Showing 147001 words to 150000 words out of 177840 words

Chapter 50 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79158

yawo a kwanyarsa, haka ya yi ribas ya fita zuwa gidansu yana jin wata sabuwar kauna da soyayyarta na ratsa shi.

***
Sadauki da Haulatu tun daga wannan ranar suka yi wata iriyar shaƙuwa mai wuyar fassara sai dai duka abin da suke yi ta waya ne. Idan ya so ganinta sai ya shigo da zummar gaida Hajja da Umma, ko kuma ita ta fita da zummar gaida su Baba Alhaji ko kuma zuwa wurin Fu'ad ɗaukar darasi, tun tana ɓoyewa Ummanta har dai watarana ta kama ta tana amsa waya, har ta shigo ɗakin ba ta sani ba, Umma ta saurara dakyau, tabbas kalamai ne masu nuni da tsananin bege da ƙauna ga wanda ake wayar. Motsin Umma ne ya sanya ta saurin miƙewa zaune gami da katse kiran. Ta sunkuyar da kai ganin kallon da Umman ke bin ta da shi. A ɓangaren Umma kuwa, kallo ne na mamaki tsantsa, waye wannan da ya yi sa'ar da Haulatu ta saurare shi? Har ta yi watsi da dukkan makaman yaƙinta akan maza? Ganin yanda yarinyar ta rikice yasa ta ƙaraso ciki sosai ta zauna gefenta, wayar sai ruri take yi amma ta ƙi ɗauka, Umma ta kai hankalinta ga wanda ya kira, Heartbeat, shi ne ke yawo kam screen.  Ita kuwa da sauri ta saka wayar a flightmode. Ɗan murmushi Umma ta yi kafin ta ce.

"Ya sunansa?"

A nan ƙirjin Haulatu ya ƙara tsananta bugu, ta ɗan ɗago kai ta kalli Umman, babu alamun ɓacin rai a tattare da ita sai dai kuma ba ta san me jin sunan zai haifar gareta ba. Tun ba yanzu ba, Umman ta nuna hankalinta zai fi kwanciya ace ba ta auri ko ɗaya a cikin samarin gidan kar ya zame musu abin magana. Ta tabbata ba za ta ji dadin amsar da zata ba ta ba, amma ta gwammace ta faɗamata gaskiya. Bayan Umma ta gama sauraronta shiru ya biyo baya. Da yanayi na damuwa a fuskarta take duban Haulatun.
   
   "Amma har ku ci sati biyu ku na abu ba ki sanar da ni komai ba? Sannan ba kya tunanin matsalolin da soyayyarku za ta haifar? Dama batun karatun da ki ka fake da shi, don ba kya son su wadancan ɗin ne?"

Tuni kwalla sun ciccikowa Haulatu, ba ta san halin da za ta faɗa ba idan Umma ta datse alaƙarta da Sadauki.

"Ki yi hakuri Umma. Tsoron da na ji kenan shiyasa ban faɗamaki komai ba."

Girgiza kai Umma ta yi cikin sanyin murya ta amsa.

"Ba laifi ki ka yi min ba Haulatu, ina dai gudun abin zai je ya zo ne. Ba na son ƙananun maganar gidan nan. Ni ban ce ki bar kula sa ba, sai dai ina mai baku shawarar ku sanya Allah a farkon lamarin, ki dage wajen nema maku zaɓin Allah. Abeed ba shi da matsala babba, mutum ne da kowa ke yabonsa daidai gwargwado. Amma ina tsoron kar mahaifiyarsa ta ƙi aminta da ke kamar yanda na baya suka yi duk kuwa da cewa ke ma ba ra'ayin auren nasu kike ba."

Umma ta ɗan numfasa, Haulatu dai shiru amma ita ɗin ma jikinta ya ɗan yi sanyi domin sam ba ta kawo hakan a ranta ba. Ƙauna da soyayyar Sadaukin su ne suka makantar da ita. A haka dai ba ta fuskantar kowace matsala daga Momi Nuratu, watakila yanzun ba ta san da meke gudana ba.

"Ki dage da addu'a. Ni ba zan yanke alaƙarku ba, amma ina roƙon Allah ya yi maku zaɓi na alheri. Sai mun dawo."

Daga haka Umma ta miƙe ta cire wayarta a chaji ta fita, dama abin da ya shigo da ita kenan don za ta fita raka Hajja asibiti ganin likitanta na ido.

Sai a sannan ta cire wayar a flightmode amma fa jikinta har lokacin a sanyaye, ko mintuna uku ba ta yi da buɗewar ba sai ga kiran Sadaukinta. Tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba ya ce.

"Kin tayar da hankalina fa, meyafaru ki ka katse kirana kuma ki ka kashe wayar?"

"Ka yi hakuri please. Umma ce ta shigo."

"Kina nufin har yanzu ba ki faɗamata ba?"

Ya tambaya da sanyin murya.

"Yau muka yi maganar da ita."

"Ta ba mu goyon baya?"

Sai ta rasa me za ta ce, ba za ta fito ta faɗamasa hangen Umman ba kawai sai ta ce.

"Eh, amma ta ce mu bar wa Allah zaɓi. Mu yawaita addu'a, kar mu biye son ranmu."

Har sautin ajiyar zuciyar da ya sauke kunnuwanta suka tsinkayo mata, tana so ta tambaye shi ko iyayensa sun san da zancensu amma kuma fargabar amsar ya hana ta, sai dai kamar ya san me ta ke saƙawa a rai kawai ji ta yi ya ce.

"In sha Allahu Umma za ta mara mana baya kamar yanda Momi da Abba suka goyi baya ɗari bisa ɗari."

Ai ba ta san sadda ta washe haƙora ba.

"Dagaske my heartbeat? Sun yarda sun amince da ni matsayin..."

Sai kunya ta hana ta ƙarasawa, ya yi dariya.

"Matsayin matata ki ke son cewa ko? Toh amsarki ita ce eh, sun yarda ki zamewa ɗansu sanyin idaniya."

Murmushi ta yi har da lunshe idanu don jin dadin kalamansa.

"Alhamdulillah. Baba Alhaji fa?"

"Ki na tunanin zan faɗawa su Abba ban fara sanar da shi ba? Ya sani, sai dai ya cemin zai tuntuɓeki. Ki daure ki ce kina sona kin ji Baby?"

Yana da ƙarashe da shagwaɓa murya sai ya ba ta dariya.

"Umm, sai na yi tunani a kai."

"So ki ke na faɗa rijiya kenan?"

"To ba kai ne ka ce ina kammala level 1 za'a yi auren ba?" Ita ma ta yi zancen a shagwaɓe. Sai da ya dauke wuta na lokaci har sai da ta furta "Hello." Kafin ta ji ya numfasa. Da muryar da ta kasa tantance ko nasa ne ya ce.

"Ki yi hakuri. Kaunar da nake maki ce ba zai bar ni na jira tsawon shekarun da za ki kammala karatu ba. Wai ba ki ga na girma ba da yawa a gida? Ƙannena su na aure su bar ni tsofai-tsofai da ni?"

Ta ƙunshe dariyar da ya ba ta.

"My heartbeat, duka duka nawa ka ke?"

"Haka ki ka ce?"

"Um, ni dai ka yi hakuri toh. Wasa ma nake maka."

"Na sani, sai ki shirya kuma, a satin nan zan zo taɗi."

Idanu waje kamar suna kallon juna ta ce.

"A ina? Aa, don Allah ka yi hakuri. Ka bari tukunna mu samu iznin iyaye."

"Me muke jira to? Idan suka gan mu muna taɗi ai za su fi yarda batun dagaske muke. Na gaji da hira ta waya, kallo daga nesa, murmushi a faƙaice."

Murmushin kuwa ta yi, tasan batun murmushin ita ya ke zolaya don ko kallon ne ma sai ta tabbatar babu mai kula da ita kafin ya ci arziƙinsa. Sun jima ana ta muhawara a kan zuwa taɗi da Sadauki ya kafe zai yi, a ƙarshe dai ya amsa mata da yanda ta so, wato a jira Baba Alhaji ya yi kiranta ya ji ta bakinta sannan.

***
ABUJA...

Jalilah ce zaune ta yi jugum tana tunani, idanunta sun kumbura sun yi tsabar kukan da ta sha. Ta gaji dagaske, ga ciki ɗan watanni hudu a jikinta ga kuma baƙin cikin Zaid wanda har ta kai a shimfiɗa yakan mance sunanta ya dinga ambaton sunan Haulatu. Hatta bacci idan Zaid yana yi, sumbatun sunan Haulatu yake. Abin ya ishe ta, a haka ya fito daga d akin ya iske ta, ya kammala shirinsa na fita ofis. Ɗago idanuwanta ta yi ta kalle shi, bai ko kalli inda take ba, duk wannan lallami da iya tattali na Zaid, a yanzu gaba ɗaya ya bar yinsu gare ta, koyaushe cikin rigima suke yi a kan Haulatu. Ita babban takaicinta yanda Haulatun ba ta san da zamansa ba, ba ta kaunarsa amma shi kamar wanda a ka asirce, ya maƙale ya nace a kanta.

"Babu abin kari ne?" 

Tambayarsa ya sa ta share hawayen da suka ƙara wanke fuskarta, ta miƙe cikin sanyinta ta ƙarasa saman teburin, shi ma ganin haka ya ja kujera ya zauna. Fuskarta babu yabo ba fallasa ta ke haɗamasa shayin. Bayan ta kammala za ta tafi ya dakatar da ita ta hanyar kiranta, ta juyo, ya ba ta umarnin zama, ba musu ta zauna tana danne damuwar dake cin zuciyarta.

"Please bana so ki dinga sanya damuwar kuskurena a ranki, ya ci ace duk abin da kika ga na aikata a yanzu ki dinga yi min uzuri a kai tunda kin fi kowa sanin ba haka nake na, yanzun ina cikin yanayi na jarrabawa ta soyayya. Ki taya ni addu'ar samun abin da zai ƙara min kwanciyar hankalina da naki baki daya. Ina kuma ba ki haƙurin duk abin da nake maki ba bisa niyya ba. Ki taimake ni, ke kadai za ki iya roƙamin Ummana gafara akan ta bar ni na je Katsina, ta yi rantsuwa babu kaffara muddin na sake na je da niyyar Haulatu babu ni, duk a dalilinki."

Wata siririyar dariyar takaici ta yi tana kallonsa tsakar idanu, ashe duka wannan tausasawar da ya yi, saboda ta fadawa Malama abubuwan da za ta iya faɗi kan irin zamantakewarsu, har ran Malama ya ɓaci ta taka masa burki daga ziyartar Katsina, ta ce ko me ake ciki idan ba mutuwa ko wani kwakkwarar dalilin ba ya yi zamansa har sai ya saita gidansa ta samu tabbacin hakan daga gareta, ashe dalilin kenan na yin wannan dogon zancen?

"Kin yi shiru? Ina roƙonki don Allah ki yimin wannan alfarmar. "

Ya fadi yana ɗan murza yatsunta da ta ke ji kamar yana murza su akan garwashi don haka ta yi saurin janye hannunta.

"Zaid, da me na rage ka da har ka ke kallon fuskata kana danganta farin cikina da kwanciyar hankalina a kan son zuciyarka?"

Ta girgiza kai tana share hawaye wasu na ƙara zuba.

"Shikenan, zan maka yanda ka ke so."

Daga nan ta miƙe ta bar shi da bin ta da kallo, har a ransa ya ji babu dadi, amma ya zai yi? Yanzu auren Haulatun ya zame masa kamar wajibi a gareshi tunda yaƙi ne tsakaninsa da Sadauki. Ya ci alwashin ba zai taɓa bari Sadauki ya ci shi da wannan yaƙi ba. Ya gwammace komai ya faru idan ya so daga baya ya gyara mu'amalarsa da kowa. Da wannan tunanin ya miƙe don komai ji ya yi ya fita a ransa. Ita kuwa yana sa ƙafa yana fita, ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta wanke fuskarta. Alwala ta yi ta gabatar da sallar walha kamar yanda ya zame mata jiki koyaushe kafin ta yi addu'o'i ta miƙe, kanta ke sarawa amma haka ta daure ta ɗauki waya ta dannawa Malama Safiyya kira. Ta yi matukar kokarin saita muryarta suka gaisa har take tambayar lafiyarsu, ta nuna mata komai lafiya kuma sosai Zaid ya chanja. A karshe ta roƙi Malama ta yi hakuri ta bar shi ya zo Katsina, duk ya bi ya damu yana ganin kamar ba ta yafemasa ba. Malama sai da ta ɗan yi jim, kafin ta ce.

"Kin tabbata komai ya wuce tsakaninku?"

Da ƴar dariyar yaƙe ta amsa.

"Eh Umma, komai ya wuce. Allah ya kara maki lafiya."

Har ta wayar ta ji sadda Malama ta sauke ajiyar zuciya, ta ƙara da yiwa musu addu'a da kuma tabbatar da cewa babu wani abu duk sadda suka so zuwa, suna iya zuwa. Da haka Jalilah ta yi godiya suka yi sallama. Ta share hawayenta, zuwa lokacin kanta sosai yake sarawa, ta sha magani. Dakyar ta iya girki a ranar. Kafin Zaid ya dawo ta kwashe komai nata daga ɗakinsa ta mayar nata. Alƙawari ta ɗauka matuƙar ba shi ne ya neme ta ba, ba za ta ƙara kai kanta kamar yanda take yi ba har sai ya san darajarta, ya kuma bar wulaƙanta ta akan Haulatu.

***
KANO...

Dagaske Hindatu ta rikice ba za ta koma gidan Ɗan Mutuwa ba. Daidai da wayarta ta kashe don ba ta kaunar ya kira, daga ranar da Momi ta saka ƙafa ta bar ƙasar zuwa Dubai, a lokacin ita kuma ta ɗaura ɗamarar nesanta kanta da shi. Ya zo gidan Momi ya fi a ƙirga ganin ba ta amsa wayarsa, ta nuna ita ta fi so ya bar ta har ta haife ɗan cikinta a gidan sannan ta komai. Tun yana lallami har ransa ya yi mugun ɓaci ya watsar da lamarinta bayan ya mata rantsuwa akan muddin ta bari wani abun ya samu yaron cikinta sai ya illata rayuwarta. Hakan da ya faɗi ne ya ƙara sanya mata tsanarsa. Ta kuma ci alwashin duk inda maganin zubar da ciki yake sai ta nemo shi ta gwada iya yin ta. A ganinta da haihuwar abin da zai faɗa hannun matsafa gwara ta yi ɓarinsa ya bi rariya. Da wannan ƙudurin ta shirya tsaf ta fita zuwa unguwa a motarta. Kai tsaye tsohuwar unguwarsu ta nufa, ba ta mantawa akwai wata Nos da har haihuwa ta ke karɓa a gida a layin nasu. Kai tsaye wajenta ta nufa, a yanda idanunta suke a rufe ta gwammace duniya ta yi mata dariya da dai ta cigaba da rayuwa ƙarƙashin inuwar mutum irin Ɗan Mutuwa. Sai dai a rashin sa'arta, ta tarar ba ta gida tana wurin aiki don haka ta yiwa yaran nata alheri da kuma karɓar lambar wayarta, bayan fitowarta daga layin nasu ne zuwa titi ta hangi wata kamar Bahijja makwafciyar su Haulatu tana tsaye gefen titi, koda ta ƙarasa ta ga dagasken ita ce, nan da nan ta saki fuska, ta jima ba ta haɗu da wata idon sanin ba a dai cikin ƴan unguwar su Haulatun. Bahijja dake tsaye ganin mota mai baƙaƙen gilasai ta tsaya a saitinta sai ta ɗan ja baya. Lura da hakan ya sa Hindatu sauke gilas suka haɗa idanu. Ganin tana niyyar matsawa ne ya ba Hindatu tabbacin cewa Bahijja ba ta gane ta ba. Ita kuwa Bahijja tuni ta gano ta a ganin farko saboda tana bin ta a shafukan sada zumunta, duk bidiyoyin da ta ke ɗorawa na ta har ma a wasu bidiyoyin da na mijin nata babu ɗaya da ba ta gani. Ta dauki aurenta na cin amana, ta kasa yarda da Haulatu wacce ta ce mata Hindatun ba ta san mahaifinta ba ne, a ganinta kuɗi babu abin da ba ya sanyawa.

"Bahijja, na san ba ki gane ni ba ko? Hindatu ce fa, Big Mama aminiyar Haulatun Umma."

Sam ba ta san ma ta fito ta biyo ta ba sai da ta ji muryarta a gefe. Ta ja ta tsaya tana wai murmushi bayan ta bi ta da kallon ƙasa zuwa sama.

"Oh, sannu fa Hajiya Hindatu, ashe kin yi sauyin da talaka ba zai iya ganeki ba ko? Uhum."

Hindatu sai ta yi sak, a sanyaye ta ce.

"Kamar ya Bahijja? Kada dai ke ma irin kallon nan ki ke yimin? Na wacce ta yi auren kuɗi?"

Wata dariya Bahijja ta yi.

"Kar ki ɓatamin lokaci domin ina da abin da ya fi sauraronki a yanzu. Ai ke da a auren kuɗin kaɗai ma kika tsaya da ba haka ba, aikin banza kawai, wacce ba ta san darajar aminta ba, kin auri mahaifin Haulatu ki zo kina wani ɓaɓatu na banza. Mts."

Daga haka ta kaɗa kai za ta tafi, Hindatu ta yi saurin riko hannunta.

"Waye baban Haulatu? Ban gane ba, waye baban Haulatu?!"

Ta karashe cikin daga murya mai nuni da yanayi na ruɗani. Bahijja ta kwace hannunta tana kallon mutanen da hankulansu ya kai garesu.

"Malama kar fa ki taramin jama'a. Kina nufin ba ki san mijinki Ɗan Mutuwa shi ne mahaifin Haulatu ba? Mijin Umma?"

Sai da Hindatu ta dafe ƙirjinta saboda tsananta bugun da ya yi, har wani jiri ta ji ya na neman kwashe ta, da wannan damar Bahijja ta samu ta tsaida napep ta bar ta, ganin yanda zufa ke wanke ta ga kuma jama'a duk wanda zai wuce sai ya kalle ta yasa ta komawa cikin motar da sauri, daƙyar ta sanya seatbelt tana ambaton sunayen Allah.

"Alhaji Ibrahim Ɗan Mutuwa? Shi ne mijin Umma?"

Hannu na rawa ta dauki wayarta ta dannawa Haulatu kira sai dai a kashe, ta mance shaf Umma ta ce mata ta sauya layi kuma ba ta da layin, ba ta son kiran Umma, wani irin nauyi da kunyarsu duka ya mamayeta. Ta yi kuka sosai kafin a karshe ta ja motar ta soma tafiya sai dai duk rabin tuƙin a tunani ya ke tafiya. Cikin iko na Allah, wani hatsari ya faru inda motarta ta bugi motar dake gabanta da ƙarfi don ta lula tunani ba ta ma san an tsaida su ba a danja, ita kuwa tuƙi kawai take ya yin da motar dake gabanta ke tsaye. Kanta ya bugi da sitiyari har sai da mararta ta yi waki irin azabbaben ƙullewa, kafafunta duka sai da suka bugu sosai, tuni ta suma. Motar dake gabanta kuwa ba karamin lahani ta yi musu ba, da ace akwai rai a bayan motar zai wahala ya fito a raye.

***
Tun zuwan Haidar ya sanar da ita kiran Baba Alhaji take cikin faɗuwar gaba. Jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi, ta san dalilin kiran amma kuma ta kasa gane meke zuciyar Ummanta. Ita ba ta ƙara zancen ba kuma ba ta sauya mata a komai ba. Hajja tuni ta samu labari daga Umman, kuma ɗari bisa ɗari ta ji dadi ta goyi bayan al'amarin. Ganin Haulatu ba ta da niyyar tashi ta wuce ne ya sanya Hajja kallonta.

"Ke Haule, kiran ne ba za ki ba ko me? Ji min ƴa? Za ki tashi ko sai na zo inda ki ke?"

Ta ɗan saci kallon Umma wacce ko kallonta ba ta yi ba tana aikin shafawa Hajja man zafi a kafafu sakamakon kafafunta da ke mata ciwo. Ganin dai Umma ba za ta ce komai ba sai ta miƙe a sanyaye ta yafa gyalen da ta fita da shi makaranta da safe sannan ta fice. Bayan tafiyarta ne Hajja ta dubi Umma dakyau.

"Wai ni Na'imatu kodai bakya son lamarin Sadaukin Alhaji da Haule?"

Da ɗan mamaki Umma ta ce.

"Hajja me kika gani? To ai ban ce komai ba."

Ɗan murmushi mai hade da dariya Hajja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login