Showing 111001 words to 114000 words out of 260321 words

Chapter 38 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42678

daya fini?
Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar nan zanyi miki dan duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne” Baffa ya fada cikin dakewa alamar babu wasa a maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar Baffan nawa tana qara ratsani nace

“Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali, kaga yanzu baya iya fita kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda zaka iya yi akai”.

“Ash sha yanzu shi Bashir din baya aiki kenan, kinga ko jiya seda mukayi maganar da Muhammadu (Alhaji Qarami) yace mun yana iyakar qoqarinsa akan maganar aikin, kinsan qasar tamu ne yanzu da lamarin aiki ko kana da hanya fa idan wanda yafi ka yazo se kiga an samu tangarda.

Sannan yace daman su masu kwalin Irin nasa me martaba ta daya (first class) suna wahalar samun aiki a ma’aikatun mu na cikin qasa saboda yawanci manyan gurin suna ganin kamar in suka dauke su zasu fisu sedai a ma’aikatu mallakin qasashen waje su daman sunfi buqatar irinsu din ze ci gaba da bada takaddun in Allah yaso za’a dace.

Shiyasa ni nafi ganewa kasuwanci amma ku yaran yanzu gaba daya kun ta’allaqa akan aikin gwamnatin nan da gaba daya abinda kuke samu a wata se kiga Dan kasuwa ya same shi a sati daya wani ma cikin yini, yanzu dai ki turomun shi, idab yana da sha’awa yazo kasuwa idan Allah yasa yana da nasibi a ciki se ki gani.

Maganar Alhaji Amadu kuma zan duba abinda za’ayi, kama daga kan rashin lafiyar tasa har zuwa matsalar iyalin se muga abinda Allah zeyi”.

Sosai na ringa zubawa Baffa Godiya da Addu’oin fatan Alkahiri, har na tashi zan tafi ya tsaidani da cewa

“Yawwa na tuna kuwa Jiya Manager Bankin da nake ajiya munyi magana naji yace zasu dauki Ma’aikata, shi bangaren nasa ze iya aiki a banki ne?”

Cikin farin ciki na koma ina cewa “Eh Baffa, shi aikin banki indai ka iya kwanfuta da kana da lissafi a takardun ka zasu dauke ka, kuma duk yana dasu”

“Toh bari na kirashi yanzu naji idan da hali se ya fara wannan din kafin sanda Allah ze kawo wani”.
Ina tsaye ya kira Manager ya kuma amsa tareda cewa ze turowa Baffan Email yanzu a tura da CV din, sannan ranar Litinan yaje Bankin ya same shi da hardcopy na takaddun.

Haka na koma gida raina qal na tarar da Bashir ya rigani komawa yana zaune yana shan Shayi.

“Se yanzu” ya faaa yana kallona, seda na ajiye jaka da mayafina na zauna kusa dashi tareda rungumo shi nace

“Canki”
“Kinsan ban iya cankar abu ba ko” ya fada yana kallon fuskata, sena dakko wata ta na bude inda na rubuta Email din na miqa masa ina cewa “Gashi yanzu kaje Cafe ka tura da Soft copy na CV dinka sannan ranar Monday zaka kai hard copy din”.

Kallona yayi da rashin fahimta, nan da nan na gaya masa yanda mukayi da Baffa na rufe da cewa “Idan kuma kafi son kasuwar yace kaje ka same shi, ni da zaka hada dukka ma kana aikin kana taba kasuwancin se ya fi yanda su Yaya sukeyi.

A zatona zanga farin ciki a fuskar Bashir irin wanda nake ciki amma se naga akasin haka, cikin daure fuska ya kalleni yace

“Yanzu Ma’u har kin fara gajiya ne yasa kika tafi nemar mun taimako a gidan ku, daman dazun ina gida an kai kaya yaran suka ce kece kika kawo yanzu kuma kinzo da wannan”.

Tsabar mamaki ma kasa rufe baki nayi na tsaya ina kallon Bashir, a zatona abun kirki nayi ashe shi a nasa girman kan gani yake baya yaci kenan na nema masa taimako a gidan, se kawai na miqe na kwashi gyalena da jaka na ajiye masa Key din motar ina cewa

“Ban shigo da ita ba tana waje naga ka datse get din da kwado” nayi shigewata daki. Yanzu fisabilillahi da ace na samar masa aiki da kuma na zama ni nake dauke da dawainiyar mu wanne yafi? A zatona tunda ya fadi hakan baze yi ba se gashi washe gari yana ce mun ya tura ranar litinin din kuma yaje ya kai Takaddun cikin ikon Allah ba’a rufa sati ba sega shi sun tura masa da takarda sun daukeshi aikin wani satin ma ze fara zuwa.

Haka muka cigaba da tafiya zuwa yanzu duniya tayi mana daidai, Baffa ya dauke nauyin makarantar Sa’ad, Samirah da Naziru ya saka su cikin foundation din sa da yake biyawa Marayu da wadanda iyayensu basu da qarfi makaranta, shikansa Alhajin ya saka Ahmad Yayan mu da yake likita ne yana aiki da Asibitin Malam Aminu Kano su acan ana samun tallafi daga qungiyoyi dan haka ana daukar nauyin magungunan masu lalurori ansamar wa Alhajin kyauta yanzu ake bashi magani ga ganin likita duk sanda ya tashi har kanon yake zuwa tunda sunfi mu kwararrun likitoci se gashi a dan lokaci ya dawo hayyacin sa ramar da yayi duk ta cike ya koma fita kasuwarsa yanzu sannan ga Kayan Abinci da ake rabawa maqota yanzu suma duk wata se an kai musu Albarkacin surukuta nasu rabon ma daban yake.

Dan haka yanzu dan abinda Bashir zeyi musu be wuce na neman Albarka da duk da yakewa iyayensa ba idan yana da hali ni kaina yanzu se sambarka dan babu abinda Bashir ya rageni dashi ya karbi ragamar gidan sa komai yana yi yanzu har kudin makaranta yake bani daman tuni na bashi mota ta saboda zuwa aiki wanda dakyar ya karba acewarsa Wanda ya siyamun bazeji dadi ba, be karba bama seda na kira Alhaji Yasir din a gabansa na gaya masa Bashir ya samu aiki dan haka na bashi motata saboda sauqin zirga zirga tunda ni ina dab da kammala karatun Jarabawa zamu fara,

“Babu komai ai taki ce kina da damar yin duk yanda kika so, daman saboda bana so naga kina hawa motar haya ne ko ki ringa neman lift yasa tunda mijinki ne kinga ze kaiki ko ina kuma ya dakko ki, Allah yaci gaba da baku zaman lafiya mu shine fatan mu kawai” Alhaji Yasir din ya fada.

“Wallahi Ma’u rayuwar gidan mu tana burgeni, yayunku nada mutunchi sun kuma riqe girmansu ba tareda nuna banbanci ba ko yau Baffan ku ya mutu bashida damuwa yasan kanzuri’arsa a hade take ba kamar yanda yake faruwa a yawancin gidajen masu kudi ba da zaki ga kowa yan dakinsu ya sani kuma burinsu ace sune a gaba sun fi sauran” Bashir ya fada bayan da muka gama wayar, se nayi murmushi nace

“Idan Namiji ya zama tsayayye a gidan sa tabbas kan zuri’arsa zata hadu, amma daga inda ka nuna banbanci tsakanin matanka shikenan kayiwa zaman lafiya gibi a gidan ka dan yayan ko wacce zasu tashi wasu na ganin an fi son uwarsu sune yan gata sauran kuma zaau qullace ka na ganin kana wulaqanta uwarsu ka banbantata da dayar kaga baza’a taba samun zaman lafiya ba.

Kaima idan ka tashi qara aure kayi koyi da halin Baffan mu wallahi zakaji dadin rayuwarka”

“Ni ai dan ke kadai aka halicceni Ma’u babu sauran gurbin da wata zata sake samu a cikin zuciyata” ya fada yana janyo ni jikinsa.

Haka rayuwa taci gaba da shudawa. Nagama Diploma ta har sakamakon mu ya fito Bashir ya siya mun DE form dukda ban so ba yace gara naci gaba na gama lokaci daya na huta kawai.

Zaman gida da nake yanzu yasa Amirah ta dawo da zuwa, ba laifi yanzu ta dan saitu tunda ta qara girma ga makaranta da take zuwa kuma nima ba kamar da ba da bana saurara mata yanda zan tarbiyyan tar da Dan dana haka haka nake kula da ita dukda wani sa’in in ta koma taja gayawa Addah haka zata qaraci mitar ta nidai bazan kukata ba.

Indai har zata ci gaba da turomun ita to kuwa dole na saita ta yanda nake so. Yanzu kusan kullum a nan take wuni dan Addah bata zama, tun safe in zata fice qantalinta zata kawo mun Uniform din Islamiyyar Amiran da farko har Ummi ta fara Bari Bashir ya hana kai tsaye yace mata karta sake barinta dan matarsa ba me raino bace ai kuwa munga ruwan masifa dan har Dada seda ta karbi rabonta haka dai aka dena se Amiran ake barmun.

Wani lokacin ma har kwana takeyi idan Addah tayi dare bata dawo ba ko Bashir yace ta tafi ta zauna a gun Sauran Matan gidan se nace Yabarta kawai dan har ga Allah ina son yarinyar daman rashin jin ta ne ya ke hadamu nima kuma zuwa yanzu na fara sha’awar ajiye nawa Dan dan duk su Alawiyya sun haihu shekarar mu daya da kusan wata takwas yanzu da aure amma ni shiru.

Akwai ranar da na taba yiwa Bashir maganar nace masa ko zamuje Asibiti yace muna Aa

“Komai lokacine kuma bamuyi dadewar a har zamu ce zamu Asibiti ba, mu qara haquri Allah yasa jinkirin ya zama Alkahiri” ya fada dole na haqura.

Da zaman haka da nakeyi akwai wata makaranta a qasan layin mu nacewa Bashir zan nemi koyarwa acan be hana ni ba kuwa dan da kansa ma yaje ya tambayarmun suka ce naje ai kuwa aka sauke ni zan ringa koyarda yan JS1-3 Computer Science, qarfe 8 nake shiga 12 na gama classes dina in tafi gida kuma sosai nake jin dadin aikina haka yaran suna ganewa dan Allah yayi mun baiwa ta iya magana, sannan yanda nake da Sakin fuska yasa muka saba sosai da dalibaina.

Cikin hukuncin Allah se gashi na samu ciki wanda sam ban san dashi ba seda ya kai kusan wata uku a jikina sannan naje Asibiti saboda rashin ganin Al’adata na tsahon lokaci se gashi gwajin farko an tabbatar mun ina da ciki bayan an yi scanning aka gayamun watanninsa.

Tun ina Asibitin na kira Bashir na gaya masa, sosai kuwa ya nuna murnar sa yace na tafi gida na huta kafin ya dawo haka muka kwana ranar cikin farin ciki kamar mu ciro dan haka muka ringa kallon hoton scanning din da ba ganinsa ake yi sosai bama.

Kamar kuwa cikin nan na jiran a san dashi se Laulayi ya taso ni gab, kuma wani abu safiya nayi idan Bashir ya fita haka zan wuni da zazzabi da ciwon kai amma duk inda La’asar tayi kafin ya shigo gida na ware dan haka ko nayi masa qorafin baya yarda musamman idan ya dawo banyi girki ba ya ringa mita kenan in ce bani da lafiya kuma yace shi be gani ba.

A daidai lokacin kuma Admission dina ya fito, wannan karon na samu daman Business Administration na nema sun bani Level two haka na fara jigilar zuwa makaranta ga ciki ga karatu dan ma farkon semester ne, randa naji ba kanta kwanciyata nakeyi a gida naqi zuwa, haka muka ci rabin zangon, an tafi hutun Midsemeater aka tsunduma yajin aikin da ba qaramin dadi abun ya mun ba na ringa Addua Allah yasa kar a koma sena haihu.

Haka mukayi ta lallabawa, ina rainon cikina, Addah kullum tana tafe da kayan kwalamar da tasan zan so amma fa idan tazo ita ma haka zata koma da niqi niqin tsaraba dan duk abinda idonta ya kai se ta dauka ni kuma bana hanawa sedai Bashir yayi ta fada idan ya gani ko ya tambayi abu nace babu dan yasan ita kadai ce take zuwa ta dauka.

A lokacin su Fainusa sunyi candy dan haka suna zuwar mun sosai wata ran ma ni zan kirasu idan naga kwana biyu basu zoba haka zasu wuni suyi warkaja min su son rai, kayan sawata da duk suka mun kadan saboda ciki haka zan tattara in basu, kayan kwalliya turare duk zuwa da abinda zan basu har seda ta kai ta kawo ko bikin qawaye zasuje gurina za’ayi aron su takalmi, jaka sarqa wani lokacin in suka karba nace su barshi.

Lokaci daya maganar auran qannen Bashir Mata su ukun ta taso. dafarko auran Afiya aka saka, wane tudu wane gangare se ji nayi a bakin Addah wai ai gaba dayansu za’a hada”.

“Ni nacewa Nafi a hada yaran nan dukka kawai lokaci daya a huta to me za’a jira tunda duk da tsayayyun maneman su gasu da garin jiki ai bata jerasu a gaba su zamar mata kamar wasu kishiyoyi ba.
Tana wani ya za’ayi hidima zatayi yawa bayan ga Bashir Allah ya rufa masa asiri aikin Banki fa yakeyi har a tsaya ana wani zancen kudi” Addahn take gaya mun.

Niko banda “Allah ya sanya Alkahiri” ban ce mata komai ba dan mamaki take bani yanda take ji da aikin Bankin nan na Bashir seka rantse wani babban Manaja ne a CBN idan ba haka ba ta yaya za’a tattago auran yaya mata har uku kuma a dan qurarren lokaci kwata kwata wata hudu fa suka saka rana. Ai ko bashi da nasa hidindumun a bashi isashshen lokaci ya shirya balle ga hidimar haihuwa a gabansa dan kusan lokaci daya bikin ze kama da haihuwata.

Haka Bashir ya ringa mita kullum ya zauna saurin me akeyi da za’ace su uku za’a hada ina laifin Afiya da Sadiya dan duka duka Fainusa bata cike sha shida ba kawai girman jikine yasa aka mata tsallake a makaranta suka gama tareda Sadiyan.

Haka naci gaba da rainon ciki na a can kuma suna ta shirin biki, Alhajin su yayi iya qoqarin sa ya bada kudin gadajen Amaren kowa daya harda katifa dan shi kansa ba’a san ransa aka saka auran duka ba amma bala’in nacin Addah da har ta zuge Dadan itama ta hau ta zauna dole yasa musu ido sannan ya kira Bashir ya gaya masa karya kuskura ya takura kansa su saka shi yin hidimar data fi qarfinsa akai kowacce da abinda Allah ya hore tunda sun nace se anyi.

Dan haka gaba daya dan Albashin nasa da duk wani saving dinsa ya basu akayi musu kujeru gudummawar da aka samu daga sauran yan uwa da abokan arziqi suka harhada aka yi abunda ya samu.

Ido kawai na zubawa Bashir ganin har cikina ya kusa fita daga wata na takwas amma ko pant din jariri be siyo ba ko ya bani kudi yace na siya se hidimar auran qannensa yake yi. Raina ya sosu da abin har na kasa haqura wata rana nayi masa magana se ce mun yayi

“Ma’u kenan saurin me kike yi ki bari a haihu mana ko bakiga hidimar data ke a gaba na bane duk qoqarin da nayi kina kallo kullum da sabon abunda zasu ce akai ni gaba daya ma na gaji Allah Allah nake ayi bikin nan kowa ya huta”.

Sosai naji zafin maganar sa a lokacin, cikin bacin rai nace masa “Amma shima wannan abu me muhimmanci ne kuma kasan dai kaine meyi sannan ba yau kasan ina da ciki zan haihu ba tun ma kafin maganar bikin ta taso cikin ne a gaba yanzu kake cewa a bari a haihu tukunna cikin da ko a yanzu za a iya haife shi amma ko rigar da za’a saka masa bamu tana da ba ai shikenan” na tashi na bar masa gurin.

Nakuma qudurce a raina bazan sake masa magana ba dan daman tuni na sissiyi wasu wasu kaya unisex dana gani suka mun kyau se kawai na hada akwatina ta zuwa Asibiti na jingine in yaso naga iya gudun ruwan Bashir.

Wannan Abun yasa gudummawar danayi niyyar bayarwa ma na maida abata tunda a take takensa nasan ba abin arziqi zeyi mun idan na haihu ba nayi amfani da kudin na toshe wata kafar, Addah tayi shaguben harta gaji akan biki nata matsowa wai matar babban Yaya bance komai ba, ai ni ma ina da wayona ni na iya bauta musu amma abinda yake doke ayi mun saboda tasu buqatar tafi tawa ana nema a tauye ni sannan na kwashi gudummawa na bayar lallai ma se kawai nayi dariya nace mata

“Ai babban yayan ya wakilce ni yayi komai sedai mu jira Allah ya kaimu musha biki”.

Ana saura sati daya bikin Matan gidan nu suka aika wa Dadan da saitin Kuloli manya guda uku, a ranar ta kirani a wata tana ta godiya wai an kawo kula masu kyau da tsada daman suna ta yanda za’ayi a qara musu duk wanda suka siya ba wasu na arziqi bane yanzu gashi an samu sun gode sosai.

Haka kawai kuma se naji nauyin qin bayar da komai din da nayi, dan haka washe gari naje Awo da yake da mota na fita dan Asabar ce Bashir yana gida sena Biya na siyi wasu kulolij masu kyau guda uku da zannuwan gado manya masu abun rufa suka uku na wuce gidan Dadan na kai mata.

Taringa zubamun godiya amma qiriqiri Addah dana tarar ta nuna sunyi kadan, har tana cewa “Yanzu a matsayin ki guda a nuna wadannan kayan ace ke kika kawo ai se a raina ki ni dana ga wadanda akace an kawo daga gidan ku inji su hudun duka se naji wani iri nida na dauka mota za’a sauke mana” da wasa da dariya tayi maganar amma duk me hankali ai yasan me take nufi. Dan haka nima cikin wasan na mayar mata da martani nace

“Yo Addah kin manta ance taqamar mace gidan mijinta kudin uba ai ado ne kawai, kuma a iya qarfin mijina nayi wannan ai kuwa na kai a yabamun su kuwa da suka bayar fa kara suka mun bawai dole ya zamar musu fa se sunyi ba”

Washe garin ranar muka tashi da Alhinin Rasuwar Aliyu Abokin su Bashir, mutuwar ta dake ni kwarai dan A jiya bayan na dawo a gidan na tarar dasu shi da Bashir harda Bala suna hira, yana ta tsokana ta wai bana jin nauyin jikina nake iya tuqi nace masa ai Laifin abokinsa ne da be kai ni ba, na wuce ciki na barsu yana ta faman yi mun Addu’ar sauka lafiya ashe rabuwar kenan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login