Showing 198001 words to 201000 words out of 260321 words

Chapter 67 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42697

gani ya sakashi dagawa da sauri.

Bayan sun gaisa take ce masa
"Bashir Ashe Amirah bataji dadi ba har tana Asibiti?"

"Eh wallahi Dada jiya da daddare ne zuwa yau amma gobe ma zasu sallameta ai" Ya fada yana mamakin waya kirasu ya gaya musu bata da lafiya.

"Toh ai shikenan Allah ya bada lafiya amma ya kamata ta samu wani babba a kusa da ze ringa kula da ita saboda yanayin jikin kaga tana da zafin laulayi dole seta samu mataimaki"

"To ai anan din ma ba abinda takeyi tun tana da lafiyar ma se shirme kawai ta iya" ya fada a hasale

"Haka za'ayita haquri dai, seka turo da kudin jirgi na wanda ze zo ya tayata zaman dai, ya bangaren su Asma'u kuwa in ce dai abubuwa sun dai daita ko?"

"Hmmmm" kawai Bashir ya fada daga nan sukayi sallama dan besan me ze ce mata ba ma, qarin haushin sa ma wani da tace za'a turo ya taya Amirah zama in dan ta shine a barta ta gane kurenta wallahi haka ba yadda ya iya ya turawa da Naziru kudin dan yana tunanin Fainusa za'a turo ko banza gidan ya samu kulawa ai.

Shiru ya sakeyi yana tunani, kiranta zeyi ko kuwa kawai zuwa zeyi suyi magana fuska da fuska?

Yanke shawarar ya fara kiranta yayi a waya nan da nan yayi Na'am da wannan shawara ya shiga loda lambar wayar Ma'u da ya dade da haddacewa ya dannan mata kira.

Seda tayi ringin harta katse bata dauka ba, be haqura ba ya sake kira nan ma bata daga ba seda yayi mata kira uku ana hudu ta daga cikin muryar nan tata me sanyi tayi masa sallama.

Shiru yayi, ta sake maimaita sallamar se kawai ta kashe bayan data ja qaramin tsaki. Be sare ba ya sake doka mata kira, cikin dan fada fada ta daga wannan karon tace
"Waye wai? An kira ni kuma anqi ayi magana" jin ya sakeyin shiru ta sake kashe wayarta shi kuwa tsabar mamakine ya daskarar dashi wannan karon, kenan ta goge lambarsa ma kai ko ta goge ai bazata ce bata gane lambar akai ba shi Ma'u zata ce waye sannan ta kashe masa waya???

ASMA'U
WatoΒ  wata irin sabo da shaquwa da ban taba tsammani ba ya ringa shiga tsakanin na da Yusuf. Zuwa yanzu idan muka wuni bamuyi magana ba ji na nakeyi kamar bani da lafiya.

Dukda ba wata doguwar magana mukeyi ba amma duk sanda ya kirani seya gaya mun maganar da zatayi Rugurugu da zuciyata ta tsaya mun a zuciya har zuwa sanda zamu sake magana.

Aikina kawai nasa a gaba gefe ina kurbar madarar soyayya a ruwan sanyi wadda har yanzu ni ban yarda wai ina son sa bane,kawai ina jin dadin magana dashi na kuma dauke shi kamar wani Aboki ne domin dai so dayane kuma Bashir nayi wa shi.

Daren yau ina zaune nayi daidai a qasa ina duba wasu takaddu dana taho dasu daga office, gaba daya na gaji, Allah Allah nake na gama na kwanta na huta ga yara da suka isheni da hayaniya na korasu daki dan gaba daya yanzu kusan rayuwarsu a nan gidan sukeyinta tunda Bashir ya kwanta rashin lafiya suka dawo kwana anan gidan Aliyu ne kadai yake komawa se fa Jafar wata rana idan yaga dama ya bishi su tafi gida.

Wayata da na saka a chaji ce ta dauki qiwar in tashi na dakko tasaka na barta tayi tayi harta katse dan kanta idan na gama na kira dan nasan baze wuce Yusuf ba ko sabon Mayen daya maqalemun Hayatuddeen.

Jin ana ta kira ba qaqqautawa ya sakani jan tsaki na miqe na jawota, lambar Bashir ce, na tsurawa wayar ido ina so na gano dalilin da ze saka Bashir kirana a waya yanzu to qila yace Yayansa su tafi gida ko amma me yasa baze kira Aliyu ba tunda yana da waya ko Amna se ni ze kira?

Ina wannan tunanin har kiran ya sake katsewa wani ya shigo sena daga na saka a kunnena tareda yin sallama. Shiru naji anyi, na cireta na duba dan na tabbatar ko kiran katsewa yayi amma naga sakannin suna tafiya na sake maimaita sallama naji ba'a amsa ba se kawai naja tsaki na kashe.

Ta yuwu ma bani ze kira ba ko kuma besan kiran ya taho bama gaba daya ina qoqarin ajiyewa se ji nayi ta sake daukar qara alamar shigowar wani kiran hakan ya tabbatar mun da yana sane kenan wulaqancin nasa ne ya motsa dan haka na gyara zama tare da dagawa nace

"Wai waye ne yake kira ana magana kuma anyi shiru? Idan baka da abin fada ni ina da aikin yi" na sake kashe wayar.

To haka kawai ze ringa kirana yamun shiru me zan masa, ni kadai nayita mita ina ci gaba da duba takadduna can jimawa se shigowar saqo naji nayi banza da wayar ban tashi dubawa ba seda na gama abinda nakeyi kaf na je kwanciya dan har na manta ma seda na janyo ta zan saita Alam kafin naga saqon akan wayar se na bude na fara karantawa kamar haka.

"Zuwa ga Ma'una. Nasan ni mai laifi ne a gareki kuma na karbi kuskurena da hannu biyu sannan a shirye nake da karbar ko wanne irin hukunci daga gareki in har hakan ze saka ki huce daga abinda ya faru.
Kiyi haquri mu komawa kyakykyawar rayuwar da muka faro ko dan saboda so da qaunar da yake tsakanin mu.
Bashir".

Dogon tsaki naja bayan dana gama karanta saqon nasa nan take na goge. Ashe ma nayi haquri ne mu komawa rayuwar mu, juyawa nayi na kwanta ina rufe idona na tashi na zauna ina sake tuna dalilin daya saka Bashir yimun sakin wulaqanci.

Akan Mace fa, me daura zani da dan kwali Macen ma yarinyar dana raina da hannuna harta zama abin sha'awar daya gani ya aura ya hadamu zaman kishi da ita a saboda ita ya kassaramun rayuwa ya hadani da zawarci shine yanzu saboda tsabar rashin kunya ze turo mun wannan saqon yana tunanin wannan ya isa ya wanke tarin laifin sa a gurina kenan? Lallai ba shakka ya dauke ni sakarya.

Baccina na kwanta, washe gari da wuri muka fita tun a hanya kuwa na kaftawa yaran warning akan kan kar wanda ya sake zuwa ya kwanar mun a gida kowa ya zauna a gidan ubansa. Idan taqamarsa su to yanzu na rigada na saki zuciyata ko da su ko babu su a tare dani babu abinda ze chanza daga walwalata. Na barsu a hannun ubangiji nasan ze kulamun dasu.

Sau kusan hudu ina ganin missed calls dinsa a office dinma amma naqi dagawa to me ze gayamun wai? Ko kuwa ni din an gaya masa sakarya ce da zezo yana wani kirana a waya kuma na kulashi.

"Ko dan darajar so ai zaki iya saurar sa Ma'u" wata zuciya ta raya mun se gashi yau nida kaina na qundumawa wannan zuciya tawa me qoqarin tsayawa Bashir zagi, ban haqura ba na janyo wayata na goge lambarsa daga ciki sannan na dora layin akan tsarin da kiran baquwar lamba baze shiga ba sedai naga missed call ni na kira dan idan ma nayi blocking nasa ze iya chanza lamba ya kira amma yanzu kuwa koda ace ze sake lamba dari bazata taba shigowa ba.

Ina shirin tashi Yusuf ya kirani. Duk wunin ranar bamuyi waya ba saboda ya gaya mun tun daran jiya daman yana da Meeting se sanda ya samu sarari ze kira shine se yanzu.

"Nayi fushi" ya fada bayan da muka gaisa.
"Me kuma ya faru? Kai da waye zakayi fushi?" Na tambaye shi dai dai sanda na shiga motata.

"Badai se yanzu kike tashi daga aiki ba?" Yusuf ya tambayeni sanda yaji na kunna motar, seda na mayar da wayar jikin sipikar motar kafin na amsa shi da cewa

"Wallahi se yanzu, kwana biyun nan ayyuka ne suke yi mun yawa shiyasa nake dadewa a office"

"Gaskiya aikin nan yana wahalamun da mata ya kamata na dauki mataki akan sa fa, ko dai a rage yawansa ko kuma suyi asarar haziqar ma'aikaciya wadda mayar da kamarta se an duba".

Murmushi nayi ina ci gaba da tuqina nace

"Naji kace kayi fushi, me akayi maka ne?"

"Oh tambaya ma kikeyi? Kece mana. Gaba daya yau ko kirana bakiyi kinji ya nake ba ko da yake daman ai baki damu dani ba, ni kadai nake damuwa dake idan banji lafiyarki ba amma ke nasan ma mantawa kikeyi dani idan ban kira ba".

Yanda yayi maganar ne ya bani dariya har seda na dara kafin bace

"Haba dai waya gaya maka ban damu dakai ba?"
"Ni na ga haka da kaina amma ki fada naji idan kin damu dani din"

"Na damu da kai mana ko ban fada maka ba kaina ai ka sani" na sake fada. Seda yaja wani murmushi kafin yace

"Na dai jiki kawai amma ni banga haka ba. Kinga ni ina sonki amma nasan ke duk duniya ma baki da maqiyin daya kaini yanzu".

"Haba wacce irin magana ce wannan Yusuf? Taya zaka ce bani da maqiyi kamar ka yaushe na gaya maka haka?"

"To idan ba gaskiya bane ki fada da bakinki cewar kina sona mana sena yarda" ya sake fada yana yin qasa da murya kamar me rada. Ba tare da tunanin komai ba nace

"Ina sonka mana Yusuf kaifa dan uwa....."

"Karki qara komai kin rigada kin gama magana ai tunda har kika furta kina sona da bakin ki yanzu zan kira Alhaji Qarami na gaya masa. Daman yace na nemi soyayyarki shi kuma ze tsaya mun da izinin Allah a wannan karon sena sameki Asmyta" Yusuf ya katse ni ciki tsananin murnar da muryarsa ta kasa boyewa.

Be barni nayi magana ba ya kashe wayar, mamaki da dariya suka kamani duka lokaci daya. Wai da girmana da komai Yusuf yayi mun wayo dukda ni bada wata manufa na fadi Ina son sa ba kawai dai na fada hakan ne jin yanda yayi magana bawai dan har cikin zuciyata abin da yake raina kenan ba.

Tuqina naci gaba dayi hankali kwance harna isa gida. A bakin qofa na tarar da Bashir a tsaye ya harde hannaye da alama ni yake jira, na gama daidaita fakin kafin na fito fuskata a sake na shiga gaishe shi ina qare masa kallo yanda naga gaba daya ya zabge yayi baqi kamar wnada yayi jinyar shekara daya.

"Bari na shiga sena turo maka yaran seda fa na gaya musu su ringa zama a gidan ubansu amma saboda rashin ji irin nasu shine suka taho Yi haquri yanzu dana shiga zan tattaro maka su kuwa" na fada ina qoqarin wuce shi na shiga gida seya dakatar dani da cewa

"Ba gurinsu nazo ba Ma'u gurinki nazo ina so muyi magana".

"Toh gurina kuma?" Na fada ina kallonsa da mamaki, be amsani ba na ci gaba da magana ina cewa

"Kaga yanzu na dawo ko sallar magriba banyi ba ga gajiya na kwaso, idan ba abin sauri bane ka bari ko zuwa gobe Juma'a da wuri zan taso ko kuma Weekend ma kawai kaga ina gida se muyi maganar"

"Maganar sauri ce Ma'u, na kiraki a waya ma bata shiga na tura miki da saqo duk babu amsa" ya fada yana tsatstsareni da ido. Ko a jikina, gaba na sakeyi ina cewa

"Koh? Qilan saboda idan banyi saving lambar ba kira baya shigowa ne, to tunda kace abin sauri ne bari idan na dan huta zan aiko yara se su gaya maka" na fada ina tura qofa na barshi a tsaye.

Har qarfe tara na gama cin abinci kenan sega Abdallah wai Abbi yace yana jirana. Da mamaki na kalle shi nace ina Abbin yake dan nifa shaf na manta da mun hadu da wani Bashir ma har munyi magana ban qarasa cika da mamaki ba seda Abdallan yace mun wai ai yana qofar gida tun dazu ya saka kujera ya zauna.


Haka na saka dogon hijabi ba na fita saboda dai wulaqanci babu kyau. Yana nan zaune kamar wani sabon Almajiri na zauna a Empty kujera dana tarar ina cewa

"Kasan shaf na manta ma da munyi magana, koda yake ban zata zama kayi ba tunda nace idan na gama zan aiko yara su kiraka ai".

Zamowa qasa naga Bashir yayi kamar wanda yaje neman gafara a gaban Dada ya kama qafata na janye ya riqe qasan hijabina yana cewa

"Ma'u haquri nazo baki akan abinda ya faru tsakanin mu. Wallahi nayi nadama, sharrin shaidan ne ya angizani kuma na gane kurena na yarda idan babu ke a tare dani rayuwa ta bazata taba cika ba. Dan Allah ki yafe mun ki Yi haquri mu koma wa auran mu nayi miki alqawari baza kiyi nadamar komawa zama dani da dan nasan kina sona nima ina sonki zamu ci gaba da zaman mu cikin aminci kamar yanda muka faro shi".

Ido kawai na saka masa ina kallon wannan wasan kwaikwayo har ya kai qarshe kafin na miqe ina cewa

"Ka tashi dan Allah ko da yake kai naga baka tsoron kaga hotonka a Ticktock yanzu idan ba haka ba meye na durqusa mun. Asma'u ce fa Bashir daka danqara mun har saki biyu saboda matar so ka kuma bani rana daya tak dana tattara inawa inawa na bar maka gida har ka manta wannan shine zaka zo kana durqusa mun wai nayi haquri na komawa auranka?

To bari kaji, shi son da kake iqirarin a koma Saboda darajar sa daga sanda ka tsinke igiyoyin auran nan suka tattaro Son gaba daya sukayi awon gaba dashi, dama ai saboda auran ne ko tunda babu shi kaga babu sauran wani so tsakani na dakai, ko da kaga ina gaisuwar mutunci dakai darajar zuri'ar da take tsakanina dakai ne amma badan haka ba kai Bashir baka isheni ni Asma'u kallo ba ka sani.

Ada tabbas na So ka amma a lokacin da bansan menene So ba ba ayanzu da na hadu da limamin So ya fayyace mun shi na gane ma'anarsa ba. Dan haka idan kana mafarkin ni zan komawa auranka to ka tashi dan kuwa tamkar a baka tsinke a ce ka zunguro sama ne kaga kuwa wannan abu ne da baze taba yuwu ba kayi sake Bashir nayi maka nisan da har abada bazaka tarar dani ba"

ina gama fadar haka nayi shigewata gida na barshi a tsaye zuciyata kuwa yanda take bugawa ina tsammanin wanda yake tsaye kusa da ni ma ze iyajin bugunta.

A karanta da haquri, wani qundumemen uzuri ne ya taso mun beyond my control πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™πŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸπŸŒŸ


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 55

BASHIR

Kamar wani dolo haka ya rakata da idanu harta bacewa ganinsa kafin ya sauke ajiyar zuciya me qarfi ya miqe daga durqushen da yayi yana jin kamar an sare masa qafafu tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.

Tabbas Wannan ba Asma'u daya sani bace data jiqu cikin so da qaunar sa, ba Asma'un da take shiga damuwa saboda damuwarsa ba bace wadda take hana kanta bacci a duk sanda yake cikin damuwa ko bacin rai wannan wata Asma'u ce ta daban a gabansa.

"Idan ma kana mafarkin zan koma gidan ka to ka farka dan nayi maka nisa na har abada Bashir kayi sake" kalamanta suka ringa dawo masa a sanda yake jefa qafafunsa inda shikansa be sani ba dan burinsa a sannan ya ganshi a cikin gida kawai ya samu makwanci.

Shirim ya fada kan kujera ya dafe kansa da hannaye biyu yana juya shi. Wai menene SO?Yaya SO yake? Menene tattali da kulawar da mace take da buqata wanda Asma'u ta rasa a gurinsa da har take iqirarin ta samu wanda ya fayyace mata su?

Allah shine shaidar sa yana son Asma'u son da duk duniya be taba yiwa wata mace irinsa ba. Yana sonta tana kuma da wani matsayi na daban a zuciyarsa ta yanda tayiwa sauran mata zarra amma kowa ya gaza fahimtarsa mutane suna yi masa gukunci da zahirinsa ne kawai ba tareda sanin ainihin abinda yake cikin zuciyarsa ba wai me yasa kowa ya gaza fahimtarsa?

Dole ya san abinyi ba ze zuba ido yana gani ya rasa Asma'u ba faruwar haka daidai yake da yankewar duk wani farin ciki da walwala daga cikin rayuwarsa ya shaida hakan dan kuwa gashi a iya lokacin da suka rabu tun sannan be sake kwanan farin ciki ba. A kullum sabuwar damuwa da tashin hankali ne suke dirar masa.

Gidansa ya rushe, nutsuwar sa ta gushe lafiyarsa kanta ta tabu a cikin qasa da watanni shida besan yaya ze tsinci rayuwarsa ba ace ze qareta ba tareda Asma'u a cikin ta ba.

Wai ma wane ibtila'i ne ya haushi da har ya kaishi ga sakin Ma'u?
"Qaddarah" zuciyarsa ta raya masa se ya dafe kansa da hannu biyu yana fadin

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" a fili yana jin yanda qirjinsa yake masa quna wanda ya zame masa jiki yanzu a duk sanda ya zauna yana tunanin makomarsa da Ma'u to se yaji wannan ciwon kamar numfashinsa ze dauke wani lokacin.

Wayar sa ya janyo daqyar idanunsa sunyi jajir sun kawo ruwa, lambobinsa yake bi yana karantawa ya rasa waze kira a yanzu. Duk wadanda ya kamata ya fadawa damuwarsa a yanzu ya dade da datse alaqa me kyau a tsakaninsu saboda a da yana ganin kamar suna masa katsalandan a rayuwarsa da qoqarin nuna masa yanda zeyi gashi yau ranar su tazo amma bashi da kwarin guiwar kiransu.

Lambar Bala ya kalla, wani tuquqin baqin ciki ya taso masa nan take ya danna mata block tareda goge ta gaba daya. Ba tun yanzu ya kamata ya ankare da ingiza me kantu da Bashir yake masa ba amma se yanzu da komai ya lalace sannan ya fito masa da ainihin kalar sa gaskiya.

"Allah sarki Aliyu, Amini na kwarai Rahmar Allah ta kai maka" ya fada yana dauke kwallar data ziraro masa ta gefen ido, yana kewar Aliyu da gasken gaske Aboki ne irin wanda ya zamar masa dan uwa wanda samun irinsa se an tona.

Aliyu ne kadai yake iyawa da halinsa, koda ace ya nuna masa gaskiya yaqi binta baya haqura ze yi ta naci da nusar dashi har se dan karan kansa ya fahimci hakan ya kuma ya aikata abin hirar su ta qarshe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login