Showing 150001 words to 153000 words out of 260321 words

Chapter 51 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42689

abin kari baga kayan shayi nan ba harda buredi kawai ruwa za’a saka a kettle fa kawai shine sena tashi nayi muku” ta qarasa tana juyar da fuska gefe, Bashir kuwa kallonta kawai ya ringa yi, badan ba seya kwada mata mari wallahi amma dukan Mace ba dabi’arsa bace, dan haka ya juya kawai yana cewa

“Wallahi Kinji na rantse idan na dawo na tarar da wani abu ba yanda ya kamata ba a gidan nan se kin gane kurenki tunda naga alamar ke ba’a gaya miki magana kiji da kunnenki to masan maganin ki” bamm ya buga mata qofa ya fice.

Amirah kuwa ko a jikinta ta miqe tana cewa “oho dai, girki ne bazanyi ba haka kawai ni ban haifa ba a ringa sakani tashin Asuba. Dama kai kadai ne na daure nayi amma wallahi bazan girkawa wasu qattin yara har shida abinci da Asuba ba suci su zageni ko to sedai suje uwarsu ta basu badai ni ko in ka gaji ka ringa dafa musu” tayi shigewarta bandaki, ba ita ta gama rashin hankalinta tayi sallar Asuba ba se kusan takwas na safe.

Bashir kuwa yana fitowa yaga basa palour, yasan bazasu wuce gidan Ma’u ba a ransa yaji wani sanyi ko banza zaman ta a kusa dasu Alkahiri ne.

Yaransa basu taba tafiya makaranta basu karya ba ko shi kansa se dai idan baqin halinsa ya motsa yaqi ci amma babu ranar banza da bazata dafa masa abinci ba amma yanzu daga zuwan wannan yarinyar ta fara yi musu horon yunwa dole ya taka mata burki.

Yana sane ya ringa fafara musu horn ga haushin yasan yanzu suna can suna cin dadi shi kuwa sedai yaje yaci a Cafeteria kawai yayi manaji gashi har an fara saka masa ido kwanakin nan da yake ci acan har suna tambayarsa ko dai Madam tayi tafiya ne yace musu Eh yanzu hakan dai zeje yau ma amma daga gobe dole ta shiga hankalinta, idan batayi wasa ba harna rana seta girka ta aika masa dashi kuwa.

Ganin da yayi wa Ma’u y sake hasalashi, tayi qara fari tayi kyau abinta a yanda ta fitan nan babu me mata kallo matar aure ma bare har a hasaso mata yaya shida dole itama yaja mata kunne gaskiya tunda dai haryanzu ai da auransa akanta. Haka ya wuni ranar a gurin aiki cikin quncin dashi kamsa be san na menene ba, sanda ya tashi ya tsaya ya siyi fruits da kaza kafin ya wuce gida.

ASMA’U
Hankali kwance na ringa tuqina harna isa ma’aikatar mu, muka gaisa da abokanan aikina cikin mutun taka suna yimun sannun rashin lafiyar danayi qaryarta har na zauna ranar aka bani tukuicin saki nidai se yaqe nake ina amsa musu dan a yanzu bana son wani abu da ze ringa tunamun da wancan Al’amari.

Se da muka fita break din rana Olivia wata abokiyar aikina ta same ni ina cin abincin da se a sannan na samu na siya.

Cikin harshen turanci take cewa
“Asma’u Juliet tana gaya mun wata magana ranar amma ban yarda ba wai dagaske ne kun rabu da me gidanki baku tare yanzu?”

Sak nayi ina kalllon Olivia, daman Olivia irin mutanen nan ce maso shegen gulmar bala’i duk wani abu na ma’aikatar nan kaji shi a bakinta ka rasa ta inda ma take samun labarai akan mutane kuma idan taji daman ka qaddara kamar anyi yekuwa ne dan kowaanne ma’aikaci se labarin nan ya isar masa.

Dagaske yanzu dai mutane sun dena kiwon akuya sun koma mutum tabbas, Juliet din da take magana qawarta ce ni kuma a estate dinmu take budurwar wani abokin aikin su Bashir ce a gidan sa take da zama bama fa layin mu daya ba suna can qasan mune amma ace har labari ya kai musu ashe dai ba a arewa kadai mata suka iya gulma da sa ido ba harda suma a nan kudu.

Bude baki nayi da niyyar bata amsa Maman Islaha qawata ta gurin aiki ta qaraso wurin, cikin fada fada tace da Olivia din

“Wannan wane irin rainin wayo ne zaki ajiyeta kina mata wannan tambayar ina ruwanki da auranta da kike tambaya akai ita wadda ta baki labarin meya hana ki tsayawa kiji inganjinsa a gurinta? Dallah malama bar gurin nan tunda baki da aiki se soka baki a rayuwar mutane da shegiyar gulma kawai” sosai ta balbaleta da fada dan Maman Islaha irin yarabawan nan ne da basa daga qafa.

Olivia kuwa simi simi ta bar gurin tana waiwayena, mayar da kai nayi ina juya abincin dan gaba daya ya fita a raina Maman Islaha ta dafa ni tana cewa

“Ki manta da ita kici abincinki ni wallahi mamaki kika bani ma da baki dauke ta da mari ba ace kina zaune tazo tana miki irin wannan maganar se kace ubanta ne ya kashe miki auran, idan kuma mijinki take so tun wuri se ki san me ake ciki...” seta dakata ganin ina hawayen da ni kaina bansan sanda suka fara zuba ba.

“Maman Faridah lafiya meya faru?” Ta fada a rude tana ruqoni, sena saki kukan gaba daya ina cewa

“Yanzu dan aurena ya mutu shikenan har na zama abin gulma ana yayatani a duniya kenan?”

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un auranki ya mutu Maman Faridah dagaske? yaushe? Kardai yarinyar nan son mijinki takeyi din da gaske kiyi mun magana” ta jero mun tambayar daga ganinta kasan hankalin ta ya tashi da jin maganata.

Seda na tsagaita kukan dan har hankalin masu cin abinci ya fara dawowa kanmu kafin nayi mata bayanin komai cikin sanyi tun kafin na kai qarshe ta qundumo wata ashar me maiqo da yarbaci ta aunawa Bashir ta qara lailayo wata ta watsa mun kafin cikin fushi tace mun

“Amma kin bani mamaki Maman Faridah yo se me shi ya tafka asara fa ba ke ba dan wallahi harya mutu baze taba maida kamar ki ba shine har zaki tsaya kina kuka wani ana yayata ki a duniya an dade ba’a fada ba tunda ba kanki faru ba sakin aure har a sakeki akan kishiya kintaya kina wani zubda hawaye mtsw,

Kansa ya cuta in sha Allahu se kin samu me sonki wanda yasan darajar ki kuma akan idonsa zega yanda za’a ringa tarairayarki sedai ya hadiyi zuciya ya mutu, Allah ya kaimu ki gana iddah ni kaina ina da Candidates se wanda kika zaba kika darje”.

Haka Maman Islaha taci gaba da gaya mun maganganu da suka sake bani kwarin guiwar yakice Bashir daga rayuwata, har tana ce mun se na chanza shiga tunda yanzu bani da aure na dena zumbula wadannan Dogayen rigunan da suke boye dirina se nayi dariya nace mata

“Maman Islaha ko da aure ko babu dole in rufe jikina in kare mutunchin kaina, bafa yarinya ce ni ba sannan ga yara ina dasu nan da kika ganni ma babu lissafin sake aure a gabana zan ci gaba kawai da neman kudina na kula da yarana shikenan”.

A ranar bamu tashi da wuri ba saboda mitin din gaggawa da mukayi, abin takaici ina zuwa na kunna motata taqi tashi bayan nasan lafiya qalau take ba’a ko yi sati uku ba da a ka kaita a dubata a sannan dinma ba abinda ya sameta shine yanzu zata mun halin qarfen nasara.

Ina tsaye ina ta faman zabga tsaki, David daya daga cikin yaran da suke kula da gurin pakin ya qaraso yana tambayata lafiya nagaya masa abinda ya faru shine ya bude gaban motar yana duddubawa duk ya gama yan dabarunsa amma taqi tashi, haka na kwashe kayana daga ciki na kulleta, ga Magriba tayi gashi duk yan arear mu sun wuce haka dai na kira uber dukda bana son hawa da daddare.

Ina tsaye a daga can gaban get ina jiran me uber wata dalleliyar mota Marsandi qirar shekarar da muke ciki baqa wuluk se qyalli ta wuceni, da ido na bita a raina ina yaba motar aga quginta kadai zaka san ba qaramar mota bace a raina nace

“Allah kayi mana arziqi muci me kyau mu saka me kyau mu hau mota me kyau” ina cikin haka se ganin motar nayi tana dawowa da baya. Matsawa nayi daga inda nake ina waiwaya wa bayana dan naga tazarar gurij da cikin ma’aikatar mu idan ta kama da abin gudu in fece kar inje masu satar mutane ne se gani nayi motar ta sake biyo ni ai kuwa na daga qafa na fara sauri, sunana danaji na ciki ya ambata ya saka na juya da sauri na kalle shi.

“Asma’u” ya sake ambata yana kallona, nima kallonsa nakeyi ina so na tuna ko na sanshi amma banga alamar hakan ba.

Baqi ne amma ba irin wukuk din nan ba fatarsa a goge take alamar hutu da jin dadi sun ratsata a kallo daya zaka tabbatar da kyakykyawa ne irin kyau na maza me cike da kamala. A zaunen da yake na tabbatar da dogone irinsu Bashir sannan yana da cikar halitta bashida qiba amma jikinsa a murde yake alamar yana daga qarfe daga damtsen hannunsa da yake a bude ma zaka tabbatar da hakan.

Gaba daya a abinda be wuce second talatin ba na qare masa kallon, nayi guntun tsaki dan ban gano wata alama da take nuna na taba sanin ko me kama dashi ba a rayuwa qila irin samarin nan ne ya canki suna akayi sa’a ya fada daidai se kawai na juya na fara tafiya a raina ina mitar abinda ya tsayar da me Uber kusan minti talatin shiru bayan a map naga yana dab da inda nake. Maganar da saurayin ya sakeyi ce ta sakani juyawa a sukwane ina kallonsa

“Ma’u danja wutar baya Ma’un lelen Baffanta” ya fada yana sakin wani murmushi daya saka gabana yankewa ya fadi.

“Yusuf” na fadi sunan a rarrabe ina qare masa kallo dan ya fito daga cikin motar ya jingina shima yana kallona. Murmushinsa me kyau ya sake yi mun kafin yace

“Har kin tuna ni kenan da yake kinji kirarin naki ko, daman na fada miki ko kin manta fuskata a rayuwa na barmiki abinda bazaki taba mantawa ba gashi kuwa ina fada har kin gano ni, me kikeyi a gurin nan ga duhu ya yi haka?”

Jinsa kawai nakeyi ina kuma qare masa kallo dason tabbatar da dagaske Yusuf din ne dai ko kuwa wani ne daya san tsokanar da yakeyi mun ada, se kuma dana nutsu na gane shidin ne amma canjin daya samu a rayuwa tabbas ya zarta ace ka gane shi a kallo daya yanda kasan wanda aka saka a inji akayi masa qare qaren abubuwa, Babban abinda yafi bani mamaki ma yarintar da ke tattare dashi.

A sanda nasan Yusuf ma a qallah ya haura shekara talatin kenan yanzu yana hararo hamsin ne amma nake ganinsa kamar yanzu ne yake talatin din da yan kai.

“Ki dena kallona haka karna komawa matata a rabi ina tambayarki me kikeyi a nan baki amsa ba” ya sake fada cikin sigar tsokana ya baro jikij motar zuwa inda nake tsaye, se naji kunya na sunkuyar da kai ya gane kallon qurillar da nake masa.

Ma’aikatar mu na nuna masa ina cewa “Daga gurin aiki nake motata ta lalace tana ciki shine na fito ina jiran Uber da nayi order”.

“Anan kike aiki Masha Allah Ma’u shiyasa mana seda nayi dagaske na iya gano ki, idan ba damuwa muje sena ajiye ki shiga motar haya da daren nan babu dadi.

Ban musa masa ba, muka qarasa ya bude mun gaban motar wani sanyi da qamshi suka bugoni har seda na lumshe ido ina shiga naji na wani lume a cikin kujera kai jama’a kudi dai yayi a rayuwa.

“Wace unguwa mukayi” ya fada yana kallona, se na gaya masa ya kunna motar muka fara tafiya shiru, Yusuf ne ya katse mana shiruj yana cewa

“Yaushe kuka dawo lagos da zama nasan dai a Gombe kikayi aure koh?”

“Eh Gombe nake bamufi shekara shida da dawowa nan din ba ai bayan daya samu chanjin aiki” na fada ba tareda na kalle shi ba.

“Ban sani ba ai, ina yawan shigow Lagos dan bana sati biyu banzo ba ga qanwata a gari ai da na tinga shigowa muna gaisawa. Ina Mijinki Bashir ne sunan sa ko wanda ya kasamu karma muje fa yaji haushina na dakko masa mata babu izini yanzu yaranki nawa?” Ya sake fada hankalin sa na kan titi, seda na waiwaya na kalle shi kafin nace

“Yana nan, yanzu yaranmu shida harda twins kaifa?”

“Kai lallai rabone ya kore mu yara shida ai ba wasa ba kice dana matsa da yanzu ana irgamun shekaru goma sha a qasa” ya fada yana yar dariya nima nayi dariyar ina cewa

“Ba wani nan kawai dai komai ka gani da yanda Allah ya shirya faruwarsa ne kawai”.

“Hakane amma dai ai Ya shammaceni da yawa ya rabani da Ma’u lokacin da na tabbatar nafishi sonki” da sauri kuma ya buga sitiyari tareda rufe bakinsa yace
“Astagfirullah, Afuwan Ma’u wallahi na manta nake dawo da maganar baya”.

Murmushi kawai nayi se nace “wai ma ya akayi ka gane ni?”

“Ma’u kenan, wallahi ko fuskarki ban gani ba seda na dawo da baya kawai zuciyata ce naji ta buga irin bugun da ke kadai kike sakata tayi shiyasa na tsaya dan na tabbatar ko ba kece bace tabbas akwai abinda yake da alaqa dake a gurin shiyasa na tsaya se kawai naci karo dake, kinsan dai ke baki chanza kama ba kyau da qiba kawai kika qara amma kina nan a Ma’un nan dai me yawo babu dankwali”.

“Yusuf ka bari”
“Na bari Ma’u, Allah na tuba ka yafe mun kasan bada niyya nakeyi ba kawai dai kai ka jarabceni da son baiwar nan taka har na rasa yanda zanyi a rayuwata”. Yanda yayi maganr har fuskar ta nuna gaskiyar abinda ya fada ya sakani sunkuyar dakai na qasa, gaba daya se naji kamar ya daure ni da igiyoyi, haka muka qarasa tafiyar kamar kurane shine ma yake tambayata kwatance har muka qarasa bakin Eatate din.

“Ko na sauke ki anan ki qarasa?” Ya fada yana kallona se nayi murmushi kawai ya shige da motar bayan da ya sauke glass suka kallemu ganina ya saka masu gadi bamu hanya tunda sunsan motar bata gurin bace.

Har qofar Flat dina Yusuf ya paka motarsa, na riqe jakata a hannuna ina cewa “Nagode sosai Yusuf, ko zamu shiga ku gaisa da yaran?”

“Tab so kike Mijinki ya harbeni kenan, ki bari dai tunda naga guri ai kuma se kun gaji dani zanzo naga yarana sedai idan kuma mijinki ne ya hana, ina fata dai babu matsala kawo kin da nayi ko?”

“Ba matsala, Nagode sosai ka gaida madam da yara, baka ma gayamun su nawa bane”.

“Zasu ji, guda daya ce Ma’u tana nan ta isheni da fitina yanda kika san ke kika haifeta” yayi maganar yana miqomun wayar sa dake dauke da hoton wata kyakykyawar yarinya fara tas kamar yar turawa amma kamanninta sak da Yusuf din bazata wuce sa’ar Abdallah na ba.

“Kai masha Allah, ya sunanta” na fada ina sake kallon sauran hotunan nata.

“Baki ji ba nace miki Ma’u takwarar ki ce”

“Wasa kakeyi amma ko? Ina hajia baka saka sunanta ba zaka ce sunana ka saka” na fada ina kallonsa.

“Wallahi Ma’u ke nayiwa takwara, bama ita kadai ba na qudurce a raina ko yaya mata goma zan haifa sunanki zanyi ta maimaita musu”

Yanda yayi maganar cikin wani yanayi ya sakani kama hannun motar zan bude ina cewa
“Nagode kwarai toh ka gaida takwara, idan tare kukazo seka kawo su mu gaisa” na danna mabudin naji qofar a rufe, daga bangarensa ya danna wani abu qofar ta bude, mukayi sallama na wuce ina jin yanda kayan jikina suka kama qamshin da motar takeyi.

“Tab tsautsayi ace ina gidan Bashir na shigo lift din nan da yau tsirena kawai zeyi ya huta” na fada a fili ina kaiwa qofar gidana se ji nayi naci karo da mutun, ina daga kai muka hada ido da Bashir da idonsa ya kada yayi jajir ga wasu jiniyoyi da suka tashi a goshinsa alamar yakai qololuwar bacin rai.

“Wane Dan iska ne ya sauke ki a mota Ma’u” ya fada yana kallona.




Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku

BONONZA; BONONZA;BONONZA;

Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K


MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 45

"Magana nakeyi miki Ma'u nace wane dan iska ne ya saukeki a mota a cikin wannan tsohon daren?" Bashir ya sake fada cikin hargagi.

Ban tankashi ba haka ban matsa daga inda nake tsaye ba sema waiwayawa nayi na kalli wasu samari su uku da suka zo wucewa suka tsaya kallon mu gashi kuma ko wanne da waya a hannunsa.

"Ka matsamun na wuce gasu can suna kallonka idan kuma so kakeyi suyi maka video seka bada himma" na fada kafin na raba shi zan wuce cikin gidan se kuwa ya biyo ni kamar wani kububuwa ya sake shan gabana yana cewa

"Kinsan Allah idan baki gayamun waye wancan ba ba video ba ko gidan Tv zasu dakko su kawo gurin nan sedai duk wacce za'ayi ayi amma bazaki shiga gidaj nan ba".

Wata dariyar rainin hankali nayi kafin naja da baya ina kallonsa nace
"To wai kai a na me kake so kasan waya kawo ni, kana da matsala da hakan ne? gida kuma kalli dakyau a qofar gidana kake ba wai gidanka naje zan shiga ba da zakace zaka tare ni dan haka ka matsamun na wuce malam banyi sallar magriba ba ga Isha ta tarar dani"

ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login