Showing 186001 words to 189000 words out of 260321 words
Chapter 63 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
saboda qofar ba ta wasa bace, Cikinsu Salmanu ya shiga suka ci gaba da kici kicin, Abba na kusada Hajiya da ta kasa cewa komai ya na bata baki.
Kamar an ce Habiba ta waiwaya ta hango haske ta gurin qofar Kitchen ta baya, hannun Hajiya ta janyo da qarfi ta nuna mata suka yunqura zasu tafi gurin Abba ya dakatar dasu da yi musu alamar kar suyi motsi ya fara sanda a hankali har ya isa gurin da Umaimah take kiciniyar kunna cylinder Gas saboda duk dare suna kashe ta ne daga wajen, ko wani abun zasuyi sedai suyi amfani da electric yana zuwa kuwa beyi wata wata ba ya dauke ta da marin da seda taga taurari a idonta Halifa dake bayansa yayi azamar kashe Gas din data kunna dan sosai suka jiyo qarar fitar sa daga Kitchen din.
"Me kike yi Umaimah" Abba ya fada ciki matuqar bacin rai yana dubanta.
"Igiyar Gas na cire daga jiki, zan sake shi ya cika gidan sannan na kunna mana wuta dani dasu dukka mu qone dan wallahi da nayi zaman kishi da wata mace akan Khalil gara mu mutu, kuma yanzun ma ba fasawa nayi ba, ko ba yau ba wallahi se na kashe ta, na kashe Khalil sannan na kashe kaina" Umaimah ta fada babu alamar wani tsoro ko nadama a fuskarta.
Duka Abba ya sake kai mata kafin ya angizata suka shige cikin gidan Hajia ta tare tana cewa
"Kayi Haquri Alhaji kodan halin da take ciki, Umaimah me yasa kike haka me yasa bazaki bar mu mu huta ba ki dauki haquri da dangana dan Allah?"
"Karki sake taba ni munafuka Annamimiya, idan da kina so na haqura ai tun farko seki hana danki yin auran tunda yana jin maganar ki amma saboda baqin munafunci kika mara masa baya yanzu kuma kizo kina bani haquri se kace ke har naki mijin ya mutu kin bari anyi miki Kishiyar.
To wallahi bazan fasa abinda nayi niyya ba kuma duk wanda yayi yunqurin hanani se ta shafe shi Idan yaso kowa ma ya mutu a huta” tana gama fadar haka ta sake yunqurawa kafin su ankare har ta kai matattakalar kai bazakace ciki wata tara ne a jikinta ba a yanda take tafiya.
A daidai lokacin Khalil ya fito tareda Humairah dake sharbar kuka a bayansa ta tsorata sosai ta gama saddaqarwa yau kwananta kawai ya qare a gidan, Umaimah na hangota ta kai mata wata muguwar cakuma ta goce, mantawa tayi da duk wani ciwo da take ji a jikinta ta ware qafa uku uku ta hada matakalar ta diro qasa tana ganin mutane da mugun gudu tayi bayana Hajia tana sauke numfashi.
“Ka fito ko to kuwa ka shirya baquntar lahira yanzu Khalil sena kashe ka” Umaimah ta fada tana daukar Abin flower da yake akan benen ta nufi Khalil da yayi mutuwar tsaye gadan gadan, tana dagawa marata ta katsa mata ba shiri ta wullar da abin hannunta ta dafe ciki tareda durqushe wa Khalil yayi kanta kafin ya qarasa taja baya tana cewa
“Karka taba ni munafuki karka kuskura qazamin hannunka ya tabani kuma ba barinka nayi ba se naga bayanka da duk wata mace da kace zaka hadani da ita”
“Kai Khalil wuto daga nan ka rabu da ita” Abba ya daka masa tsawa kafin da kansa ya hau benen ya kamo hannunta, tana tirjewa da komai seda ya direta a tsakiyar palour sannan ya qyaleta.
Idanunta da suka tigada suka qeqashe ta daga tana binsu daddaya da kallo kamar yanda suna suke kallonta ko wanne da kalar tunanin da yakeyi akanta.
A saitin Khalil ta tsayar da idonta se kawai ta fashe da kuka tana cewa “Kasan ina kishinka Khalil me yasa? Me yasa zaka hadani da wata Mace dame na rageka da zakayi mun kishiya Khalil me nayi maka” ta qarasa cikin daga murya tana sake rushewa da kuka.
Halifa ne ya matsa kusada Hajiya qasa qasa yace “Anya Hajia Anty Umaimah bata da motsi a kwakwalwarta nidai ina ga akaita gurin likitan kwakwalwa dan abinda takeyi ya fi kama da na masu motsi a kai”
“Uwarka Aisha gata nan a kusa da kai itace take da motsin kwakwalwa, se kaje ka tono ubanka Ummaru a kabari yazo yayi mata magani” Umaimah ta fada idonta cikin na Halifa babu ko dar da tunanin matsayin uwar tasa da ta zaga a gurinta.
“Umaimah ashe baki da mutunchi har haka? Hajiya Aishar kika ambata kika zaga harda Mijinta da yake kabari saboda ke baki da mutunchi kin kuma zubar da tarbiyyar da muka baki a titi ko kin kyauta nace kin kyauta, ki tashi ki wuce mu koma Asibiti ga motar Ambulance nan sunzo da ita zasu dauke ki” Mama da shigowarta kenan ta fada cikin tsananin fushi tana qarasawa inda take ta kama hannunta. Seta fizge tana cewa
“Wallahi babu inda zani, indai kuma ana son zaman lafiya se dai Khalil ya saki yarinyar nan. Ba’a halicce shi dan kowacce mace ba bayan ni dan haka bazan taba raba shi da wata ba”.
“Ki a wa? Yanzu har kin isa mace da zaki tsaya kice baza’ayi miki kishiya ba ko kuwa kenan har wata macece data san ciwon kanta balle tayi kishin mijinta? To bari kiji kishi ba hauka bane idan zaki dawo hankalin ki tun wuri ki dawo saboda kinga ana lallabaki ya saka kike botsarewa ko to daga yau zanga uban da ze sake lallabakin, ki tashi ki wuce muje aure kuma Khalil da Humaira har mutuwa idan yaso baqin ciki ya kashe ki shasha sah mara tunani” Mama ta sake fada a mugun fusace.
Se Umaimah ta miqe tana cewa “ai ko baki fada ba nasan kina baqin ciki da zama na ni kadai a gidan mijina ina yin yanda naga dama bayan ke kina da kishiya dole kiyi murna tunda anyi mun, to wallahi daga ke har ita Hajiyar baku isa ba, naga itama ba ayi mata kishiyar ba shine ni zaku taru ku hada baki ayi mun ko to sedai ya zaba koni ko ita,
Idan kuma ita ya zaba to se na kashe shi in yaso kowa ya rasa”
Mari Mama takai mata kafin ta rufeta da duka tana cewa
“Kaiconki Umaimah kaiconki, wallahi da ba’a gida na haife ki ba tabbas zance ke ba yata bace ba jinina bace dan kaf ahalina dana Ubanki babu me mugun hali wanda be dauki kalmar kisa a bakij komai ba irin ki, kafin ki kashe shi ni gara na miki dukan da lahantaki Muguwa me baqar zuciya”
“Aa Hajiya ki bari ki dena jifanta da wadannan kalaman yawun uwa kaifi ne dashi akan Da, Ke kuma Umaimah kiyi haquri mu bar komai zuwa safiya in Allah ya kaimu” Hajiya Aisha ta fada tana qoqarin janye Umaiman ai kuw ata hankada ta da yake a bazata abin yazo mata se gata tim a qasa ta bugu da qugunta sosai har seda tayi qara.
“Karki sake tabani munafuka tun farko ai komai yana hannunki da kinso ki gyara da ba’a zo haka ba se yanzu ne zaki ce na bari da safe toh an qi a bari din” Umaimah ta fada tana zarewa Hajiya data zuba mata ido kawai tana kallonta ido.
Khalil kuwa runtse idonsa yayi, Allah kadai yasan irin daci da qunar da zuciyarsa takeyi masa a duk sanda Umaimah ta zagi mahaifiyarsa amma yana danne zuciyarsa ne ya hanata aikata mata abinda take raya masa saboda uzurin cikin da take dauke dashi.
Yasan Umaimah nada kishi amma be zata zata bati hankalinta ya gushe ta ringa abu irin na mahaukata ba akan abinda ita ce silar faruwarsa, meye lefinsa dan yayi aure bayan ita ta bashi qofar na yaje yayin sannan yanzu zatazo tana tambele da rashin hankali har taba iqirarin zata kashe shi?
Hadiye wani abu daya tsaya masa yayi ya bude baki dakyar yana nufar ta yace
“Duk abinda zakiyi Umaimah ni zakiyi wa ni nayi miki laifi karki sake zagin Mahaifiyata ko wani akan wannan abun ina kuma yi miki uzurine kawai saboda halin da kike ciki a yanzu”
“Ni kake yiwa uzuri Khalil? Idan ka sakeyi mun uzuri kai ba dan halak bane, idan baka dauki mataki akaina ba to Aisha da Ummaru shegenka sukayi kai ba dan halak bane
Sannan kace karna sake zaginta ko? (Seta waiwaya ta kalli Hajiya datayi suman zaune tun dazu kawai tana kallon Umaimahn) tace
“Aisha kinci uwarki, Khalil ka tsireni na zageta kayi abinda zakayi”
A mugun fusace Halifa yayi kanta amma se Hajiyar tayi saurin riqe shi tana cewa
“Barta Halifa wannan ba Umaimah bace, na tabbatar idan ba shafar Aljanu ba to ta samu tabin kwakwalwa amma wannan ba Umaimar da muka sani bace”
“Uwarki ce mahaukaciya bani ba” Umaimah ta sake fada kafin ta rufe baki Abba ya kai mata wata mahangurba ba shiri ta durqushe a gurin ko ihu ta kasayi saboda yanda duka ya shigeta .
“Khalil kana tsaye, mace ta zagi uwarka a gabanka kana tsaye baka dauki mataki ba Hajiya ko dai bake kika haifi Khalil ba?” Mama ta fada cikin kidima tana tafa hannaye,
Khalil da idanunsa suka rine zuwa ja jijiyoyin kansa gaba daya sun tashi ya kalli Mama yace
“Mama ta bakin Hajiya wannan ba Umaimah bace Aljanu ne suka shafeta amma ina son Umaimah itama tana sona na tabbatar ba a hayyacinta take wadannan abubuwan ba”.
“Allah ya wadaran soyayya irin taka Khalil Allah kuma ya wadaran zuciyarka zuciyar da kana tsaye matar aurenka zata zagi uwar data haifeka ka saka mata ido ba tareda ka chanza mata kamanni a bugu daya ba, Umaimah ko dai kin siyar da Imaninki kin bi bokaye ne ban sani ba dan dai wannan yafi kama da zuciyar wanda aka tsafance Dodo ya cinyeta dan Ubanki me kika aikata masa?
Ko da yake ba banza ba, tun tuni ya kamata na fahimci cewat Umaimah kin bar turbar Allah da Annabi amma ban gane hakan ba wayyo Allah na ni Malika ubangiji ka yafe mun ka sassauta mun wannan jarabta da kayi mun da kangararriyar yarinya da take neman kaini kabari” Mama ta fada tana fashe wa da kuka, se ta sake kallon Khalil tace
“Saketa mara zuciya, ka saki Umaimah yanzun nan Khalil”
“Mama mu fara mayar da ita Asibiti a bincika kwakwalwarta, idan basu ga komai ba se mu tafi gurin Malam Ishaq qila a can a dace amma nasan ba yin kan Umaimah bane dole akwai abinda yake zungurinta” Khalil ya fada cikin rawar Murya kamar yanda jikinsa ya dauki rawa.
“Wallahi seka saketa, kai ko kashin awaki na haife ku yau Khalil seka rabu da Umaimah idan kai baka san darajar kanka ba to ni bazan zuba ido yata ta wulaqanta uwar mijinta ba nima na haifa na kuma san zagin abinda takeyi idan ni akayiwa bayaj saki wallahi se na saka an hada mata dan bura uban duka ta yanda ko akuya bazata sake yiwa tsawa ba bare ta zagi bil’adama” Mama ta sake fada cikin hargagi.
“Ai wallahi ko be saketa ba a yau se Alqali ya kashe auran nan, ni kaina da zan iya canzaki daga cikin Ahalina da a take a yanzu zanyi dan banyiwa iyayena haka ba ban san dalilin da yasa Allah ya jarabce mu da ya irinki ba amma muna roqonsa ya kawo mana dauki” Abba ya fada cikin qololuwar bacin rai.
“Abba Mama dan Allah kuyi haquri, ku bari muga safiyar nayi alqawarin idan har aka tabbatar lafiyar Umaimah qalau a take zan rubuta mata takaddar sakinta” Khalil ya fada yana kallon Hajiyarsu da sigar roqo, Hajiya da kwallar baqin ciki ta zuraro mata ta kauda kai.
Kai da Fata Mama da Abba suka dage se Khalil ya saki Umaimah da tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya.
“Shikenan, taje na saketa saki daya” Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka.
“Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan” Mama ta sake fada,
“Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba” Hajiyar su Khalil ta fada
“Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu” Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa.
“Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu” Umaimah ta fada tana miqewa kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 52
ENGINEER BASHIR
Watanni ukun da suka shude Bashir yayi su ne cikin wata rayuwa me cike da qunci da rashin sukunin zuciya. Ya sake zama shiru shiru duk da daman shi ba me yawan magana bane amma a yanzu kana kallonsa zaka san shirun sa yana da nasa ba da tarin damuwa da yake ciki.
Abun ne ya hadar masa goma da Ashirin, kewar Ma'unsa tana neman zauta shi ga rashin kula da rashin abinci me kyau da baya samu a gidansa kullum se tashin hankali da hayaniya idan ya fita har baya so lokacin tashi aiki ya dawo gida.
Gaba daya a yanzu idan ka ganshi se ya baka tausayi yanda gaba daya ya fige ya fita hayyacinsa, hidimomi sun sako shi a gaba, wata daya da rabuwarsa da Asma'u gaba daya ya kasa gane kan cefanen gidansa.
Be taba sanin cewa Neman da Asma'u takeyi rufin asirinsa bane se ranar daya dawo daga aiki ya tarar da Amirah ta dafa masa farar shinkafa ta soya manja da yaji ta ajiye masa a ranar Azumi yayi, kuma kafin ya fita da safe ya gaya mata azumin yakeyi be shigo gida ba seda yayi sallar magriba dan haka yana shiga kan Dining ya wuce kai tsaye dan ya ci abinci.
Yana budewa yayi arba da abinda ta ajiye masa gaba daya se ya gagara bude baki ma yayi mata magana, mai da yaji a gidansa abinda rabon dako a ido ya ganta tun zamanin da yana Jami'a shine yau aka dafa masa a matsayin abin shan ruwa.
Yar gasken kuwa daya tambayeta dalili kai tsaye ta gaya masa cewar kayan miya sun qare kuma ita bata da kati a wayarta bare ta kirashi ta sanar masa shiyasa taga daya dawo bata girka komai ba tunda tana da yaji gara ko fara da mai dince tayi masa.
Yanzu shine ajiye buhun huna, shine cefane, dai da Maggi se ya siyo ya ajiye mata sannan in dai bashi ya duba ya sake siyowa ba babu ruwanta abinda yake da akwai shi zata sarrafa tayi abincin da kusan kullum Asarar sa akeyi dan yaran basa ci shi kuma bashida nutsuwa da kwnaciyar hankalin da zeci da yawa, da ya zauna cin abinci in sha Allahu seta qirqiro abinda zata bata masa rai ya tashi daga gurin.
Ya rasa wace irin macece Amirah da bata taba tashi kawo qorafi da mita se a lokacin da za'aci abinci ko lokacin kwanciya wadannan abubuwa suka taru suka sake dagula masa lissafi.
Be qara shiga uku ba seda Amirah ta fara laulayi. A iya saninsa bayan haihuwar da tayi an saka mata Implant a Asibiti saboda ta huta jikinta ya dawo daidai amma se gashi ba'a rufa shekara ba ta samu wani cikin.
Lokacin da yayi mata magana akan ya haka ta faru kai tsaye tace masa cirewa tayi sanda zata taho saboda itama tana so ta tara Yaya a dena mata gadara dasu, be ja ba ya barta tunda ai jikinta ne ta sani idan dadi taji idan ma wuya ce duk tafi kowa sani shidai tunda ta fara Amaye Amaye da wasu abubuwa ya tattarata ta koma dakinta dan wata muguwar qazanta ta farayi abin dai ba'a cewa komai.
A bangaren matsalar Ma'u kuwa yankewa kansa shawara yayi akan ze saka mata ido ne yaga iya gudun ruwanta, ze jira daga nan har shekara har zuwa sanda zata huce ta saurare shi a sannan baze sha wahalar shawo kanta ba su komawa auransu amma babu qarya yayi kewar Asma'u koma yace yana kan kewarta, fuskarta, muryarta, qamshin ta da gayunta daddadan girkinta ga murmushinta me saka shi manta kowa da komai kai wallahi dole ya maido da Asma'u rayuwarsa dan kuwa tabbas rasata babbar Asarace a gareshi.
Yanzu haka tun daya rabi da ita baya iya bacci saboda tunanin ta, idan kuwa har bacci yayi nasarar sace shi me nauyi to cike yake da mafarkin Asma'un.
Abu dayane yake dan kwnatar masa da hankali yanzu da be sake ganin wannan mutumin yazo gurinta ba, tun waccen ranar ma babu wani Namiji da ya sake gani tare da ita idan ba Yemi ba wanda ya bincika ya tabbatar abokin aikinta ne kawai babu wata alaqa a tsakaninau bayan ta aiki.
Sedai kuma guiwar sa tana yin sanyi irin yanda yaga gaba daya ta ci gaba da rayuwarta babu wata alama da take nuna tana da damuwa ko tunawa da shi dan yanzu ko sun hadu a hanya gaisawa sukeyi kamar wasu maqota, yanda zata gaisa da sauran mutanen da suke cikin layinsu shima irin wannan gaisuwar take yi masa babu wani abu da yake nuna sun taba hada wata alaqa ta soyayya bare har aje ga batun aure amma kuma baze sare ba, zeyi ta binta a hankali har zuwa sanda ita da kanta zata sakko ta neme shi.
A ranar Lahadin yana kwance a dakinsa kamar yanda yanzu ya mayar da hakan dabi'arsa zaman daki kamar wata sabuwar Amarya. Amirah ce ta shiga dakin fuskar nan qozai qozai da ita kana ganinta kaga me yaron ciki duk ta firgice ta saka doguwar rigar bacci cotton ta daura zani akai kanta ko dankwali babu ga gashinta me laushi duk ya tashi.
Kan gadon ta nufa ta zauna daidai kansa se yayi saurin miqewa zaune ya matsa can gefe yana hade fuska, Amirah da abin ya mugun bata mata rai, bakinta cike da yawun da yake yawan taruwan mata tace
"Wai wane irin wulaqanci ne