Showing 207001 words to 210000 words out of 260321 words
Chapter 70 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
dari na dari uku ta watsa masa tayi gaba abinta.
Kamar Amirah zatayi kuka ta shiga roqon ta data bayar zata biyata dan ita sisi bata magani a hannunta ko a cikin gidan gashi babu motar Bashir ballantana tace yana gida zata shiga karbo ita kuwa Addah fafur taqi qara ko sile sema masifa da take zazzagawa me Taxi daya juya P cap baya yana jira yaga zasu bashi kudinsa ne ko se ya dauki mataki.
Ganin suna neman bata masa lokaci gashi wadda yaga kamar kudin a hannunta suke na neman shigewa gida yasa ya fizge jakar Addah, babu bata lokaci ya zazzage komai a qasa sega kudi kuwa suka zubo ya irigi dubu gomansa cif ya shige mota ko kula ihun barawa da Addah take zundumaqa beyi ba ya qara wuta abinsa to masu wucewa ma babu wanda ya kulasu dakyar Amirah ta turata suka shige gida se dafe kanta take daya dauki ciwo saboda bala’in Addah.
A cikin gidan ma Sabon tashin hankali ta dasa mata akan kudinta ganin babu sarki se Allah yasa ta shige daki ta kullo kanta, wayarta ta shiga dubawa dan ta kira Bashir ko ze zo ya kashe wannan wutar ta ganta amma babu chaji seta jona ta shiga wanka saboda jikinta sam babu dadi.
Lokacin data fito wayar tadan caju, lambarsa ta shiga kira yanzu a kunne take amma kiran na shiga za’a katse shi ta kira yafi sau biyar qarshe dan kanta ta haqura ga yunwa tana ji amma tsoron karonsu da Addah idan ta fita palour yasa ta gwammace ta sha ruwa da wani Biscuit da yake a dakin ta kwanta ledar magungunanta kansu suna palour haka ta haqura bata sha ba.
BASHIR
Daga Asibiti kai tsaye gidan Musa ya wuce dan yanzu can kadai yake iya zuwa ya rage zafi tunda Musan shi kadai ne bashi da mata.
Cikin jimamin abinda ya sami qafarsa ya tare shi, ya ringa masa sannu kuwa qasan ransa kuwa dariya ce fal musamman dayaji wai da surukarsa ake fada tsautsayi ya fada kansa suka qonashi shi kuwa Bashir wace irin sirika yake da ita me fada da mutane a Asibiti?
A gidan ya wuni zir, duk dai hirar da sukayi akan yanda ze gyarota da Ma’u ne dan ya gayawa Musan yanda sukayi da Abubakar, shi ya qara bashi kwarin guiwa akan ya ci gaba da binsa yana bashi haquri wata rana ze dace sannan kar ya daga qafa a Gurin Ma’u duk irin wulaqanci da cin kashin da zata masa ya daure daman ance ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi amma idan yayi haqurin buqata ta biya shikenan shi yaci riba.
Shi ya sake bashi shawara ya ringa tura mata text na ban haquri akai akai. Gyara zama Musa yayi yaci gaba da ce masa
“Kaifa matsalar ka Bashir na fuskanci gaba dayanka se a hankali yar soyayyar nan naga alamar baka iyata ba se tsare gida da hade fuska kawai. Sufa mata da ka gani suna son tattali da kulawa ko baka da sisi indai mace na samun nutsuwa da Farin ciki a gurinka zata Yi haquri ta zauna dakai amma ko kafi qaruna kudi indai ta rasa wannan ba ko wacce bace dukiya take a gabanta zata iya rabuwa dakai ta tafi inda aka san darajarta ne ko kuma tana tare da kai ta ringa kula wasu cana waje da suke bata kulawa suna yabonta.
Da yawa maza mu muke bada qofar da matan mu suke aikata wasu abubuwa da basu kamata ba a bayan idon mu. Yanzu misali kaine kullum cikin hade rai a gidanka, kaida matarka idan taga haqoranka to magana kakeyi babu dariya babu lafazi me dadi balle ace tayi kwalliya ka yaba ko ka zauna kayi wasa da raha da ita tsakanin ku se bada umarni kamar wata yar aiki da ubangidanta dan Allah ta yaya kake tunanin idan ta hadu da wanda ze bata duk irin wadannan kulawar data rasa a gurinka ba bazata kulashi ba?
Ba kowacce mace ce take da qarfin zuciyar daure wasu abubuwan ba, wata koda ba ta sigar fasiqanci ba, wata da sunan aboki zakaga ta hadu da wani namiji da zasu zama kamar wasu Qawaye ko Aminai duk wani sirri nata daya kamata ta yi shi tare dakai shi ze maye mata gurbi ya zama abokin shawararta se kaga matar aure wai tana da wani Besty duk waya ja Mijinta kuma ka tabbatar duk dakon zunubin da zatayo tare za’a kasafta muku dan kai ka yanka mata tikitin da har zata kula wani banza can da auranka.
Ka duba yanzu ko a gurin aikin mu yanda mata suka lalace matan aure kaga suna qazamar rayuwa suna mu’amala da wasu mazan a waje da bana auransu ba a kaso goma idan ka tarasu bakwai wallahi mazansu nada sa hannu cikin fadawarsu wannan halakar saboda basu da ma lokacin su ballantana su san damuwarsu har su maganta musu ita da yawan maza muna dauka kudi shine maganin ko wacce matsala idan ka wadata mace shikenan ka gama mata komai wanda sam abin ba haka yake ba dole ka kula da matarka ta kowanne bangare ka tabbatar da cewa ka toshe mata duk wata buqata idan kayi haka kuma kaga wata matsala ta faru seka qaddara cewa jarabawa ce kuma daga ubangiji amma ba wai dan kai ka bayar da qofar faruwar hakan ba.
Dan haka nidai shawarata Bashir ka canja takunka, ba Asma’u ba ko wacce mace zaka zauna da ita dole ne kasan qima da martabarta. Ka sani cewar ba Alfarma kayi musu daka auresu ba ballantana ka dauka dole suyi haqurin zama dakai da halinka Aa zamane na ibadah da Allah ya hadaku kowa yana da haqqi akan dan uwansa”
“Haka ne kuma zanyi qoqari na gyara kuskurena Musa dan ina buqatar Ma’u a rayuwa ta wallahi” Bashir ya fada bayan daya sauke tagumin da yayi.
“Au saboda ka dawo da Asma’u zaka chanja hili kenan? Bashir bari fa na gaya maka gaskiya Halinka cikin goma bakwai basu da kyau ta fannin zaman takewa. Kai bafa matanka ba kadai mu kanmu haquri muke dakai wani lokacin saboda shi hali zanen dutseaka ce ba’a chanza wa mutum shi amma a wannan karon in har kana so lamuranka su daidaita dole fa seka daidaita sahu a to.
Kai in banda ma halinka Bashir a zamanin nan ka samu mace kamar Asma’u bafa ajinka bace wallahi in ma gaya maka gaskiya Allah ne kawai ya kashe ya baka ka samu tana sonka take hidimta maka da jikinta da Aljihunta, matar nan fa ko daure fuska kayi se hankalinta ya tashi. Ka tashi ka tafka mata kishiya ta wulaqanci koni Namiji naji zafin abinda kayi ballantana ita sannan ka qara mata da tukwuicin saki kai ni idan ta haqura da wuri ta dawo maka gaskiya bata mun daidai ba”.
Daure fuska Bashir yayi tamau yana kallonsa yace
“Karka kuskura kace mun kaima kana son matata dan shine mafi girman kuskuren da zaka aikata, mu kadai ne a gidan nan yanzu zan murqusheka ka mutu Ba wanda yasan meya faru”.
Dariya Musa yayi harda fadowa daga kan kujera kafin yace
“Maida wuqar Malam ashe daba ka fara ban sani ba. Ai ni idan zan so Ma’u bazaka sani ba, qila se kaji nayi aure kawai kazo gidana ka ganta a matsayin matata amma ni sam ba haka nake ba, babu kuma haka a tsakanin mu kawai dai ina nuna maka irin girman asarar daka tafka ne a rayuwarka kuma idan baka hanzarta ba kana ji kana kallo sedai ka mutu kana cizon yatsa da daka sani ka mayar da yayanka marayun dole ka rabasu da uwar su haka kawai”.
Ganin da yayi daga shawara kuma abin na Musa na neman ya koma wulaqanci yasa yayi masa sallama ya kamo hanyar gida, a hanya ya tsaya wani guri da suke siyan Shawarma da wani Gas meat da Ma’u take bala’in so ya siya da yawa ya hado da Madarar ruwa da kwali itama kalar wadda take sha kafin ya kamo hanyar gida.
A qofar gidanta ya ci burki, a waya ya kira Amnah yace tazo ba tareda ya fito ba ya ce ta bude bayan motar ta kwashe ledojin ciki.
Ya dade a mota kafin ya fito qafa daya da takalmi daya babu ya dauki tasa ledar Naman da Madarar ya shige gida, Hajia Addah na zaune a palour ta tasa Amirah data gama zaman dakin ta fito a gaba har sannan dai zancen dubu goma yaqi ci yaqi qarewa.
Kallo daya ya musu sanda Amirah ta masa sannu da zuwa ya wuce daki tabi bayansa, tun dazu take jira ya dawo ita dai ya taimaketa ya biya Addah kudinta kota samu ta shaqi iska a gidan yana shiga dakin kan ya rufo tayi wuf itama ta fada ya kuwa balla mata harara ta sunkuyar da kai se ya wuce ya ajiye ledar hannunsa ya shiga bandaki.
Tana zaune se hadiyar yawu take saboda qamshin naman da duk ya cika dakin ya fito, kamar munafuka tayi qasa dakai tana gaishe shi ya amsa a taqaice yana cire rigar jikinsa ganin taqi fita yace mata
“Lafiya?”
“Am daman Yaya an sallamo mune na kiraka da wayar Addah lokacin baka dauka ba na kira Samuel shima yace mun...”
“Na sani na aike shi ba gashi kun dawo ba se akayi yaya to?” Ya katseta murya a cunkushe, qasan ransa har yana tunanin wane hankali ne yazo mata da har tayi tunanin zuwa ta duba shi kodai Addah ce ta sakata dan yasan a kalar nata tunanin dai bazatayi ba, maganar tace ta katse shi da take cewa
“Daman Taxi muka hawo ta dawo damu, shine seda muka zo yace wai kudin motar dubu Ashirin tunda drop muka dauka to Addah ce ta biya tun safen take ta mun masifa akan na biyata kudinta kuma ni ko sisi bani dashi nayi ta kiranka ma dazun kana rejecting gata can wallahi ko abincin kirki ta hanani naci da masifarta”
Wani mugun kallo me nuna zallar bacin rai yake aika mata, wato kudi take da buqata tun dazun dalilin kiran da ta ringa masa kenan, qonewar da uwarta taja masa ma bata dameta balle taji ya qafarsa kawai kudi ze bata a mugun fusace ya nuna mata qofa ba tareda yayi magana ba.
Amirah dake ta Addu’a a ranta Allah yasa ya bata goman ta ajiye dan tunda tazo sile biyar bata hadasu ba kai ko katin waya bashi ne kusan dubu biyar taci na Mtn saboda ya dena saka mata, da tana Gombe kuwa duk satin Allah yar dubu dayar nan dai seya saka mata wani lokacin ma biyu ga yar cuwa cuwar da takeyi ta karbi kudi a hannun Naziru na cefane anan kuwa shi yake siyo komai kuma se abinda ta gani kawai dan waca wacar nan data san anayi a gidan bata san me yasa yanzu kusan komai a qididdige yake ba ba yanda ta saba ganin sanda Anty tana nan komai na danqare a Freezer ba sedai su bude su diba.
Ita da yake ya raina mata hankali se abinda yaga dama yake siya ya ajiye kuma idan ya qare abinda yake ci ze siyo da wuri, daman nama ne yafi damuwa dashi, tana son kifi amma tunda tayi masa wani farfesun kifi ita kanta dai ranar data ci haka qarnin yayi ta taso mata be sake siyowa ba tayi nacin harta gaji to tunda ta samu ciki ma ya dena cin abincinta, daman yaran ba ci suke ba sedai su dafa abinda suke so ko su shigo dashi daga can gidan sedai tayi ta qara qararta ita kadai ga cikin me dan banzan kwadayi haka zata yita hadiyar yawu idan ta jiyo qamshin abincin makwafta.
Tsawat daya daka mata ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi dan ashe yana ta mata magana ma bata ji ba, da sauri ta tattari qafarta tayi waje tana fita suka kusa karo da Addah dake labe a bakin qofa cikin matuqar takaici Amirah ta kalleta kafin ta wuce dakinta wata kwalla na sakko mata.
Bashir kuwa sallah kawai ya tayar dan idan ya tsaya takaicin Amirah yana iya shaqe shi kawai aga ya fadi, so kuma yake yayi isha ya zauna ya tsarawa Ma’u Saqo ya tura mata dan ya qudurce indai soyayya ce matsalar to kuwa ko Sharukan se dai yazo ya kwashi kos a gurinsa a wanna karon.
ASMA’U
Bayan dana dawo daga rabon abinci sallah kawai nayi na kwanta dan na gaji sosai bani na farka ba se dab da magriba. Kiran Yaya Abubakar na gani guda biyu na shiga bandaki na wanko fuskata da bakina kafin na dawo na zauna na danna kiran lambar sa.
Bayan mun gaisa yake cemun
“Dazu Bashir ya kirani a waya wai yana bani haquri, ban san rashin kunyarsa harta kai haka ba se yau tukunna nadai ja masa kunne akan karya kuskura ya sake kirana in ba haka ba yasan sauran”
“Lallai Baban Ali shi har yana da qarfin guiwar kiran ka kenan, haka fa jiya yazo qofar gidan nan wai yana bani haquri harda durqusawarsa” na cikin mamakin tsaurin idon Bashir.
“Asma’u” ya kira sunana da sautin da yake nuna muhimmancin abinda ze gaya mun sena gyara zama dakyau na amsa ina sauraronsa yaci gaba da cewa
“Kafin ki auri Bashir kin taba tambayata abinda yasa bana farin ciki da auran ku ko to yau zan baki amsa. Bashir Abokina ne kin sani tun na yarinta dan haka nasan halinsa ciki da bai, halayyata da tashi sunyi kamanceveniya ta wani bangaren saboda dani dashi murdaddun mutane ne da ake shan wahalar gane gaban mu.
A bangaren auratayya muna da buqatar samun tsayayyar mace me taurin zuciya da ra’ayin riqau ta yanda dole sedai ko mu zubda makaman mu mu bita ko kuma ya zamana anyi 50 50 ma’ana kowa ya riqe bangare daya bawai wadda zamu taka yanda muka ga dama ba kuma ta biyu.
Baki dace da Bashir ba saboda ke mace ce me sanyin hali da saurin yarda tareda sadaukarwa inda ace Aliyu marigayi ne ya nemi auranki dukda yaso hakan amma Bashir yayi masa shigar sauri, a lokacin da na zamo kan gaba a komai saboda nasan bazaki taba nadamar zabarsa ba saboda halayyat ku kusan daya ce, dake dashi zaku ringa rige rigen kyautatawa junan ku amma Allah be hukunta faruwar Al’amarin a haka ba ya qaddara cewar Bashir din dai shine Mijinki harda rabon zuri’a a tsakanin ku.
Banaqin Bashir saboda shima mutumin kirki ne kuskurensa kuma ajizanci ne irin na ko wanne dan Adam kuma na tabbatar da nima da ace irin ki nake aure da ko ba dukka ba se an samu kwatankwacin halayyar Bashir a cikin gidana saboda nasan duk abinda na dakko zata yarda kuma ya zauna.
Bance Bashir baya son ki ba amma ki sani son da kike masa ko nace kina bayyana soyayyarki sama da tasa shi kansa wannan babban dalili ne da Namiji ze riqe ya kuka juyaki duk ta yanda yaso saboda yasan kina sonsa zakuma ki zauna dashi a duk yanda yake.
Abinda nake so na gaya miki Ma’u, Bazan hanaki ba idan har zuciyarki ta aminta da ki koma gidan Bashir amma ki riqe abu guda daya shine ke din dai kece ba wata sabuwa ta daban ba haka Bashir yana nan a Bashir din da kika sani babu abinda ze chanza daga halayyarsa ta ainihi duk wani chanji da ze zo miki dashi na dan lokacine dole wata rana se an koma gidan jiya.
Karki duba kowa ko wani abu ki duba makomar rayuwar ki, Kin cancanci samun rayuwa me cike da Farin ciki Ma’u kiyiwa kanki gata, idan har farin cikin ki yana tareda Bashir ki koma gidansa ku zauna zamu ci gaba da binki da fatan Alkhairi kamar yanda muke miki a koda Yaushe idan kuma kina da zabin daya fishi Allah ya tabbatar miki da Alkahiri yasa kiyi farin ciki dashi na har abada”.
Shiru nayi kamar wadda aka zarewa laka har Yaya Abubakar ya gama mun magana dakyar na iya cewa
“Nagode Yaya, nima a yanzu banida wani zabi se abinda Allah ya zaba mun, in sha Allahu yau zan fara istikara ina kuma fatan Allah ya saka mun duk abinda yafi Alkahiri a zuciyata Nagode kwarai Yaya Allah ya saka da Alkahiri”
“Babu komai Allah ya jishshemu Alkhairi, Ina Yaran ina fatan dai babu wata matsala ko?”
“Babu komai Yaya, ai yanzu ma kusan anan suke dan bacci ne kawai yake mayar dasu can gidan shima wani lokacin anan suke kwana kuma baya magana dan Farida daman ta dawo nan gaba daya”
“Toh haka ake so, kin gani ko tashin hankalin daman bashi da amfani yanzu gashi a ruwan sanyi ai kusan sun dawo hannunki, Allah ya wuce mana gaba”
“Amin yah rabb Nagode yaya a gaida su Anty Nasiba” daga haka mukayi sallama ina ta juya maganganunsa a raina, matsaya daya dai na zauna akai itace ta neman zabin Allah tunda shine dahir
Bayan sallar Isha ina zaune ina lazumi sega Amnah da leda niqi niqi tun kafin ta ajiye qamshin abinda yake ciki ya doki hancina nan take kuma na gano na ina ne.
Kallonta nayi da alamun tambaya ta ajiye su kusada ni tana cewa
“Abbi ne ya kirani a waya yace na kawo miki”
“Zaki tattara ki wuce mun dasu daga nan ko yaya, me yasa daya kiraki baki zo kin gaya mun kafin ki fita ba” na fada ina rufeta da fada. Setayi rau rau kamar zatayi kuka tace
“Mami Abbi ne fa ba wani ba, kuma ai...”
“Amnah ni kike gayawa Abbi ne ba wani ba Abbin ubanki ne ko yaya? Ki shiga hankalinki Amnah kuma ki kwashe kayan nan ki fita dasu kafin na bata miki rai”.
Kayan ta diba seda ta kai bakin qofa kafin ta waiwayo ta kalleni tace
“To mu zamu ci Mami idan ke ba zaki ci ba”
“Amnah se naci ubanki idan na taso wallahi ki tattara ki mayar masa idan ba haka ba zamu gamu”
Da sauri ta fice ta barni ina mita ni kadai, qamshin naman kuma seya tado mun da tsohon kwadayi dan ina bala’in son Gashin gurin. Seda nayi