Showing 147001 words to 150000 words out of 260321 words

Chapter 50 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42698

ya daidaita.

“Mami nima na bisu” Amna ta fada tana kallona, sena daga mata kai kawai alamar “Eh” da saurinta kuwa ta shiga daki ta hau shiri Faridah ma ta bita dan ita kayan ta ba dukka aka kwashe ba daman. Suna gama shiryawa muka jiyo horn dinsa daga waje sukayi mun sallama gaba daya suka fice.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi bayan fitarsu dan kaso saba’in cikin fargabar rabani da yarana da Bashir yayi ya kau dan a zatona ze rabani dasu ne kwata kwata ya hanamun ganin su amma indai har haka za’a cigaba komai ze zo da sauqi kenan.

Yan gyare gyarena na tashi na shigayi bayan na gama na hau kwaba musu cake na tafiya makaranta tunda basa zuwa da abinci acan suke basu harna rana shiyasa se nayi musu dan abin tabawa su tafi dashi bayan sun karya a gida shima Bashir na zuba masa to yanzu kuwa sedai Can Matar sa tayi masa indan zata iya su dai zan ci gaba da yi musu yanda na saba in zasu tafi na basu.

Ina cikin kwabin cake din Aliyu da Jafar suka shigo, ina kallonsu nace
“Aa ku ban da ku aka tafi yawon kenan?”

“Ban da mu, Mami akwai Abinci?” Jafar ya fada yana nufa yana bude tukunya, Aliyu kuwa kan deep frizzer ya hau ya zauna yana kumbura fuska,

“Ali mazan fama ya akayi ne ko kaima yunwarce ga abinci nan ku diba ku ci to”.

“Wallahi Mami watarana sena sumar da matar can idan ta sake shiga harkata” ya fada yana sake hura baki. Se na ajiye Mixer hannuna na juya dakyau ina kallonsa nace

“Wace mata zaka sumar kuma Aliyu?”
“Amirah mana” ya bani amsa kai tsaye.
“Kana jina ko Aliyu, karku kuskura kuce zaku saka abinda ya faru tsakanina da mahaifinku a rai har hakan ya shafi alaqarku dashi.

Rabuwar mu qaddarah ce daga ya rigada ya tsara iya lokacin da zamu zauna kunga babu abinda ze chanza hakan, sannan tsakanin ku da matarsa babu rashin kunya dan ba ita ta raba mu ba Allah ne ya kashe auran mu.

Koda wasa karna ji dayan ku yayi mata wani abunda ba daidai ba dan idan ma kunyi a maimakon ku ce kun rama abinda akayi mun qaramun laifi zakuyi aringa cewa ni na saka ku dan haka babu ku babu sabgarta. Duk abinda kuke nema a gidan baku samu ba kuzo nan shikenan”.

“Amma ki gaya mata wallahi Mami duk randa ta qara zagar mun uwa ko tace zata dakeni kafin ta fara ni zan doketa tam” Aliyun ya sake fada kafin ya sauka daga kan freezer ya fice daga Kitchen din gaba daya. A yanda yayi maganar hatta da muryarsa se najita kamar ta Bashir idan yana cikin fushi se kawai na bishi da kallo kafin nace
“Allah ya shirya ka ya rage maka wannan zafin zuciyar” se na juya kan Jafar dake kwasar abinci nace

“Meya hadasu da matar Babanku yake cewa ze daketa?”

GIDAN BASHIR BAYAN FITAR SA
Bayana Bashir ya fita seda Amirah ta tabbatar taji tashin motarsa alamar sun tafi ta sake leqawa taga basa nan kafin ta kulle qofar ta ciki ta yanda dole se an buga zata zo ta bude.

Dakin su Aliyu ta wuce kaitsaye, A zaune ta tatar dashi da Jafar suna magana sama sama tana shiga ta kama qugu daga bakin qofa cikin isa da taqama tace
“Ku tashi ku fito, kai Jafar kaje ka share abincin da qannenku suka zubar kai kuma Aliyu ga kwanukan can a Kitchen seka shiga ka wanke”.

A tsakanin su babu wanda ya tanka mata dan ko inuwarta basu kalla ba suka ci gaba da maganar su, wata Asharvta lailayo ta aika musu da ita kafin cikin Masifa tace

“Wato ga yar iska ina muku magana kunyi mun banza ba kuna zato zan zauna kamar jaka na dafa muku abinci ne a bata guri na gyara duk kuna zaune babu me tayani? Naga da uwar ku tana nan shara wanke wanke duk ku kukeyi mata dan haka yanzu ma lazim kuyi idan kuna so kuci abinci a gidan nan”.

“Seki bari wadanda suka bata suzo su gyara miki ai kuma aike ba uwar mu bace da zamuyi miki aiki, abinci kuma daman bamu ce ki dafa mana ba dan ko kin dafa bazamu ci ba. Kuma daga yau karki sake shigowa dakin nan idan ba haka ba se kin raina kanki Allah” Aliyu ya fada yana tsatstsareta da ido kamar wani Sa’anta aikuwa tayi kansa fuuu da niyyar kwasa masa mari ya goce hannunta ya bugi katakon gado.

Sosai taji zafi dan da qarfin ta ta kai mari ta riqe hannun tana girgizawa da cije baki Jafar ya kwashe mata da dariya kuwa nan da nan ta shiga zaginsu tana cewa

“Shegu yan iska marasa mutunchi wallahi se naci ubanku yau a gidan nan naga me kwatar ku” bata daddara ba ta sake yin kansu, seda taje daf da Jafar zata kai masa Duka ya matsa da sauri kusada Aliyu daya harde hannu a qirji yana ayyana abinda zeyi mata idan ta kuskura ta tabashi, a yanda yake jin haushin ta badan wani abu ba da wallahi rufeta zasuyi su mata shegen duka dan daga shi har Jafar din masu manyan gabbai ne girmansu ya zarta shekarunsu.

Yana cikin wannan tunanin ta kuma kawowa Jafar dake mata dariya duka tana aunawa Uwarsu ashar ai kuwa ya saka mata qafa ta baya ta tafi kamar zata fadi kafin tayi gaba ji kake Qum ta buga goshi a bango da qarfin gaske kafin kace me gurin ya tashi.

Ihu ta kwalla tana shafa gurin dan ta bugu ba qarya ji tayi kamar ma har idonta buguwar, tana kuka tana zaginsu suka tsallaketa suka fice daga gidan ma gaba daya.

Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku

BONONZA; BONONZA;BONONZA;

Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K


MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 44

Har Magriba Amirah na sharbar kuka kamar qaramar yarinya ga takaicin qulun da goshi ta yayi gashi har yanzu Bashir basu dawo ba ta kira shi kuma bema tsaya ya saurareta ba yace mata se ya dawo ya kashe wayarsa.

Seda akayi sallah suka shigo gidan da ledoji niqi niqi na kayan maqulashen da suka siyo.

“Kai Anty kalla wani bump a goshinki” Abdallah ya fada yana kwashewa da dariya qannensa na taya shi tayashi.

“Bari muga, faduwa kikayi a toilet? yah Aliyu ma ya taba yin haka kun tuna?” Farida ta qara tana qoqarin kai hannunta kan goshin Amirah a mugun fusace kuwa ta doketa har seda ta fadi qasa dai dai lokacin da Bashir ya shigo gidan.

“Baki da hankali me tayi miki da zaki bugeta haka idan taji ciwo fa” Bashir ya fada yana dago Farida daga qasan, se kuwa ta kwararrabe fuska tana matsa hannunta tace

“Abbi hannuna akansa na fadi” se hawaye sharr kai kace wadda ta karye ko wani abu.
A rude Bashir ya shiga duba hannun, ya jefawa Amirah mugun kallo yace

“Wallahi idan wani abu ya samu hannunta se kin gane kurenki saboda baki san zafin ta ba shine zaki tureta ta fadi uban me tayi miki”.

Itadai Amirah gaba daya ma seta kasa magana, daga shigowarsa baze tambayi ba’asi ba se ya hauta da Fada harda yi mata gorin haihuwa, tana shirin buda baki ya tare ta da cewa

“Dallah tashi ki dubo mun man zafi na saka mata, kuma wallahi koda wasa karki sake yin abinda ze taba mun lafiyar yara dan bana hada komai dasu kin sani”

Baiwar Allah haka ta tashi zugui zugui ta dakko masa se hadiyar zuciyata takeyi tana rarrashin kanta dan kartayi kuka a gaban yaran su mata dariya, haka ya shafawa Faridah man zafin ita kuwa saboda sharri se sake langwabewa takeyi ya gama ya dorata akan kujera se sannu yake yi mata, yana juya bayansa tayiwa Amirah dake tsaye tana kallon ikon Allah gwalo kafin ta koma ta noqe a cikin kujera sauran yaran suka wuce dakin su suna yi mata dariya.

Bashir kuwa dakinsa ya shige, da walwalarsa ya shigo gida amma daga dawowa har ta bata masa rai. Yana cikin cire riga ta shigo dakin, se a sannan ya kalli fuskarta yaga kumburin goshinta, ba tareda wata damuwa ba ya kalleta yace

“Meye wannan a fuskarki kuma bugewa kika yi?”

Kamar tana jira se hawaye shaaaa harda sheshsheqa tace masa
“Ba su Aliyu bane suka tadeni na fadi shine na buge goshi ita kuma Faridah suna shigowa tazo zata taba naji zafi na tureta shine ka dauka da gangan nayi”.

“Su Aliyu suka tadeki kika fadi kamar yaya? Meya hadaki dasu da har zasu tadeki?” Ya fada yana tsatstsareta da ido, kanta a qasa tana tunanin qaryar da zata shirga musu yanda idan suka dawo ze rama mata, can ta dago tace

“Kawai fa dan na sake shiga nace su fito suci abinci shikenan suka hau zagina shida Jafar, ban kulasu ba na juyo zan fito kawai Aliyu ya sakamun qafa na fadi kuma suka fice sunayi mun dariya. Yanzu dan Allah kamar ni ko babu aure tsakanina dakai ai akwai yan uwantaka ya kamata su girmamani amma ba haka ba se ma kaji irin zagin da sukayi mun ta uwa ta uba” ta qarasa tana goge majina da hannun rigarta.

Bashir kuwa sakare yayi yana ji da ganin ikon Allah, wai suka tade ta ta fadi to ai koda Aliyu da Jafa nada girman jiki ya tabbatar Amirah bazata tsaya su kada ita ba tunda itama ba kadan bace idan ma sun kayar da itan dole akwai abinda ya hado su dan haka kawai bazasu kamata da komawa ba.

“Kina ji ko? indai kina so ki zauna lafiya da yaran nan to ki kama girmanki a cikin gidan nan. Babu ruwanki da shiga shirgin Aliyu ko Jafar. Su ai ba kamar twins bane da se kin ajiye su kin zuba musu abinci ko su ci abinci ko karsu ci ba damuwarki bane abunda yake naki ki dafa musu ki ajiye idan sunji yunwa da kansu zasu fito su nema.

Bana so na sake jin wani abu makamancin haka ya faru wai kin shiga dakinsu har ta kai ku gayin rigima wani yaji ciwo, ki kiyaye”.

“Oh abinda ma zaka fada kenan, laifina ka gani yanzu bana su bama kenan? Toh wallahi bazan yarda ba, daman na bari ne ban dauki mataki ba ina jiran seka zo amma tunda bayansu kabi wallahi se jikin yara ya gaya musu a gidan nan dan babu shegen dan da ze taka ni in saka ido ina kallonsa” Amirah ta fada tana miqewa tsaye zata wuce, a fusace Bashir ya tsayar da ita yana cewa

“Na rantse da Allah kika sake kiran yarana da shegu sena chanzawa bakin ki halitta tunda ke baki da hankali ba kuma kisan abinda zaki fada ba, sannan karki fasa dukan su ni kuma babu yaron da zan tsawatarwa a gidan nan idan ya miki rashin kunya tunda abinda kika zaba kenan” fuu ya wuce daki ya barta a tsaye tana qunquni.

Tana tsaye a gurin su Aliyun suka shigo, ta waiwaya ta kalle su, badan ba wallahi seta tsinka musu maruka koma ta rufe su da duka dan gani takeyi zata iya, amma tsoron abinda Bashir ze iyayi ya sakata watsa musu harara kamar idonta ze fado suma kuwa basu bata lokaci ba suka maida mata har Aliyun yana cewa

“Da magana ne?”
Seta ja tsaki kawai ta wuce dakinta, tabbas da sake dole ta dauki matakin gaggawa tun kafin abubuwa su rin cabe mata yanda bata tsammata ba daga uban har yaran seta dauki mataki akan su ta yanda babu wanda ya isa ya sake nuna mata yatsa a cikin su.

Haka ta kwana saboda tsabar takaici ko dakin Bashir bata je ba, sanda Faridah ta shiga zata kwanta ma da masifa ta hauta yarinyar na kuka ta tafi dakin uban lokacin yana zaune yana aiki a laptop dinsa. Gobe Monday, gashi yana da ayyuka a gabansa da yake so ya qarasa dalilij da ya saka be fita ya kulata ba kenan se kawai ya cewa Faridan ta hau Gadonsa ta kwanta ya ci gaba da aikinsa yana ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah.

Washe gari da Asubar fari ya buga mata qofa sanda zasu wuce masallaci akan ta fito ta samar musu abin karyawa da wuri.
Har suka dawo kuwa yar gaske bata leqo ba dan daman daya tasheta yana fita ta koma baccinta dan tace ba shegen da zata yiwa girki da Asubar nan su tafasa ruwan shayi akwai komai har Buredi su sha ita bata saba wannan wahalar ba.

Sanda suka suka shigo a zatonsa ta tashi tayi sallar harta shiga Kitchen dan haka dakinsa kawai ya wuce ya tashi Faridah yace taje dakin Amirahn tayi wanka ta shirya shima ya shiga wanka.

Da dari dari Faridah ta shiga dakin se ta tarar da Amirah ta shanya baki tana bacci abinta dan haka sadaf sadaf ta shige bandakin ta rufe a hankali dan karta tasheta, har kuwa ta gama wankanta ta shirya ko motsi Amirah batayi ba, saboda neman tsokana ta kwashi turaren Amirah ta feffesa da sauri ta kwashe kayan data cire ta fella gidan Ma’u da gudu dan ita daman Uniform kadai ta dauka a kayanta komai yana dakinsu na gidan a can ta barsu.

Sanda ta je ta tarar da Amna na hada Breakfast Ma’u na wanka dan sun makara tashi da safen, tana ajiye kayanta ta wuce Kitchen takwashi dankalin da Amna take soyawa tana cewa

“Yah Amnah ki qara wani nasan yanzu yunwa zata koro su Yah Aliyu zasu zo har Abbi, bafa ta tashi daga bacci ba haryanzu Anty Amirah bare ta bamu breakfast” se ta miqe da sauri kuma ta shiga hada tea tana cewa “bari na zuba a Water bottle na sha a mota dan nasan yanzu Abbi ze fara a fito a fito bata rufe bakinta ba sega sallamar su Aliyun yan biyu suka tuga Kitchen da gudu jin qanshin abinci babu bata lokaci kuwa suka dirar wa Dankalin dan ma kamar Amna tasan za’ayi haka ta soya da yawa daman niyyar ta ta zuba musu su qara ko a mota kafin suje makaranta.

Tas suka cinye kowa ya dauki container cake dinsa da inibi da yar cakulatin da ake saka musu Suna haka ma’u ta shigo Kitchen din ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar Jallabiyya baqa da bata da Adon komai ta saka hula a kanta kafin tayi rolling mayafin rigar hannunta riqe da qaramar handa bag Fara se qamshi me sanyi takeyi.

ASMA’U

Da mamaki na kalli yaran ina cewa “ku kuma daga ina haka da sassafe se dambe kukeyi da abinci kamar wadanda sukayi kwanan yunwa”.

“Mami ai tashin yunwar mukayi shiyasa ba’a bamu abin karyawa ba” Jafar ya fada yana dariya,

“Allah ya rufa asiri, se kuyi saurin kunsan yana jiranku” na fada ina rufe baki kuwa sega horn din Bashir kamar wanda ze tashi gari.

Tareda su muka fito tunda sun cinye abincin na haqura idab naje office na nemi wani abun, kallon second daya nayi wa Bashir daya bude mota ya fito a fusace inaga da binsu cikin zeyi, har zan wuce se na sake waiwaya wa nace

“Baban Ali ina kwana” be amsa ni ba nima kima daman ban saka raiba, na kunna mota ta na ajiye jakar na sake komawa ciki dan na manta da wayata. Sanda na fito sun yafi nima naja na wuce nawa uzurin a raina ina ta mamakin ya akayi Amirah bata basu abin kari ba?

“Qila tana ta baccin nan nata na asara” na ayyana a zuciyata kafin na tabe baki na ci gaba da tuqina.

BASHIR

Qarfe bakwai saura ya fito daga dakinsa tsaf cikin shirin tafiya aiki, gaba daya wani daban ya ringa jinsa, kayan kansu ji yai kamar ba daidai ya saka ba seda ya ringa kallon kansa a mudubi ya tabbatar dai daidai yake kafin ya fita palour.

Ya rigada ya saba daga litinin zuw Juma’a Ma’u ta ware masa Suit din da ze saka hatta da takalmi da agogo komai seta ajiye masa sannan idan ze shirya tana tsaye tana taya shi ya gama ta fesa masa turare sannan su fito suci abinci cikin nishadi kafin kowa ya tafi aikinsa.

A shirye ya tarar da yaran, Aliyu ne yayiwa yan biyu wanka ya shirya su tsaf kowa ya fito goye da jakar makarantar sa suka zauna a palour shiru dagani shi suke jiran fitowar sa. Yan biyu ne suka gaishe shi ya amsa dan sun rigada sun gaisa da ragowar tunda Asuba, seya kalli kan Dining yaga wayam dan haka ya nufi Kitchen a zatonsa tana ciki amma yana zuwa nan ma babu kowa babu ma alamar an girka wani abu a cikin sa.

Dakin Amirah ya tafi yana shiga tana miqewa zaune da alama tashinta kenan ta gantsare tana miqa, cikin muryar wanda ya tashi daga bacci tace
“Kai qarfe nawa ne naga harka shirya yaya ko daman da Asuba kake fita?”

Be amsa tambayarta ba, ya ce mata “kinyi sallah?”

Shiru ta masa alamar bata yin ba kenan abinda ya qara bata masa rai a mugun fusace yace mata

“Da zan fita sallah ban tasheki ba sannan na gaya miki kiyi mana abin kari da wuri shine saboda rainin wayo kika ci gaba da baccinki ko?”

Seda ta zauna sosai kafin ta kalle shi tana tura baki tace “ni banji sanda ma ka tasheni ba, kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login