Showing 54001 words to 57000 words out of 260321 words

Chapter 19 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42667

ba yau a gidan nasu kiransa ya shigo. Daga yanda ya amsa sallamarta tasan ba qalau ba se tayi shiru tana jin yanda yake magana ta inda yake shiga bata nan yake fita ba masifa yake mata akan me yasa tun farko bata gaya masa zasuyi taron sunan ba.

Galala ta saki baki tana sauraronsa ganin fa ba shiru zeyi ba yasa ta katse shi da cewa “Dakata Malam wai ko baka san wa kakira bane To Asma’u ce ba Amirah ba”.

Cike da masifa yace “oh maganar banza zaki gayamun kenan ce miki nayi bansan wanda na kira ba ai koma mene laifinki ne tunda kina gaba da ita ya kamata ki nuna mata abinda yake daidai da ba daidai ba data tace zatayi taron seki hanata tunda kinsan bana so”.

“Ashema ni ce gaba da ita, meye darin gami na da ita da zatayi abu na hanata ko an saka ni a ciki ballantana kuma nima gani nayi anayi. Kuma da kake maganar daidai ko rashin sa qarewarta naga da sa hannun yan uwanku tayi komai danginku kaf babu wanda bezo gurin ba su a cikinsu babu wanda yasan daidai kenan, kuma naga ai ita da uwarta suka shirya kamai se kuma kazo kana gayamun wani qabali da ba’adi dan Allah in baka da abin fada ni bacci zanyi kabarni inji da hayaniyar da suka jazamana a gida har sha biyu sannan muka samu salama Allah yasa kar cikin dare kuma wata sabuwa ta taso”.

Jin da yayi ta fitittike masa yasan halin Ma’u sarai itama ba baya bace seya sassauta muryarsa yana cewa

“Kina nufin dangina ne basu san daidai ba kenan, kuma da kikaga za’ayi ai seki kirani ko a wayane tun da safen ki gayamun ni na tsaqatar amma fa kalli duk abinda akayi se a gari naji ke baki kirani da kanki kin gaya mun ba”.

“Nidai ai kasan ban iya sa ido da munafunci ba bare kace duk abinda wata takeyi sena kwasa na gaya maka, bayan haka tsakanin ku can nasan koda yardar ka suke abunsu? Yanzu dai aikin gama yarigada ya gama mudai ka tiro azo a chanza mana keys din gidan nan kar muje wani ya sata shima muna zaman mu a ringa diro mana da daddare tunda yau gungun barayi aka hada a gidan”.

Dagaske dai yaga alama Asma’u neman sa take ta magana tunda gashi shida ya kira yayi fada amma ta samu se gasa masa maganganu takeyi dan haka yace mata

“Shikenan, da safe ki daure ki leqa Asibiti kiga jikin Iman koda wasa karki bari ta sake taba mun yarinya..”

“Nan fa daya, zuwa dubata zanje da sassafe ma kuwa insha Allah amma batun kar uwarta ko wasu su tabata be taso ba ka nemi wani ka saka wannan aikin amma bani ba. Ba abinda yai mun zafi da lamarinsu ka sani” Asma’u tayi saurin katse shi. Se da yaja kwafa sannan yace mata seda safe suka ajiye wayar ta gyara kwanciya tana cewa

“Haka kawai can ta qare muku kunfi kusa ni ai yar kallo ce irin haka kuma yanzu aka fara duk abinda ba’ayi shi dan Allah ba ai qarshen sa kuwa dana sani ne fal, Allah sarki sun jawa yarinya bata ji ba bata gani ba zanje na ganota da safe insha Allah badan halinsa ba” tana motar taja bargo tayi kwanciyarta bacci ya dauketa.

Bashir kuwa yanda yaga rana haka yaga dare, ina ace gobe Friday ce ba Alhamis ba amma yanzu dole ya jira se goben ya tafi Gombe kafim nan yasan matakin da ze dauka akan daga Addan har Amiran.

Su Addah dai wunin Alhamis ziri cikin rashin nutsuwa sukayishi, masu kujeru sunzo sun kwashe akayi lissafi kusan dubu Ashirin na wadanda aka lalata a drawer dakin Bashir Amirah ta lalubo aka biya DJ ma yazo ya kwashe sifikunsa yanzu ya rage me sarqa da kuma masu qananan bashi da basu biyo sahu ba. Har dare suna zaune suna saqawa da kwancewa babu wanda ya sake zuwar musu ko Dada da tayi zaton zatazo shiru har dare basu ganta ba gashi babu waya da alama ma su kafai suka wuni a gidan dan tun Azahar sunji fitar Ma’u itama bata leqa ko jaje tayi musu ba.

Amirah shirun Bashir yafi daga mata hankali koda yake ta ina ze kirata ma tadai tabbatar gobe Juma’a ze zo Gombe Addua dai tayi tana kan yi ta Allah ya rufe bakinsa akan wannan Abu to bamu sani ba kota karbu Allah dai ya kaimu juma’ar mu gani.

Washe gari kuwa qarfe hudu yana Gombe, kai tsaye Asibiti ya nufa a can ya tarar da Asma’u data sake komawa dan halin data ga yarinyar jiya ya tsaya mata arai matuqa. Ganin da Bashir yayi wa Baby Iman ya sanyaya masa jiki dan ya ma cire rai da yarinyar. Wani kalan numfashin wahala takeyi idan ta jashi kamar qirjinta ze burma, sanyi ya mugun shiga jikinta ga rashin kaita da wuri da sukayi.

A hanya Asma’u ce tayi ta qarfafa masa guiwa ganin yanda yayi shiru damuwa qarara a fuskarsa, tasan Bashir yana son yaya amma wannan yarinyar ma dai daban take a zuciyarsa taga alama to amma ya zeyi abinda Allah ya qaddara dole ya faru. Suna isa gida ta shige part dinta shi kuma ya nufi na Amirah da tundaga qofa yake jiya hargagin muryoyin dabe tantance kona waye ba.

Kallo daya yayi musu Addah, Amirah se mata biyu dabesan ko su waye ba ya dauke kansa kai tsaye ya wuce dakinsa yana jin Addah na cewa
Alhamdulillahi ga me gidan ma yazo amma be tsaya ba, to ya tsaya yayi musu me tsaf dai ze iya hada su duk hudun ya nada musu na jaki ko ze rage wani abu daga baqin cikin da yake ji a cikin zuciyarsa.

Murmushin takaici ya saki lokacin da idonsa ya sauka kan aika aikar da akayiwa dakin, kansa ya girgiza kawai ya juya ya fito daidai daya daga cikin matan tana cewa

“Wallahi daga nan se kotu zan wuce dan bazan tsaya ma yansanda su batamun lokaci ba, ni zaki yaudara ki bani takaddun bogi? Seda na nemi Dillalai muka je suka ga gidan ayi masa kudi muji idan chanji zan baki ko ciko zaki mun aka ce na bada takaddu suna dubawa sukace mun na bogi ne da an riga an siyar aka gano ni se anyi qarata to wallahi kafin ki kaini prison ke zaki fara zuwa.

Ni daman jikina seda ya bani tun zuwanku amma Innah tace mun babu matsala to kuwa ku zaku dauki Asara ki riqe warin dan kunnen ki siyar kya samu na daukar lawyer dan nidai kudina cis na sani gobe ma ku sake daukowa kanku abinda yafi qarfin ku kuce se kunyi”.

Jin fitowarsa tasa Addah tun kuda Amirah tayi qasa da murya tace “ kiroqeshi yai mata magana in ba haka ba mun shiga uku wallahi banida sauran wani abu kuma”.

Bata so ba amma ya zatayi seta tare gaban sa ta fashe masa da kukan da inda haka kawai ne kowa tayiwa shi seya tausaya mata dan kuka ne da kana jinsa kasan meyinsa yana cikin tashin hankali ne ta shiga cewa

“Dan girman Allah yaya kasa baki matar nan tayi haquri ta bamu lokaci za’a biyata.....”

“Dauuu” ya kwasheta da marin da kaf seda suka rufe fuska dan ji sukayi kamar su akayiwa bata dawo daga gigitar ba ya sake sauke mata wani a daya bangaren kafin ya hankadata gefen kafin ya nunata yace

“Na rantse da Allah idan na sake shigowa na tarar dake a gidan nan sena illa taki, ya fice yana huci tabbas kuma idan ya sake tarar da ita se ya mata dukan mutuwa yau a gidan nan.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

*INA MANYAN MATA NE*
*INA MASUSON FARA SANA'A*
*HANNUR COLLECTION tazo maku da alkairi domin qarin bayani kobiyo💥🔥💥*Munada amarya da uwargida package wannan package ya* *qunshi,abubuwa guda goma*
*maganin sanyi da basur*
*Nasha da madara*
*Nasha da lipton*
*Na dahuwar kaza*
*Na tsarki*
*Nasha da kankana*
*Garin tsumi*
*Hadadden tsumi*
*Na matsi*
*Nahadawa da zaitun*
*Muna saida tahnia me gyaran aure*
*Akwai kayan ORIFLAME*
*Akwai kayan GHT*
*Akwai kayan faforlife*
*Akwai chocolate da coffee na mata*
*Akwai turaruka,sabulai mayuka da duk wani kayan gyaran jiki da aure*
*Munada dogayen riguna sari,yadin hijab materials,atamfofi,shadda,laces dss*
*Albishirunku ina registration din ORIFLAME, GHT, FAFORLIFE ,Duk kayanmu farashin sarine,kuma muna aikawa kowanne gari cikin aminci*
https://wa.me/message/3BCXWNGTI7ILC1


Page 21


Ihu Amirah ta fasa na zafi biyu ga mari ga maganar tafiya gida, me yake nufi badai sakin ta Bashir zeyi ba? Wannan tunani yasa bata san sanda ta bishi da gudun bala’i ba tana kiran sunan sa lokacin harya kai kan Balcony Ma’u ze shiga.

“Na rantse da Allah kika qaraso nan Amirah sena karyaki, karayar da babu me iya gyara miki ita kuma karki bari na fito kina cikin gidan nan idan kuma so kike ki qure ni shikenan” ba Amirah da yai wa maganar ba hatta da Ma’u dake cikin palour seda ta tsorata, yanda yai maganar cikin tsananin masifa idanunsa sun kada sunyi jajir harwata qwallar bala’i ce ta taru a cikin su yasa ta kasa tunkararsa harya haye sama yana hada stair case bibbiyu.

Amirah kuwa Kamar wanda ya sakawa pause haka ta bishi da kallo kafin ta juya zoqai zoqai ta koma part dinta tana toshe baki gudun kar ma sautin kukan ta ya fito ya dawo ya tattaka dan tayi bala’in tsorata da hanayinsa . A qofa suka hade dasu Hajia me gwal data bi Amiran da kallo kafin ta ja uban tsaki tana kallon Amiran tace “kadan ma kuka gani Allah yasa shima ba wata satar aka qunduma masa a daki ba, kinga Hajia muje nidai na gama magana in sammaci ya iso ma hadu a kotu kawai” ta yi waje abunta tana ci gaba da yada musu da magana.

“Toh Fatu Allah fidda A’i daga rogo mun tafi” Hajiya Nuratu qawar Addah datayi musu hanyar sarqa ta fada dan ita kasa magana tayi ma tunda sukazo se ta juya tabi bayan Me gwal itama. Se Addah ta kalli Amirah data zube a qasa tana kecewa da sabon kuka.

“Kukan me zaki zauna kiyi, shiga mu hada abinda zamu dauka muje kawai dan in kin zauna nasan ba mutunchi ne dashi ba ze miki abinda ya fada ne toh gara mu tafi gaban uwarsa duk abinda za’ayi akan idonta”. Dakin Amiran Addah ta shige tana sababi ta fara tattara komatsanta zuciyarta ko kamar tayi bindiga wannan bala’i har ina?

Har Addah ta gama ta yafo gyalenta Amirah na zaune tana Kukan da bashi da Amfani.
“Au kina zaune ko to shikenan ni kinga tafiyata se kiyi tayi idan kuka ze miki magani” Addan ta fada tana nufar qofa, se Amirah tayi saurin riqota cikin kuka tace

“Addah idan na tafi ina zani? Kinsan dai idan na biki gida qila sena gwammace hukuncin Yaya akan na Baba to ina zanje”

“Gidan uban sa mana, ni daman nace ki bini gida ne gaban Nafi zaki je ki zauna duk ma wacce za’ayi ayi da wanne zanji idan kin bini gidan da nawa tashin hankalin koda Masifar Ubanki”.

Daki Amiran ta wuce ta shiga hada kaya a akwati tana kuka amma taji dama daman cewa gurin Dada zata tafi dan dai ko hauka tayi bazata je gidan su da sunan itace me laifi ba yanda Babansu yake a zuciye da lamarinta harda Addan ma tasan qiris yake jira wallahi ya samu dama akansu yaci musu mutunchi.

Tare suka fice kowacce da jaka tana Ja Addah na gaba taba ta sababi ko tausayin Amiran da haryanzu jikinta bawai ya warke bane bataji ba bare ta karbar mata uwar akwatin da take ja ita dai masifarta kawai take, seda suka ci tafiya har bakin titi kafin suka samu Napep da ze kaisu gidan su Bashir.

A qofar gidan Dada me Napep ya ajiye su, Amirah da tunda suka taho bata dena kukan nan ba kasa daukar jakarta tayi se me Napep din ne ya shigar mata da ita har tsakar gidansu Bashir din.

Alhaji Ahmadu na zaune a tsakar gidan akan Kekensa Naziru da physiotherapist da yake dubashi suna tsaye a kansa bayan sun dorashi akan keken dan gama Exercise dinsa kenan suka shiga Addah na Masifa Amirah na kuka gaba daya suka juya suna kallonsu, wuce su Addah tayi bata ko kalli barin da suke ba itama Amiran ta rufa mata baya sallamar me Napep ce ta saka su Nazirun juyawa daga kallon su Addah.

Akwatin Amirah ya dire musu ya kalli Naziru yana cewa “yi musu magana su bani kudina na wuce dan Allah”
“Nawane kudin?” Naziru ya tambaye, bayan ya fada masa ya zaro daga aljihunsa ya bashi.

Me Napep na fita shima Physiotherapist din yayi musu sallama ya tafi dan ya gama aikinsa, kama keken Naziru yayi da niyyar maidashi dakinsa ya dakatar dashi da cewa

“Kaini daki Naziru” Alhaji Amadu ya fada dukda yaso ya zauna a tsakar gidan yasha iska amma zuwan Fatu baze barshi ba, yanzu haka yana jiyo bambaminta daga palour Dadan amma baze kula suba dama ya fada musu ai ayi dai su gani idan Tusa zata hura wuta kuma gashi da alama dai tun ba’aje ko ina ba da sun fara karbar sakamakon abinda suka aikata.

A palour Dada kuwa Addah ce take sababi kamar zata hadiye harshenta,
“Daga abin arziqi se ya zama na tsiya, yar nan naga kuma jikar kuce yanzu ta girma ace cikin yan uwanta kaf itace ba’ayiwa taron suna ba ai setace ba’a qaunarta. Ni kinga tafiyata gata nan ku qarata nima inje naji da masifar nawa mijin dan nasan su Binta munafukai sun kaimasa rahoto tun jiya” Addan ta fada tana kwasar jakarta data watsar tun shigowarsu, bata saurari Dada dake mata magana ba ta fice abinta ranta tana qissima duk abun Bashir be isa yayi a gaban Dadan ba tasan zata ta ka masa burki.

Bayan Fitar Addahne Dada ta mayar da hankalinta kan Amirah dake durqushe har sannan tana kuka,
“Amirah yanzu kina ganin biyewa Addah da kike kuna aikata duk abinda kuka ga dama daidai ne ko? Ke bazakiyi hankaliki zauna a gidan auranki lafiya ba se ki ringa biye mata kina saba umarnin mijinki to ki sani dai shi Allah babu ruwan sa, idan ya tashi ke kadai ze kama da laifin saba umarnin miji banda Addah tun wuri idan zakiyiwa kanki fada ki bi hanyar gaskiya kiyi dan nidai babu ruwana da duk wani shirginki yanzu” tana gama fadan haka ta miqe ta shige dakinta ta bar Amirah na cigaba da share hawaye.

Sosai ranta ya baci da abinda ya faru a gidan Bashir din, ta rasa meyake damun yayarta ta har ji takeyi daman itace gaba da Addah qilan da ta ringa dorata akan hanya ta dena wadannan abubuwan zubda mutunchin da take yi amma ya zatayi sedai tayi ta binta da addua kawai.

Wayar Bashir ta kira bayan ta shiga dakin, lokacin yana tsaye kan Asma’u yana zuba mata ruwan tijara kaman itace Addan ko Amirah. Yanda yake bambamin tasan ransa yakai qololuwar baci yasa bata tankashi ba ta sunkuyar dakai kawai tana jinsa saboda Bashir Miskiline, ko zeyi rashin mutunchi a ruwan sanyi yake dafa mutum. Auran Amirah nema taga yana neman ya mayar dashi mafadaci tunda yanzu yana iya bude baki yai fada idan an masa laifin sabanin da da ko laifi ta masa sedai ya dauki gaba da ita ko yayi ta gasa mata aya a hannu ta ruwan sanyi yanda ko qararsa ta kaiwa wani baza’a yarda ba dan babu shaida.

Sau biyu wayar tana qara amma be kula ba se ana ukun ya zarota da niyyar kashewa dan a lokacin bayajin ze iya magana da kowa sedai ganin suna Dada yasakashi saurin dagawa bayan ya zauna akan kujera dan Uwa ba wasa ba, a magagin mutuwa ne kadai yakejin baze iya amsa kiranta ba amma inda yaji ya kuma gani ko halin yaya ne seya amsa idan yaso ya bata uzuri ya kira daga baya.

Gaisheta yayi ta amsa tana karantar bacin rai a cikin muryarsa, kiran da tayi masa ta so ta tambayeshi ne shiya tura Amirah gida amma yanayinsa yasa ta fasa dan tasan qarshe wani laifin zata jangwalo mata yace ta kai qarar sa danhaka se tace cikin taushin murya

“Bashari idan babu abinda kakeyi kazo gida yanzu mana ina son magana da kai”

“To Dada gani nan zuwa” ya fada yana miqewa dan daman yana da niyyar zuwan a yanzun yaje ya gaya mata abinda Addah da Amiran sukayi dukda yasan ta sani amma dai gara yaje da kansa yaji ko harda sa hannunta a ciki.

“Ku shirya gobe da safe zamu wuce kuma a mota zamu tafi” ya fada yana kallon Asma’u da kanta yake a sunkuye har sannan kafin ta dago harya kai qofa, kallonsa tayi tana zare ido a fili ta furta “kan bala’i Gombe to Lagos a mota” miqewa tayi ta bi bayansa da sauri dan baza’ayi wannan gangancin da ita ba, haka siddan Allah ya rufa musu asiri ya basu yanda zasuyi subi jirgi se yace a mota zasu tafi kamar ma itace tayi masa laifin kenan aikuwa wallahi bazata sabu ba shidai ya tafi su zasu jira Moday din su tafi dan daman already sun siyi tickets ta barsu a bude saboda bata san sanda zasu tafi ba.

Ya kunna motar yana qoqarin bude get ta shige ta zauna, tana jin yanda yake kallonta a jikinta amma taqi daga kai bare su hada ido dan gara aje gaban Dadan itama ta saka baki a wannan al’amari kar goben tayi ma suzo suna wallahi tallahi. Tafiyar kamar ta kurame harsuka isa gidan Dada, ta rigashi shiga gidan dan sanda suka isa daidai ana kiran Magriba shi seya tsaya ya daura alwala ya shiga masallaci ita kuma ta shige gidan.

Amirah na zaune har sannan a palour ta dena kukan dai se ajiyar zuciya take fuskarn nan ta kumbura tayi jajir abinka da Farar fata ansha kuka. Kallon kallo sukayi da Asma’un kafin ko wacce ta dauke kanta gefe Ma’u ta nemi kujera ta zauna tana zaro wayarta daga aljihun Diguwar rigar jikinta ta danna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login