Showing 117001 words to 120000 words out of 260321 words
Chapter 40 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL
din Beyi miki bayani ba? Hidima ce ta taso mun yaro na zeyi aure dan haka ina buqatar gidan nan ze zauna a ciki, dalilin zuwan mu kenan yanzu ma dan ya duba ya gani ko akwai wani abu da za’a chanza kafin lokacin bikin” Alhajin ya fada ba tareda damuwar komai ba.
“Amma kuma Alhaji muna da sauran lokaci kafin kudin hayar mu ya qare ko ba wannan ba ma ya kamata ka bamu notice da wuri domin mu nemi inda zamu koma ko?”
“Ta yuwu kece baki da masani domin shi mun dade dayin magana dashi daga lokacin kuma zuwa yanzu ya kamata ace ya nemi wani gurin daban, maganar ragowar kudi kuma ba matsala bane zan mayar muku da abinda yayi saura a kudin hayar ku dan haka se ku fara shiri zuwa nan da sati daya nake da buqatar gurin”.
Seda na hadiye abinda ya tokare mun maqoshi kafin nace “Shikenan, zamu tashi in Allah ya yarda amma yanzu babu yanda za’ayi ki shigar mun daki se ku jira idan mun kwashe kayan mu daga baya ku duba” ina fadar haka na mayar da qofar na rufe.
Bansan hawaye nake ba seda naji Jafar yana goge mun fuska se kawai na saki kuka ganin haka yasa shima yaron ya fashe da kukan.
Kuka ne na zallar baqin ciki da takaicin nake yi, yanzu saboda Allah ace an bamu notice mu tashi daga gida Bashir ba ze gaya mun ba kenan da se ranar da aka bashi ta cika zece na fita ko kuma se masu gidan sun watsar mana da kayan mu tukunna.
Kwata kwata ni banga Lefin Ahaji Buba ba tunda gidansa ne yana da damar da ze buqace shi a duk sanda yaso sannan ya gayawa Bashir din tuni nice beyi niyyar gaya mun ba to yanzu ina zamu dosa wane tanadi yayi mana?
Da dare yana dawowa na tare shi da maganar
“Na sani kuma ina ta qoqarin ganin an samu wani gurin har yanzu dai babu, samun gidajen yayi wahala sannan kuma sun qara kudi” Abinda ya gaya mun kenan yaja bakinsa yayi shiru.
Nayi masifar nayi bala’in amma ko kallo ban ishi Bashir ba qarshe na fashe da kuka haka na kwana ina tunanin mafita a raina, idan nace zan jira naga abinda zeyi bana tunanin samun mafita daga gareshi dan ko an samu gidan nasan bashi da kudin da ze biya dan chanjin da za’a bashi ba isa zeyi ba qarshe dai ni din ni zanyi fafutukar yanda za’ayi.
Kafin safiya na yanke zuwa gurin Baffa na, shi kadai nake dashi da ze share mun hawaye masan kuma baze kasa sama mun mafita ba dan ko kusa ban hasaso rabuwa da Bashir ba akan wannan dalilin, gari na waye wa kuwa na shirya yara muka tafi gidan mu saboda haushi ko Bashir ma ban gayawa inda zani ba shima be tambayeni ba.
Kuka na fashewa Baffa daya zuba mun ido yana kallon yanda na lalace na fita hayyacine kamar wata matar qauye. Seda na gama lissafa masa matsalolina yana ji, murmushi yayi kafin yace
“Ko wanne aure da kalar qalubalensa Ma’u ayi ta haquri zan duba naga yanda za’ayi kafin lokacin da suka dibar mukun, tashi ko shiga cikin gida ku karya kin debo yara ga Sheik Jafar nan da gani bacci be ishe shi ba”.
Haka na wuni a gida ranar ina jin kamar kar na tafi duk yanda Na ringa shan zagi a gurin yan uwana kowa na fadar ni na jawa kaina.
“Ba kalar mutanen arziqin da basu zo kanki ba Ma’u amma kika nace se wannan Bashir din da ba mutunchi ne dashi ba. Ki ajiye maganar bashi da shi a gefe dan mu ba itace matsalar mu ba Aa girman kansa da yake hana shi fita ya nema shi ya jefa ku a duk halin da kuke ciki shi se aikin office zeyi ko ke ce yar wahala yana zaune ki fita ki nemo masa.
Se kije kiyi tayi, ina dai jiye miki ranar da dadi ze zo ya dakko miki yar tayin cin arziqi ta hanaki zaman lafiya idan ma be yar dake a sannan ba tunda kin gama masa aiki” Anty Zubaida Yayar mu ta biyu a Mata dana tarar a gidan ta gayamun.
Haka suka ringa gayamun maganganu kala kala wanda ko dar banji a raina akan Bashir ba, abinda na yarda na kuma amincewa zuciyata Bashir yana so na ba kuma ze taba juya mun baya ba dan haka zan taimakeshi da iya qarfina in har ni ina dashi.
Da zan tafi Goggo ta sake yi mun nasiha akan nayi haquri na zauna lafiya da mijina kar na yarda da abinda yan uwana suke gayamun. Allah sarki ita kadai ce take qaunar Bashir a gidan mu se ko Baffa da bazance ga bangaren da yake ba. Haka na koma gida ba tareda na cewa Bashir komai ba.
Kwana biyu a tsakani Baffa yace naje gida, a gaban Yayyena dukda suke gari da Iyayen mu ya mallaka mun takardun gida wanda aka siya da sunana sannan ya bani kudi naira miliyan biyu a sannan yace naja jari.
“Ku zama shaida nayiwa Asma’u kyautar wannan gidan sannan ga kudi nan taje suja jari ita da mijinta su riqe kansu”.
Haka na tattaro na dawo gida cikin dimbin farin ciki bayan Yah Abubakar ya karbe kudin daga hannuna yace naje nayi tunanin abinda zanyi dasu. Godiya sosai na ringa zuba wa na kuma qudurce a raina in sha Allahu bazan sake komawa gida da niyyar neman wani taimako ba.
Zanyi tunanin abinda zanyi da kudin ba kuma zan gayawa Bashir batun su ba gida dai gashi nan muje mu zauna a ciki.
Da na nuna masa takardun gidan ma kada ran kada han fuskarsa, washe gari mukaje muka ga gidan.
Sabon gida ne me kyau ginin zamani a cikin GRA Flat me dauke da Qaton palour da Dining se dakuna bibbiyu a cikin corridor hagu da dama ko wanne da bandakinsa a ciki ga qaton kitchen da store tsakar gidan kansa a qalla zeci mota uku zuwa hudu sannan ga dakin me gadi.
Ni kadai na ringa tsalle ina murnata Allah sarki Baffana Allah ya biyashi da Aljanna, tun a ranar muka fara kwashe kaya, a kwana na uku muka tare bayan da yan uwana da Abokanan Arziqi suka rakani kowa se yaba guri yakeyi yanda yayi kyau dan har kujeru da labulaye na sake.
Satin mu daya a unguwar na fahimci matsalar masu kantina da take damun gurin duk abinda kake nema seka fita can babban titi ko kaje kasuwa.
Ni da nake neman abinyi se na yanke shawarar bude provision store kawai dana gayawa Yah Abubakar shima yayi na’am da maganar nan da nan yasa aka fashe dakin me gadi aka sake ciyo filin cikin gidan aka yi babban shago a gurin.
Lokacin da nakeyiwa Bashir zancen muna zaune se yake cemun “ai kuwa hakan yayi dan kinga ko ni ma se na ringa zama a gurin kafin na samu wani abinyin”.
A lokacin ba qaramin dadi naji ba, dan daman tunanina kenan amma ina tsoron na gaya masa ya fassara maganar da wata manufa ko yace na rainashi shi yasa na yanke kawai zan sa a nemo min yaro da ze ringa zama tunda ga qofa anyi ta cikin gida na ringa leqawa naga yanda abubuwan suke tafiya.
Cikin dan lokaci aka hada shago sosai aka shaqe shi da kayan masarufi harda su ruwa da Lemo duk muka zuba cikin ikon Allah kuma ya samu karbuwa dan sosai ake ciniki kafin cikar wata biyu seda ya zamana har buhun huna muke siyarwa na kayan abinci da muka ga ana yawan tambaya.
Bashir ne yake zama se wani yaro Shafi’u dayazo yace ze ringa taya shi. A dan qasan mu yake maraya ne ake ruqonsa a gidan qanin Babansa sedai beyi sa’ar mariqiya ba ai kuwa na riqe shi sosai gashi da amana.
Shekarar mu daya a gidan na sake haihuwa yar mace da se naga kamar Bashir yafi yin murna akan ta sama da sauran haihuwar da nayi har na ringa tsokanar sa wai saboda an samu Dada ne yasa yake murna amma yace Aa shi ba sunanta ze saka ba.
A raina har na dauka ko ni zeyiwa kara ya saka Goggona se ji nayi ya mata huduba wai da Aisha Farida.
“Ni na zata Dada ko Goggo zaka saka ai” na fada bayan daya gaya mun sunan, se ya kalleni yace
“Bani da ra’ayin yiwa wani takwara, ko Aliyu da kuke zaton sunan marigayi Aliyu ne kawai ra’ayin kainane”.
Haka naci gaba da rainon Faridata dan tuni an saka Aliyu da Jafar Makarantar Boko da Islamiyya.
Nisan da mukayi dasu Addah be sa Amirah ta dena zuwa ba dan yawanci duk Juma’a se sunzo musamman tunda na haifi Farida wani lokacin ta kwana daya ko biyu wani sa’in ma ni zan kira Addah nace ta turo mun ita tayi mana kwana biyu dan yanzu ta fara zama yammata ta rage fitsara da rashin kunya abu daya yake hadani da ita qazanta da rashin son aiki dan in tazo se nayi da gaske take kama mun ayyuka ga bata guri haka zasu ci abinci su bata ko ina idan bani nace a kwashe ba sedai su zauna a cikin dattin.
Daman batayi mun raino qarqari ta in zanyi wani abun na ajiye mata Faridar ta kula da ita amma fa ko zata kwana tana kuka Amirah bazata goya mun ita ba bare naci arziqin tayi mun wankin yara ko yi musu wanka ba tayi to kanta ma se nayi dagaske take wankan bare tayiwa wani.
Watannin Farida Shida Allah ya karbi rayuwar Baffan mu sanadiyyar ciwon ciki da yayi na kwana daya har seda aka kaishi Asibiti inda acan ya rasu. Fadar irin tashin hankalin da muka shiga ma bata lokaci ne, munyi kukan rashin Baffa babban bango ya fadi se dai mu bishi da fatan Alkahiransa da halinsa na gari su bishi. Rasuwar Baffa da kwana Arba’in aka yi mana rabon gado kamar yanda ya bar wasiyya bayan an gama tattara komai kowa aka bashi kason sa.
Wannan karon ma ba’a bani komai nawa a hannuna ba dan ana gama rabon Yah Muslim ya danqawa Alhaji qarami nawa dana Amna. Bansan dalilin da yasa sukeyi mun haka ba, amma koma menene banyi magana tunda nasan baza su cutar dani ba.
Seda Alhaji qarami ya gama tsara duk yanda yake ganin yayi sannan ya sameni har gida wata rana yake gaya mun, mota biyu ya kawo mun cikin rabona yace gashi nan se na dauki daya na bawa Mijina daya. Na samu gonaki manya har biyu yace za’a ci gaba da noma su kamar yanda akeyi dabbobi na suma ze zuba mun su a gidan gonarsa.
Akwai fili manya guda biyu dana samu se ya bani shawarar tunda mun samu wani gida me flat takwas a Abuja aka raba mana ni biyu, Junaidiyya biyu se nasa guda hudu idan na yarda ayiwa kowanne kudi muyi musanye ya karbi filayen ya bani gida itama idan tana so ayi haka mu ringa karbar kudin hayar duk shekara dan a cikin gari suke nan take na amince na kuma bar masa duk sauran abubuwa a hannunsa yaci gaba da kular mana dasu kafin ya tafi ya turamun zunzurutun miliyoyin kudade na a account da seda jikina yayi sanyi da ganinsu.
Rayuwa kenan, shi wanda ya tara su yanzu tasa ta qare muma da muka samu wata rana haka zamu tafi mu barsu, shawara muka yanke akan gidan mu kar a tabashi, abar shi a yanda yake tunda kowa sun san kason su kowa mahaifiyarsu tana ciki sannan muka samu Qaton fili muka siya akayi Babbar Makarantar Islamiyya da masallaci Muka kuma bude foundation ta tallafawa Marayu da mabuqata me sunan ABDULLAHI TUKUR KUMO FOUNDATION ladan Allah ya kaiwa Baffan mu.
Duniya sabuwa tuni al’amura suka daidai tar mana. Na bawa Bashir mota daya sannan na hada masa da kudade masu nauyi, Alkahiri babu wanda na manta dashi dan hatta su Fainusa da suka yanke alaqa dani yanzu sun dawo kuma ban qisu ba na karbe su da hannu biyu ba wai dan bani da wayo ko ban san me nake yi ba, Aa shi wanda kafi a rayuwa har abada ka fishi arziqi kuma kashi ne kowa yazo ya dangwala.
Har sannan Bashir na zama a shago amma ba na qofar gidan mu ba dan a cikin kudi na na bude babban super market acan kan titi shine manager muka dauki ma’aikata tsohon kuma na barshi a hannun Shafi’u da sabon yaron daya samo yake tayashi saboda na mayar dashi makaranta se da yamma yake zama a Gurin.
Bayan fitar Su Goggo takaba kawai ta taso da wata maganar wai zata koma Yola ta daura aure da Baffa Sama’ila. Qiri qiri muka nuna qin Amincewar mu gaba daya seda Alhaji Qarami ya tsawatar mana sosai akan me yasa mu zamu haramta abinda Allah ya halasta, babu wanda ya isa ya hana mahaifiyarsa qara aure a cikin mu gaba daya ko da kuwa cewa sukayi zasu kawo mazan cikin gidan mu tunda dai suka da kason su.
Haka muna ji muna gani aka daura musu aure da Baffa Sama’ilan ta shirya komawa Yola nan na tada sabuwar rigimar sedai ta bar Amna bazata tafi da ita ba a wannan karon dai na samu goyon baya se kuma rigima ta koma tsakanin manyan cikin mu mu Ashirin da bakwai a sannan maza da mata masu aure kowa yace shi ze riqeta daga qarshe dai nayi nasara riqon Amna ya dawo hannuna wanda Bashir da kansa ya goya mun baya aka bani ita.
Riqon Amna da na karba wane tudu wane gangare se ganin Amirah nayi da faggon kaya Addah ta kawo ta wai Addahn zasuyi tafiya zata je Niger, daga tafiyar sati biyu taji dadi da su Addan suka dawo se cewa tayi bazata tafi ba, Bashir zeyi fada nace ya barta ta zauna zan riqe dan har ga Allah ina son yarinyar kuma ina so naga tarbiyyarta ta inganta dan duk in tazo mun sena ga abinda beyi mun ba a cikin halayyarta wannan shine mafarin dawowar Amirah hannuna.
Sosai Allah ya sanya Albarka a cikin kasuwancin mu, kudin da na bawa Bashir a cikin super market din shima ya saka ake juyawa, wata dabara da nayi masa muka zauna akayi rubutu kudinsa da yake ciki nace masa ya cigaba da juya su duk ribar daya samu ya barta a ciki karya cire sannan za’a ringa biyansa a matsayinsa na manager kamar sauran ma’aikata, da Allah ya sakawa abin Albarka se gashi muna neman yin kankan kan dashi a mallakin shares na super market din.
Salin Alin muke zaune rana daya Bala da rabon dana ji duriyar sa har na manta yazo mana ziyara. Faran faran muka gaisa na basu guri shida Bashir na koma ciki, bansan me suka tattauna ba bayan tafiyarsa na fara ganin chanjin fuska a gurin Bashir.
Kwanaki biyu a tsakani ya dena fita super market, a rana ta uku ne nayi masa magana se ce mun yayi
“Akwai sauran Ma’aikata nasan zasu kula da komai”
“Amma baban Ali kasan dai yanda mutane suke yanzu idan babu idon ka zasu iyayin yanda suka ga dama, ka manta rungon lissafin da suka ringa yi mana kwanaki ko” daga wannan maganar da banga abin zafi a cikinta ba se Bashir ya hau fada yana cewa
“Ni na gaji naga alama kin mayar dani wani yaronki kina zaune ina miki neman kudi ko? wato kina so na saka ido a Shago dan kar a cuceki amma kika kasa aminta ki damqamin gadonki a hannuna na kula miki dashi. Daga yau na dena zuwa, kinemo wanda ze ci gaba da kular miki da gurin” haka yai ta fadar maganganun sa ni dai na tsaya kawai ina Jin ikon Allah.
Kusan sati baya fitar dan haka na nemi Nasir qani na ya maye gurbinsa a gurin sannan ga Naziru qaninsa da daman yana zuwa na kwashe shi shida duk tsiyatakun da yake ji dasu na watsar dan ni yanzu hidimomin gabana sun ishe ni.
Beci gaba da zuwan ba amma dai ya dawo yana neman shiri dani, nima ban nuna masa komai ba muka ci gaba da sabgogi cikin hukuncin Allah se gashi ya sake samun aiki a Ma’aikatar haraji ta qasa reshen Gombe.
Aikin da Bashir ya sake samu ya tabbatar mun da cewa idan har yana dashi babu abinda baze yi ba, rayuwar mu se sambarka idan ka cire sabanin irin na yau da kullum da a kowanne gidan aure anan samun irinsa bani da wata matsala da Bashir.
Albashin sa nada tsoka dan haka a wannan karon na bashi shawara daya siyi gidan da muke ciki ya zama nasa, kai tsaye ya amince yace ze ringa biyana duk wata na yarda, da na gayawa Yah Abubakar a take ya karbe takaddun yace kuma A ringa tura kudin ta account dinsa har zuwa sanda ze biya sannan a chanza suna ya koma nasa abun nan kuwa ya qona ran Bashir ya ringa mita yana masifa nidai bance masa komai ba cikin qanwanin lokaci kuwa ya biya kudin tsaf aka chanza takaddu aka bashi ni kuma Yayan ya siyar mun da shagunansa guda biyu a wata babar plaza dan ina so na fara siyar da kayan yara Anty Suhaima zata ringa turomun su daga UK.
Bayan Farida na haifi na sakw haihuwar Da Namiji, kai da fata a wannan karon na kafe se Bashir ya sakamun sunan Baffana, dan gaske kuwa ya murzawa idon sa toka yace sedai na siyi ragon suna, dukda naji zafin abun amma haka na siyi manya manyan raguna guda biyu harda Bijimin Sa na qauri aka yankawa Abdallah na.
TUSHEN MATSALATA
Shigar Amirah Ajin Babbar Sakandire yazo mata da wani sabon tashen fitsara da rashin mutunchi. Amirah Kyakykyawar Yarinya ce Fara tas me gabaren girma a shekaru sha hudu qugunta ya bude qirjinta ya cika tazama budurwa sosai da bazaka yarda ba idan aka fada maka shekarunta.
Abinda ya fara hadani