Showing 153001 words to 156000 words out of 260321 words
Chapter 52 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
gama fadar haka na sake yin gaba da niyyar shiga gidan ba zato se ji nayi Bashir ya fincikoni ya watsa ni baya, takalmin qafata ya gurde na tafi zan fadi Allah ya taimakeni na durqushe ai kuwa ina dagowa banyi wata wata ba na sauke masa wani bahagon mari da ni kaina seda na aikata sannan na gane menayi.
Wallahi a lokacin mantawa nayi da Bashir ne a gabana, gani nayi tamkar wani random guy ne haka nan yayi mun wannan wulaqancin ni kuma zuciyata izani naga ta haka kadai zan rama abinda yayi mun se bayan danayi marin sanan na dawo hankalina amma se na aro dakiya na dorawa kaina na gyara tsayuwata sosai ina kallonsa nace
"Koda wasa karka sake yunqurin dora hannunka a jikina dan tuntuni ka haramtawa kanka hakan, sannan daga yau babu ruwanka da duk abinda ya shafeni, aurene tsakanina dakai kuma ya qare dan haka ina da yancin yin duk abinda naso ko shiga motar wanda naso ba tareda kai ko wani ya tuhumeni ba ka kiyaye" na dauki jakata da wayata da suka fadi na wuce shi zuciyata kuwa kamar ana kidan mandiri, seda naga na tura qofar na shiga be janyoni ya watsa mun marin daya fi wanda na masa ba sannan na sauke ajiyar zuciya ina share gumin dana hada a goshi.
BASHIR
Wata qara yaji "quuu" kamar gidan radio sun tashi daga aiki haka ya ringaji a kunnensa. Ba zafin marin ne ya sakashi suman tsaye ba Aa tsabar mamaki da tsoro ne wai shi, shindin dai ENGINEER BASHR AHAMAD yau Asma'u ta mara da yatsunta guda biyar kuma da gaske ido biyu ba magarki ba abun ya faru?
Harta gama surunta ta wuce kallonta kawai yakeyi, ji yakeyi dama ace wani ya tashe shi ya zaman mafarki yakeyi dan wannan abun beyi kama da wanda ze faru a gaske ba ace yau shi Ma'u ta daga hannu ta mara akan yana tuhumar waya kawota gida a mota sannan har take iya gaya masa aure ne ya hadasu kuma ya qare dan haka babu shi babu sabgarta, seda ta shige gida ta rufo qofa sannan ya motsa.
Ya waiwaya inda samarin dazu suke yaga basa nan, waya sani ma ko sun nadi abinda ya faru kafin suka wuce oho. Gaba daya kansa nema ya qulle ya rasa me ya kamata yayi, binta zeyi ya rama marin da tayi masa ko kuwa ci gaba zeyi da bin ba'asin wanda ya kawota? Kokuwa ya wuce gida ne ya qarasa cin uban waccen yarinyar da tayi masa jalof din taliya da kifi me qaya a matsayin abincin daren sa wai mema zeyi a ciki yanzu??
Harya juya kalaman ta suka sake dawo masa "karka sake yunqurin dora hannunka a jikina dan hakan ya haramta a gareka"
Se kawai ya fasa tafiya ya bi bayanta zuwa cikin gidan, dole ya dakatar da Ma'u daga wannan dogon mafarkin data shiga ya nuna mata cewa haryanzu igiyar auranta tana hannunsa.
A da yayi niyyar seta zaunu ta nemi sulhu dan kanta amma yaga alamar hakan gangancine, yau wani ya kawota gida harta daga hannu ta mareshi gobe kuma besan abinda zata sake aikatawa ba dan haka yabi bayanta dan ya katse mata duk wasu fukafukan rashin kunya data daura a jikinta.
ASMA'U
Turo qofar da akayi ce ta sakani waiwaya da saurin ina ja da baya dan nasan Bashir ne, seda na matsa ciki dakyau dan na cire takalmana daman na riqe qugu da hannu biyu kafin cikin tsiwa nace
"Wai meye kuma meka manta a gidan nan da zaka ringa shigomun duk sanda kaga dama gaskiya baze yuwuba, yara ne na baka abinka baka da sauran hujjar da zata ringa kawo ka cikin gidana dan haka yau ta zama rana ta qarshe da zaka sake sako wadannan qafafun naka anan" na qarasa maganar ina girgiza jiki kamar wata me fada da Sa'arta.
Da hannu ya nuna ni kafin ya nuna kansa yace
"Ni kika mara ko Ma'u? Ni kika mara saboda a matsayina na mijinki ina tuhumar ki wanda ya dakko ki a mota da aure na a kanki ya kawo ki gida shine kika daga hannu kika mare ni"
"Malam ka dai gyara kalaman ka tsohon mijina dai ko ka mantane saki biyu masu kyau ka hada ni dasu kaga kuwa yanzu ni matar me rabo ce, shima da ka gani Bazawarina ne yana cikin sababbin yan takara wanda Allah ya bawa sa'a shi ze dauka..."
"Ya isheki Ma'u" ya dakamun tsaqar data sakani yin shirun dole ina sake matsawa cikin palour dakyau saboda gudun kota kwana. A fili nake ganin harzuqar da yayi da tsananin bacin ransa wanda ko dazu dana mareshi banga hakan ba.
"Qarya kike yi ke tawa ce kuma dan ni kadai aka halicce ki, Wallahi kika sake danganta kanki da wani Namiji Ma'u se na miki abinda baki zata ba" Bashir ya fada cikin daga murya da har seda Faridah da Amna suka fito daga cikin dakinsu amma kallo daya ya musu suka maida qofar garam suka kulle.
"Saboda na sake ki ne yasa kika samu lasisin da zaki ringa yawo a gari maza suna daukar ki a mota ko kin manta da cewa har yanzu kina cikin iddar aurena, to kici gaba da yin duk abinda kikaga ya dace dani dame mu zuba mu gani wanda zeci riba, amma ki tabbatr duk dan iskan da na sake ganinki dashi se munyi shari'a".
"Kayi shari'a dasu awanne dalili Bashir saboda sunyi maka me" na fada ina binsa da kallon sama da qasa, ba abinda ya bani dariya irin daya ce wai ina cikin iddar auransa.
"Saboda sun tsaya da mata ta alhalinbata gama iddah taba" ya bani amsa yana kallona. Seda nayi dariya kafin na dauki jakata ana ajiye na bude na zaro takardar Asibiti ta shedar barin da nayi, daman yau nayu niyyar tura masa da ita dan jiya Goggo ta sake kira ta jaddadamun na sanar masa gudun rigima.
Takardar na miqa masa ina cewa" Bashir nida kai fa Allah ya raba tsakani, gashinan ka gani da idonka tun wuri ka goge wannan tunanin na wata iddah daga zuciyarka dan tuni Allah ya yaye mun.
BASHIR
A mugun kidime ya daga kai ya kalli Asma'u bayan daya karanta abinda a ka rubuta a jikin takardar, kalmar Abortion' (Abortion itace medical term na bari ba Miscarriage ba 😨 kar yan uwansu Addah suce Ma'u ta zubar da ciki 😂😂) din da kawai ya gani ya saka wata zufa ta shiga tsatstsafo masa gaba daya ma se yaji iskar gurin tayi masa kadan se ya shiga fifita da takardar hannunsa yana cewa
"Ma'u ki gaya mun gaskiya tsakaninki da Allah bari kikayi dagaske ko wasa kikeyi".
"Lallai Bashir, kaga alamar wasa anan gurin ne ko kuwa, baqin cikin ka ya saka shima cikin yaga baze iya zama ba ya kama gabansa ka kalli date din dakyau ka gani in yaso seka hada sadakar uku data bakwai duk kayiwa Yar dan inaga ma macece" na fada irin ko a jikin nan nawa amma can qasan zuciyata ina jin zafin rasa aurena da cikina da nayi.
"Wallahi Ma'u na mayar dake, na maida auran mu fada miki ne kawai banyi ba" Bashir ya fada cikin yanayin da yake bayyanar da tashin hankali da yake ciki, ni kaina a kidime na kalle shi, duk yanda nake son Bashir nake qaunar zama dashi se naji hankalina ya mugun tashi da jin kalamansa na wai ya mayar dani, a rude nace masa
"Yaushe ka mayar dani Bashir yaushe ka yi hakan kuma wanene shedar ka"
"Tun ranar da na karbi su Aliyu a daren na qudurce a raina na mayar dake amma ban gayawa kowa ba" ya sake fada ya na matso inda nake, senaja baya da sauri ina sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya nace
"Idan ma ka mayar dani ban komu ba Bashir tunda baka gayamun ba kuma baka gayawa kowa ya zamar maka shaida ba sannan ni a washe garin ranar daka sake ni Bashir a ranar nayi bari ka duba daye din da yake jikin takardar nan idan ma baka yadda ba kaje clinic din da kanka zasu tabbatar maka.
Dan haka tsakanina dakai yanzu be wuce zumunchi irin na wadansu da wani abu ya taba hadasu ba shima albarkacin zuri'ar da take tsakanina dakai, bayan wannan ka qaddara Bashir baka da wata alaqa dani a rayuwa ba ka kuma da hutumij da zakayi mun katsalandan a rayuwa.
Mun rabu rabuwa ta har abada ka gogeni daga cikin lissafin rayuwarka dukda nasan ka dade dayij hakan" shiru nayi da maganar da nakeyi jin kuka yana neman kufce mun, bana buqatar na karaya a gaban Bashir balantana har yayi tunanin akwai sauran burbushin soyayyarvsa a zuciyata.
"Asma'u karki ce haka, ta yaya kike zaton alaqar mu zata yanke kema kinsan wannan bame yuwu ba bane, muje a kinyi barin na yarda kin fita iddah amma ai da sauran igiyar auran mu ko yanzu zamu iya zuwa Limamin masallacin can ya mayar mana da aure nasan ko Engineer Abdullahi ze yi miki walicci ni kuwa na isa na karbarwa kaina aure, dan Allah mubar maganar nan Ma'u bazan iya ba, bazan juri ganinki tare da wani mutum ba zuciyata zata fashe" Bashir ya fada yana sake damqe takardar dana bashi.
Tsaki nayi dan naga abin nasa ma tsagwaron rainin hankali ne dan haka na kalleshi nace
"Bashir fita zamu rufe gida"
"Naji zan fita amma ki gayamun kin yarda za'a mayar mana da aure ko gobe ne tunda yanzu dare yayi, na sani Ma'u kina sona bazaki taba iya rayuwa babu ni ba dan haka mu manta da komai mu koma wa auran mu kinji Ma'u".
"Bashir kenan, wato kasan ina sonka bazan taba rayuwa babu kai ba ko ashe tunanin ka kenan shiyasa ka ringa garani kamar kwallo baka san qima taba bare daraja, ka auro muj qanwar bayana da nagama shan wahala akanta sannan ka fifita ta sama dani daga qarshe a dalilinta ka hada ni da saki ka rabani da yayana ko duk saboda kana tunanin ina sonka bazan iya rayuwa babu kai ba tunda tare aka daure ruhinmu aka jefi cikij duniya ko?
To bari kaji, ka qaddara kaine numfashina kasan dai idan babu shi babu rayuwa ko? To dana koma zama dakai Bashir na zabi na mutu akan ka, idan sonka shine Ajalina to ka je ka fara irga kwanakin da suka ragemun dan wallahi Bashir na gama auranka na gama zama dakai ko kaine autan maza sedai na mutu ban sake aure ba, mugu me saka soyayya da qiyayya wanda be dauki dan Adam a bakin komai ba" na qarasa maganar kuka yana kwace mun sena shige dakina na bar Bashir da yake jinsa kamar an sare masa qafafu tsabar yanda jikinsa yayi sanyi.
Kuka na ringayi kamar zan shide, Allah ya sani ina son Bashir na kuma san har duniya ta nade da bazan dena sonsa ba amma in Allah ya yarda ko zan mutu na haqura dashi.
Bani Bashir yake so ba, alfarma yayi mun ya zauna dani tsahon shekarun nan saboda ina son sa badan shi a qashin kansa yana sona ba.
Meyasa ban taba gane hakan ba se a yanzu, me yasa tuntuni nake daukar kalaman yaudarar sa a matsayin so ashe duk na ya cimma wata manufa ne yanzu daya gama samun yanda yake so a rayuwa gashi nan ya fito mun sak a halayyarsa ta gaskiya.
Hannayena na daga sama ina kukan nace
"Allah kaine shaidata naso Bashir saboda kai badan wani abu ba kamar yanda kayi mana umarni da mu so mutum dan Allah sannan na kyautata masa da dukkan iyakar iyawata a zaman aurena dashi, Allah kagani halin dana shiga Ubangiji na roqeka kayi mun sakayya da mafificin Alkhairinsa, idan kuma bani da rabon samun farin cikin Namiji a rayuwata Allah ka sanya mun dangana har zuwa ranar dazan koma gare ka" na shafa Addu'ata kafin na shige goge hawayen fuskata amma sun kasa tsayawa, haka na shiga bandaki, ina wanka ina kukan harna gama na dauro alwala nayi sallar magriba da Isha.
Ina kam abin sallar ina ci gaba da kaiwa Allah kukana anan bacci yayi awon gaba dani ban ma sani ba.
BASHIR
Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida yana shiga ya zube akan kujera yana sakin numfashi a jere a jere tamkar wanda yayi gudun kilomita goma. Gidan shiru da alama duk sun kwanta yaran haka Amiraj beji motsinta ba daman tunda ya dawo dazu ta bashi shirmen abincin data dafa yayi mata tijara ta shige daki baya tunanin ta sake fitowa hakan ma dadi yayi masa dan tabbas idan sukayi ido hudu da ita a yanzu dai a yanda yake jinsa din nan to komai yana iya faruwa.
A daddafe ya tashi ya shige dakinsa yana jin yanda kansa yake juya masa kamar an kunna fanka ga wani abu me maiqo da yake taso masa kamar zeyi amai haka ya zauna a qasa gefeb gadonsa ya hada kai da guiwa ya rasa ina ze kama abin duniya ya hadu yayi masa yawa
"Dana koma gidanka na zabi na mutu, idan sonka shine ajalina Bashir kaje ka fara irga kwanakin mutuwata dan na gama auren ka" kalam Ma'u suka ringa masa tilawa a kwakwalwa.
"Allah karka jarabce ni da wannan, Allah ka sani bazan iya dauka ba, nayi kuskure Allah dan darajar Annabinka Muhammad SAW kayi mun sassauci karkasa wannan ya zamo mun qaddadar da bazan iya dauka ba Allah karka rabani da Asma'u" sambatun da ya ringayi kenan shikadai kamar zararre, wayarsa ya zaro faga aljihu ya fara laluban numbobi, waze kira ya gayawa damuwarsa? Waye ze bashi sharar yabda ze gyara wannan kuskuren tun kafin dare yayi masa.
"Bala" hannunsa ya tsaya akai, ba bata lokaci kuwa ya dannan masa kira cikin Sa'a bugu biyu Balan ya daga yana cewa
"Engineer Mijin Asma'u, na Amirah ko dubu ta taru"
"Bala akwai matsala, ina cikin masifa ina cikin tashin hankali ka taimaka mun ka gaya mun yaya zanyi na fita wallahi zan iya rasa raina Bala akan wannan tashin hankalin" Bashir din ya katse Bala kamar ze fashe da kuka ko da yake tuni ma ya fara na zuciya kawai dai hawayen ne suka qi fitowa a fili".
"Subhanallahi Bashir meya faru badai korar ka akayi daga gurin aiki ba?"Bala ya fada
"Wallahi gara na rasa aikina Bala, gara na bayar da komai dana mallaka a rayuwa ta da abinda nake shirin rasawa"
"To menene meyake faruwa kayi mun bayani yanda zan fuskanta se musan ya zamu kamo bakin zare wane abune haka daya fi dukiya muhimmanci a gurinka Bashir?" Bala ya sake tambayarsa a tsorace dan gaba daya kalaman Bashir din firgita shi sukayi.
"Asma'u, itace Bala, Ma'u tafi mun komai zan kuma iya bada duk abinda na mallaka akan fansar ta, Zan iya bada raina akan Ma'u ka sani Bala" Bashir ya fada dakyar dan qirjinsa ya fara yi masa nauyi, wani irin zafi zuciyarsa take masa kamar wadda ake watsawa ruwan zafi, Tsakin da Bala yayi ne ya katse masa tunani kafin Balan ya ci gaba da cewa
"To me Ma'un tayi maka yau kuma yanzu? Kai wai kullum baka da aiki sena kawo qarar Ma'u ne haba ni wallahi na gaji da jin Ma'u tayi Ma'u tace idan ka gaji ka saketa kawai kowa ma ya huta mana".
"Bala na saki Ma'u shine Bala'in da nake ciki a yanzu ta gama iddah kafin na mayar da ita kuma tace bazat sake komawa gida na ba ta gama aure na" Bashir ya fada kamar ze fashe da kuka.
"Kace ka saki Ma'u harta gama Iddah Bashir" Bala ya tambaye shi da son tabbatar da daidai yaji ko kuwa kunnensa ne yajiyo masa abinda ya dade yana fatan faruwarsa.
"Dagaske nake Bala na saki Ma'u saki biyu kuma tayi bari a washe garin ranar dana saketa kaga kenan iddarta ta ciki ka gayamun ya zanyi na shawo kanta ta haqura mu koma auran mu wallahi ina son matata idan na rasata zan iya mutuwa ka sani Bala" Bashir ya sake fada a matuqar raunane.
Bala kuwa seda yayi matuqar qoqari gurin danne farin cikinsa kafin ya aro damuwar qarya ya saka a muryarsa yace
"Ashsha Mutumina ya akayi haka a garin yaya? Amma dai koma yayane aikin gama ya gama yanzu sedai nemi mafita kuma ayi fatan Allah ya kiyaye na gaba.
Kana ji ko ni nasan Ma'u duk fushin da zatayi ba wani me yawa bane kasan irin son da takeyi maka, dan lokaci kawai zaka bata dakanta idan ta sakko zata nemeka ku daidaita kaima kasan duk abinda zata fada buyagine kawai amma Ma'u bazata iya rayuwa babu kaiba kowa ya shaida hakan"haka Bala ya cigaba da dorashi a keken bera har seda ya yarda kafij sukayi sallama.
Suna kashewa kuwa Bala ya daka tsalle yana cewa
"Allah na gode maka, badai kai wawa bane ka raina ni'imar da Allah yayi maka zaka gabe kurenka wallahi muje zuwa yanzu aka fara wasan Ma'u kuwa nasan bazan same ta ba amma tunda kaima ka rasa ko haka aka tashi wasa nayi nasara kuma in sha Allahu bazat taba dawo maka ba".
Allah sarki Bashir shi kuwa Sosai kalaman Balan suka kwantar masa da hankali dukda wani bangare na zuciyarsa yana so yaqi karban hakan dan a yanayin da Ma'u ta nuna tabbas yaga chanje chanje da yawa a gareta yana kuma jin gaskiya ta fada a maganganunta amma yasan so ba qarya ba, ba kuma ya zaton Ma'u zata taba tsanar sa a rayuwa ta bakin Balan zafin abinda ya mata ne ya sakata fadar duk wasu maganganu amma idan ya bata lokaci ta huce yasan zasu daidaita.
Da wannan ya lallashi kansa ya koma kan gado ya qudundune yana so ya manta maganganunta amma ya kasa ga wani irin tsoro da tashin hankali dayake shigarsa a duk sanda ya tuna kalaman ta na dazu har wani zazzabi yaji yana neman kama shi.
Anya ze iya bin shawarar Bala na ya bata lokaci harta huce dan kanta? Ya lura idan mafa fushin tayi ba kadan bane dazu fa har mari yasha, kai ina baze tsaya ya zuba ido yana kallo kwado ya masa qafa ba, a wannan gabar dole ya ajiye girman