Showing 57001 words to 60000 words out of 260321 words
Chapter 20 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
Number qaninta dan karya mayar da yara gida ba kowa da yake suna nan Babban gida tunda safe ta kawo su.
Fitowar Dada da hijabi a hannunta da alama itama alwalar tayo ta kalli Amirah tace “au haryanzu kina zaune a qasa sanyi na shigarki da danyan jiki se ance ki tashi ko? Kiyita zama jikinki ne ai bana wani ba” ta fada tana zura hijabinta inda Abun sallarta yake ta nufa se a sannan ta ankare da Asma’un dake zaune seta sassauta fuskarta tana cewa “Aa Asma’u Yaushe kika shigo”
“Yanzu na shigo Dada ina wuni” Ma’u ta fada tana zamowa daga kan kujerar, seta amsa mata tana cewa
“Ki shiga kiyi sallah bari nima nayi gashi can har an yi raka’a daya” ta tayar da Sallah ita kuma Ma’u ta miqe ta shiga dakin Fainusa dukda ba sallar zatayi ba seta nemi gefen gado ta zauna tana duba wayarta.
Batafi minti uku ba Amirah ta shigo tana jan akwati, kallo daya tayi mata ta ci gaba da dannan wayarta ita kuma ta jingine jakar tana dafe gefan kanta dayake sara mata ga wani jiri jirin yunwa dake son kayar da ita haka ta daddafa ta shige toilet dan wanka take son tayi.
Da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dan yanzu base ance tayi ba tsamin jikin kadai yana sa ta shiga hankalinta ta gargasa jikin gashi taci sa’a jikinta me kyau ne tuni dinkin ya kame in banda ma kata’in da take jefa kanta aida ta fi haka warwarewa.
Sanda ta fito har sannan Ma’u na nan ta sake bararrajewa akan gado da alama waya takeyi, a darare ta ja akwatinta ta ciro duguwar riga da undies ta sake komawa toilet din ta sako kayan ta dauro alwala ta fito daidai sanda Dada ta leqo tana kiran Asma’u, bayan ta idar tana zaune ita ba lazimi ba tayi zuru akan sallayar aka bude qofar.
Dadan ce ta sake dawowa, cikin bacin rai tace mata “wai bazaki tashi kije kici abinci ba Amirah ko kin manta jego kikeyine idan kuma wani kike jira ya kawo miki se ki zauna”.
Yunwa takeji ta gaske dan haka ta miqe salaf salaf ta fito palour inda take jiyo muryar Asma’u da Naziru da alama hira suke, a tsakiyar palour ta tarar dasu, Asma’u nacin tuwo da miyar kuka shi kuma yana mata hira, wuce su tayi ta nufi kitchen tana kaiwa daidai qofar Bashir ya shigo da sallama ciki ciki ai se kawai ta qame a gurin ta kasa gaba ta kasa baya, bata so su hadu ba, a yanda ta tsara in ta shige daki bazata sake fitowa ba abincinma idan an gaji a ringa binta dashi har seya bar garin gashi yanzu tun ba’aje ko ina ba sunyi kicibus.
Shi kuwa Bashir bema lura da ita ba ya nemi guri kusada Asma’u ya zauna, Dada ce ta shigo itama daga Gurin Alhaji tan cewa Naziru yaje Alhajin na kiransa. Kallon Amirah dake tsaye kamar an dasa ta tayi tace
“Ke kuma lafiya kike tsaye kin qi gaba kinqi baya” kidan duma zuciyar Amirah ta shigayi daidai sanda ta waiwayo idanunta suka hadu dana Bashir, wani mugun kallo ya aika mata dashi daya saka hanyar cikin ta kadawa bashiri ta shige kitchen din ta fara matsar kwalla.
“Me yarinyar nan takeyi a gidan Dada oh danace ta tafi shine ta taho gidanmu saboda raini ko tam” ya fada yana sakin qwafa dagani yama rasa me zeyi kawai. Seda Dadan ta zauna tana kallonsa tace
“Dalilin kiran dana maka kenan ai nima ina zaune sukazo ita da Addah sunce kace ta tafi gida”
“Eh nace ta tafi gida Dada wannan yarinyar bata da mutunchi ta raina ni ban isa na bata umarni tabi ba se abinda ta rayawa kanta, seda na gargadeta nace baza’ayi taron sunan nan ba amma saboda ta nuna mun ban isa ba taje tayi”
Bakiga dakina irin barnar da akayimun ba iya abinda na gani kenan ma Allah kadai yasan me aka dauka a ciki tunda ban duba ba, shikansa gidan karkiso kiga yanda suka maidashi. Ga Iman can a Asibiti babu tabbacin ta tashi sannan saboda ma sun raina mun hankali na dawo na tarar da wata mata ta biyo karbar bashinta wai ni suke cewa na roqar musu ita tayi haquri. Wallahi Dada Idan yarinyar bata kama gabanta ba ta bari hannuna ya sauka akanta sena mata dukan mutuwa wallahi....”
“Babu inda zataje kar kuma ka fasa mata dukan mutuwar” Alhaji Amadu da Naziru ya turo akekensa ya katse wa Bashir Hanzari, se suka juya gaba daya suna kallonsa bayan da Nazirun ya kawo shi tsakiyar Palour.
Kallon Bashir da yake ta qoqarin hadiye malolon daya tokare masa wuya Alhajin yayi ya girgiza kai kafin ya Kalli Dada yace “Ina Amiran take kirawo ta nan” Miqewa Dadan tayi ta shiga kitchen suka fito tareda Amirah dake risgar kuka kamar an ce mata Addah ta mutu ta nemi can gefe ta zube tana ci gaba da kukanta.
Kallonsu Alhaji Amadu yayi daya bayan daya ya tsaida idonsa akan Asma’u da tunda ya shigo ta tsame hannunta daga cikin tuwon ta gyara lullubinta, se ya saki wani murmushi da bazaka tantance na mene ne ba ya kalli Bashir yace
“A lokacin da zaka auri Amirah me nace maka”
Sunkuyar da kai Bashir yayi yana cigaba da komawa da abinda yake taso masa idanunsa sun kada sunyi jajir,
“Ba magana nake da kai ba” Alhaji Amadu ya katse shi cikin daka tsawa se Bashir din ya dago da sauri yana kallon mahaifin nasa, kalaman sa suna dawo masa daya da daya a kwakwalwa ranar dayazo yace masa ze qara aure ze auri Amirah diyar Addah tamkar a yanzu yake fada masa su.
“Sharadi zan kafa maka Bashir, yanda ka dakko auran nan to ka tabbata Babu Yaji har qarshen rayuwarku. Ina raye ko bana raye idan ka rabu da yarinyar nan ban yafe maka Ba Bashir kaje ku zauna duk wuya duk dadin da zata zo maka dashi”
“Kace babu Yaji babu saki” Bashir ya fada da kyar kamar me ciwon haqori.
“Madallah, ka tashi ka dauki iyalan ka ku tafi aje ayita haquri, daman shi wanda ya siyi rariya ai yasan zata zubda ruwa”.
“Asma’u ya gidan ya Mutane nawa dazu sun shigo Ina bacci kafin na yunqura kuma suka fice” Alhajin ya fada yana maida hankalinsa kan Asma’u. Seta sunkuyar da kanta tana dan murmushi tace “ lafiya lau Baba suna Babban gida ai yanzu zaka gansu ma tunda na fada musu ina nan”.
“To masha Allah, yaushe zaku koma hutu ya qare ko?”
“Eh Baba daman litinin muka shirya dazu kuma yace wai gobe zamu tafi amma a mota gashi bamu qarasa shirye shiryen mu ba” Asma’u ta fada tana janye fuskarta gefe dan karma su hada ido da Bashir.
“Wane irin tafiyar mota kuma ana zaune lafiya, ko a zamanin da da muke tafiye tafiyen ai munji jiki bare ku yanzu da baku saba ba ga yara kuma, kudai jira litinin din dai kubi jirgin safe kamar yanda kuka saba, Allah yayi muku Albarka yaci gaba da ruqo da hannunku” Baban ya fada suka amsa gaba daya da Amin.
Naziru na zaune kamar ya buga tsalle tsabar yanda da Al’amuran suka masa dadi, yanda aka tilasta Yayan nasa maida Amirah gida ya mugun masa dadi aransa fadi yake “Allah ya qara ai kadan ma ka gani in bakayi da gaske ba wataran se sun saka a kulleka kana zamanka da matar rufin asiri ka kwasowa kanka kaska.
Baban ne ya katse shi yana cewa “zo Naziru ka maidani na kwanta kaji Dare ya farayi” yayi musu sallama Naziru ya maidashi.
Kamar kurame haka sukayi jugum jugum a gurin, Amirah dai a tsorace take da hukuncin na Baba dan data bi shi su koma gara ta zauna agidan kai gara ko can gidan su ne ace ta tafi ita kuwa Ma’u ba abinda ya shalleta masifa ce dai tasan zeyi ya gama tunda dai an rushe zancen mota ai shikenan, shikuwa oga Bashir har wata zufa yake kamar wanda ya hadiyi kunama.
Makwallaton wuyansa se sama yake yana qasa ya kasa furta komai se “hmmm” kawai. Miqewa yayi dakyar ya iya ce musu su tashi su tafi ya fice ko sallama be yiwa Dada ba, Asma’u ce ta fara miqewa tayiwa Dada seda safe tabi bayansa Amirah dai ko motsi ta kasayi.
Kallonta Dada tayi tace “ki tashi ko so kike ki qara wani laifin a gurinsa” ai kamar tana jira ta sake fashewa Dadan da kuka tana cewa “Dan girman Allah Dada ki roqi Baba Ya barbi yau na kwana a gidan nan idan sun koma Lagos sena tafi wallahi idan na bishi yau kashe ni ne kawai Yaya bazeyi ba Dada dan baki san irin abubuwan da nayi masa bane” ta qarasa tana sake rushewa da kuka.
Miqewa Dada tayi tana cewa “koma mene ai ke kika ja gara ki tashi ku tafi dan nima bazaki ja mun wani fadan a gun Alhaji ba kije kawai ba bu abinda zeyi miki” tayi shigewarta daki ta barta.
Amirah tana kuka tana komai ta hado jakar Naziru ya daukar mata suka fita yana mata dariyar mugunta, dakyar ta bude bayan motar ta shiga dan tuni Asma’u ta kame a gaba abunta cikin ranta qal da wannan abubuwa da suke faruwa.
Afuwan 🙏🙏🙏🙏qundumemen uzuri ne ya riqeni kwana biyu amma komai ya dawo daidai zaku ci gaba da jina insha Allah🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
*INA MANYAN MATA NE*
*INA MASUSON FARA SANA'A*
*HANNUR COLLECTION tazo maku da alkairi domin qarin bayani kobiyo💥🔥💥*Munada amarya da uwargida package wannan package ya* *qunshi,abubuwa guda goma*
*maganin sanyi da basur*
*Nasha da madara*
*Nasha da lipton*
*Na dahuwar kaza*
*Na tsarki*
*Nasha da kankana*
*Garin tsumi*
*Hadadden tsumi*
*Na matsi*
*Nahadawa da zaitun*
*Muna saida tahnia me gyaran aure*
*Akwai kayan ORIFLAME*
*Akwai kayan GHT*
*Akwai kayan faforlife*
*Akwai chocolate da coffee na mata*
*Akwai turaruka,sabulai mayuka da duk wani kayan gyaran jiki da aure*
*Munada dogayen riguna sari,yadin hijab materials,atamfofi,shadda,laces dss*
*Albishirunku ina registration din ORIFLAME, GHT, FAFORLIFE ,Duk kayanmu farashin sarine,kuma muna aikawa kowanne gari cikin aminci*
https://wa.me/message/3BCXWNGTI7ILC1
Page 22
Gudu ya ringa fellawa dasu kamar masu barin gari sanda ya tsayar da motar a bakin Get kuwa har qauri takeyi, a Get din ya watsar dasu yai gaba dan Amirah bata ko samu damar daukar Akwatinta ba Asma’u ta saka key din hannunta ta bude musu Get suka shiga.
Yanda taga Amiran tana tafe tana layi se ta bata tausayi dan haka ta qarasa ta riqo kafadarta ai kamar me jiran majingini kawai ta fashe mata da kuka tana cewa”Dan Allah Anty ki bashi haquri, wallahi ba laifina bane Addah ce kema kin santa ita tace se anyi”.
Asma’u bata tanka ta ba har suka shiga dakin Amiran ta zaunar da ita akan Kujera tana qarewa palour kallo baki bude saboda mamaki. Duk wani abu daya danganci glass an fasa harda Tv ba’a barta ba daidai da labulaye duk duk an sauke su qarafunan sun karyo.
Ajiyar zuciya tayi kafin ta Kalli Amirah da har sannan kukan take tace “Kiyi shiru komai zai daidaita Insha Allah, ina zuwa”.
Part dinta ta koma, Farfesun Tsokar rago ta ciro a freezer ta dumama kafin ta hada Shayi a qaton Mug ta dora su a kan Try hade da Bread ta dauka ta koma part din Amiran. Bayan ta ajiye su ta sake komawa ta debo mata tuwon semo da miyar danyar kubewa da tayiwa Bashir bema ci ba ta sake komawa part din Amiran.
Tana zaune a qasa ta zamo daga kan kujerar riqe da cikinta tana murqususu, da sauri Asma’u ta ajiye try din ta nufeta tana “lafiya Amirah meya same ki?” Ita dai se juyi take tana malele
kuwa akan Tiles saboda bala’in qullewar da cikin yayi mata.
Dakyar ta nutsu ta kamata ta koma kan kujerar, Shayin ta fara bata a baki tana karba, kurba uku tayi Amai ya taso mata ko kafin ta miqe tayi shi a Gurin Asma’u na tsaye se sannu take mata. Bowl babba ta dakko ta debo ruwa a babban kofi da dawo gurin Amiran, ta zuba mata ta kurkure baki da dauraye fuskarta Ta koma yaraf ta kwanta tana sauke Numfashi.
Abincin ta ajiye mata nan ta shiga ci kuwa dan Aman ya taimaka ya bude mata ciki ita kuma ta dauke robar ta tafi dakko mopper da packer, Duk Kyankyami irin na Asma’u haka ta daure ta kwashe aman tsaf ta zuba ruwan omo ta goge Gurin kafin ta sake saka ruwa ta goge tas ta nemi freshener amma bata samu ba sanda ta gama itama ma Amirah ta cinye farfesun tsaf ta shanye shayin se ajiyar numfashi takeyi.
“Nagode Anty Allah ya biyaki” ta fada tana sunkuyar da kai, se Asma’u tayi murmushi kawai tace “bakomai, ki samu kisha magungunan ki se ki kwanta ki huta. Ga ragowar abincin nan koda zaki buqata anjima Allah ya qara kiyayewa” ta fada tana nufar qofa.
Tashi tayi ta rakata tana sakeyi mata godiya ta kulle qofarta gam ta ciki karma ya dawo kenan ya shigo bata kwashe kwanukan ba ta haye kan kujera se baccin wuya ya kwashe ta.
Asma’u ma tana komawa part dinta kulle qofar tayi idan Bashir ya dawo da akwai key a hannunsa dan sunyi waya yaran sunce a can zasu kwana ma bazasu dawo ba. Sama ta wuce ta shiga wanka, seda ta gyara jikinta tsaf lokacin har sha daya tayi ganin Bashir be shigo ba yasa tayi kwanciyarta kawai dan daman dai yau koya dawo tasan bazasu kwashe qalau ba.
Bashir
Yana sauke su kai tsaye tsohuwar unguwar da suka taso ya wuce gurin Bala, Abokinsa ne tun na yarinta tare suka tashi a unguwarsu su Hudu Bashir, Marigayi Aliyu, Bala da Sadiq yayan Asma’u su hudun Abokaine na rai da rai tun daga Primary ajinsu daya har jami’a sannan suka rabu kowa ya karanci course dinsa daban.
A qofar gida ya tarar da Bala da yan majalisar sa kamar yanda yayi tunani, kashe motar yayi tareda jan kujerar baya sosai ya tokare qafarsa da stiyarin motar , zafafan numfashi yake saukewa a jere a jere zuciyarsa jinta yake tamkar ana soyata a mangyada.
Me yasa meye dalili daya kasa samun nutsuwa tunda ya auri yarinyar nan? A shekara biyu an tafi ta uku da qara auransa be sakeyin sati daya na cikakken farinciki ba wai dama haka qarin auran yake ko kuma shine beyi dace ba.
“Me yasa baka nemi wata ba me yasa se Amirah zaka aura Bashir? Yau da ace wata daban ka aura wallahi ko mata uku ka auro lokaci daya bazan damu kamar wannan auran da kayi ba amma shikenan haquri ko nayi haquri. Idan dan Allah kayi Bashir Allah ya bamu zaman lafiya ya bani ikon cinye jarabawar da yayi mun, idan kuma kayi ne dan kaci mutuncina to Allah baze bari na tozarta ba ba kuma zaka samu nutsuwar da kake iqirarin samu ba” kalaman Ma’u na qarshe wanda daga su bata sake tayar masa da hankali ko wata magana ba sanda ya auri Amirah.
To wai alhakin nasa ne ko nawa shidai Allah ya sani beyi auran nan da wata manufa ba yayi ne kawai dan yana ra’ayi bakuma dan ya tozarta Matarsa ba kamar yanda take tunani amma gashi nan shi yake karbar sakamakon sa da Hannun hagu wai ta ina toh ya kuskure?”
Glass din window da aka kwankwasa ya dawo dashi daga tunanin daya tafi, se ya dago yana gyara zamansa. Seda ya saita yanayinsa sannan ya bude qofar ya ziro dogayen qafafunsa yana sake kokawa da dacin ransa kafin ya fito gaba daya.
“Kaga Na Ma’u Angon Amirah uban Aliyu ko dubu ta taru” Bala daya gaji da jiran fitowar Bashir din ya zo ya kwankwasa masa glass ya fada cikin sigar tsokana sedai yana yin fuskar Bashir din tasa ya gintse maganar tasa.
“Lafiya kuwa Engineer kaga idanunka” Balan ya sake fada, se Bashir yaja tsakin da ya aure shi ya bude murfin motar ya koma ciki yana cewa Balan ya zagayo. Cikin zaquwa Bala ya shiga motar dason jin meya faru, dan Bala irin mutanen nan ne masu son bin kwakwkwafin duk wanda suke tare se sun san komai nasa.
Shiru sukayi na kusan minti biyar, Bala da gulma take cinsa har ya gaji ya ceda Bashir din “Engineer wai yane kodai akan climax kake ne kaima ka fara busa eh yane”
Wani mugun kallo Bashir ya jefe shi dashi kafin dakyar ya bude baki yace “Abinda banyi da quruciyata ba shi kake mun fatan yi yanzu insha Allahu har na mutu nida hayaqi sedai na murhu balle na kai ga shan wata kwaya kai dai da ka riga ka illata rayuwarka shikenan amma ka ringa tunawa Yaranka Mata ne kodan su ya kamata ka dena abinda kake yi”.
Hade rai Bala yayi dan yasan dama qarshe seya jefe shi da maganar, tun suna secondary Bala ya fara bin wasu Sa’anninasu a unguwa har suka koya masa dabi’ar shaye shaye, babu yanda basuyi dashi ba akan ya dena amma ina qarshe har yaso koyawa Sadiq da taimakon Allah da jajircewar Iyaye beyi nisa ba ya bari amma shi Bala ya rigada yayi nisa dukda abun nasa harda daurin gindi daya samu gurin Babarsa dan shi kadai ne danta Namiji.
Lokacin da aka ringa ankarar da ita akan ta ringa masa fada seta nuna an takura mata Da ba’a qaunar sa seda yayi nisan da baze ji kira ba sannan tazo tana kuka da idanunta akan dabi’ar tasa dan seda takai kayan maye har a cikin gida sha yake babu abinda baya ta’ammali dashi in banda Giya da Cocaine har kuwa ta mutu da wannan baqin cikin toh yanzu dai yayi sauqi saboda girma da iyali daya tara amma fa ko yanzu ba abin kunya bane a gurinsa ya murza wiwi yasha ko a gaban waye su kansu su Bashir dan dai babu yanda suka iyane suka ci gaba da zumunchi dashi musamman Bashir da Yake ganin Balan na bashi shawarwari daidai da ra’ayinsa.
Shiru suka sakeyi kafin can Bashir ya mula dan yana buqatar abokin tattaunawa, idan so samune Sadiq ya kamata ya