Showing 174001 words to 177000 words out of 260321 words

Chapter 59 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42694

cirko cirko suna kallonsu dan duk abinda ta ke fada sunji saboda ba a hankali take magana ba.

Daman sun san da qishin qishin din maganar yanzu gashi sun tabbatar suna fita kuwa Binta da tafi kowa tsugudidi ta shige daki ta dauki wayarta ta kira Alhaji Murtala.

Yana zaune a kasuwa a daidai lokacin wani Amininsa Alhaji Yero ya same shi da maganar cikin Ummi daya ji a bakin Matansa.

Hankalin Alhaji Murtala yayi qololuwar tashi da jij maganar wata irin tsanar Addah yaji tana saukar masa shidai tunda ya auri Fatu bazece ga wani abun Alkahiri daya same shi ta dalilin ta ba a kullum cikin jefa shi a masifu kala kala take.

Kiran wayar Binta na shiga ya daga, ba maganar gaisuwa ta shiga rattaba masa cewa
"Alhaji ka kira Addah duk inda take ta dauki Ummi tana kuka da komai sun tafi tackaita a zubar da ciki kar yarinyar nan ta mutu mu shiga uku ka kirata ka dakatar da ita".

Wata zufa yaji tana sakko masa, kiran wayar Addah ya shigayi tana ringing amma bata dagawa seda ya kirata sau goma a na sha daya ta kashe wayar. Babbar rigarsa ya cire saboda yanda yaji tana neman shaqeshi ya ringa safa da marwa a cikin shagonsa yana ayya na irin wulaqancin da zeyiwa Fattu a wannan karon, tabbas yakai bango kuma dole ya dauki matakin da ze shigar da ita hankalinta.

Wayar Amirah ya shiga kira ringing biyu ta daga tana gaishe shi, be amsa mata ba cikin kakkausar murya yace mata

"Ki kira uwarku ki gaya mata wallahi idan wani abu ya samu Ummi a sanadiyyar zubar da cikin data tafi kaita se na daureta dauri har qarshen rayuwarta sannan ki gaya mata daga inda ta tafi karta dawo mun gidana na saketa saki biyu" yana gama fada matan ya kashe wayar sa.

Sosai zuciyarsa take tafarfasa, Addu'arsa Allah yasa kar wani abu ya samu Ummin dan wallahi bega wanda ze hana shi shari'a da Fattu ba.

Hajia Addah kuwa Napep suka haye se gidan Hajia Balaraba suna tafe a hanya tana surfawa Ummi zagi har suka isa.

Ta tarar da Hajia Balaraba tana wanka dan haka suka zauna a palour suna jiranta ba adauki lokaci ba kuwa se gata ta fito daga dakinta a kallo daya Addah ta hango irin yanda tayi sanyi laqwas kamar ba Balaraban data sani ba mace me izza da taqama.

"Aa Fattu kece yau a gidan namu yaushe rabo" Balaraba ta fada tana zama akan kujera, se Addah ta tabe baki kafin tace

"Zaki fadi haka mana tunda kin samu yanda kike so kij watsar dani bayan da kika kaini gidan dan damfara ya cinye mun kudi ai dole kice yaushe rabo, ni ba wannan ta kawo ni ba ma.

Likitan da ya cirewa Sarai qanwar ki ciki zaki hadani dashi wannan tsinanniyar yarinyar taje ta kwaso mun abun kunya dama yana qare da maqiya ballantana yanzu ta janyo mun abun magana a ringa nunani a gari"

"Kai kai Fattu ki bari dan Allah, irin wadannan mugayen kalaman da muke jifan yaran mu dasu su suke tasiri akan su suke lalatasu.
Ummi a garin yaya me ya kaiki irin wannan abu ke da nake yiwa kallon nutsatstsiya ko yar uwarki da take da rawar kai ta gama yammatancinta lafiya Me ya sa Ummi" Hajia Balaraba ta fada cikin Jimami.

Ummi ta qarawa kukan ta volume tana cewa "Wallai Hajia sharrin shaidan ne kuma da laifi Addah, seda na gaya mata ga wanda nake so tace ko zan mutu bazan aure shi ba"

Duka Addah ta kai mata tana cewa "Na fada din yanzu ma na maimaita ko zaki mutu bazaki aure shi ba shegiya da bata san ciwon kanta ba.

Ke kuma ni ba mayar da zance ne ya kawo ni ba ki bani lambar waya ko Adireshi na tafi dan a yau nake so ayita ta qare kafin maganar taje kunnen ubanta".

"Cikin wata nawa ne?" Balaraba ta fada tana janye tagumin da tayi, se Addah tayi caraf ta ce

"Ko wata tara ne se an cire shi babu ruwanki kawai nidai ki hadani da me aiki badai maganar kudi bace zan bayar ba matsala"

"Dan Allah Hajia karki barta ta kaini cikin fa wata hudu ne wallahi mutuwa zanyi Nasan gara ta barni ko a gurin haihuwarsa na mutu nasan nayi shahada Allah yasa haka ya zamar mun kaffara" Ummi ta fada tana sake rushewa da kuka, se Addah tayi kanta da duka Hajia Balaraba ta shiga tsakani tana bata haquri

"Fattu Yarinyar nan tafiki gaskiya, ko sarai da kikaga a lokacin munje an cire wata biyu ba'a ko busa masa raiba magani kawai ya bata tasha cikin ya fita amma wannan wata hudu fa, kisan rai zakiyi qarshe idan ba'a dace ba itama a rasata gaskiya kiyi haquri ki dauki qaddarar data zo miki a haka tunda ke kika jawowa kanki. Yarinya ta kawo mijin aure kinqi ai dole ki karbi duk sakamakoj daya biyo baya kuwa".

"Tashi mu tafi dan Uwarki ai ba ita kadai tasan likitan zubar da ciki ba ke ni da kaina nan ma sena zubar da shege idan na naushe ki yanzu" Addah ta fada tana finciko Ummin, se Balaraba tayi saurin tareta da cewa

"Ba a nan ba wallahi ku fita can idan ma kin kasheta a daure ki ke kadai baza'a ce a gidana a kayi ba" haka ta taso qeyar Addah har Get Addah na zazzaga rashin mutunchi tuni yan unguwa suka fara taruwa ana kallonta haka dai ta angiza qeyar Ummi har tati tana kuka kafin suka samu Napep kai tsaye tace a kaita wani Sha ka tafin Private Asibiti data taba zuwa duba wata qawarta a can qasan gurin GSU, a yanda taga kalar likitan ta tabbatar ze iyayin komai in dai ze samu kudi.

Ita se yanzu ma ta tuno dashi da meze kaita gurin wata balaraba harta bata lokacin ta a banza.

AMIRAH


M&Z FASHION DESINGNERS
INA MATA YAN KWALISA
KU GARZAYO M&Z
FASHION DESNGNERS DAN SAMUN IN GANTATTUN KAYA MASU AMINCI.
IRINSU
ZANNIWAN GADO
TROW PILLOWS NA ZAMANI
TUM TUM
BABY SET
TOILET SET
KITCHEN SET
LABULAYE DA SAURAN KAYAN KWALLIYAR GIDA.
HARMA DA ATAMFOFI DA KAYAN KITCHEN AKAN FARASHII ME RAHUSA
KU NEMEMU AKAN LAMBAR WAYA 07064870087.08127423783.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 50


AMIRAH

Wuntsulawa tayi daga kan gadonta zuwa qasa tayi zaman yan bori. Number wayar Addah ta shiga nema cikin tashin hankali ta ringa kira amma a kashe seta mayar da akalar kiran zuwa Ummi itama dai amsa daya aka bata wato a kashen.

Bata san sanda kuka ya kwace mata ba, ita ba sakin da Babansu yayiwa Addan ne ya dameta ba illah zancen zubar da ciki dataji. Bazata taba manta qawarta wata Harira Sani ba lokacin suna Sakandire tayi ciki a gurin zubarwa ta mutu tun daga sannan take bala’in tsoron abinda ze hado ace za’a zubar da ciki. Yanzu idan Ummi ta mutu yaya zatayi bayan duk duniya bata da wata shaqiqiyar yar uwa sama da ita.

Ganin ta kasa samun wayoyinau yasa ta yanke shawarar kiran Sa’adah maqociyarsu, tasan bazata rasa sanin wani abu da yake faruwa ba nan da nan ta danna lambar tayi sa’a tana shiga kuka ta daga.

“Anty Sa’adah ki taimaka mana ki kaiwa Addah waya nayi ta kiran layin ta dana Ummi baya shiga” Amirah ta fada bayan da tayi qoqari sosai gurin danne kukan ta.

Sa’adah dake kwance akan gadon ta tayi daidai dan tashinta daga bacci kenan ma ita ta yatsina fuska tareda hararar wayar kafin tace
“Ayyah ai kuwa anyi rashin sa’a kin ganni ina gidan mu a can na kwana jiya.

Idan ba sauri kike ba anjima kadan zan tafi idan yaso sena kiraki kuyi maganar”

“Shikenan toh idan ban same ta ba na sake kiranki” Amirah ta fada tana kashe wayar.

Daga can bangaren kuwa Sa’adah tsaki taja kafin a fili tace “gayyar tsiya kawai, ni blocking number ki ma zanyi bazaki sake samuna ba tunda ku baku san mutunchi ba haka kawai da na saki baki sedai inji ana in matsa za’a shigo da Amarya ko toh Allah ya toni asirin ku gashi nan kuma yayi mun sakayya ya hada ku da dan shege” ta sake tabe baki tana gyara kwanciya.

(Abinda ya faru mijinta ne ya ringa soyayya da Ummi a boye ba tareda ta sani ba se daga baya shine ta janye alaqa dasu gaba daya)

Amirah kuwa rasa wa zata kira tayi, fuskarta shabe shabe da hawaye, daga ita se yar bingikar rigar baccin ta net data kwana da ita wanda hatta da pant din jikinta ana gani ta fito daga dakinta da tun jiya data shige bata sake fitowa ba kai tsaye ta wuce su Aliyu dake zaune a palour suna karyawa ta nufi kan Dining inda Bashir yake.

Wata muguwar tsawa ya daka mata daidai sanda ta isa kansa ta tsaya. Kallonta yakeyi da idanunsa da suka chanza kala nan take saboda bacin rai dakyar ya bude baki yace mata

“Ke wace irin dabba mara tunani ce zaki fito a haka ki wuce ta gaban Yara samari? Saboda baki da tarbiyya ko baki kuma san mutunchin kanki ba bace mun daga nan kafin na kifar dake”.

Duk yanda ta tsorata da irin tsawa da hargagin da yake mata bata ko motsa taku daya daga inda take ba, cikin kuka tace masa

“To nima ai dole ce ta fito dani, Baba ya kirani yace ya saki Addah kuma ta tafi ta kai Ummi a cire mata ciki tsoro nake ji karta mutu ban san ina zan saka kaina”

“Zaki matsamun daga nan ko se nayi ball dake mahaukaciyar banza kawai, ta mutu mana ina ruwan wani ko ni na aike? Wallahi kika bari na miqe sena karya miki qafa idan yaso naga da yanda zaki sake fitowa nan gurin” ya fada yana qoqarin miqewa amma ciwon kan daya samu dakyar ya barshi ya sake dawo masa yanzu sanadiyyar bacin ran da zuciyar sa ta shiga.

Waiwayawa yayi inda su Aliyu suke zaune yaga babu kowa seya sauke ajiyar zuciya a hankali ya kalli Amirah data juya dakinta tana rusa ihu hannaye biyu akai. Ture abincin gabansa yayi wanda shima Aliyu ne ya hada musu dan ita gwanar se yanzu ma yaga idonta tun jiya da yamma.

Gaba daya kansa ya masa zafi, ya fahimce wannan yarinyar kwata kwata batasan me takeyi ba. Idan ma yace ze cigaba da zama a gidan qara masa ciwo zatayi se kawai ya dauki muqullin motarsa ya fice daga gidan.

Yana fitowa yayi mugun gani, Asma’u ce tsaye da wannan mutumin daya tsana sama da kowa a duniya yanzu suna magana se dariya sukeyi kamar wasu masoya.

A fusace ya nufi inda suke sedai kuma meya tuna yaci burki ya koma da baya zuciyarsa na masa zafi kamar wanda ake watsawa tafasashshen ruwa.

Motar sa ya bude ya shiga ya kifa kansa akan sitiyarin yana sauke numfashi a jere a jere, ya tabbatar idan har yaci gaba da ganin Ma’u da wani namiji zuciyarsa tana iya bugawa ya mutu lokacin sa beyi ba.

A zatonsa tunda har ya bata haquri yace su komawa auransu zata saurareshi ko dan darajar so da kuma yaran da suke tsakanin su amma se yake gani kamar ma ta goge shine ma daga babin rayuwarta.

Al’amuranta kawai take yi kamar babu wani abu me suna so daya taba shiga tsakaninsa da ita, to wai yanzu wa ze kaiwa kukansa ya samr masa mafita ne??

Bala ne ya fado masa arai, se ya janyo wayarsa ya kira lambar Balan a ransa yana lissafa tsahon lokaci rabonda suyi waya tun ranar daya gaya masa ya saki Ma’u.

Seda ya kirashi sau biyu amma ta qaraci qararta ba’a daga ba be haqura ba ya sake kira dan dai yau Sunday yasan Balan yana gida ko baya da haka yana da buqatar wanda ze tattauna dashi ko zeji sanyi a ransa.

Sake kira yayi yana ringin daya aka kashe, ya kalli wayar dan ya sake tabbatar da rejecting kiran akayi seya sake dannanwa tana shiga kuwa aka sake kashewa abin yayi bala’in bashi mamaki dan tunda yake da Bala be taba qin daga masa waya ba kai ko lokacin aiki ne balle har ya kira ya katse se yau amma dai ya kyautata masa zato qila yana wani uzuri ne a lokacin.

Motar ya kunna kawai ya hau titi yayi ta tafiya idan ya gaji da tuqin ya samu guri ya tsaya gaba daya zuciyarsa ta hargitse da tunanin Ma’u, ya kasa hasasowa kansa rayuwa babu ita.

Sati biyun nan kadai yaji jiki dauriya yakeyi dan karya nuna gazawarsa amma yaga alamar a wannan karon Ma’u ta daura aniyar kaishi qasa so takeyi se taga raunin sa.

ASMA’U
Da safe Yusuf ya kirani akan ze zo anjima ya dauki Ma’u, dakaina na tashi na hada mata kayanta da yan abubuwan da ba’a rasa ba a nake dasu duk na hada mata kafin na koma daki na kwanta amma sena kasa komawa bacci.

Tunanin makomata na shigayi a yanzu. Har yanzu na kasa yarda da cewa dagaske Bashir ya cire ni daga rayuwarsa ba kuma ya buqatar sake zaman aure dani tunda tun waccen ranar be sake tarata akan makomar auran mu ba kai ni bamu sake haduwa ba ma se jiya a gurin taron su Amnah.

Wasu hawaye ne suka zubomun na saka hannu na share, tabbas dole na yarda da gaskiya komai dacinta cewar Bashir baya sona, alfarma yayi mun ya aureni ya zauna dani saboda tarin soyayyar dana nuna masa.

Haka nan se kuma banji haushin sa ba, so ba qarya bane dan ni zan bada shaidar hakan kuma ba’a tilastawa zuciya taso abu na yarda duk hasasheb da nakeyi akansa a baya kawai dan ni ina cikin mayen sonsa ne shiyasa ban taba ganin laifinsa ba amma yanzu na gane Bashir baya sona idan ma ya soni to be kai ko kwatan irin son da nayi masa ba, qaddara da rabon haihuwa ta tsawaita zaman mu yanzu kuma da Allah ya kawo qarshen gashi ya raba mu.

Dole na haqura da Bashir na koyawa zuciyata yanda zata rayu ba tareda shi ba duk da nasan ba abu bane me sauqi dan da soyayyarsa na raini zuciyata idan har nace zan cire shi gaba daya daga raina na tabbatar daidai yake da zare duk wata walwala da jin dadi da sukayi saura a rayuwata ko da yake meya tage mun nema?

Tunda Bashir ya sake ni nayi ban kwana da farin ciki, duk wata walwala da nake nunawa a iyakan fuskata take amma qasan zuciyata Allah kadai yasan irin wutar da take ruruwa a ciki amma dole na na koyi rayuwa ba tare da shi ba.

Dole na daraja kaina na haqura dashi tunda har ya fito ya nuna mun alfarma yayi mun daya zauna dani tsahon lokaci yanzu daya samu zabin ransa ya gwammace rabuwa da ni uwar yayansa saboda farin cikinta.

A yanzu babu lissafin aure a gabana dan na rufe, bana tunanin akwai sauran gurin da zan iya saka soyayyar wani kuma bayan Bashir a cikin zuciyata.

Zan riqe kaina na tsaya da kafata na nemi na kaina na zamarwa mata irina da muka dauki soyayya da zafi madubi na kuma haska musu cewar rabuwa da Mijin da kike so ba shine qarshen rayuwa ba, sannan duk son da kake yi wa mutum idan har ya nuna baya buqatarka a rayuwarsa ka barshi koda kuwa hakan yana nufin rasa komai naka in dai zaka tsira da mutunchinka.

Ina cikin wannan tunanin bansan lokaci yaja ba seda naji wayata tana qara ina dubawa naga Yusuf ne ashe har qarfe goma da rabi na safe tayi.

Bandaki na shiga na wanko fuskata kafin na dora dogon Hijabi har qasa akan riga da wandon baccin da suke jiki na, ina shirin Fita Farida ta shigo tana cemun ga Dadyn Little yazo muka fito tare har qofar gida inda yake tsaye jikin wata shegiyar mota ya saka qananan kaya a raina na ringa mamakin yanda sam Yusuf baya tsufa, duk sanda na ganshi gani nakeyi kamar qara zama yaro yakeyi.

“A kwana a hantse se kyakykyawa, Allah yasa dai ban tashe ki daga bacci ba” ya fada fuskarsa dauke da murmushi yana kama hannun Farida, nima murmushin na mayar masa ina cewa

“Aa, ai tun sanda mukayi magana dazu ban ma koma ba ina zaune, ban ma zata da wuri zaka zo ba ai”.

“Ta matsa na mayar mata da yarta inaga gobe zasu wuce” ya fada yana bina da wani kallo da gaba daya ya saka ni diriri cewa. Sakin hannun Farida yayi yace mata taje ta hadawa Ma’u kaya tana wucewa ya matso inda nake tsaye yana cewa

“Kinga yanda kike wani kyalli kuwa daman ashe kin fi kyau babu kwalliya ban taba sani ba”

Saurin ja da baya nayi nace “Yusuff..” be bari nayi magana ba yayi saurin tareni da cewa

“Yi haquri, ni kaina idan ina tare dake kasa riqe bakina nakeyi amma dagaske kin yi kyau Ma’u, ina so naga Mace da Hijab ga wannan qamshin naki ya ilahi Allah kadai yasan yanayin da yake jefani”

Juyawa nayi, seda na kai bakij qofa nace masa
“Bari ta fito, na gode kwarai Allah ya qara zumunchi”

Se kawai ya tuntsure da dariya harda sunkuyawa yana kallona yace
“Matsoraciya, naga ma rowar gidan naki kike yi mun ko bayan nasan miskilin mijinki baya ciki. Wai ma ya akayi kika bari ya ajiye ku maqotaka da kishiyarki? Kinga idan nine ko qasa bazan hada muku ba bare unguwa daya saboda bazan yaba bari wani abu ya sosa miki rai ba indai ina da ikon hanawa”.

Cikin gida nayi shigewata ina jin yanda zuciyata take bugawa da qarfi kamar wadda tayi tsere, na rasa dalilin da yasa indai Yusuf yayi mun magana nake shiga irin wannan yanayin, yanzu da ace ina da aure muka hadu dashi haka zamu ringa dibar wannan dakon zunubin??

Seda nasha ruwa me sanyi dukda banci komai ba kafin na wuce dakin Amnah na tarar suna drama da Ma’u ta riqe akwatinta qam baza’a fita dashi ba.

Duk yanda naso na lallabata na nuna mata Dadynta ne yazo amma fafur tace itafa bazata tafi ba taga gurin zama, haka ta ringa birgima tana buge buge a qasa mamaki yasa kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login