Showing 222001 words to 225000 words out of 260321 words

Chapter 75 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42673

Mami ina ruwana da su dazan gaishe ni ai ban san tare kuke ba tunda bada su muka zo ba"

"Zaka rufe mun baki ko sena kwade ka anan, idan ba tare muke ba daman haka kukeyi idan kunga na gaba da ku? Ko darajar shekarunsu beci ka gaishe su ba tunda ai ba kai ba ko ubanka sun girme shi" na fada cikin masifa.

Seya miqe tsaye ya kwashe kudin gabansa yana cewa
"Nidai kiyi haquri"
"Ajiye su dan ubanka, ka wulaqanta su saboda baka da kunya ka dauki kudin da suka baka" na fada ina fizege kudin, saboda wulaqanci se ya saka dariya ma yana cewa

"Toh Mami ai ba roqar su nayi ba, ki bani kinga se na kaiwa Abbi ya auro wadda zata ringa dafa masa abincin da kika ce".

Tsabar mamaki kawai bude baki nayi ina kallonsa, lallai Aliyu ko da yake ba laifinsa bane wannan yafi kama da Tunanin Bashir qila shi yake karanta masa duk abinda zeyi to kuwa duk zasu ci ubansu shida Bashir din.

Haka muka wuce gida dani dashi babu wanda ya sake cewa komai. Tare muka ci abincingaba aya aka gama aka tattare gurin, Seda akayi Isha ina daki Aliyu ya leqo yana cemun ze tafi seda safe

"Ba anan zaka kwana ba?" Na tambaye shi,
"Eh zanje can gidan da safe na dawo" ya fada yana sosa kai.

"Allah ya kaimu, kuja mana qofar idan kun fita" na fada ina ci gaba da lazumi na.

Washe gari da wuri na shirya fita aiki saboda babu makaranta duk yaran ma suna bacci abinsu. Naci gayuna, Shayi kawai nasha na dauki jakata ina cikin kulle qofa Bashir ya qaraso qofar gidan shima cikin shirin fita aiki.

"Barka da Safiya Ma'u" ya fada yana kallona.

"Ina kwana Baban Ali?" Na mayar masa da amsa ina ciro muqullin mota daga jakata.
"Ashe kun dawo, se ganin Aliyu nayi yace jiya da yamma kuka dawo"

"Uhm wallahi saboda aiki kasani, da se satin sama idan hutu ya qare zamu dawo" na bashi amsa cikin sauri sauri ina danna mabudin motata.

"Nace in ba damuwa inaso zamuyi magana ne dan Allah ko zuwa anjima idan na dawo se nazo gida" ya fada yana shafa kai kamar wani yaro,

"Toh magana kuma dani? Allah ya kaimu" na bashi amsa ina shigewa motata, shiya rufo mun murfin yana mun adawo lafiya wai sabon salo kiran sallah da usur, seda na kai qofar gidansa na hangi Amirah tsaye cikin shiri kamar a tsikara mata tsinke ta fashe tsabar kumburi da alama fita zasuyi ya tsayar da ita.

Da yamma kuwa gurin qarfe shida sega Bashir, na fito wanka kenan dan nima ban dade da dawowa ba sannan Farida ta shiga take gayamun ga Abbi.

"Ma'u wata magana naji da hankali na ya kasa nutsuwa da ita wai aure zakiyi" ya fada bayan da muka gaisa. Sena kalle shi yanda gaba daya yabi ya rikita kansa duk ya sukurkuce gayun nan da yakeyi da yanzu babu da alama ko hutawa ma beyi ba yana dawowa ya taho nan dan rigar saman kayan sa kadai ya cire.

"Toh ashe labari ya iso maka a ina kaji?" Na tambaye shi da dan murmushi a fuskata seya zaburo kamar ze sauko daga kujerar da yake yace

"Bangane ba kina so kice mun da gaske ne Ma'u aure zakiyi? Wane irin Aure? ki zauna da wani namiji bani ba ko hada soyayyata da ta wani a zuciyarki?"

Seda na gyara zama dakyau na dora qafa daya kan daya ina girgiza su kafin nace

"Aure kala nawa ne Bashir? Shi din dai wanda ka sani na mata da miji da zasu zauna a qarqashin inuwa daya.
Batun na zauna wani namiji kuma da Mace yar uwata kake so na aura ko yaya? Ita kuma soyayya ai yanzu tashi ce kadai a cikin zuciyata tuni anyi waje road da taka tsohon labari kenan".

Miqe wa tsaye yayi har yana tunkude kayan Lemon da aka kawo masa suka zube a qasa ya nunani da hannu yana cewa

"Qarya kike Asma'u bazaki taba son wani Namiji a duniya ba bayan ni idan ma zakiyi aure da gaske sedai kiyi kawai amma badan so ko jin dadi ba ina kuma tabbatar miki da cewa duk ma inda kike tunanin zakije sekij dawo dan zuciyarki bazata taba aminta da wani bayan ni ba wannan alqawari nayi miki"

Ko a jikina na miqe tsaye nima ina kallonsa cikin ido nace
"A lokacin dana nuna maka kaine rayuwata Bashir ka dauka shirme nake ban san kaina ba a sannan, a yanzu kuwa ka bude mun ido ka kuma bani damar da nayi karatun sanin matsayina da abinda ya cancanta dani.

Oh wai fata kake mun nayi aure na sake dawo maka? Toh ai tunda na iya zama da kai da halinka Bashir ni kuwa wane kalar miji ne zan gagara yin haquri dashi zance ma kawai kake yi wannan" ina gama fada nayi gaba zan bar gurin yayi saurin shan gabana tareda riqo hannuna, kallon dana jefa masa na kayi hauka ne yasa shi saurin sakina yaja baya yana cewa

"Kiyi haquri naji koma menene ki gaya mun duk abinda bakya so zan dena wallahi nidai kiyi haquri ki dawo dakinki muci gaba da zama kinji wallahi bazan iya rayuwa babu ke ba".

Ni kuwa kaga yanzu ma na daura danbar rayuwa ba tareda kai ba, kai ni ai yanzu bama zan iya maimaita zaman da nayi a baya dakai ba Bashir kaje kawai ka zauna da matar da Allah ya zaba maka ka barni nima na gwada wata rayuwar haba karka zama me son kanka mana"

"Ma'u dan Allah..."
"Dan girman Allah Bashir ka fita, da nasan wannan maganar ce zata kawo ka ma da tun da safen munyita wallahi base kazo ka tasani gaba da magiya ba ko da dole ne nace bana so bazan koma ba ka qyale ni mana idan kuma kana da qarfi seka dauke ni aka ka maida ni gidanna ka haba" na fada a hasale dan ya ishe ni kuma.

"Shikenan seki shirya ganin gawata dan duk ranar da kika auri wani bani ba nasan daga lokacin rayuwa ta zata zo qarshe".

"Allah ya jiqanka, karka damu su Aliyu bazasuyi maraici ba" na fada ina wuce shi. Ina ji a jikina yanda ya bini da kallo harna shige daki.

BASHIR

Jiki a sanyaye ya kama hanyar gidansa yana tunanin wai shi mezeyi Ma'u ta dawo masa?
Ya gwada duk yanda akace masa yayi nasa dabarun amma duk a banza kullum ma sake botsarewa takeyi a maimakon ta sakko. Yanzu mutum biyu suka rage masa da yake ganin zasu iya shawo kanta daga Babansu se Alhaji Qarami.

Kai shi yana kunyar Alhaji Qarami wallahi abinda ya masa a rayuwa ko darajar wannan yaci ace ya dagawa Ma'u qafa koda ita ta takaleshi yaci ya dauke kai. Baban dai ze kira tunda dai ai duk tsiya ubansa ne bakuma ze zabi Ma'u akansa ba kuma ai shima yana son zamansa da ita dan haka ze saka baki ta dawo masa.

Wayar Baban ya kira amma Dada ta daga take gaya masa yana bacci saboda jikinsa ya matsa kwana biyu. Shi se sannan ya tuna da zancen kudin maganin da ze tura musu gashi account dinsa yayi qasa sosai saboda hidimar sallah da yayi kuma wata ya raba balle ya saka rai da zuwan Albashi.

"Kai komai ma ya rikicewa mutum kudin kansu sun dena Albarka kamar wanda ake kwashe su" ya fada a fili bayan da yayi wa Sa'ad transfer abinda ya samu na siyan maganin, dan abinda ya masa saura baya zaton ze rufa masa watan gashi za'a koma makaranta biyan school fees kadai ya ishe shi yana ganin dole seya karfi wani abu a kudin super market saboda biyan kudin makarantar dan da wuya ya taba kudin idan an hada lissafi ribar sake mayar da ita ake se idan ta qure masa ne yake taba wani abun a ciki.

Yana shiga gida ya tarar da Amirah na murqususun ciwon ciki kuma, kai Jama'a haka suka kwasa se Asibiti likita ya ringa fada akan wai wani abun tasha irin magungunan Hausa, daya matsata qarshe take gaya masa wai magani Addah tasa aka aiko mata daga Gombe a qaryar su na zaqi ne tunda cikinta ya shiga kusan wata Bakwai yanzun shine ta karbo mata zancen gaskiya kuwa sabon malami ta samu ta hannun Anty Talatu ita tayo musu aiken saboda sun gaya mata sun rasa kan Bashir din zaman dai se a hankali.

Ya kuwa ringa bala'i kuwa yana cewa Idan wani abu ya samu cikin ita ta sani babu ruwansa tunda ita bata tausayin kanta haka suka dawo bayan da aka bata magunguna su kansu seda ya kashe kusan dubu Hamsin a daren.

Kwana biyu a tsakani aka kirasu a waya cewar Ummi ta haihu ta samu ya Mace amma ta koma murna Addah ta ringayi tana hamdala da  akace yar ta mutu sedai murna ta koma ciki jin wai an daurawa Ummin aure da dai shi mijin da bata so ta aura din dan daman seda sukayi yarjejeniya da iyayensa akan tana haihuwa za'a daura aure suka yarda dan haka ana kiran Alhaji Murtala daga can Katsina inda ya kaita gurin wani Amininsa cewar ta haihu ya tashi ya tafi gidan su saurayin ya gaya musu. Ana sallar Azahar kuwa a masallaci aka daura musu aure se saka ranar da zata dawo ta tare.

Kusan Sati guda gaba daya Bashir ya zama gashi nan ne, abubuwa sun rikice masa duk yanda ya dauki shawo kan Ma'u da sauqi abinya shallake haka nacin yake roqon yake amma kamar wanda yake shika dusa dukda shima dai da tasa irin wautar.

Wani irin biko yakeyi me kamada fin qarfi saboda a duk sanda ya tashi yi mata magana nuna mata yake kamar ya zamar mata dole bazata oya rayuwa babu shi ba dan haka ta haqura ta dawo masa wanda sam shi be dauki hakan da wani laifi ba gani yake kamar yana tuna mata da girman soyayyar da take tsakanin su ne wanda ita kuma wannan abun shi yake wara qona mata rai take jin dole ta barshi ko dan ta nuna masa cewar ba tare aka dauro rayukansu aka aiko duniya ba.

Ana saura sati daya a koma makaranta kamar yanda aka saba suka tura mata da Takardar biyan kudi saboda daman lambar wayarta ce akai in an turo mata seta turawa Bashir din ya bada kudin.

A yanda aka saba an samu qarin kudin makaranta ga kudin littattafai saboda sabuwar shekara aka shiga za'ayi canjin aji ga kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB na Aliyu da ze shiga aji shida dan haka da aka hada lissafin sega kudi sun tasarma kusan Miliyan biyu.

Ita kanta seda ta jimanta wannan al'amari ta rasa abinda yasa makarantar suke haka basa bada notice na qarin kudi sedai kawai idan an kawo maka teller ka gani kamar wadanda suka bawa iyayen yaran ajiya koda yake makaranta ce ta yayan masu dashi suma karanbani ya saka suka kai yayansu ai.

Ta Whatsapp ta tura masa da takaddun lokacin yana zaune a Office be dade da gama waya da Amirah ba da take masa zancen kudin siyayyar haihuwa gashi jikin Alhajin su ya qara zafi dan shirin kaishi Kano akeyi ma Asibitin Malam nan ma dai duk wani lissafin kudin ne dai yanzu ga wannan ubannin kudi na makaranta kuma sun taso masa duk a ina ze qwaqulosu?

Wai to ta yaya da duk yake hidimomin sa har ya samu rara a asusun sa ba taredaya girgiza ba? Albashinsa Miliyan daya ne duk wata saboda babu Fansho babu garatuti idan ka gama banda sauran alawan da suke samu kala kala musamman yanzu daya samu qarin matsayi packages harda na banza basu ake dan haka yake facakarsa baya ma lissafi bare ya ajiye na buqatar kota kwana tunda kudinna shigo masa koda yaushe daman Super markets dinsa Gombe sune tanadin Bayan Ritaya wanda se a yanzu yake hango tarin gatan da Ma'u tayi masa data saka shi a harkar kasuwanci nan dan yanzu ba qaramin habaka jarinyayi ba tunda ba'a tabasu duk ribar da  aka samu ciki a ke maidata.


Text ya tura mata akan ayi masa haquri kafin a koma ze bayar nan ya shiga hado ta inda zasu fito, dole dai ya karbi kudi a gurin Sa'ad din idanyaso daga baya ya mayar dan su makaranta babu ruwansu ba jira zasuyi ya samu ba shawarar daya yanke kenan a take kuwa ya kirashi akan yana san ya karbi miliyan uku se Sa'ad din yake gaya masa sunyi sarin kaya, kudin da suke dasu a qasa ko Miliyan daya bazasu kai ba na banki kuma ze dauki lokaci dan yamamta account din ya samu matsala ta yanda sedai kudi su shiga amma bazasu fita ba dan haka dole sedai idan zeje Gomben da kansa ya gyara tunda shine signatory din.

A daren ranar yana zaune a qofar kujera ya dasa kujera yana aikin tunani, daga inda yake yana iya jiyo hayaniyar yara daga gidan Ma'u saboda yanda Estate din yayi shiru.
Hira suke cikin raha anata qyaqyata dariya kamar yanda sukeyi a ko wanne dare lokacin da tana gidansa wani lokacin idan yaga dama ya zauna ayi dashi wani lokacin kuma yana daga gefe yana sauraronsu yana murmushi dan ita irin mutanen nan ce masu biyewa shirmeb yara ta haka take sanin duk abinda suke ciki basa boye mata tunda ta mayar dasu kamar qawayenta.

Ya ilahi me yasa duk beyi tunanin komai ba ya rusa Wannan kyakykyawar rayuwar ta gidansa? Yanzu da ace bata kusada yaran a ina zasu ringa samun wannan walwalar da farincinin saboda yanzu sam babu wata damuwa a tattare dasu, kamar daman a haka suka tashi tsakanin gidaje biyun musamman da baya takura musu da zancen kwana duk inda suka so yanzu zamansu suke shiyasa Aliyu ne kadai yake rayuwar qunci da damuwa a cikinsu kodan shine babba yafi su tunani da gane abinda yake faruwa.

"Abbi tunanin me kakeyi tun dazu ina tayi maka magana baka ji ba" maganar da Aliyu yayai tareda girgizashi ta dawo dashi hayyacinsa. Se ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa yace

"Tunanin da yawa Aliyu, gaba daya kaina ya qulle ga Maminku sam ta kasa fahimta ta tayi haquri akan abinda ya faru ban san yaya zanyi ba Aliyu".

"Abbi duk abinda ya faru ai laifinka ne, haka kawai kaje ka qara aure kuma Abbi ka rasa wa zaka aura se Anty Amirah bayan kasan Mami cefa ta riqeta, kazo ka ringa yi mata abubuwa duk akanta kawai saboda kaga tana da haquri sannan fa Abbi saboda ita ka sake ta sannan yanzu saboda kaga baka jin dadi bata nan kazo kana cewa ta dawo ai kasan bazata yarda ba" Aliyun ya fada bayan daya zauna.

"Na sani kuma duk na karbi laifina, auran Amirah da rabuwata da Maminku duk qaddarace Aliyu gaba daya ba a san raina komai ya faru ba amma babu yanda muka iya da abinda Allah ya qaddar. Ni dai yanzu ku taimaka nasan ai ku zata saurare ku ku bata haquri ta dawo gidan nan nayi Nadama bazan sake maimaita duk abinda ya faru a baya ba.

Idan ma so take Amirah ta koma Gombe zata tafi nidai tayi haquri a mayar da auran mu kawai zanyi mata duk abinda take so kaji kuje dukkan ku ku sameta dan Allah Aliyu nasan ai kai bazaka so kaga rayuwata ta shiga garari ba saboda rashin Ma'u" Bashir ya fada yana kama hannun Aliyu daya tsura masa ido.

"Zanje na sameta dukda tace karmu sakeyi mata maganar ka amma ina so kayi mun alqawari.."

"Koma menene na yarda in har zaka shawo mun kan Ma'u duk abinda kake so zan baka" Bashir yayi saurin tare shi. Seda ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Kayi alqawarin idan Mami ta yarda zata dawo zaka saki Anty Amirah saboda nasan indai kana tare da ita Mamai bazata taba samun farin ciki a gidan mu indai kana so ta dawo to ka sake ta kawai gidan mu ya koma yanda yake kafin ta shigo rayuwar mu".

Kasaqe Bashir yayi yana kallon Aliyu da jin abinda yake fada, ya saki Amirah fa me yasa se wannan sharadin ze saka na shawo masa kan Ma'u?
Shida yake qoqarin gyara kuskure shine yake so ya sake aikata wani ita kuma idan ya sakeya yanzu kuma wata jarabawar ta sake afko masa fa gaskiya Aliyu yayi haquri banda wannan ya yarda dai ze raba musu gida yanda suke da har na can Gomben ma idan Amiran ta koma ze raba musu kowa gidanta daban.

Hannun Aliyun ya kama yana sake marairaicew kamar wani kalar tausayi yace
"Haba Aliyu so kake na sake yin wani sakin kenan bayan nayiwa kaina alqawarin ko dukana mace zatayi bazan sake sakinta ba. Baka san yanda nake ji akan rabuwata da Maminku ba, Baba fushi yake dani ko magana baya mun yanzu haka su Amiru duk sun dena kulani saboda abinda ya faru so kake na sake maimaitawa itama Dada da sauran yan uwana su tsane ni?"

"Ai daman Baba dasu Uncle Amir ne kawai suke son Mami ni ina ruwana idan sunji haushi kawai in dai kana so Mami ta dawo to kayi alqawari zaka saketa koma zaka dawo da itama daga baya ni babu ruwana amma yanda aka saki Mamanmu saboda ita itama taji irin yanda mukaji" Aliyun ya fada kansa tsaye babu wata damuwa a tatttare dashi.

Bashir kuwa ido ya saka masa yana mamakin a ina ya samo wannan tunanin ko kuwa Ma'u ce ta fada masa hakan ita take so a saki Amirah sannan ta dawo. Kansa ne ya dauki dumi, yanzu idan da gaske ya amince zata dawo din ko kuwa kar ta sake rufta shi se daga baya yayi biyu babu ko daya.

Numfashi ya sauke yana kallon Aliyu da yayi kicin kicin yace

"Na yarda amma se randa aka mayar da aurena da Mamin ku sannan zan cika maka alqawarin"

"Ka dai san hukuncin cika alqawari" Aliyu ya fada yana kallonsa.

Kai shi abun ma ya zarce mamaki wai yau shi Aliyu ya titsiye haka yake bashi umarni, ya ya iya? Haka ya rausayar da kai yace

"Na sani kaima se kayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login