Showing 42001 words to 45000 words out of 260321 words

Chapter 15 - WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) COMPLETE HAUSA NOVEL

27 Dec 2024

42671

ba haka tunda ga abinda likita yace se kibi na dan lokaci ne ko cewa akayi zata dawwama ba wankan ne se ki mata yanda suka ce.

Yanzu kizo ki zunduma musu ya a ruwa bayan naji ance tana da munoniya wani abu ya faru kinsan dai wannan sirikin naki manta komai zeyi wallahi har ni nan da babu ruwa na qila se yayi qarar mu ai wannan ruwan yayi yawa...kaii” maganar ta katse bayan data tsumbula hannu a ruwan, seta kalli Addah ido waje tace

Fatu kice kisan kai kika shirya wannan ruwan ko uwarta bata wanka da me zafinsa shine zaki jefa wannan tatsitsiyar yar a ciki? To nidai inaga watan tafiyata gida ya kama dan bazan iya zuwa polisteshan bada sutotimen ba”.

Addah da tayi tsilli tsilli dakyar tace “nifa ji nayi jikin ba kwari shine nake so na gasata jikinta ya hade amma tunda banyi abin kirki ba shikenan kuda kuka iya se ku mata” fuu tayi waje.
Wunin ranar haka ta yini mita duk wanda yazo seta gaya masa abinda Amirah tayi mata kuma dai kowa ita yake bawa laifi.

Ganin dai dagaske Bashir baze bada kudin taro ba Addah ta shiga ta fita da abinda Baban Amirah da yan uwanta suka hada da bashin Jama’a duk ta ganganda za’ayi bikin suna. Kayan abinci dama ba matsala bane sunyi akan na Store dinta za’a diba ayi komai.

Kaji kawai zasu siya se ruwa da lemo da kayan snacks se kuma kayan rabo da Amirah ta nace se tayi dan har ta kira me hoto yazo ya dauki Baby wanda za’a saka ajikin Jaka da Memo. Duk shirin nan basu gayawa Dada ba tunda tace bada yawunta ba balle Bashir da ya rantse ya kuma rantsewa baza’ayi ba shiyasa ma suka tsaida ranar Laraba bayan ya tafi litinan sannan zasuyi sunan.

Allah kaimu ranar suna lafiya 😂😂😂🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)

Page 17

Ranar Litinin Bashir ya tafi a ranar kuma Asma’u ta dawo dan ta tabbatar daman kafin su iso ya tafi. Da wuri suka taso dan haka sun sauka da wuri.

Gaba daya ranar baccin gajiya sukayi har zuwa washe gari talata sannan suka wartsake. Da yamma ta shirya dan tana so ta fita harta kunna motar ta amma taqi tashi tayi duk abinda zata iya amma taqiyi dole ta haqura ta kira Naziru ya zo da bakanike suka dubata yace dole seya tafi da ita gareji haka suka lallaba suka tafi se fasa fitar tayi.

Seda aka yi Sallar Isha tayi order Bolt, itada yaran suka fita, Shagonta na siyar da kayan yara sukaje dan tana so ta siyowa Baby Iman riguna, basu bata lokaci ba ta zabi masu kyau yan turkey guda uku se Shawl shima me kyau daya sannan tacewa yaran kowa ya dauki abu daya da ze kaiwa Baby Iman.

A leda aka zuba musu kowa aka bashi nasa suka juyo zuwa gida, seda ta dakko Atamfar data ajiye da zata hada musu da ita ta saka da qaramar Barimar Gold da tun cikin su Ahmad ta siyeta da aka ce mata mace ce qarshe se gashi ta haifi yan Biyu duk Maza tama manta da ita se zuwan nan ta ganta shine ta dakko ta hada musu da ita.

Yan uwan Amiran Suna zaune a palour sun baje kayan rabo ana zuzzubawa ita kuma tana daga gefe tana duba dinkunan ta ga gadon Iman a kusa da ita Asma’u sukayi sallama ita da yaran gaba daya.

A sake suka amsa musu, Amirah ta ajiye Kayan hannunta tana kallonsu, hada ido sukayi da Ma’u, seda ta murguda baki ta juya ido sannan ta gaisheta ita ko Ma’u data na ankare da duk abinda takeyi murmushi tayi kawai ta amsa mata a ranta tace “zaki gane kurenki yarinya Allah sa kiyi kuskuren zagina wata rana”.

Addah da tajiyo muryar Asma’u tai wuf ta fito daga daki, bakin kaman ze tsage saboda fara’a suka gaisa tana satar kallon Ledojin da suka shigo dasu.

“Miqo musu Yar mana Amirah kina zaune” Addah ta fada tana yiwa Amiran signa da ido, se Amiran ta daga ido ta kalleta fuskarta na nuna alamun “kin san me kike cewa kuwa” Ma’u da duk tana kallonsu tayi saurin cewa”Aa barta ma kawai bari mu qaraso mu ganta kar a jagwalgwalata”.

“Wane irin magana ne haka ke gafara da Allah ki gani se ayita wani saka ya a ke ji kamar kaza tunda tazo duniya ai dole a dauketa a haka zata saba” ta kwashe Net ta ciro Iman ta miqawa Ma’u.

Bakinta dauke da Bismillah ta karbeta cike da taka tsan tsan, masha Allah kuwa ga kamannin Farida nan a Fuskarta koda yake ai duk yaran da Bashir suke kama saboda ita macece shiyasa kamar ta da Farida tafi fitowa. Tana hannunta duk yaran suka leqata har Ahmad yana kama dan hannunta ya riqe.

“Mami muna son ta mu tafi da ita Lagos” ya fada yana wasa da hannun yarinyar, se Ma’u tayi murmushi kafin ta amsa shi Addah tayi caraf tace “Da ita zaku tafi ai Malam Amadu ko kuma in kunyi gaba zata biyo daga baya”.

Sunyi kaman minti Goma Ma’u ta miqe ta kwantar musu da ita kafin ta turawa Amirah ledar kayan tace gasu nan babu yawa a sakawa Baby nan suma yaran kowa ya dire tasa duk kowa da abinda ya tsinto mata banda Aliyu da daman shi a qofar palour ya coge bema shiga ba.

“An gode madallah” Addah da sauran Yan gurin suka fada, sukayi musu sallama ta tattara yaranta sukayi waje kamar suna jira suka shiga zazzage kayan a qasa.

“Ke Amirah kinga rigar da nake gaya miki wallahi yar dubu Ashirin da biyar dinnan kin gani ga kudinta nan ma a jiki” Nusaiba Diyar Inna Gaji ta fada dan zancen rigar da za’a sakawa babyn lokacin Shagalin suka gama take gaya mata akwai wadda tagani ta fita kunya a gurin wata qawarta har sun fara shawarwarin yanda za’a samu kudi aje a siyo se gashi Allah ya kawo mata daga sama.

Atamfar ta sake dagawa ta riqe baki tace “Amirah Embellished ce fa, bari dai muga ko qaramar ce” ta hau duba lambar Atamfa da fentin jiki seta dau sowa tana cewa

“Wallahi babbar ce, ke harda dan kunnen Gwal kai lalai matar nan dagaske take Dama Allah ya bani kishiya irin haka ai na huce takaicina se in ta haihuwa duk shekara tana kawomun kayan arziqi” Nusaiban ta fada tana ta faman daga kayan.

“Ke na taba ki da Arziqi, wannan uban kayan da kudinta ko na mijin aka siya?” Asiya yayar Amirah ta fada se Ummi da bata sa musu baki ba tayi caraf tace

“Ce miki akayi itama cima zaune ce irinku kuna zaune kuna jira se abinda miji ya dakko ya baku, toh nema takeyi tana aiki tana kasuwanci ta kayan nan ma da kika gani a shagon ta take siyarwa ga ledar nan kina gani”.

Ledar suka duba gashi nan kuwa “Asma’u Kiddies shop” a rubuce, se Nusaiba ta riqe baki tace

“Lallai kice ta kama qasa irin wannan kaya yan order kodai ma shagon ne naji ana zancen sa an ce duk Gombe Albarka ko da yake wannan iwar dukiya da aka mutu aka bar musu dole suyi ta bude gurare, jifa Salon din Yayar ta Bilkisun nan ba abinda ba’ayi na gyaran mace a gurin” Inji Asiyar,

daga nan kace nace ya kaure aka shiga fadar irin abubuwan da yan gidan su Ma’un suka kafa, kowa fadi yake suna birge shi yanda kansu yake a hade bazaka taba ganin wani abu wai shi yan ubanci a cikinsu ba.

Ran Amirah in yayi duba ya baci jin yabon da suke wa Ma’un, ta rasa a duniya dalilin da yasa Asma’u keda farin jinin mutane, duk wanda ya budi baki sedai ya fadi Alkhairinta badai sharri ba.

“Ke kanki shaida ce akan kyawawan halin Asma’u ai da mu’amarata me kyau” zuciyar ta ta raya mata. Seta ja tsaki tabbas ita sheda ce akan karamcin Anty Asma’u, tana da kyakykywar zuciya tabbas da mu’amala me kyau. Sannan sam abun hannunta be rufe mata ido ba gata da sauke kanta matuqa bazaka taba cewa ta fito daga gidan arziqi ba sedai idan ka dubi halayyarta kasan tabbas daga babban gida ta fito da suka tashi cikin Arziqi suka jiqu dashi dan haka basu dauke shi a matsayin wani abun dagawa ko da zesa suyi girman kai ba.

Tsaki ta kuma ja ganin itama ta bige da yabon Ma’un a zuciyarta, tabbas tana kishi da Asma’u da duk wata halayya ta ta. Ta kan ji dama ita ce Asma’un, bata kasance yar Babban Attajiri kamar Baban Asma’u ba kuma wannan ne kadai tasan bazata samu ba amma baya ga haka tayi Alqawarin duk abinda Ma’u ta mallaka seta seta same shi.

Tayi zurfi cikin tunaninta har bata san sun gama zuba kayan ba kowa ya fara neman makwancinsa se itama ta miqe ta dauki Iman suka shige daki suka kwanta saboda su samu tashi da wuri.

A bangaren Ma’u ma suna komawa kowa ya nemi makwanci da wuri nan da nan bacci ya dauketa dan bata ma ji jerin missed calls din da Malam Bash ya ringa jera mata ba har bakwai seda Asuba data farka. Seda tayi sallah ta kirashi, qorafi ya hauyi mata akan rashin Amsa wayar ta samu ta bashi haquri akan bacci ne ya dauketa, basu jima ba sukayi sallama kafin ta sake komawa bacci.

Qarfe goma na safe sautin kidan kwaryar da ake a filin gidan ya tasheta, da farko ta zata ko kunnenta ne beji daidai ba, seda ta kasa kunne sosai sannan ta tabbatar dagaske fa a cikin gidan ne dan ga hayaniyar Mata nan tana jiyowa.

Miqewa tayi zuwa jikin window dan tana dakin ta na saman Bashir ne, labulen ta janye ta leqa da mamaki take kallon Mata masu kidan kwaryar da kuma wadanda suke juyi a fili suna watsa musu kudi.

“Ikon Allah to me akeyi a gidan?”Ta fada a fili, ganin babu me bata amsa yasa ta saki labulen, gadon ta fara gyarawa kafin ta shige toilet tana ci gaba da mamakin abun. Wanka tayo ta shirya cikin wani danyen Lace Baqi da akayiwa kwalliya da Jan Zare ya karbi farar fatarta sosai da sosai ta kashe dauri tareda baza turarenta kafin ta dauki wayarta ta fito daga dakin takalmin qafarta na kwas kwas.

Palour kasan qal dashi Aliyu da Amna na zaune akan Dining suna karyawa duk sunyi wankan su. Gaba daya suka gaisheta tana shirin tambayarsu sauran Ahmad ya bude qofa ya kwaso da gudu Muhammad na bayansa har yana neman faduwa ta tare shi

“Ya haka bana hanaku guje gujen nan ba se kunji ma kanku ciwo ko” ta fada bayan ta tsaida Ahmad din.

“Mami biki akeyi a waje zo ki gani harda masuyin kida da calabash irin na gidan Baba Sarki” Ahmad din ya fada.

“Nima naji kidan tun ina sama ai me yake faruwa a gidan ne?” Tayi tambayar tana kallon Amna da Aliyu dan sune manya.

“Wai suna waccen matar sukeyi” Aliyu ya fada ba tareda ya dago ya kalleta ba.

“Wace matar“ ta tambaya tana tsare shi da ido dukda ta gabe wa yake nufi amma se yaqi ya dago bare ya kalleta kuma yaqi magana se ma kaida kansa gefe da yayi.

“Yayi kyau matar Baban naka ce waccen matar ko Aliyu idan na sake ji se ranka ya baci tabbas” ta fada tana jan kujera ta zauna. Tea ta hada ta debi dankalin da suka soya dan da zafinsa ta hada ta fara ci a ranta tana ayyana kenan bikin suna sukeyi yau, sekace dole su kuwa ai da sun haqura sa hadu a wani karon amma to ita ina ruwanta ma.

Tsaf suka gama cin abincin ta koma cikin palour ta zauna, wayarta ce ta shiga qara Amna dake kusa da ita ta miqa mata. Zahra ce take kiranta Qawarta ce tun ta yarinta tare suka tashi daman sunyi da ita yau din zata zo bayan sun gaisa kuwa take shaida mata tana nan tafe fa gurin qarfe biyu na rana sukayi sallama ta kashe wayar.

A hankali hayaniya ta kaure gidan mata kuwa se shigowa suke kamar ana tunkudo su lokacin har sha biyu tayi ta dena jiyo kidan kwaryar da alama sun tashi ne sedai hayaniyar mata kawai.

Saboda zuwan Zahra yasa ta shiga kitchen, fried rice ta dora ta window kitchen din da yake kallon tsakar gidan take kallon ikon Allah yanda Jama’a ke tururuwa a gidan nasu wasu na shiga wasu na fita. Bata tsinke da lamarinba seda ta ga an wangale get ana shigo da kujeru harda Wata rumfa da kayan decoration ba bata lokaci suka shiga har hadawa kuwa

“Shagali kace abin nayi ne to Allah yasa a tashi lafiya” ta fada a fili tana hada salad dinta, kafin ta gama kuwa har sun gama sauke kaya sun hau shiryawa ga kayan DJ an ajiye daga gefe suma.

Harabar gidan nasu nada dan girma ba laifi dan a qalla zataci mota biyar zuwa shida saboda filin gefen su da Bashir ya shigo dashi yayi ginin Bangaren Amirah ya ragu sosai shi ya qarawa gurin girma. Tsaf suka gyare ko ina aka jera kujeru can daga gefe ga High-table an shirya se zama kawai ya rage.

Tsaf ta gama girkinta suka jere kayan akan Dining tana shirin shiga daki tayi sallah dan har biyu ta kusa a ka kwankwasa qofa, jafar tacewa yaje ya bude ta dan daka dan taga wanene.

Sadiya da Afiya ne qannen Bashir se Suwaiba diyar qanwar Baban su suka shigo ko wacce da shirgin Jakar kaya a hannunta ga yara na biye dasu. Kada ran kada han take kallonsu har suka qaraso tsakiyar palour suka zube akan kujeru suna wash Allah jij sanyin Ac da qanshin turare na ratsa su.

A kusan tare suka gaisheta, Asma’u da bata dara daga inda take ba ta amsa tana kallonsu da jiran ji da wacce suka zo kuma.

“Ku tashi mu shirya lokaci ya na tafiya dan nasan yanzu zakuga shagali ya kankama fa kuma ni ko wanka ma banyi ba na fito daga gida” inji Sadiya

“Ai bake kadai ba nima banyi wankan ba haka na fito” Suwaiba ta mara wa Sadiyan Baya suka miqe kowacce ta sabi jakarta suka doshi corridor da dakunan suke inda anan Ma’u ta coge. Seta qara gyara tsayuwarta ta yanda ta raba hanyar biyu ba ta yanda wani ze wuce fuskarta na nan a yanayin da bazaka iya fasaltawa ba.

“Bari mu wuce Anty” Sadiyan ta fada
“Zuwa ina?” Asma’u ta tambayeta, se suka kalleta duk su biyun da mamaki, Suwaiba ce tayi qarfin halin cewa
“Wanka zamuyi”.

“To yaushe gidan nan ya zama gidan wanka kuma bani da labari?” Ta fada tana gyara tsayuwarta da jinjinawa rainin hankalin wadannan yaran ta kuwa shirya nuna musu iyakarsu yau dan yanzu ba da bace.

Kallon kallo aka shigayi tsakanin Suwaiba da Sadiya, still Sadiyar ce ta sake magana dan tafi sauran baki tace “ban gane ba Anty wanka fa mukace miki zamuyi anan kine zancen wani gidan wanka kuma ko bamu da damar da zamuyi wanka a gidan dan uwan mu ne?”

“Allah sarki masu Dan uwa dama kuma babu ita kuna iya juyawa kuje wani Gurin tunda bani kadai bace a gidan ko? Ina ga ai kamar a kwai yar uwarku ma kuna iya zuwa gurinta”.

Ba qaramin mamaki ne ya kama su ba da jin kalaman ta, Antyn da ada a dakinta suke duk wata dabdalarsu qarewar wanka har kayan sawa ta kama basu take idan ana wani taro ka zo da kayan da basu kamata ba seta dakko na fita taro ta baka ko yanzu ita Sadiya bata zo da mayafin da zata hada kayan da zata saka ba dan a safiyar nan suka samu labarin taron sunan suka kuma qudiri niyyar se sunzo duk kuwa da gargadin da Dada tayi musu amma sunce baza’ayi babu su ba wallahi.

Sabon Leshinta ta dakko zata saka bata rigada ta siya masa mayafi ba dan ta tamawa bikin Qanwar mijinta ne zata saka saura sati biyu yanzu se kuma ga wannan taron ya taso shiyasa ta dakko tasan bazata rasa mayafi gurin Anty Asma’u ba tunda tana gari qila harda jaka ta samu amma shine take gaya musu wadannan magananganu haka.

“Ku nake jira zan rufe qofata lokacin sallah ya kwace mun” suka ji muryarta ta dawo dasu daga suman mamakin da sukayi, har Suwaiba ta budi baki zatayi magana Afiya da tun farko bata ce komai ba ta dakatar dasu da cewa

“Sadiya ku muje mana ko bakiji me tace bane”
Dukyanda suka so su sake magana kuwa ta hanasu haka suka tattaru kayansu sukayi waje Sadiya da Suwaiba na kumfar bakin bazasu yarda ba su zata wulaqanta suda gidan dan uwansu ai se sun kira yayan suji idan shi ya bata sabon lasisin wulaqanta su.

Oho bata ma san sunayi ba dan suna fita Jafar ya tura qofar ya rufe dan bata buduwa ta waje dole seta ciki suka ci gaba da kallonsu ita kuma ta shiga daki ta tada sallah. Tana dakin Jafar ya shiga da sallama

“Mami ga Umman su Jawad tazo”(Zahra qawarta)
“toh gani nan zuwa” ta fada ya juy ya fita. Daurin ta ta gyara da fuskar ta ta fito fuska a washe suka rungune juna ita da Zahran da murnar yaushe gamo dan an dade ba’a hadu ba kafin suka zube akan Two sitter ta shiga yiwa Zahra tsiyar qiba.

“Kai matar nan gaskiya wayo kikewa Yah Sayyadi ji yanda kike narka qibar kamar wata Aisha Buhari 😂😂🤐”
“To ya za’ayi barni nayi qibata kowa ya ganni yasan ina jin dadi tunda jikin yaqi zama irin naku jikin models” Zahra ta fada da sigar shaqiyanci suka kwashe da dariya tareda kashe wa, Sallamar da akayi ta katsew Ma’u maganar da tasoyi.

Rahma ce matar Amiru qanin Bashir bayanta kuma Kamila ce itama qanwar su Bashir dince da me aikinta dauke da danta dagaje dagaje dashi ga ledar kaya a hannun Kamilan. Da sauri Kamilan ta shigo dan seda Rahma ta matsa gefe ta bata hanya ta dire ledar a kan centre

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login