Showing 27001 words to 30000 words out of 260321 words

Chapter 10 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42654

ko da abinda ze qara bamu ma” kai Amirah ta daga mata kawai nan ta maida akalar kiran kan Hajia Balaraba sedai itama kamar Wizy waya a kashe harta gaji ta bari akan Gobe idan Ummi ta dawo zata karbi Number Ruqayya a gurinta (Ummi tana gidan yayarsu da suke uba daya ta haihu).

Gidan Hajia Balaraba

Waccen ranar yanda suka watse suka barta ta dade a zaune a gurin tama rasa tunanin me zatayi, wai itace bata da Sa’a ne ko kuwa aikin Malam ne beyi ba? Tana zaune tana tunanin me zatayi, wannan hukuncin da Alhaji ya dauka yayi mata tsauri da yawa ta yaya ma za’ayi ta zauna bazata fita neman taimako ba? Dole da sake idan dama taqi se a kona hagu ai saqesaqen yanda zata wanke kanta ta farayi a zuciyarta har zuwa sanda taji Alhaji ya sake fitowa daga dakinsa. Cikin qarfafawa kai guiwa ta miqe tana cewa

“Alhaji kayi haquri wallahi sam ba abinda kuke tunani bane, kafin gida ne na karbo mana ba kuma iya dakinta na saka ba wallahi kaga kwana biyu unguwar nan anan fama da sace sace shi....” kallon da yake binta dashi ya sakata hadiye sauran maganar ta. A tare suka juya Gurin Dining da Ruqayya ke qoqarin zuba tuwo abinta dan tana wanka bata ma san wainar da aka toya a gidan ba.

“Mayar da miyar nan Ruqayya ki miqomin harda na shayun” ya fada murya a dake dan dukda be gani ba ya tabbatar ta saka wani abun aci ba kuma ze bar kowa yaci ba dan ba yau ta saba ba ita idan ta tashi abun tana ma ba kansa kadai yake tsaya wa ha kowa da kowa take hadawa na gidan.

Karbar flask din yayi ya shige kitchen dasu Hajia Balaraba naji tana gani ya kwarara miyar a sink din ya bi da ruwan Tea kafin ya dauraye ya kora ruwa. Idon sa ne ya sauka kan wani flask daban a ajiye ya janyo ya bude, murmushin takaici yayi zargin sa ya tabbata duk sanda tayi irin haka seta ware nata daban be bata lokaci ba ya dauka tareda sabon plate da spoon se koma Dining.

Tuwon sa ya diba ya zuba miyar ya miqawa Ruwayya ragowar yai shigewar sa daki ya bar Balaraba a tsaye da baqin ciki goma da ashirin, abincin ne sauran taqamarta taso ta lallashe shi yaci gashi yanzu ya zubar da miyar wadda ta ajiyewa kanta kuma ya kwashe duk wuyar da taci tayi girkin nan me kyau amma bata da rabo sena baqin ciki bata san sanda hawaye ya fara zubo mata ba kamar yarinya.

Dakin ta ta shige tayi kukan ta me isarta ta share, ta kuma quduri niyyar ko bataje da kanta ba se tayi aike daga yanzu ma bazata qara karbar aikin da zatayi dakanta ba gara ta samu wanda ze yi mata komai da kansa bate ma har ta kuskure asake kamata.

Washe gari tana zaune Alhaji ya shigo dakinta, wayar ta na hannunta tana shirin kiran Addah ta gaya mata yanda akayi su kuma yi shawara ya shigan. Hannu ya miqa mata ta bashi wayar cikin mamaki ta miqa masa tana tunanin to me kuma ya fatu yanzu? A gaban ta ya cire layin ya balla, kafin ya kalleta yace
“Wallahi ko da wayar wani kika karba kikayi amfani da ita ki kira wani Boka Ban yafe ba” ya sa kai ya fice ya barta da baki a bude.

Matakan tsaro na gaske ya saka mata ba waya ba fita ita ma kuma ya hana kowa zuwa gurinta har kuwa da Yayanta da suke gidan aure. Ruqayya kanta cewa yayi ta tattara ta koma Hostel haka me aikinta yace karta dawo ta zauna ta qara hutawa na wani lokaci duniya fa tayiwa Hajia Balaraba zafi Raba zafi inuwa quna gashi babu abokin shawara ita da Alhaji kuwa sedai tajiyo qarar bide qofarsa ko rufewa.

Seda Addah ta jera kwana biyu tana kiran Hajia Balaraba da Wizy dukka bata samu ba, ranar Talata ta yanke shawarar zuwa gidan nata ta gano ko lafiya.

Dakyar da sidin goshi Me gadi ya barta ta shiga shima seda tayi masa qaryar Ita Yar uwar Hajia Balaraba ce suna ta kiran wayarta ba’a samu shine tazo taji ko lafiya, be barta ba seda ya kira Alhaji ya shaida masa sannan yace ya qyaleta ta shiga.

Halin da taga Aminiyar tata ya girgiza ta nan ta shiga tambayar ta meya faru, Hajia Balaraban na kuka ta shaidawa Addah komai harda sharadin da Alhaji ya gindaya mata.

Addah tayi buqwi tana sauraronta kafin tace “Ikon Allah kinga dama akace magani dace ne to ni kuma kinga dai mun dace wallahi dan yanzu lafiya lau abubuwa suke tafiyar mana. Kema din nasan akasi aka samu wannan shegiyar ta ganki amma da abubuwan sun kammalu na tabbatar yanzu wani zancen ake ba wannan ba Allah dai yajiqan Malam na kan tufu shine Maganin Fitinannen Alhajin nan naki mtsw” taja tsaki kafin ta dora da cewa

“Yanzu dai ai cewa yayi idan kika qara zuwa ko a sharadij nasa shikenan kiyi zamanki ni zan koma insha Allahu za’a gyaro komai base kinje ko kunyi waya ba”

Cikin jin dama dama Hajia Balaraba tace “Yawwa Aminiyata shiyasa nake qaunar ki wallahi yanzu to zaki gane gurin? Dan Allah idan kinje ki gaya masa so nake ayi mun maganin Alhaji yafi da kamuwa yanda ko kara na ajiye ba ze tsallake ba ke ko magana in banace ya bude baki ba karya yi”.
Da haka sukayi Sallama Addah ta kama hanyar zuwa Gurin Malam Wizy.

Tiryan tiryan ta nunawa Me Adaidaita hanya har qofar gidan Malam dan Addah akwai gane hanya, da dan mamaki ta kalli shagon na Malam Wizy da ta gani cike da kayan provision ana siyar wa. Gaba tacewa Me Adaidaita ya qara ko basu zo gidan ba sedai har suka kai qarshen layin suka jiyo babu wani gida me kama dashi ma.

Fitowa tayi ta tsaya dason tabbatar da nan din ne gama dakalin da suka ga yaran nan a zaune ranar, qarasawa tayi gurin me shagon suka gaisa kafin tace

“Dan Allah tambaya nakeyi me shagon nan”
“To hajia ai gani”
“Aa ba kai ba Malam nake nufi” ta bashi amsa.
“Malam kuma Malam wa?”
Wata sabuwa inji yan caca ita ai se yanzu ta tuna da ko sunan sa bata sani ba, cikin ta ne ya bada qululu ta daure tareda korar abinda zuciyar ta take hasaso mata tace

“Malam dai wanda yake zama a shagon nan Mijin Maimuna me wannan gidan” ta fada bayan ta tuno da sunan matar malam din.

“Toh gaskiya hajia ban san wanda kike nema ba, hasalima nan shagona ne nafi shekaru goma ina saida kaya a ciki gida kuma da kike magana ba gida bane kangone da Almajiran waccen makarantar suke kwana zaki iya leqawa ki gani” me shago ya fada yana nuno mata makarantar daga nesa.

Addah bata qi ta tashi ba ta leqa gidan, kamar yanda ya fada kuwa incomplete ne ta cikin ga kayan Almajirai nan tsubi tsubi, wata hajijiyace ta kwasheta jin zancen da wani saurayi da yazo siyya shagon yakeyi

“Tab Malam Musa Allah dai yasa ba itama tafada komar Wizy bane dan a satin nan mata sunfi Goma da suka zo neman Malam” yana kaiwa nan ya karbi kayansa yayi gaba yana wa Addah dariya.

Allah sarki Addan mu Allah maida Asara 😂😂😂https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 12

Lagos

Asma’u bata tsammaci dawowar Bashir a yau litinin ba ganin tun ranar Asabar din be ko sake bi ta kansu ba dan haka koda ta tashi aiki ta biya ta dakko yaranta suka wuto gida.

Bayan Sallar Isha suna baje a palour, Dan wake sukayi abinsu sunaci suna kallo sukaji tsayuwar mota. Basu kawo shi bane dan baya haura 6pm a waje tsananin hold up ne ze riqeshi zuwa Magriba yanzu kuwa har 8 ta gota shiyasa ma suka fidda ran dawowar sa a yau dukda dai tasan akwai aiki to qila excuse ya dauka.

Bude kofar da akayi ya saka su juyawa gaba daya , Bashir din ne hannunsa dauke da rigar coat din sa se waya a kunnensa. Da gudu yaran suka nufe shi suna murna, taso ta basar amma wata zuciyar tace “ki tura masa aniyar sa” se itama ta miqe tana gyara zaman hular kanta ta nufeshi.

Side Hug ya mata tareda pecking goshinta bayan yaran dukka sun ruga mota debo kayan daya bari dan sun saba in dai ze dawo se yayiwo musu tsara ba ita kuma ta karbi rigar hannunsa tayi gaba ya rakata da ido bayan ya zauna a daya daga cikin kujerun palour ya ci gaba da amsa wayarsa.

Ruwan wanka ta hada masa kafin ta fito masa da duk abinda ta san ze buqata. Sanda ta fito ya gama wayar yana tsakiyar yaran da suke zuba masa surutu se murmushi yakeyi Muhammad na kan cinyar sa yana cin Pizza.

“Oh bama za’a jira ni ba kenan ko” ta fada tana daga Muhammmad din kafin ta ci gaba da cewa
“Oya kowa ya kwashe nasa duk kunyi scattering palour,ga plates din nan ma ba’a kwashe ba”.

ledojin suka shiga tattarewa kowa ya dauke tasa suka shige kitchen su ajiye seta juya ta kalleshi shima ita yake kallo. Murmushi me kyau tayi masa tace “Yallabai ai mun zata se gobe, ga ruwan wanka can na hada maka”

“Jazakhillah” ya fada yana miqewa dan a gajiye yake sosai, tunda ya diro be huta ba aiki sosai yau yasha a office din ba. Sanda ya fito daga wanka tana zaune akan kujerar dake dakin sa. Ita ta taimaka masa ya shirya kafin ya tada Sallar isha ita kuma ta fita hado masa Tea da yace ta kawo masa.

A babban Mug ta hada ta saka masa madara da Ovaltine sosai banda sugar se Cake din da tayi musu na makaranta ta zuba masa a bowl ta hado akan dan Try ta fito. Sun gama ciye ciyen an tafi yin Brush se Jafar kadai dake tsaye yana jiranta.

“Ya akayi” ta tambayeshi
“Gurin Abbi zani na tambaye shi abu”
“Muje toh” ta fada tayi gaba yana binta a baya.

Suna shiga dakin ta ajiye masa ta shiga toilet yin fitsari shi kuma Jafar ya zauna, ba abinda yake son ya tambaye shi ta sani qulafucin uba ne da Jafar dan gani takeyi yafi son Bashir akanta. Indai yana gida tofa yana nane dashi in ko tafiya yayi ya ringa kiransa a wayarta kenan shi kuma haka yake.

A dakin ta barshi ta tafi nata tayi wanka, seda ta shirya sosai tabi dakunan yaran ta tabbatar sun kwanta har Jafar din ya dawo sannan ta kashe Fitilun palour ta tafi dakinsa.

Yana zaune da waya a hannunsa yana juyawa Asma’u ta shigo, tunani yake ya kira Amirah ko yaya tunda ita Allah besa tayi hankalin jin ya ya sauka ba yauma. Yanayin walwalar da ya gani a fuskar Asma’u yasa ya fasa sema ya kashe wayar gaba daya ya ajiye kafin ya miqe ya fita.

Seda ya leqa ko ina ya tabbatar da komai lafiya ya tofe ko wacce kusurwa da falaqi da nasi kafin ya koma Dakin har Ma’u ta kwanta taja bargo zuwa rabin jikinta. Kwanciya yayi shima yana jawota jikinsa, hannunsa ya tura cikin gashin kanta ya zame band din data daure shi dashi, Bashir nason Gashi sosai yana daga cikin abubuwan da suka sake jan sa akan Amirah yanda take kwalliya da gashi.

“Madam ya akayi ne da alama ko missing dina bakiyi ba tunda na tafi bako waya”.
Gajeran murmushi tayi tace

“Qalau fa kawai dai mun barka ne ka huta sosai ka kula da Amarya, ya ka baro su suna lafiya ko?”

“Lafiyar su qalau suna gaishe kuma”
“Muna amsawa” daganan taja bakinta tayi shiru, shima shirun yayi tana jin sa yana jagwalgwala gashinta kafin bacci ya dauketa. Da Asuba ta rigashi farkawa, harta dauro Alwala be tashi ba dan haka ta shafa fuskarsa da sauran lemar ruwan hannunta jin ana qoqarin tada sallah. Kafin kuwa yayi Alwala an shiga, dole se a palour suka hadu da yaran dukka ya jasu sallar.

Bayan sun idar ma bacci ya sake komawa tayi mamaki dan da wuya Bashir ya koma bacci da Asuba kai ko ba zashi aiki ba ze zauna yayi ta lazumi har se rana ta daga yayi walaha sannan yake komawa bacci. Tana wanka tana gulmarsa a ranta wato yaje ya gama kashe Arnansa ze zo yana baccin gajiya a nan ko.

Tsaf suka shirya, tana jira taji shi ze tafi dasu ko kuwa ita zata ci gaba da jigilar har suka fita yaran suka shige motarsa taga ya kunna beyi magana ba , Hamdala tayi a zuciyarta kafin ta kunna tata motar suka hau hanya seda suka je junction din da suka saba rabuwa tayi musu horn ta shige kwanar office dinsu.

Bayan tayi parking tana qoqarin Daukar jakarta da system Ilhama Abokiyar aikin ta ta qaraso gurin motar,
“Aa Maman Farida yau da wuri haka” Ilhama ta fada bayan sunyi musabaha.

“Wallahi fa Maman Khairi Allah ya ceto ni daga yawo kai yara makaranta” tare suka jera suna yar hira har suka isa 3rd floor inda anan office din Asma’u yake ita kuma Ilhama tana 4th floor ne.

Tana isa office dinta ta tarar da takaddun da zatayi aiki a kansu kamar koda yaushe. Seda ta kintsa komai sannan ta fara duba su daya bayan daya kafin wani lokaci ta gama har ta shiga replaying mails da suke jiranta.

Asma’u nada hazaqa sosai ta kuma qoqarin aiki gata Allah ya bata fasahar harshe, duk baqin abu Idan Asma’u ta tsara ka tace Fari ne bazaka san sanda zaka yarda ba dalilin da ya saka ta karantar Business Administration kenan dukda a farko taso ta karanci Law ne yanzu haka tana aiki ne da wanni babban company hadahaar ma’adanun qasa (Mineral resources) tana matsayin Sales Manager (manajan siye da siyarwa).

Yanda take qoqari gurin janyo musu customers yasa take samun cigaba da Alkahiri sosai a kan aikin nata ga damammaki da suke shigo mata saboda yanayin aikin yana bata damar hulda da manyan mutane sosai masu siya ko wadan da suke kawo hajar su company ta siya.

Tana tsaka da aiki Kiran Fainusa ya shigo mata
“Tauraruwa me wutsiya” ta fada a fili dan ita dai duk kiran wayar Fainusa ba Alkahiri bane a gurinta, seda ya katse ta sake kira sannan ta dan dakata ta daga.

Cikin sabuwar girmamawar da Fainusan takeyi mata tunda ta fara zaman gida suka gaisa Fainusan ta ke tambayarta yara tace suna makaranta itama ta tambaye ta ya Dada tace tana lafiya.

Shiru ne ya biyo baya tana jiran taji dame tazo yau kuma can kuwa ta nisa kafin tace

“Anty jiya har dare mutuniyarki suna nan gidan da yaya”

“Uhm” kawai ta amsa mata, ita tarasa wannan abu kamar wadda take biya ta kawo mata rahoto kuma duk sanda ta tashi kawowar ba masu dadi bane.

Fainusa kuwa bata damu ba taci gaba da cewa “wai fa in gaya miki ta samu Dada wai tayiwa Yaya Magana ya tafi da ita Lagos, to wai ke take so ki dawo nan ko kuma hadaku dukka ze yi anan?”

Shiru Asma’u tayi tana so tayi tana sauraronta, jin tayi shiru alamar ta gama kenan yasa tace mata
“Toh Nagode ina office ne ki gaida su Dada” taa kashe wayar.

Duk yanda taso ta ci gaba da aikin seta kasa, ita sam ta manta da maganar da yai mata ta komawa Gombe se yanzu wato Amiran ce take Son dawowa nan kenan shine ita za’a tarkatata ta koma gida tunda tasan bazasu barshi ya debo su su dukka biyun ba dole ya bar daya acan Gombe. Lallai ma tayi yaya da aikinta toh? Bama wannan ba makarantar yaranta fa ko kuma yanzu Amiran ta shirya zama tayi mata rainon Yayan kamar yanda suka ce a lokacin da ya nemi su ringa karba karba

A sannan Amiran ai cewa tayi kowa ta zauna a matsayin ta, dan baza tayi mata bautar Yaya ba, daga baya ma tace ita gara ta zauna cikin yan uwanta kuma ya yarda da hakan shine yanzu data juyo mata zata ce tana so ta dawo nan still kuma ya sake yarda wato ita ga sauna tana zaune se dai su juyata yanda suka so ko? To maji ma gani.

Aikin ta taci gaba dayi a ranta tana shirya irin dibar Albarkar da zata masa duk ranar da ya sake tado da zancen ma wallahi se ta masa tatas, qaton sa dashi yazo yai tayi mata muzuran qarya se yaje yarinya qarama ta ringa controlling dinsa kawai.

Data tashi kaitsaye ta biya ta dakko yara, sun dan bata lokaci a hanya dan ta tsaaya yin cefanen abubuwan da suka qare musu sam ta manta cikin weekend bata damu tayi ba dan haka kusan tare suka isa gidan dashi.

Jakarta kadai ta ajiye ta shiga kitchen sauqinta daya tana da miya a Frizzer dan haka ta cirota ta dumama bayan ta dora white rice ta zuba kwan da zata hada salad dashi su dafu tare. Bata bar kitchen din ba seda ta kammala komai ta jere a Dining yana zaune a palour da yara suna kallo bayan sun dawo daga masallaci.

Sannu suka yi mata yaran banda Oga daya bita da ido kawai Amna da Aliyu suka shiga kitchen din dan su jera kayan da suka siyo aikin su ne wannan. Seda tayi wanka da ruwa me zafin gaske tayi sallah sannan taji dan dama dama. Kai gaskiya mata na qoqari, kayi hidimar gida da yara kayi ta miji sannan in kana aiki ko Kasuwanci duk ka hada wallahi bataga laifin Cina zaune ba indai za’a basu komai na buqata dan aiki wahala ne amma dai ko yaya dai gara ka nemi na kanka kodan bacin rana.

Kishingida tayi a gurin da tayi sallah kafin kace me baccin gajiya ya kwasheta se farkawa tayi taga Bashir a tsaye a kanta da alama tashinta yayi. Agogo ta kalla goma harta wuce, cikin dan baccin da be gama sakin ta ba tace

“waifa na idar da sallah ina zaune ashe bacci nayi, wallahi yau din nan na gaji da yawa kullum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login