Showing 48001 words to 51000 words out of 177840 words

Chapter 17 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79156

Sadauki farin sani. Haka ta koma falon Hajja tana kuka wiwi, Hajiya Hadiza ranta ya ɓaci da wannan hukunci na Sadauki. Hajiya Fatima ke fadin ai gwara da hakan ta faru tunda ita ba za ta iya saita bakinta ba. Umma dai ba ta tanka ba.

A ɓangaren Haulatu kuwa, kuka wiwi haka ta dinga yi, har Safina ta shigo tana aikin rarrashi amma ko kallonta ba ta yi ba. Ita a ganinta ai wannan son kai ne da son zuciya. Ta ya ya ita aka yiwa laifin kuma zai ɗau hanu ya mare ta? Ita tun ganinsa da ta soma yi dama ta fahimci baƙin azzalumi ne da ba ya ƙaunarta. Da ace ya san yadda ta tsani namiji mai bugu da bai yi kuskuren ɗora yatsunsa a sama fuskarta ba. Hajja itama ta shigo ta hau rarrashi da sababin ita Sadauki bai kyauta mata ba. Yanda ta dinga nuna fushinta a kai har tana ikrarin za ta kira shi ta yi mishi tas tunda dai ko ubansa bai isa ya ja da ita ba. Sai abin ya ɗan yiwa Haulatu dadi a rai, ba ta kuma taɓa ji Hajja ta burgeta ba sai yanzun. Kiran da aka shigo yiwa Hajja kan cewa ta yi baƙi yasa ta fice daga dakin, lokacin hayaniya sosai ya kaure a falon ga dukkan alamu an ƙara yawa ne a gidan.

"Ki yi hakuri ki tashi muje ƙasa ki ci abinci."

Jin abin da Safina ta ce yasa Haulatu miƙewa zaune cikinta har yana ƙara amma damuwarta da ɓacin ran sun shafe wancan.

"Don Allah Safina wai rashin kunya na yiwa Umma?"

Safina ta ɗan yi jim, ita kuwa Haulatu wai wace iri ce ne? Yanzu ba ta ga irin katse zancen Umma da ma ɗaga muryar da ta yi mata ba? Can ta dube ta dakyau cikin sanyin murya ta amsa.

"Gaskiya har ga Allah kin ɗaga wa Umma murya. Ta kuma nuna ƙarfin iko da isa a kanki ta hanyar dakatar da ke daga maganganun da kike yi sai ki ka nuna ba ta isa ba. Ba zan ɓoyemaki ba ni kaina yanayin da kika yiwa Umma magana bai min dadi ba Haulatu. Wannan kuskure ne babba. Ki yi hakuri da marin da Yaya Sa..."

"Ni ba maganarsa nace ki yimin ba. Na yarda na yiwa Umma laifi. Wallahi na ji babu dadi, ta ya ya zan ba ta hakuri? Ni na sani Umma yanzu ranta ya ɓaci da lamarina. Wallahi ni ban san ma sadda na ɗaga muryar ba."

Sai ta fashe da wani sabon kukan mai nuni da tsantsar nadamarta da dana sani. Shigowar Umman ya sa suka dube ta. Fuskarta a sake ta dubi Safina.

"Safina, maza je ki wajen Baba Saude ki karɓo muku abinci, an kammala."

Ta amsa da toh kafin ta mike ta fita. Umma ta shigo dakin sosai, da sauri Haulatu ta mike tsaye ta ma kasa kallonta, ta rasa me za ta yi? Sai kawai gani ta yi Umman ta riƙo hannunta ta zaunar a gefen gadon.

"Ba ki kyauta ba ko kadan Haulatu. Me kika son ki nunawa mutanen gidan nan? Ni uwar banza ce?"

Har a sannan murmushi mai ciwo Umma ke yi, Haulatu ta girgiza kai sai ta ƙara karfin kukanta. Fuskarnan ta yi ja, ga kuma shatin hannun Sadauki kwance a gefen kumatunta.

"Wallahi ban san na yi ba. Ki yafemin don Allah Umma. Ba zan ƙara ba."

"Ya wuce. Amma ki ƙara hankali da rayuwa da kuma zaman duniyarnan Haulatu. Idan ba ki iya zama da mutane ba, za ki wahala a rayuwarki. Yanzu dai kusan a farko ke aka yiwa laifin, amma me? Sai ki ka nuna gajen hakuri har kika dauki matakin da ya haifar maki da dana sani. Da kin yi shiru da bakinki, kina tsammanin Fahima za ta sha ne a hannun mutanen da ke falon koda kuwa ni ban yi magana ba? Don Allah ina roƙonki ki koyi hakuri da kuma danne zuciyarki. Kar ki sake kuma ki ce za ki tsani ɗan uwanki don ya mareki, gyara ya yi maki. So yake ya ga kin fahimci kuskurenki. Kullum ina ƙara fahimtar da ke yanayin rayuwa, idan ba ki koyawa zuciyarki hakuri yanzu ba, sai yaushe? Akwai namijin da zai dauki wannan sakarcin naki?"

Ta turo baki kaɗan jin Umma ta sako batun wani namijin.

"Ki yi hakuri." Ta ƙara maimaitawa karo na biyu. Sai a sannan Umma ta yi murmushin da ya fito tun daga zuciyarta.

"Ya wuce. Allah ya shiryamin ke, ya yi maki albarka."

Cike da jin dadi ta yi dariya tana mai amsawa da amin gami da rungumar mahaifiyarta. Dawowar Safina dakin dauke da faranti na abinci har da flask na ruwan shayi ya sa Umma mikewa ta bar dakin zuwa falo. Nan suka shantake suka shiga hira ran Haulatu ya yi fari ƙal tamkar babu wani abu da ya faru don a yanda ta zuciya ta rantse ma ko wayar ya maido ba za ta karɓa ba tunda ta ji Safina ta ce wai ya dauke wayar bayan ta bar falon.
Su na kammalawa, Safina ta dube ta.

"Zo mu tafi kiga Anti Raudha, suna can gidan Abba."

Zuwa sannan ta gane waye Abban tunda yana shigowa su gaisa da Hajja, kuma ta gan shi mutum mai sakin fuska, koda ba ta falon to fa sai ya tambaye ta. Alhaji Ridwan kenan mahaifin Sadauki. Wannan ne ba ta sani ba. Ta yamutse fuska.

"Da wannan yatsun da suka kwantamin a fuska na wancan mugun kike tunanin zan fita a samu abin magana?"

Safina ta dubi fuskar sosai.

"Lah, wallahi ko kadan ba a ganewa gaba daya ya goge sai ɗan ja da wurin ya yi kuma shi ma nasan zuwa anjima za'a nema a rasa. Don Allah taho mu je ki gan ta."

Jin haka Haulatun ita ma ta miƙe, sai da ta ƙarasa gaban madubi ta ga dagasken ba lallai a gane ba kafin ta yarda da fitarsu.

Falon Hajja a cike ba ta ko kalli kowa ba ta fice ta bar Safina na aikin gaishe-gaishe tunda dai ita ba sanin su ta yi ba duka baƙin fuska ne.

Gidan Alhaji Ridwan a cikin kewayan babban gidan yake, shi ne kalarsa ta bambanta da na su Hajja da Alhaji. Ba ta taɓa shiga ba, ko sadda Hajja ta kai Umma gidajen yaranta da na yan uwanta koda wasa ba ta yi yunƙurin bin su ba don a lokacin sosai take jin haushin Hajjar.

Tun daga farfajiyar gidan da suka shiga ƙaton ƙyauren, ta ga ya sha bamban da duk gidajen da ta taɓa sa ƙafarta ciki tun zuwanta Katsina. Baki ta buɗe tana kallon yanda aka ƙawata shi har da wani gefe na ƙaramin garden da aka zagaye da wani gajeran katanga an yi shuka mai kyau da burgewa a cikinsa ga wani kujera mai lilo, a iyakar hangen Haulatu dai ta tabbata wajen akwai abubuwan burgewa a ciki. Idan yamma ta yi zai fi dadin zama. Ba ta ƙara tsinkewa da tsaruwar gidan Alhaji Ridwan ba sai da suka shiga wani babban falo da ya ji kayan ƙawa iri-iri masu tsada koda kuwa ba a fadi, inda anan ne suka ji tashin waƙa da kuma muryoyin yanmata wadanda suka iya waƙar su na bi muryar kowa a sama, ga rawa su na tiƙa abin su. Ga dai Ac ta ko'ina tana aiki amma ina, tsabar rawa da suke tiƙa da kuma yawan da aka yi ya sa falon ke tashin zafi.

"Ikon Allah, yanzu wannan duk murnar na kawo lefe ne?" Fadin Haulatu a fili, amma kasancewar wurin akwai ƙara da hayaniya bai bari ko Safina dake gefenta ta ji ba. Wuri ta nema ta zauna ta dora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallonsu. Daga yanayin yanda ake yiwa wata ƴar baƙa gajeriya mai ɗan jiki guɗa a kai bayan wata ta shigo ta sanar da batun zuwan masu kawo lefe ya sa Haulatu fahimtar ita ce Amaryar. A lokacin ne kuma suka kashe kiɗan aka hau rububin zuwa ganin lefe jin wata na fadin ai lefen haɗe yake da kyautar wata haɗaɗɗiyar mota.

"Wash! Wallahi ni dai na gaji, ku je ku dawo ku bani labari."

Haulatu ta dubi mai maganar, kusa da ita ta zauna gumi duk ya gama jiƙa mata jiki, sai numfashi ta ke saukewa yayinda hannunta ɗaya ta dafe kanta da shi da ya ɗan soma sarawa. Za ta girmi Haulatun da shekara ɗaya ko biyu ma. Siririya ce baƙa. Tana sanye da wata doguwar riga ƴan kanti da ta kama jikinta.

"Haba ta Yaya Sadauki, don Allah ta so muje."

Haulatu ta ɗaga kai ta kalli mai wannan kirarin, ta ji ɗazun an kira ta da suna Jannat. Sai ta ji wasu hudu a gefe sun kwashe da dariya gami da cafkewa.

"Ta Yaya Sadauki manya, aikin ɓurr, da ace ma ya san da zamanta shi ne. Amma babu abin da ya haɗa fura da kashi. Manyanta ma basu ishe shi kallo"

Nan da nan sai ta gefen Haulatun ta zabura ta mike tana mai nuna wacce ta yi zancen da yatsa, cike da jin masifa har idanunta na ƙanƙancewa take fadin

"Kinsan Allah, ina gargadinki da babbar murya ki fita a harkata Fa'iza, idan ba haka ba zan maki rashin mutunci. Ai gwara ni akan ke da kike son Yaya Khaleefa kuma kina ji kina gani ya yi aurensa da masoyiyarsa ya ƙyale ki kika yi bandaro."

Jin haka sai abin ya kusan zame musu faɗa, Haulatu wani takaicinsu ya kama ta, ta mike ta fice a falon tana jan tsaki. Ta yarda akwai mahaukata a wannan zuri'ar tasu. Ita kaf a matasan gidan nan ba ta ga wani wanda har a rai ta ji ya burge ta da sunan soyayya ba. Daga wancan mugyambon da ya mare ta, sai wancan likitan mai shegen taƙama kamar wani basarake, sai kuwa wancan ɗan Malamar mai shegen kallo kamar idanunsa za su faɗo. Mu'az kuwa ta ɗan ga kirkinsa tunda ya ci darajar ƙawarta kuma ƴar uwa Safina, uwa uba ya nuna damuwarsa a kanta har ya siya musu waya ita da Ummanta.

Kai tsaye sashin Hajja ta yi niyyar komawa sai kuma ta tuna Umma ta ce ta dinga zuwa tana gaida su Baba Dakta da Alhaji, hakan yasa ta fara da ɓangaren Baba Alhaji. Da sallama a bakinta ta shiga, babu kowa sai ƴan aiki don su Nene suna can wurin lefe sashen Hajja. Bayan sun gaisa ta tambayi ko Alhaji yana ciki. Dije ta ba ta tabbacin yana can barandarsa. Ganin ba ta fahimci wajen ba ne sai Dije ta taka mata har can cikin falonsa gami da yi mata nuni da wata ƙofa dake a bude ta hango kafafunsa yana daga kishingiɗe ne saman darduma. Da sallamarta ta ƙarasa bayan ya amsa ta shiga. Ganinta ya sanya shi ajiye littafin da yake dubawa, ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa fuska a sake yana dubanta ta cikin gilashin dake idanunsa

"Kamar ɗiyar Na'imatu?"

"Ni ce." Ta amsa tana murmushi. Shi kuwa ƴar dariya ya yi.

"Wato ke sai na dinga biya zan dinga ganinki ko? Yaushe rabon ki zo mu gaisa?"

Sai ta ɗan ji kunya ya kama ta. Ai za ta iya cewa rabonta da ɓangarensa tun sadda suka yi dirama da Sadauki, gwara ma Baba Dakta ya gan ta a jiya sadda ta shiga kai wa Maama saƙon dambun da Ummanta ta dafa.

"A yi hakuri Baba Alhaji."

Ya yi murmushi.

"Ba kya laifi ai ke Amarya ce."

Ta zaro idanu.

"Eh? Ban fahimta ba, Amaryar wa? Aure za'a yi min?"

Dariya ya ɗan yi.

"Aa, wa zai maki auren dole? Ai ke ce ta ƙarfen tawa."

Ta sauke ajiyar zuciya na samun sukuni.

"Au, ni fa na yi zaton ko aure ku ka yi shawarar yimin. Hum um, ai wallahi da ba zan zauna ba. Ni na tsani aure."

Alhaji ya kalle ta dakyau. Bai ga alamar wasa koda a fuskarta ba, hakan ya ba shi tabbacin iyakar gaskiyarta ta faɗi.

"Kul, kar ki ƙara cewa kin tsani aure. Aure ai sunnah ce ta Ma'aikin Allah (s.a.w). Kuskure ne babba ki ƙara furta hakan. Mu a gidannan ba ma yiwa yara auren da ba su so, idan har ya kasance ɗaya ke so, ɗaya ba ya so, akan haƙura da yin sa, domin mun fi kyautata zaton barin shi ya fi alheri. Idan kuwa ɗaya ba ya so, amma ya kwantar da kai da niyyar yin ladabi ga hukuncinmu, mukan girmama ra'ayinsa mu kuma ji dadin ya yi biyayya gare mu. Ƙarshe kuma cikin iko na Allah sai ki ga auren ya yi albarka, an samu ƙauna da fahimtar juna a ciki."

Ta jinjina kai tana ɗan murmushi.

"Na gane Baba Alhaji. Ni amma ba zan yi auren ba ne a rayuwata. Ba zan jure namiji ya dake ni ba, na rantse ramawa zan yi. Ni ina da zafi ba irin Umma ba ce da ta yi sake mijinta ke tafkarta kamar ya samu jaka ba."

Alhaji ya ɗan girgiza kai, ya fahimci illar da Ɗan Mutuwa ya haifar a tunani da kallon da ɗiyarsa ke yi wa aure. Yana daga babbar illar dukan uwa gaban yaranta, wataran ma idan hakan ya ci gaba da faruwa, tsaf za su kai hannu su ramawa uwarsu. Kafin Alhaji ya ƙara magana, ta ɗauko masa hirar irin dukan da Ummanta ke ci a wurin Ɗan Mutuwa. Bai katse ta ba, yana sauraro ne da ka lura da yanayin fitar lafuzzanta wadanda ke cike da kura-kurai da ma rashin nuna ladabi ga wanda ke gaba da kai. Ganin muryarta ta raunana za ta fara kuka ya sa shi saurin dakatar da ita.

"Ya isa hakanan, na fahimce ki, na kuma fahimci dalilinki na rashin son aure duk da kin ce Ummanki tana son ki yi shi. Ke yanzu karatun kika fi sha'awa kenan?"

Ta yi saurin jinjina kai tana kauda hawayen da suke yunƙurin zubo mata.

"Sadauki? Yaushe ka shigo?"

Jin sunan da Alhaji ya ambata ya sanya ta saurin juya kanta, yana tsaye jikin ƙofa, kusan zai ce tun soma hirarsu ya shigo sai dai ganin da ya yi hankalinsu gaba daya ba ya kansa ya sa shi yin shiru har sai yanzun da Alhaji ya ankara da shi. Ita kuwa Haulatu nan da nan ta miƙe.

"Zan je wurin Baba Dakta." Alhaji kamar zai tsaida ta sai kuma ya fasa gami da fadin.

"Ki je amma gobe ki zo kamar yanzu ina son mu yi magana."

"Gobe Umma ta ce wai zan soma zuwa makarantar islamiyyar su Safina." Ta fadi tana ɗan yamutsa fuska da hade rai, don ita tun ganin Sadauki a wurin ta ke cike da jin haushinsa.

"Masha Allahu. To kar ki damu, ki bari har ku taso. Ba ki gaida Yayanki ba."

Ta turo baki ba ta ko kalli Sadauki wanda tuni ya ƙaraso ciki ya zauna yana danna waya ba.

"Ai mun gaisa ɗazu."

Daga haka ta juya ta fice. Sashin Baba Daktan ma ba ta je ba kawai sai ta koma wurin ƴan ganin lefe, duka ana falon ƙasa, Safina ta jawo hannunta ta katse yunkurin hayewa sama da ta yi.

"Ina kika shige ne? Muna can muna raba faɗa na neme ki na rasa. Zo ki sha kallon abin arziki, har da mota fa aka kawo mata. Akwatuna har set biyu."

Yamutse fuska ta yi.

"Ni kaina ke ciwo, zan koma daki."

Daga haka ta fice ta bar Safina da bin ta da kallo kafin ta juya ta koma cikin ƴan uwanta.

***
Yana kwance saman kujera ya lumshe idanu, tun dawowarsu garin Abuja gaba daya hankalinsa ya kasa kwanciya. Komai yake yi sai ya dinga ganin fuskarta da kyawun diri da Allah ya yi mata na mishi gizo a idanu. Dagaske, Zaid bai taɓa ganin abin da ya fisgi hankalinsa lokaci guda kamar Haulatu ba. Sanadinta ya tattara ya dawo Abuja bai shirya hakan ba, hatta Jalilah ta yi mamakin dawowarsu da wuri tunda ya ce sati guda zasu yi kafin su juya sai dai lura da cewa kamar akwai abu da ke damunsa ya sa ta ja bakinta ta tsuke. Shi kuwa kafin su taho koda ya shiga Babban gida, sam bai kalli ɓangaren Hajja ba, alhalin yana da tabbacin a can ɗin ne zai gan ta. Abin kunya ne a gan shi ɓangaren Hajja a yanzu, kowa ya shaida cewa ba ya shiga ɓangarenta tun faruwar lamarinsa da Jikarta Zaituna.

"Honey, wai lafiya kuwa?"

Ya sauke ajiyar zuciya jin muryar Jalilah a gefensa tana mai shafar gefen fuskarsa. A hankali ya buɗe idanunsa, cike da kasala ya amsa.

"I'm ok. Kaina ke ɗan sarawa kawai."

Ta numfasa fuskarta na nuni da tsantsar kulawa da damuwa.

"Sorry, bari na kawomaka ruwa da magani ka sha. Watakila gajiya ce."

Gyaɗa kai kawai ya yi. Daga haka bai ce uffan ba har ta mike ta nufi ɗaki don ɗauko maganin. Ya maida duba ga ƙaton frame na hotonsu da ke fuskantarsa. Duk wanda zai kallo Jalilah ya kawo wani kushe a halittarta to fa sai dai mahassadi. Ko shi din ma zai jima bai samu abin kushewar ba. Koda dai shi ba don kyau ya aure ta ba face yabawa da kyawawan halayyarta. A sanin da ya yi mata a shekarun da suka kwashe tare a makaranta, ta samu kyakkyawar shaida na kamun kai da kuma kamala. Wannan ne babban dalilinsa na zaɓo ta matsayin mata ba tare da ya san cewa dama can ta jima tana sonsa ba sai dai irin matar nan ce mai miƙa lamura ga Allah da kuma yawan addu'ar neman zaɓin Allah. Sai ga shi tana zaune Allah ya kawo mata shi ya furta yana kaunarta da kuma aure. Ranar kuwa da ya je suka yi zancen har hawaye ta fitar don farin ciki. Tana girmama shi, tana ba wa Mahaifiyarsa girma, zai kuma ci gaba da darajata, zai yi kokarin ɓoye halin da yake ciki ko don ita. Ba ya burin ya ɓata ranta a ƴan watanni da aurensu. Abin da ke zuciyarsa kuwa, ya bar shi matsayin wani abu na daban da zai yi gaggawar yaƙi da shi, sam ba zai bari Hajja ta ci nasara a kansa ba. Da haka ya rufe babin zancen.

***
Ta kalli kanta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login