Ac meya dameta.

Zama yayi ya gaida Addah ta amsa tana hararar sa dan haushin sa take ji, bama ya zama bare suyi magana da ita tun ranar nan da tayi masa zancen kayan sallah be kulata ba gashi har yanzu ana jibi sallah koda uwarsa yake so taje idi oho.

"Ya jikin naki? Me yasa kika zauna haka a cikin sanyi gashi kanki ko rufeshi bakiyi ga dare ba bakya son kula da lafiyar kwata kwata" ya fada bayan daya amsa gaisuwar da Amirah tayi masa.

"Kai in ka gaya mata qila taji ai mata da ciki ki zauna duk kiyita budewa Aljanu da ifiritai jiki suna kallo ai se kiyi tayi se wani abu ya same ki kuma azo ana yaya za'ayi" Addah ta fada tana gyara zama.

"Babu abinda ze sameta In sha Allah kawai dai ta ringa kula kuma meye ma amfanin zamanki idan bazaki ringa nuna mata abinda ya kamata tayi ba"

"Bazan nuna ba ubana nace bazan nuna ba, kaifa daman ba mutunchi ne dakai ba to ni banzo dan in kula da ko wacce qatuwa ba zuwa nayi nima a kula dani na hutawa rayuwata a toh" ta hayayyaqo masa.

Be kulata ba ya turawa Amirah ledar daya fito da ita Addah tayi zaraf ta dauke ta zazzage kayan ciki a qasa.

Kayane kala hudu, Atamfa biyu se Lace daya da Brocade material shima daya duk an yi musu dinkuna masu kyau. Seda ta ware ko wanne dukda a goge suke tas ta hargitsa kafin ta watsar qasa tana cewa

"Ina nawa naga duk wasu riguna fici fici babu wadda zatamun a ciki"

"To daman an ce miki da naki a ciki ne kayan Matata ne kema ki siya da kudinki mana ai kina dasu ko ni aka ce na miki kayan sallah?" Ya fada kansa tsaye.

Amirah kanta da take murna tana daddaga kayan dan babu wanda beyi kyai ba kana kallo kuma kasan masu tsada ne seta tsaya tana kallonsa jin abinda ya fada tace

"Yaya Addah ce fa kake gaya mata haka"
Harara ya maka mata yana cewa
"Gobe Solomon zezo ya kaiki ki siya takalmi da mayafi zan tura miki kudin sannan na manta ban tambayeki ba ko zakije sallah Gombe ne dan ni bazan je ba"

"Uwarka Nafi ita kake wulaqantawa Bashir bani ba shege wanda be gaji Arziqi ba. Ni zaka kalla kayiwa gori to wallahi bazanyi da kai ba da uwarka zanyi dan ita ce daidai dani se inji idan ma ita ta baka damar ka ringa wulaqanta ni. Idan ma banda lalacewa Bashir in haifar maka matar ka aura amma baka da wadda ka raina a duniya sama dani ko? Nagode.

Ke kuma kina zaune yana qarewa uwarki tana di ai Shikenan gaki gashi nan kuci kanku" Addah ta fada tana miqewa, har tayi gaba kuma ta dawo tana cewa

"Babu Gomben da zamuje uwar me muka manto acan da zamu koma dakkowa?"

Shidai be kulata ba ya kalli Amirah yana jiran tata amsar itama a sanyaye tace
"Anan zamuyi sallah"
"Shikenan, goben da wuri zezo daganan se ku biya kuyi cefanen abincin sallah"

Ya dauki wayarsa yayi danne danne kafin ya miqe ya shige daki yana cewa "gashi nan idan kunje ze kaiki inda ake siyar da Ready made ki dauki 50k ki siya mata kala biyu ai zasu isa".

Wayarta da take gefen ta ce tayi qara alamar shigowar saqo ta janyo ta duba, dubu dari da Hamsin ya tura mata tayi ihun murna daidai sanda Addah ta fito daga dakin da take da waya a kunne tana cewa

"To qarya zan miki Nafi? Zagina yayi ta uwa ta uba ko ince zagin mu nida ke tunda iyayen mu daya har yana cewa idan na isa na danne shi ma kwata mana" se tayi shitu ta zauna a kujera kafin tace gaba da cewa

"Oho dai Idan ma ke kike karanta masa cewar ya wulaqanta ni to dani dake dukka ya wulaqanta aikin banza mana, daman nasan ai ba son zuwana nan kike ba kina baqin ciki nazo naci arziqi ke kina can to wallahi naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login