Showing 177001 words to 180000 words out of 260321 words

Chapter 60 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42709

na tsaya ina kallonta ni ba abin na mammaketa ba ubanta na waje dan da ace yan biyu ke yi mun tabarar da tuni naci ubansu dan ni ba’a haka dani wannan yarinyar kuwa naga alamar an gama sangartata se a hankali kawai.

Dole na fita na gaya masa, badan naso ba ya shigo gidan, yayi lallashin duniya taqi ji qarshe a wuya ya dauketa tana kwala ihu kamar wadda aka sace ya sakata a mota yaja suka tafi muna daga mata hannu, haka muka wuni yara sukuku abu kadan ace Little kaza ni kaina nayi kewarta dan tana da shiga rai barta da yar banzar barna kamar beran turawa.

GOMBE
ADDAH
Tiryan tiryan me Napep ya kaita har qofar Asibitin data kwatanta masa saboda saurin da take ko musu batayi ba ta dakko kudin daya ambata mata ta bashi ta shiga jan Ummi da dauk ta galabaita suka shiga ciki.

Kai tsaye gurij Nurse din dake bada kati taje ta ce mata likita suka zo gani aka yanka mata kati dari biyar ta zaro ta bayar, babu mutane da yawa a gurin, mace biyu suka tarar su na uku ganin yanda Ummi take kuka ma Nurse din ta dauka ko ciwo ne dan haka ta roqar musu alfarma Gurin wadan da suka tarar ta ciki na fitowa suka shiga.

Likitan na zaune kai idan ka ganshi me hankali dai baze yarda ya dubashi ba saboda yanda yake a hargitse sam be mayi kala da likitoci ba, ba bata lokaci Addah ta zayya na masa abinda yake tafe dasu da kuma buqatarta.

Shiru likita yayi yana kallonta, Addah da taga yayi shiru ta har ziqo tana cewa
“Ko bazaka iya bane ka fada ka zuba mana ido kamar maye yaga nama, ni karka bata mun lokaci idan baka yi mu qara gaba ai likitocin kuna da yawa”.

Seda yaja numfashi kafin yace “cikin wata nawane Hajiya?”

“Wai wata hudu tace, kana ji ko karka damu da wani watannin sa ka markade mun dan banza ko nawa ne zan biyaka”

“Yawwa daman maganar ta kudi ce Hajiya tunda kinga cikin ya girma dole cireshi zeyi wahala dan haka se kun biya kudi da yawa amma tunda kince babu matsala to za’ayi aiki zaki biya dubu dari biyu da hamsin ne kudin aiki se kuma dubu hamsin na magunguna da jini da zamu siya saboda tsaro gaba daya kinga dari uku kenan” Likita ya fada yana wani murmushi da gani banza ta fadi

Dafe qirji Addah tayi ta zaro idanu waje tace “Likita dari uku fa kace cire cikin? Ina laifin in baka dubu hamsin shima saboda naji kace da wahala amma da ni dubu talatin ce kaga na ruqo ta” ta qarasa tana bude yar jakar ta ta zaro kudi, seda likita ya ha tareta kafin yace

“Bata mun lokaci daman kawai zakiyi Hajiya ba aiki kuka zo ayi muku ba. Kinsan hatsarin da yake cikin abinda kika zo yi kuwa idan fa aka samu matsala aka kamani daurin shekaru zansha a banza ki gudu abinki kinga ku tashi tunda naga wasa nema ya kawo ku na samu na duba sauran da suka zo da gaske”

Ganin da Addah tayi ga samu ga rashi yasa ta marairaice tana cewa
“Dan nan ba wasa bake ba kudin ne daka fada sunyi yawa amma yanzu shikenan, kayi mana ragi naji abinda zan bayar In sha Allahu baze gagara ba”

“Ki bada dubu dari biyu shine qarshen magana idan beyi miki ba ga hanya nan” ya fada yana hade rai, Addah tayi shiru, a jakarta gaba daya dubu hamsin ne ribar kasuwarsu da Alhaji ya bata jiya, tama tabasu basufi Arba’in ba yanzu ina zata kwakwulo dubu dari da sittin ta hada dan bazata taba bari wannan damar ta wuce ta ba.

Ajiyar zuciya tayi ta kalli likita tace
“Shikenan na yarda, yanzu ga dubu Arba’in zan baka idan yaso ta zauna zanje gida na karbo ragowar sena kawo maka”

“Aa ai ba anan za’ayi aikin ba Hajiya, inada guri daban da nakeyi kuma se da daddare zaku zo zan baki lambar waya da Adireshin gurin se ku same ni acan” Likita ya fada nan da nan Ummi ta qara wa kukan da takeyi qasa qasa qara, mayar da hankalin sa kanta yayi yana cewa

“Ki rarrasheta Hajiya ta dena kukan nan dan idan jininta ya hau za’a iya samun matsala a gurin aikin. Yanzu zan rubuta muku magani ku siya a waje daya zata shanye shi yanzu dayan kuma idan kunje gida kamar saura awa hudu ku taho yin aikin ta saka kwaya daya a qasan harshen ta zasu nuna muku ko wanne da yanda zaku yi dashi din”.

Godiya sosai Addah ta ringa zuba masa kamar wanda ya bata kyauta, ta kawo dubu talatin da biyar ta bashi biyar din zata siyi maganin sannan suyi kudin mota.

Tana fita kuwa a dan gurin siyar da maganin Asibitin nasa suka tsaya ta siya a take ta saka Ummi seda tasha na shan suka kama hanyar gida tana ta lissafin inda zata samo kudi.

Amirah ce ta fado mata a rai, daman shegiyar yarinyar tunda ta tafi bata tuna da ita ba balle ko biyar bata aiko mata da ita nan da nan ta kunna wayarta ta shiga kiran Amiran.

AMIRAH
Tana zaune a daki tana kuka, san baqaqen maganganun da Bashir ya gaya mata basu dameta ba ita yanzu ta yanda zata samu Addah ta hanata abinda tayi niyya take, tana tsakanda aikin kukan kiran ya shiga.

Da sauri ta faga wayar tana cewa
“Addah kina ina ne tun safe nake neman wayar ku bana samu ke da Ummi?”

“To uwata, an baki ajiyata ne da kike tambayar ina naje ko yaya ina ruwanki? Ni yanzu kirani nayi ki tura mun kudi zan samu POS na tsaya yanzu na basu lambarki ki sako kudin na cire”

“Addah me zakiyi da kudi? Ina Ummi? Kun koma gida ne Baba ya kirani dazu yana cewa...”
“Wai dan uwar ubanki Amirah zakiyi abinda nace ne ko tambayoyi zaki tsaya yimun kamar alqaliya?

Baba ya kira yace miki ubanki ina ruwanada wani Baba babo mata ni wutar gaba na ta isheni yanzu, na samu wanda ze cirewa yar uwarki abin kunyar data kwaso mana kudin nake hadawa yanzu anjima zamu koma ayi aiki” Addah ta katse Amirah.

Se Amirah ta zaro ido kamar tana gabanta tace
“Addah mutuwa akeyi wallahi kin manta Harira lokacin tayita zubar da jini har seda ta mutu dan Allah Addah karki sa na rasa Ummi kinga ita kadai ce yar uwata.

Ki qyaleta ta haihu wallahi ko ni zan dauki abinda zata haifa na riqe nasan Yaya baze hana ba”

“Idan kika sake cewa wani abu se kinci ubanki Amirah, bazaku kasheni ba yanzun nan zan turo miki da akawun na fasa zuwa POS din ma zan shiga gidan Talatu kawai mu zauna a can zuwa lokacin da zamu koma idan yaso se na turo miki da ko na Dan ta ne ki saka kudin nasan in muka koma gida wannan Uban naku ba lallai ya sake barina na fita ba” tana gama fadar haka ta kashe wayarta tana aunawa Amirah Ashar shidai me Napep se leqenta yake ta mudubi Allah Allah yake ya sauke su ya samu wanda ze bawa labari.

Amirah kuwa tana jin Addah ta kashe waya ta shiga neman layin Babansu, yana dagawa kai tsaye ta gaya masa Addah na gidan Anty Talatu ta kashe wayar tana Addu’ar Allah yasa Babansu yaje kafin su Addah su koma inda tace.

Addah kuwa a gidan Anty Talatu suka yada zango, yar uwarta ce yayan mata suke yar bala’i ce ta gaske itama dan har tafi Addah rigima.

A tsakar gida suka tarar da ita tana wa wata jikarta masifa, ko sallamar Addah bata amsa ba seda taji yarinyar na gaida Addan sannan ta waiwaya inda suke tana huci.

“Aa Fattu kune a tafe? Ku shigo mana ita kuma wannan me aka mata ta dora hannu aka tana kuka? Nifa bana son fitina shiyasa kikaga bana qaunar baqar yar nan taki saboda mugun halinta gara Amirah tafi mun ita sau dubu”

Cikin dakinta suka shiga tana gaba suna binta a baya. Seda ta kawo musu ruwa me sanyi da Fura, ta futa ta bawa jikar tata kudi tace taje qaro taliya leda daya dan gama miyar ta kenan sun maida ruwan taliyar yarinyar ta juye tayi wanka dalilin masifar tata kenan.

“Daga ina haka Fattu da uwar ranar nan fatse fatse keda bakya gajiya da yawo” Talatu ta fada bayan data zauna.

Se Addah ta janye tagumin data buga tace “ki bari kawai Talatu wannan yarinyar ce ta kwaso mun tashin hankali” nan ta zayya na mata abinda yake faruwa.

Anty Takatu ta hau salallami tana tafa hannu tace “yanzu Ummin? Ke da nakeyiwa kallon ta kirki kai yaran yanzu se abarku abinda se dai muji daga nesa shine kika kawo mana a cikin zuri’ar mu Allah ya wadaranki dai Ummi”

Nan suka hadu suna ta nanata zancen, seda ta dafa musu taliyar suka ci kafin Anty Talatu ta kalli Addah tace

“Ni Fattu maganar zubar da cikin nan ki barta kina gani dai ance mutuwa akeyi wallahi, yanzu abinda duk ya kamata ayi shine tunda tasan uban ciki a nemo shi a taru a rufawa juna asiri ko yaya ne ayi musu aure shikenan”

Hayayyaqo mata Addah tayi tana cewa
“Ban gane abar ciki ba in barta ta haihu kenan a ringa nunani a gari ace nayi jika shege to bazata sabu ba wallahi, kuma zancen aure da kije badai da wannan matsiyacin ba sedai idan mutuwa nayi”

“Ai kuwa idan baki mutu na zakiyi ta goya shegu tunda ke zuciyarki irin ta kafiran farko ce. Yanzu tashi zakiyi mu zagaya nan baya gidan me sittin tara a kwantar da cikin daga nan a nemo yaro idan sukayi aure wata kadan se a tayar dashi dukma uban da za’a fada dai daga baya ne tunda sun rigada sun yi aure”.

Shiru Addah tayi qasan zuciyarta ta yarda da shawarar Anty Talatu, miqewa sukayi Anty Talatu tace Ummi ta shiga ciki ta hau gado ta huta kafin su dawo suna zuwa qofar gida sukaci karo da yan sanda a tsatstsaye.

“Lallai Asabe, ba nace ta bani sati daya zan biyata kudin ta ba shine zata hadani da hukuma ai kuwa wallahi tayi ta kudinta muje duk uwar da za’ayi ayi amma bazan biyata ba kuwa” Anty Talatu ta fada dan a zatonta wata mata da rigimar Adashi ta hada su tace zata dakko mata yan sanda ce ta turo su.

Fitowar a Alhaji Murtala daga mota ce ta dakar dasu Addah ta shiga zare ido tana komawa bayan Anty Talatu.

“Gata nan yallabai” ya fada yana nuna musu Addah nan da nan yan sanda mata biyu sukayi kanta se ta sake riqe Talatu tana cewa

“Me kuma nayi Alhaji? Wane munafunchin aka qullamun da zaka dakko mun yan sanda saboda ka tozarta ni”

“Ai kin rigada kij gama tozarta kanki Fattu, ina Yata take? Se na tabbatar da lafiyar ta idan wani abu ya sameta daga nan kotu zamu wuce dan se nayi shari’a dake Fattu” ya fada cikin tsananin dacin rai.

Anty Talatu ce ta tare yan sandan da suke neman jan Addah tana cewa
“Ummi tana ciki Alhaji lafiyarta qalau, bari na kirawo maka ita ka ganta wannan kuma ai abu ne na cikin gida be kamata ace ka saka hukuma a ciki ba”

Daga bakin soron gidan ta tinga kwalawa Ummin kira, Ummi da har bacci yadan fara fizgarta ta fito jin muryar Talatun tana fita tayi arba da Baban su seta fada jikinsa ta fashe da kuka tana cewa

“Dan Allah Baba kar ka bari ta kaini a cire mun mutuwa ake yi ni kuma bana son na mutu”.

Riqeta yayi sosai a jikinsa zuciyarsa na tafa sa, tausayinta ya cika shi ya tabbatar duk abinda ya sameta qaddara ce da kuma halin Fattu ya janyo.

Cikin bacin rai ya kallo yan sandan yace “ku rabu da ita tunda naga Yata kuje kawai zan zo station din anjima na gode”

Sukayi masa sallama suna harar Addah sukaja mota dan sun so sun samu damar moreta.

A motar sa ya saka Ummi ya zagaya ze shiga Addah ta biyo shi ba ko dar tana cewa
“Bari nazo mu tafi Alhaji, Talatu se munyi waya ko zan kiraki idan naje gida”.

“Idan kinje wane gidan? Da alama baki ji saqona ba kenan” Alhaji Murtala ya fada yana dakatawa daga shiga motar da zeyi, Addah ko qoqarin bude mota take tana cewa

“Saqon me kuma wa ka bawa ya bani? Ni ba’a ce mun komai ba”.

“To bari na gaya miki yanzu da kaina, na yanke igiyoyin aurena biyu da suke kanki, ma’ana na sake ki Fattu saki biyu”

“Alhaji ka sake ni fa kace kuma har saki biyu? Uku fa kenan ko ka manta akwai daya daman?” Addah ta fada cikin ihu tana ja da baya hannunta aka, seda ya shiga motar ya danna lock kafin yace mata

“Ina sane Fattu na gaji da halinki na dade ina Addu’ar Allah ya yakice mun ke se yanzu ya karbi Addu’ata, zan ma aiko miki dashi a rubu ce saboda shaida” yana gama fada yaja motar sa Addah kuwa kamar sabon kamu ta bishi da gudu tana ihun ta shiga uku ta lalace.


*SODA COMMUNICATION📱💻📱
*CHEAPEST & RELIABLE DATA SERVICES*💃🏽💃🏽 with the validity of 30days at affordable price we are available 24/7 08137145294

*MTN DATA*
1GB@280✅
2GB@550✅
3GB@850✅
4GB@1150✅
5GB@ *1400* ✅
10GB@2800✅

*AIRTEL DATA*
1gb@320✅
2gb@640✅
3gb@950✅
5gb@1600✅

*Pay through👇🏽👇🏽*UNION BANK*
*0139814463
Khadija shehu soda*🥰🥰🥰we are always there at ur service. WhatsApp/Call📞08137145294🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 51

Seda motar Alhaji Murtala ta bacewa Addah kafin ta tsaya tana haki ta dora hannaye biyu akai tana rusa ihun ta shiga uku ta lalace

“Ni Murtala ze saka? Shekara Hamsin da aure ace zanyi zawarci gidan ubanwa yake so naje yanzu wallahi be isa ba, ban saku ba dole na koma” Addah ta ringa sambatu tana rusa kuka.

Anty Talatu ce ta ruqota suka shige gida tana cewa
“Se kace kanki aka fara saki ji yanda kika bishi da gudu kamar wata karya. To Fattu ai ya miki da kyau ma daya tsaya a iya sakin dan ni na dade ina hasaso miki haka a irin tashin hankalin da kika dade kina kwasowa bawan Allahn nan. Ni da ban kaini Jaye jaye bama aka sake ni bare ke? Kawai muje ki share guri ga daki nan na kusa da nawa ki shiga ki zauna Allah ya kiyaye na gaba”.

Kuka sosai Addah ta ringa sharba se kace qaramar yarinya. Anty Talatu tun tana bata haquri har abin ya bata haushi ta tashi qarshe ma ta fice gaba daya ta bar mata gidan ta tafi karbo zubin Adashen mutane dan ita uwar Adashe ce.

Se bayan Magriba ta dawo gidan, lokacin Addah tayi kukan ta dangana, dukda ba haqura tayi ba ta bari ne zuwa gobe da safe zata koma gidan ta idan Alhaji yaqi kuma zata bi Aminansa da yan uwa a saka baki dan bazata iya barin gidan nan ba.

Toh ta kama ina dan zaman ta da Talatu tasan ma ba me yuwuwa bane kawai dai zata zauna na dan lokaci kafin komai ya daidaita.

Tana kan sallaya bayan ta idar da sallar Isha Talatu ta shigo tana ta masifa akan matan sunqi bada zubi. A qofar daki ta zaune kan taburma, Addah ta leqo kamar wata me takaba murya duk ta dashe saboda kuka tace

“Talatu se yanzu? Tun dazu nake zuba ido na jiki shiru ga duhu seda wannan yarinyar ta dawo ta kunna mun fitila”

“Ba dole ki ganni yanzu ba Fattu, Mata saboda bala’i sun qi bada zubin Adashi ai basu isa ba, gobe dirar Asuba zan wa kowacce kafin mijintavya fita sedai ayi wacce za’ayi”.

Guri Addah ta samu kusa da ita ta zauna ta rafka uban tagumi, ga damuwar saki ga Yunwa tana sakadarta dan ita sam bata da jumurin Yunwa.

Shinkafa Talatu ta sake dora musu suka ci da miyar dazu kafin suka kwanta tana ta jan Addah da hira dan ta saki jikinta amma ina tayi shiru idan ka ganta bazaka ce wannan Addahr bace yar rigima.

Washe gari Asubanci tayi ta tafi gidansu Amirah, a qofar gida suka ci karo da Alhaji Murtala yana tsaye kamar daman jiran zuwanta yake yi kanta a qasa ta shiga gaishe shi ya dakatar da ita da cewa

“Lafiya Malama? Me kika zo yi mun a gida?”

Gaba daya yau se taga yayi mata wani kwarjini tsoronsa ma taji tanayi, murya a rarrabe tace masa

“Dama, am dama Alhaji kayan sawa ta nazo dauka”.

“Ki jira a nan, bari a kawo miki” ya fada yana shigewa ciki, ta yunqura zata bishi kafin ta shiga ya mayar da qofa tana ji ya kullo ta ciki se ta saki baki kawai tana kallonsa.

Tana nan tsaye kusan minti goma se gashi da Akwatu na biyu babba da qarami ya tura mata gabanta yana cewa

“Sauran idan kika samu gurin zama se ki sanar mun na saka a kwashe miki kayan dakinki dukka dukda dai da kudina kikayi su amma zan baki” ya sake shigewa gida ya bar Addah da ta qame saboda tsabar mamakinsa.

Murtala dai Murtalan da ko kara ta ajiye be isa ya tsakkake mata ba shine yayi mata wannan korat karen yau??

Almajirai tasaka suka daukar mata akwatunan nata, har tayi gaba ta tsayar dasu daidai gidan Sa’adah ta shiga buga mata qofa.

Sa’adah na tsaye da mijinta ta rakoshi ze fita sukaji ana buga get, shi yaje ya bude, yana ganin Addah ya tsugunna har qasa ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarsa Sa’adah na ciki ne a daidai lokacin da itama ta qaraso gurin, tana ganin Addah ta wani hade fuska, murya a daure ta ce mata

“Gani ya akayi?”
“Wace irin magana ce haka Sa’adah Addan kike cewa gaki ya akayi haka qatsal?” Mijinta ya fada yana kallon ta.

Seda ta harare su daga shi har Addan sannan tace
“To ba nemana take yi ba nace kuma gani ko da wani abu bayan wannan?”

Ze sake magana Addah tayi saurin dakatar dashi da cewa
“Aa babu komai, daman kudi nazo ki aramun zanyi tafiya idan yaso zan saka Amirah seta tura miki ta banki”

“Bani da su” Sa’adah ta fa mata kai tsaye tana juya wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login