Showing 123001 words to 126000 words out of 260321 words

Chapter 42 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42705

sha biyu na rana na fito daga dakin Bashir bayan na gama ramuwar bacci gidan shiru se Amirah kadai a zaune a palour tana sana’arta ta kallon Indian series yan biyu suna gidan Dada an kaisu yaye kusan sati biyu kenan ba’a dawo dasu ba. Dagowa tayi da murmushi tana kallona tace

“Sannu Anty se yanzu kika tashi”
“Yawwa Amirah sannu da gida, me kuka rage yunwa nakeji wallahi” na fada ina zama a gefenta.
“Na dai feraye miki dankali bari na soya” ta fada tana miqewa, mintina kadan ta soyo dankalin harda kwai ta kawo mun nasa ta hado mun shayi na zauna na fara ci”.

“Ai dole kisha Baccin Gajiya Anty irin wannan gurza da kika sha a hannun Yaya jiya kai, gaskiya Anty dole ki shirya ni idan zanyi aure yanda nima zan rikita shi ya ringa sambatu irin na Yaya...”

Kwarewar da nayi da shayin dana kurba tsabar kidimar jin magangan ta suka sa tayi shiru ta miqo mun ruwa tana yi mun sannu. Kallonta kawai na ringayi zuciyata tana luguden duka a raina ina ta maimaita “Hasbunallahu wani’imal wakeel”.

“Dagaske Amirah taji mu’amalar mu da Bashir? Tun yaushe hakan ya fara sannan ita kadaice ko har sauran yaran ma duk suna ji?” Tambayoyin da nayiwa kaina kenan dana rasa me bani amsar su, tabbas wannan dalilin shine silar rainin da naga Amirah tayi mun shi a yanzu har ma da Bashir din kansa ashe a banza take kallon mu amma ta ina ko ta yaya taji? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Ganin da tayi na dena tarin ba tareda damuwa ko tunanin komai ba taci gaba da magana tana cewa
“Wallahi Anty kum....”

“Rufe mun baki Amirah” na fada cikin tsananin bacin ran da fuskata da muryata suka nuna kafin na ci gaba da cewa

“Ashe baki da hankali ban sani ba? Saboda tsabar rashin mutunchi da rashin kunya har ki iya tsayawa kina maimaita wadannan maganganun a gaba na sa’arki na zama, wallahi se na yi mugun saba miki” na qarasa ina huci bayan dana ture kayan abincin gaba na dan gaba daya komai ya fice daga raina ita kuma sum sum ta tashi daga gurin ta shige dakinsu.

Wannan abun kunya har ina, tabbas Bashir irin mazan da basa iya rufe bakinsu ne a lokacin da yake mu’amalar aure amma ban dauka ihun nasa har yana karade gida da Amirah zata iya jiyo wa ba musamman idan ka duba tazarar da ke tsakanin dakin sa da inda nasu dakin yake dama dai a dakina ne ana jiyo duk motsin da akeyi a dakin Bashir.

Haka na wuni cikin rashin sukunin zuciya dan Amirah tuni ta fice ta tafi gidan Addah ina nan sukuku har yara suka taso daga makaranta su kansu seda suka gane bana jin dadi.

Da magriba muna Kitchen da Amna ina girki tana dan tayani da wasu abubuwan, tun tuni nake saqawa a zuciyata na tuntubeta da dabara naji ko suma suna jin wani abun ina ta fargabar amsar da zan samu tunda dai daki daya suke kwana, me nauyin bacci ma taji bare amma da sam bata da nauyin bacci amma kuma ya zama dole na tambayeta kodan nasan matakin da zan dauka saboda tarbiyyar su, ina ta hiqilo akai kar naje tufka nakeyi ta baya tana warwarewa.

Gundumbala nayi nace “Amnah, ni kuwa jiya kinji wani motsi ko maganganu a gidan nan da daddare?”

Seta dago daga yankan Albasar da takeyi tace “motsi kuma Mami gaskiya ban ji komai ba in banda karatun da kika kunna a Mp gurin qarfe uku ma dana tashi zanyi fitsari shine naji ya mutu na fito na duba ashe chaji ne ya qare na jona kuma dai banji komai ba wallahi”.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi kafin na sake cewa “Ni kuwa se na ringa jin kamar ana hayaniya da daddare bama iya jiya ba, duk sanda Abin ku yake gari ina ji ta windon dakinsa kuma dana tambayi Amirah ma se tace mun itama tana ji”.

“Toh Mami qila daga qidan su Faisal ne (maqotan mu ta gefen da dakin Bashir yake) kin san suna da yawa kuma Raliya tace suna kaiwa har qarfe uku wataran basuyi bacci ba suna kallo musamman weekend, Anty Amirah kuma daman ai a dakin ki take kwana itama kinga zata ringa ji”.

“A dakina take kwana kuma?” Na tambayi Amna da mamaki, seta daga kai Alamar da gaske tace

“Eh mana Mami bake kika ce ta ringa kwana a can ba duk sanda Abbi yake gari wai kince idan ana barin daki babu kowa Aljanu suna kwana a ciki shiyasa duk sanda zaki kwana a dakin Abbi to ita kuma a dakin ki take kwana se da Asuba take dawowa nan”.

“Lallai watan cin kutumar uban Amirah ya kama” na raya a zuciyata. Ban taba sanin yar is kar yarinya bace mara mutunchi se yau, daman dakina take zuwa ta kwanta tayi mana labe kenan saboda taji abinda muke tabbas kuwa a yau ba se gobe ba seta bar gidan nan wallahi.

Muna cin abinci ta shigo gidan sadaf sadaf kamar munafuka se tayi turus da ganina a zaune dan nasan hasashenta ina daki saboda idan na idar da sallar Isha se nayi shafa’i da wutri na danyi lazumi na kafin nake futuwa palour yau din kuma da magribar nan Period yazo mun.

Kallonta nayi daga sama har qasa a fili na ce “kan uban nan” ina miqewa tsaye sosai na qare mata kallo, Kayana ne a jikinta, Wata Atamface falle biyu na siya saboda kyan da tayi mun akayi mun fitted straight gown dikin yaqi shigata saboda ya matse, tunda ta gani take nacin na bar mata ni kuma naqi saboda ina son Atamfar kuma na nema tsaf an rasa samun wata se plain yadi tailor ya siya yace ze gyara mun dinkin shine taje ta dauka ban sani ba dan da zata fita ma Hijabi ta saka har qasa ban ga kayan jikin ta ba.

Irin kallon da nake jifan ta dashi ya sakata qarasowa tana cewa “Dan girman Allah Mami kiyi haquri wallahi dan Allah...” tas na kwasheta da Mari kafin na nuna mata qofar dakin su cikin kaushin murya nace

“Minti goma na baki ki shiga ki cire mun kaya ki kuma tattara yanaki ki wuce gida yanzun nan dan bazan sake zama dake ba tunda baki da tarbiyya”.

Kuka ta saka mun tana tambayata wai me tayi dan Allah nayi haquri na sake jaddada mata wallahi seta bar gidan nan a yau, tunda har take yi mana labe wata rana kuma ai leqa mu zatayi idan ba’ayi sa’a ba haka ta tattara a daren ta wuce gida tana fita muka kulle gida na kuma kashe wayata dan na tabbatar idan Addah bata biyo sahu ba toh kuwa zata kira waya.

Washe gari kuwa qarfe bakwai da rabi A gidan tayiwa Addah, mun fito zan kai yara makaranta naji ana dukan Get, Musbahu yaron shagona yaje ya bude se gata kamar an wullota ta hau tijara da diban Albarka akan me zan korar mata ya ita da gidan dan uwanta.

“Gata nan ai a gaban ki ki tambayeta me tayi mun” na fada ina kunna mota, ina ji tana ta zuba rashin darajar ta nayi banza dasu na zuba yara a mota, dai dai zan fita naji tana cewa

“Wallahi baki isa ba Asma’u, baki isa kice me kadai zaki mallake Bashir da dukiyarsa ba se Amirah ta dawo cikin gidan nan kuma a lokacin baki isa ke koreta ba” nidai nayi zooming na fice na barta a tsaye tana kumfar baki.

Dariya ma ta bani wai na mallake Bashir da dukiyarsa nayi me dasu, su kudi suka dama da har suke ganin ya tara wata tsiya dab dai ni har yanzu ina masa Kallon Bashir din dana sani me tun bashi da komai, idan ma ba haka ba babu wanda ya tayani shan wahalar sa a cikin su idan ma nace zan mallake shi ni kadai ai banyi laifi ba ko.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 38

Se bayan dana kai yaran na dawo sannan na kunna wayata, kiran Dada ne ya fara shigowa na daga na gaishe ta daga yanda ta amsa nasan labari ya isarmata kenan.

"Akan me zaki kori Amirah daga gidan Bashir Ma'u" ta fada bayan da muka gaisa.

Lallai wato gidan Bashir tana gaya mun ba gidana bane kenan, murmushi nayi, babu kunya tiryan tiryan na karanta mata abinda ya faru da duk abinda Amiran ta fada mun dama sauran abubuwan da takeyi a cikin gidantsaf seda na tsara mata.

Seda tayi jum da na tabbatar na kunya ne kafin tace "To ai koma menene be kamata ki koreta ba haka da se kija mata kunne ko ki kawo mana qararta mu se mu tsawatar mata, yanzu dai se kuyi haquri ta dawo kuci gaba da zama Allah ya kiyaye gaba".

"Wallahi Dada bazan sake zama da Amirah a gidan nan ba, ta koma gidansu idan auranta ya tashi bazan fasa yi mata duk abinda idan a hannuna take zanyi ba amma fa ba dai gidan nan ba" na fada kai tsaye dan ganin ana nema ayi mun fin qarfi, ita bataga illar abinda tayi ba kenan har ake cewa nayi haquri ta dawo to kuwa baze sabu ba.

Muna gama waya na kira Bashir na kora masa jawabi dan tun a jiya da daren nake ta neman wayar sa ban samu ba se text message na bar masa. Yanzun kuwa yana amsawa na kora masa abinda yasa nace ta tafin, zuwan Addah harma da wayar da mukayi da Dada.

"Wallahi bazan sake zama da yarinyar nan ba kama gaya musu"

"Daman ai ke kika gayyato ta gidan tun farko ai ni meye nawa a ciki?" Bashir ya fada.

Bansan dai ya suka qarke ba a batun Amirah kwanaki kadan tsakani ya tayar da maganar komawar mu Lagos dan ya samu gida babba da ze wadace mu. Nayi zaton za'a samu matsala dasu Dada saboda kes din Amiraj da mukayi amma se naji shiru haka muka fara shirye shiryen dan a lokacin ana Third term ne har yara sun fara shirin jarabawa, daga sun gama zamu tafi se a saka su sabuwar makaranta su koma sabon session.

Lokacin da zamu tafi gida gida nabi duk nayiwa kowa Sallama har gidan Addah naje muka rabu faran faran tana cewa se sunzo dan tana son zuwa Lagos in muka nutsu zata zo tayi mana sati har bakin ruwa se an kaita nace Allah ya nuna mana lokacin ta hada mana tsarabar kayan qamshi da su daddawa harda man Shanu ga dambun nama da tayiwa Jafar dan shine mutumin ta.

Haka muka tattara muka koma Ikko, gidan da Bashir ya samu babban gida ne me kyau yana cikin rukunin gidajen manyan ma'aikatan su.
Flat ne me dauke da manyan dakuna guda biyu se madaidaita suma biyu ko wanne kuma da Bandaki a cikin sa, ga qaton palour da Gurin Dining, Kitchen, store sannan ta bayan gidan da akwai babban fili da akayiwa  shuke shuke daga gefe akayi garden.

Gida dai masha Allah kuma Bashir ya saka komai na buqata a ciki. Se da nayi dagaske kafin na iya daure kewar gida na saba da garin, dan ma nayi sa'ar maqociya wadda take matar Ogan Bashir ce Anty Halima mutuniyar kirki, ita ta qara wayar mun kai da zaman Lagos na gane kan kasuwa ya zaman ina sarar kaya na turo dasu ko ina kake so a fadin Nigeria.


Kamar wasa naga tallan daukar ma'aikata na wani kamfani da suke hadahadar ma'adanan qasa anan Lagos, a lokacin na cewa Bashir zan cike ya kuma bani goyon baya na nemi aiki cikin ikon Allah se kuwa na samu suka daukeni matsayin meyi musu tallace tallace.

Na kama aiki ba dadewa wata rana kwasam muka samu baquncin Addah, Dada harda Amirah. Sosai mukaji dadin zuwan su dan baka gane dadin gida se randa kayi nesa da yan uwanka kwanan su hudu Addah da Dada suka juya aka bar Amirah da alokacin wai an saka ranar auranta da wani yaro Bashir shima sunansa dan Abokin babban su Bayan sallahr Azumi da sati daya.

Dalilin kawota kuwa saboda acewarsu na koya mata yan abubuwan da ya kamata ta iya, nayi dariya kuwa nace duk abinda bata koya ba a zaman kusan shekara goma da mukayi tare banajin zata iyashi a watanni biyu kacal, haka dai suka tafi suka barmu na kuwa dage tsakani na da Allah ina dora yarinyar nan akan hanya ta hanyar nusar da ita komai.

Tunda tazo sau daya Saurayin nata Bashir yazo da yake anan Lagos shima yake zama, nidai itin yanda naga yana ta dari dari da ita bayan ya tafi na kasa shiru seda nayi mata magana nace

"Wai ni Amirah hada ku akayi da Bashir ne?"
"Aa Me kika gani Anty?"
"Gani nayi yanda yaqi sakewa dazu da yazo musamman tunda Baban Ali ya dawo jikinsa fa har wani rawa ya ringayi".

Dariya tayi tace "haka fa yake Anty ni wallahi har tunanin yanda ma zamu zauna dashi nakeyi, nida nake son na samu miji mu sha soyayya irin taku da Yaya shi yasa fa na samo me irin sunan sa ma. Nidai ki taimaka mun Anty ki koya mun duk irin abubuwan da kikeyi nima na zama star".

Hade rai nayi, na fuskanci Amirah dai se gyaran Allah sauqin ta dai za'a mata auran taje ta qarata in huta, haka muka ci gaba da zama ina koya mata duk wasu abubuwa daya kamata macen data san kanta ta iya su.

Bilhaqqi nake bata sirrika da kuma gyara tamkar yanda zanwa qanwata ciki daya kafin cikar wata daya kuwa ta fara hawa saiti dayake ita ta saka kanta hatta girki yanzu tana qoqari sosai dama abun nata harda qyuiya da qyashi suke hanata tayi a lokacin baya yanzu da yake a rajin kanta ne wani lokacin kafin na taso daga aiki ma ta gama abinci, gyaran gidane dai se a slow, zata ci kwalliya amma gurin da zata zauna be dameta ba.

Tsakanin ta da Bashir dai bana ce komai ba dan daga gaisuwa wata magana bata qara hadasu idan yana zaune ma bata fitowa tana daki tana chatting din daya zamar musu dabi'a yanzu daga ita har Bashir dan shima yanzu muna zaune bini bini yana danne dannen waya wani lokacin kuma se naga ya zauna yayi shiru kawai kamar akwai abin da yake damun sa dan inbanyi qarya ba se nace har rama yayi amma se na ta'allaqa hakan qila da yanayin aiki, a haka muka shiga watan Azumi wanda ya rage saura sati biyar bikin Amirah kenan.

Ranar da aka kai Azumi na uku bayan ansha ruwa Addah ta kirani take gayamun sunje ganin gidan Amirah.

"Gidan yar taki yayi kyau Ma'u sena kin gani daki uku mijin ya bata da palour se ku yunquro dan kinsan gidan kishiya ne dole ki gwangwaje yar taki".

"Gidan kishiya kuma Addah dama Bashir din ya taba aure ne" na fada da mamakin maganar tata, se ta shiga in da in da tana cewa
"Au Faccala nake so nace miki, gidan su daya da matar wansa wannan kishin ai har yafi na kishiyoyi zafi, zan saka a turo miki da kudaden da Babanta ya bayar a siyi gado dana gurina da za'ayi mata kayan Kitchen tunda ai kece uwarta".

"Hakane kuwa to Allah ya sanya Alkahiri ya nuna mana lokaci babu damuwa, a turo din kinsan daman kaya anan sunfi kyau da Sauqi se mu siya a kawo kawai" daga haka mukayi sallama Allah a raina naji dadin karamcin da akayi mun aka dorani akan har kar bikin.

Haka na tasa Bashir da nacin se ya siya mata gado daya se a hada da na gurin Babanta biyu kenan daki dayan in mijin yaso se ya gyara abinsa amma Bashir ya dage akan shi bazeyi ba bashida kudi saboda a sannan gini yakeyi, ya rushe gidan mu na Gombe ya siyi filin kusada mu an qara ana mana sabon gini kuma daga yanayin plan din nasan dole zeci kudi.

Dana takurashi daga qashe yace dubu dari yayi niyar bada gudummawa nace sunyi kadan gadon nan fa dole shi ze siya mata haka dai ya haqura daga qarshe ya yarda yace na ranta masa kudin muka siya mata gado me kyau dan dubai a sannan ma dubu dari hudu muka siye shi irin nawa dana siya na chanza na dakina na mayar da na ciki dakin su Amna.

Hidimar da nayi ta kayan auran Amirah ko bikin Farida nake yi se haka dan wallahi bazan iya lissafa nawa na kashe mata ba a kayan Kitchen Anty Halima har fada ta ringa yi mun tace dangin miji nakeyiwa wannan hidimar a maimakon nayi musu gwaninta qarshe baki zan janyowa kaina suce da kudin dan uwansu nake wadaqa amma na toshe kunnena nayi mata.

Haka na tattara kaya rankatakaf aka kwasa a mota aka kai Gombe sannan muka ci gaba da gyaran Amarya kuma da shirin biki dan har dinkunan ta duk nan aka kawo na bawa sabon tailor da nayi ya yi mata dinkuna na daukar magana biki kawai muke jira.

Randa aka kai azumi na Ashirin da biyu Bashir yazo mun da Albishir din ya biya mana Umarah nida Yara Gaba daya kuma wai a gobe zamu tashi abin ne da kamar baze yuwu ba shiyasa be gayamun ba se yau da safe sannan komai ya kammala.

Nayi murna kuma banyi ba. Murnar da nayi ta tafiya Umarar ce da kuma yarana dukka gaba daya abinda na dade ina mafarkin yi inda naji rashin dadi kuma ba tare da Bashir zamu tafi ba dukda sati biyu zamuyi dakyar idan tarar da bikin Amirah qila ranar da aka gama zamu dawo amma.

Haka muka tashi hada kaya a daren dan ma tashin namu bana safe bane, ta waya na kira gida mukayi musu sallama washe gari tun safe Amirah ta fara tafiya Gombe, harda kukanta wai bana nan za'ayi biki gaskiya zataje ta cewa su Addah a qara sati se na dawo haka na rarrasheta ta tafi, mun samu delay najirgi dan haka se qarfe 7 na Magriba muma muka tashi zuwa qasa me tsarki muka bar Bashir shi kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login