Showing 219001 words to 222000 words out of 260321 words
Chapter 74 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
suna kallon mutane kamar wasu kashi ai gashi nan kinja sun gayawa mutane magana mtsw”
“Dallah gafara can an jawo din seki dakeni ai nasan kinji haushi” Amina ta fada tana harararta.
“Gaskiya dai Yaya Bashir ya luza ji yanda mata tayi luwai abinta zawarci ya karbeta ba irin wasu ba” Suwaiba data fi kowa iskanci ta fada nan da nan suka fara rigima da Fainusa dan dai ita kadai ce Bazawara a gurin kuma kowa yasan da ita take tunda daman sun ba mudai muka shige Palour Alhajin Su Bashir inda Dada harda qara shimfida mana qatuwar Dadduma akan Carpet din dayake gurin.
Cikin girmamawa muka gaishe shi gaba daya.
“Ki gafarce ni Asma’u wallahi nauyi da kunya ta saka na kasa kiran ki, Bashir be kyautawa kansa ba amma babu komai Allah yasa hakan shiya fiye muku Alkahiri” Baban ya fada daga kwance da alama jikin ya takura masa da gaske.
“Babu komai Baba, nima ai nayi laifi da ban kiraka na gaishe ka ba kayi haquri”
“Aa karki kuma ai ke kika cancanci ban haquri,ki ci gaba da haqurin dai in sha Allahu zaki dauke shi a gaba. Ina Alhaji Abdu? Dazu da safe yazo ai ya kawo mun magani kin gansu can wai shi likita ne saboda jiya na gaya masa ina ciwon kai da daddare da zasu tafi” ya fada yana nuna mun paracetamol din da yake gefensa.
“Au wai daman kai ze kawo wa? Yazo yana ta tambayata wai maganin ciwon kai na zatama shi ze sha na bashi a she nan yayiwo”
“Nan yazo ai ya jima ma, amma fa nayi nayi yaci abinci yaqi wai Mami ta hana su kwadayi banda abin Abdullahi nan ai gidan su ubansa ne ko yana inda yafi nan ne ko da yake qila ba’a fayyace masa ba” Dada ta fada da yar dariyarta, sena daga kai na kalleta kawai nayi murmushi
“Yaushe zaku wuce saboda aiki? Koda yake akwai bikin Su Bilalu na manta se an qare zaku koma kenan” Baba ya sake fada ba tareda yabi takan zancen Dadan ba.
“Eh se an gama biki Baba, daman sati biyu zamuyi gaba daya”
“Toh Allah ya taimaka yasa ayi a sa’a. Kema Allah ubangiji ya fito miki da Miji na gari kiyi auranki kinji”
“Amin Baba, Ai Allah ma ya kawo mata sedai ayi Addu’ar fatan Alkahiri kuma” Alawiyya tayi caraf ta amsa.
“Kai madallah amma naji dadi ubangiji ya tabbatar da Alkahiri yasa zamu gani kai nayi murna sosai, Nafi kinji abin Allah ko Baba ya fada har yana miqewa zaune.Dada da tun fara maganar Alawiyya tayi kasaqe tana kallon ta tace
“Uhm” tareda yaqen dole,har muka gama hirar da zamuyi Baba nata sa mana Albarka muka miqe. Jakata na zuge na ciro bandir din yan dari biyu sababbi dana tanada na ajiye a gabansa ina cewa
“Gashi Baba babu yawa a siyi Goro, an jima na turo su su duba jikin naka”
“Kai kai Haba Asma’u dauke kudinki kinji ai gaisuwar da kika zo mukayi ma tafi komai Nagode Allah yayi miki albarka” ya fada yana turomun kudin se na nufi qofa ina cewa
“Dada se anjiman ku toh”. Seda Alawiyya da Khadija ko wacce ta qara aje masa dubu biyar biyar kafin muka kama hanyar gida. Har Get Dada da duk jikinta yayi sanyi ta rakamu kafin ta juya, har mun fita Samurah ta kwaso da gudu tana tambayata wai
“Anty zan samu chanjin sabon kudi?”
“Sabon kudi ai yana banki Samirah, ki nemi Sa’ad mana sune ma’aikatan banki” na bata amsa muka qara gaba.
Oh ikon Allah, ada fa idan zanje gidan irin haka sena shaqe uwayen kuloli da Abinci kala kala, Dubu Goma nan sena aje mata ta goron sallah banda wadda zan rabawa kaf jikokin gidan idan sunzo sannan su kansu qannen nasa wasu su fake da chanjin sabon kudi wasu kuma kai tsaye ma zasu ne na basu barka da sallah idan kuma zamu tafi nawa Yayan ko yar biyar babu me basu idan ba Amiru ba shi daman har gida yake zuwa ranar idi tareda Sa’ad da Naziru suci tuwon sallah ya raba musu kudi amma matan babu me karar ko dan kunne ta kawowa Farida seni jaka na hidimta musu nayiwa Yayansu kai kar Allah ya kawo abinda baze wuce bama.
A daren ranar Alhaji Qarami yaki rani bangarensa yana tuntubata wai ya muke ciki da Yusuf?
“Mutumin nan na qaunar ko Ma’u, dukda baka shaidar Dan Adam amma ina kyautata masa zato akanki wallahi ga danginsa suna sonki”
“Uhm toh Yaya nidai ina ta Addu’a Allah ya zabamun mafi Alkahiri dai, kuma fa shi Yusuf din nan ma ni ban gama gane masa ba. Wai ita matarsa wane irin aure nema suke tana wata duniya yana wata nifa sau daya naji yace yaje can inda take” na fada ina gyara zama.
“Wayaga Ballan sori, ke har lissafin wannan kikeyi ma ai in kinji ana da ita da babu duk daya to wannan mata ta Yusuf kenan. Ita fa tsabar Gayunta ne ta girmi zaman Najeria, daman yar uban gidansa ce Ambassador Musa Manzo ya aureta uwarta Baturiya ce.
Shikansa Baban nata irin wannan gantalallen auran sukeyi da uwar tana can America shi da sauran Matansa suna Nigeria se sanda yai ra’ayi yaje ko ita tazo to itama Inteesar din da akwai yayarta itama me aure ce duk haka dai suke wannan gantali da Yusuf din.
Dan haka ma ki saka ranki a inuwa kamar ma ke kadaice bakida wata kishiya dan yanda kika San ba Mata ba wallahi. Su yawon shaqatawa da zaga duniya da kwalliya suka saka a gaba. yo tikita ta yanka masa fa yaje ya nemi duk wadda yake so akan dai tazo Nigeria tayi zaman aure wai kuma a haka sonsa take kamar me badan ma Allah yasaka nutsatstse neba aida yayi tambari yanzu a neman matan banza tunda auren fa kusan shekara biyar kenan ana wannan gantalin kawai ki amsa mana musha biki se mu daura Addu’a qanwar mu ta zama Firs Lady ai mukam ras damu” Anty Ladi da muke cewa Momi uwargidan Alhaji qarami ta koromun wannan jawabin.
Tagumi na rafka ina jinta, ikon Allah kunji wata sabuwa kuma su haka suke kenan daga uwar har yayan?
“Toh kinji ai se kuma me kike buqatar sani ki tambayeta” Yaya ya fada yana yar dariya.
“Kai ni fa Yallabai randa mukaje ganin ginin nan nasa kwana nayi da takaicin da yanzu mu zamuje muyita iyayi muna zuba kaya gidan qanwar mu, na ringa raya da ina da Yar data isa aure ko qanwa to fa duk ma yanda za’ayi se an hada auran su da dai a dakko bare taci arziqin dan nasan aure ze qara.
Harfa na fara tunanin na qyasawa Suwaiba se kuma nace kar kayiwa kishiya hanyar arziqi se abu ya samu a manta dakai kwatsam se gashi wannan abu ya wakana kai nifa harda sujudushshukur nayi kana fita randa ka gaya mun maganar nan, yo ko zuwa nayi na dauki hoto a gidan ai an biyani wallahi”
Sosai muka ringa dariya nida Yaya musamman wai kar ta gayawa Anty Suwaiba kishiyarya ae arziqi ya samu su manta da ita.
“Ku zauna kuna dariya shi ai yasan me muka gani wallahi keni ko bakyason sa dan Allah ki aure shi kowa ya san gaba kika ci ba baya ba”
“Aa dai gara tana son nasa dai, ni na zata ma sun gama komai ai yanda yake addabata da waya duk lissafina kawai mu hada danasu Bilal a daura daga baya se suyi tariya ko” Alhaji Qarami ya fada
“Ai da ka gama mun komai wallahi yallabi kawai ayi haka, kai infa aka biye ta Ma’u ba wanda zata so wannan mijin nata me fuskar shanu ya rigada ya rubuce sunanta a Allon qarfe se ta Allah kawai gara in ma dole za’a mata ayi a wuce Gurin”
Dariya sosia Momy ta ringa bani daman ita haka take akwai abin dariya, tana da matuqar kirki ta kuma kama girmanta a matsayinta na matar babban wan mu babu raini haka babu wulaqanci kowa natane sefa wanda yazo mata da abin da be mata ba bazata dauka ba.
A gaba da sakani da hudubobi dan Alhaji tashi yayi ya barmu bayan daya jaddadamun na san matsaya dan Goggo fa dagaske tace tana dawowa dole na fitar da miji nayi aure kona tattaro na dawo Gombe na bar aikinsa yayi sanadin gurgudewar aurena.
Ranar raba dare nayi ina saqa da warwara, daga qarshe na tashi na raya daren addu’ata dai a kullum zabin Alkahiri daga Allah (To Hajia Ma’u kwankwasa qofa za’ayi ace fito ga zabin da Allah ya miki ko yaya? Ke zaki saki ranki ki bude zuciyar ki sannan ne zaki fahimci abinda Allah ya zabar mikin).
BASHIR
Haka ya sallace cikin quncin zuciya da takaici da dana sanin me yasa ma be tafi Gombe ba shima. Sallah guda haka ya zauna a gida yana zare ido dama dama ran idi yaci abinci dan Fried rice Amirah ta daure tayi musu ranar harda Salad ga Zobo me sanyi da dabgen kaji.
Haka yaci ta a babu yanda ya iya to yaushe rabon ma daya samu kamarta din? Babu tuwon sallar nan dasu Sinasir da waina kai gaba daya Eatate din qiyau miyau kodan qamshin abincin sallar nan da zakaji gari ya dauka babu toh duk musulman sun wuce garuruwanau sallah shima tsautsayi ya zaunar dashi dan be tabayi ba se wannan karon.
Yana daki yana aikin kallon status din Jama’a na sallah kowa da Yayansa sunje Ido seya tuna yanda Ma’u take tasa shi su kashe hotuna ran sallah da duk wnada ya kalla seya yaba wannan karon ko Babbar rigar ma ajuye ya sakata seda yaje masallaci aka gaya masa ya gyara dan sanda ya shirya ya tafi Matar gidan bata ma fito daga daki ba bare ta taya shi shiri, daya dawo dai ya tarar ta cancada kwalliya da kayan daya mata ta kuwa yi kyau sosai masha Allah haka gidan an gyara abinda ya sauqaqa bacin rabsa kenan sannan ko ba komai ya dan samun abin kaiwa bakin salati.
A status din Amnah yaga hotunan su na Idi, shaddar gurin Yusuf me babar riga yaran suka saka sunyi kyau kamar ka sace su ka gudu haka ya ringa zooming yana murmushi da jin kansa na fasuwa wai fa yayansa ne da Ma’u, yo ko dan su ai dole ma ta haqura ta dawo su zauna.
Hoton da sukayi ita da yaran ta cakare kamar wasu qannenta sun sakata a tsakiya ya tsaya yana kallo nan da nan ya kwafa ya dora a status dinsa kuwa. Haka ya wuni kallon hotuna Daya gaji da zaman gida ya fita zaga gari, su Addah dai ana palour ana warkajami da Kajin da sukayi Dabgensu.
Ranar kwana uku da salllah da yamma sakakiya Dada ta kirashi tana gaya masa abin tashin hankali zancen wai Asma’u ta samu miji sun daidaita lokaci kadan ya rage ta daura aure.
Yana zaune a gurin da yake zuwa cin abinci lokacin ta kirashin, tsabar rikicewa besan sanda ya watsar da lemon hannunsa ba ya miqe jiki na rawa ya shiga neman layin Ma’u sam ya manta ma da cewar ta toshe shi seda yaqi shiga sannan ya koma kiran Amnah, akayi rashin Sa’a bata gida sun tafi yawon sallah gidan qawayenta.
Seda ya je mota aka bishi da bill dan be biya ba da ze tafi, Yarinyar nan ce ta kwanaki.
“Me yasa a koda yaushe kake cikin yanayin damuwa da tashin hankali ne Bawan Allah?” Ta fada bayan daya bata kudin ya shiga mota.
Harara ya zabga mata yace
“Gafara daga nan kona take miki qafafu” ya figi mota yayi gaba, seta kama baki tace
“Toh daga magana? a sauka lafiya to nima maganina kenan ta juya ciki abinta.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Wattpad @MaryamahMrsAm
Page 59
An daura auran su Bilal munsha shagali sosai dan mun dade rabon mu da biki a gidan mu.
Washe garin ranar daurin auran ba tareda na sanar da Bashir ba muka kwashe kayana na sedai yaji a gari mukayiwa gidan qaf tsinke bamu bari ba dan wannan dibar kayan harya fi na Lagos tunda da yan gidan mu mukaje daidai da gadon dakinsa daya siya da kudinsa seda suka cire wai Yaya sun bani kayansa kuwa haka suka zube masa akan Katifar dayaci arziqi aka bar masa.
Seda suka ga gida ya zama kango kafin suka haqura, na kwashi abubuwan da nake so akayi packaging ragowar kuwa Wani shago da suke siyan kayan hannu muka kaisu, sun siya da daraja sosai dan kayan masu qarko ne da kyau kuma basuyi komai ba tun kafin mu bar gurin aka fara wawason su suka cake mun uwayen kudadena a akawun muka tafi zan juya su zuwa sanda Allah ze yanke mun na sake siyan wasu. Kwana uku muka qara muka tafi dukda naso na bar su qarasa hutunsu se kuma dai muka koma gaba daya.
Tare muka gyara gidan dukda ba wani datti yayi ba dan mun kulle ko ina sanda zamu tafi. Seda muka gama komai nace wa Aliyu yayi wanka ya rakani mu siyo abinci saboda saukar Yamma mukayi base munyi girki ba.
Muna tafe a hanya Yusuf da bamu samu mun hadu a Gombe ba ya kirani mukayi magana.
"Mami dan Allah ina so muyi magana" Aliyun ya fada bayan dana gama amsa wayar, sena waiwaya na kalleshi. Tuntuni na lura da rashin walwalarsa ko biyonin da yayi nasan da dalili gaba daya ya canza dukda daman bashi da sakin fuska sosai amma yanzu abin ya qaru ko yaushe yana cikin qunci da damuwa.
"Ina jin ka nima daman inaso nayi magana dakai me yake damunka duk kabi ka takura rayuwarka Aliyu?" Na fada ina kallonsa.
Ajiyar zuciya ya sauke bayan daya faka motar dan shi yake janmu saboda gurin da mukaje babu nisa daga gida.
"Mami bana jin dadin yanda kukeyi keda Abbi, nasan yayi miki laifi amma Mami tunda ya baki haquri to ki haqura mana ki yafe masa"
"Aliyu ni laifin me Abbin yayi mun? Kuma koma menene ba kana kallo ba ai shiyake zuwa kullum har inda nake yana takala ta da fada dan haka shi ya kamata kaje ka yiwa magana ya dena abinda yakeyi tunda har kayi hankalin gane badaidai bane" na fada fuska a daure dan karma ya kawo mun wani shirme,
"Toh amma Mami.."
"Kaga ni yunwa nake ji zaka shiga ko a mota zaka zauna" na katse shi ina balle murfin qofar. Seya gyada kai kawai ya kashe motar muka fita yanda muka jera seka zata irin qanina ne haka muka shiga gurin na samu guri na zauna tareda gaya masa abinda zeyi mana order.
"Assalamu Alaikum ranki ya dade" naji an fada daga gefe na na dago da sauri jin kamar nasan muryar, Ambassador Mutallab Ali ne shida wani a teburin da yake gefen namu se wannan PA din nasa yana tsaye yana zare ido.
"Ranka ya dade barka da rana" na fada ina sunkuyar da kai da tuno yanda na dannawa lambar sa block tun a kiran farko qila yayi ta kira harya haqura tunda bata shiga.
"Daga kiran waya malama Asma'u se kikayi blocking dina kuma laifin me nayi?" Ya fada kamar ya shiga zuciyata. Kaina na qas ina dan murmushin yaqe ya sake cewa
"Tunda na kira naji line busy nace to gimbiyar bata son damuwa bari a barta ta huta, kwanabiyu abubuwa sun sha kaina shiyasa ma ban sake gwadawa naji ko an bude ni ba se gashi yanzu Allah ya hadamu dan haka a gabana zaki bude na gani".
Wato yanda ya dage yana magana ni gaba daya ma kunya ya bani ko ganin girman kansa beyi ba yake wani lankwashe harshe gashi kuma Abokin nasa se wata dariya yake kamar wanda akewa cakulkuli ni duk ya bani Haushi nama rasa me zance musu.
"Kinyi shiru Asma'u, koda yake fara dakko wayar kiyi unblocking dina mayi magana daga baya dan yanzu sauri nakeyi, Alhaji Sani ka ganta nan ita ce yarinyar danake baka labari"
"Ah ai na ganta tayi sosai kuwa bazamu bari wannan ta wuce mu ba" wanda ya kira da Alhaji Sani ya fada cikin hausarsa da bata fita sosai daga ji ba cikakken Bahaishe bane se na fara laluben wayata akan Tebur din da nake, Ajiyar zuciya na sauke dana tuna na manta ta a mota da zamu fito na juya na kalle shi da dan murmushi nace
"Ai kuwa na manta ta a gida ina sauri zamu fito" daidai sannan Aliyu ya qaraso da Waiter na binsa da ledojin abinci. Tsabar wulaqanci kallo daya ya musu ya dauke kai kamar wanda yaga kashi ya zauna a kujera yana muzurai.
"Wannan Qaninki ne?" Ambassador ya fada yana kallon Aliyun, sena qaqalo murmushi nace
"Aa, first born dina ne, Aliyu baka ga mutane bane?"
"Nagansu mana" ya fada kansa tsaye kamar be gane yaran ya gaishe su nake masa ba. Tsabar takaici na bude baki kawai ina kallon yanda ya hade fuska yaja Ice cream din daya taho dashi a hannunsa ya hau sha, zanyi magana Alhaji Sani ya tare ni da cewa
"Aa barshi yaro ya gida? Ina qannenka kana taya Babanku kishi ko banga laifin ka ba".
Murmushi Ambassador yayi kafin ya miqawa PA hannu se yayi saurin bashi wata briefcase dake hannunsa, budeta yayi ya ciro rafar Dala dari dari guda biyu ya ajiye mun daya yace
"Gashi idan kun gama seki biyu kudin muna sauri ne bari mu wuce, Yaro ka saka katin waya ko" ya ajiye ragowar dayar a gaban Aliyu.
"Haba Ranka ya dade ai da ka barshi mun rigada mun biya ai" na fada ina tura masa kudin, gaba yayi abinsa yana cewa
"Zan sake gwada wayar naji idan kin koma gida" ya wuce suka take masa baya bayan da Alhaji Sani ma ya sake ajiyewa Aliyun wata Dalar harda dafa kansa yace yana yar dariya yace
"Yaron kirki me taya Babansa kishi" suka fice gaba daya.
"Wallahi sekaci ubanka Aliyu ni ka kunyata a idon mutane ka nuna musu baka da tarbiyya ko?" Na fada kamar zan kwada masa mari Saboda haushin abinda yayi din. Ice cream din ya ture kamar zeyi kuka yace
"Toh ni