Showing 162001 words to 165000 words out of 177840 words

Chapter 55 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79151

za ta shiga ya kasance da safa a ƙafarta. Kofi ne a hannunta wanda a ta dama quaker oat, ya ji madara har ya yi fari fat. Daidai lokacin ya shigo da sallamarsa. Muryar da har abada ba za ta gushe a kunnuwanta ba, da wani irin sauri ta kalle shi, ya yi kyau cikin farar tshirt da blue jeans. Yanda ta ke kallonsa haka shi ma ya ke ƙara mata kallon daga sama har ƙasa. Jin muryar Hajja na amsa sallamar gami da yi masa lale marhabin ya ankarar da ita, ta tuna ba sa shiri nan da nan ta yi sama da sauri-saurinta ba ta ko tsaya amsa kiran da Hajja ke mata ba. Ajiyar zuciya ya saki ya ƙarasa ciki. Umma da Safina sun je duba Maman Radiya da ba ta jin dadin jikinta. Fahima kuwa tun da yamma ta koma gidansu bayan mahaifinta ya zo Baba Alhaji ya roki alfarmar ya janye batun aure, ya dai amsa da toh amma babu wanda ya san meke ransa. Da kansa kuma ya yi umarnin ta shirya su tafi.

"Yaya Sadauki sannu da zuwa. Ina yini." Fadin Zaituna da ke zaune a gefe fuskarta a sake. Shima da sakin fuskar ya amsa mata. Yana tambayar ko su Mama sun iso.

"Sun ce suna dab da shigowa Katsina, nasan nan ba da jimawa ba za su karaso."

Ya jinjina kai.

"Allah ya kawo su lafiya."

Suka amsa da amin. Zaituna ta kula dai hankalinsa na ga benen da Haulatu ta haye, kafin ta ce wani abu sai ji ta yi Hajja na fadin.

"Ka ji kuma wani tsohon gulma wajen yarinyar can, ta ishi mutane da zancenka amma yanzu ka zo ta wani kama hanya ta gudu. Ke Zaituna maza kira ta su gaisa."

Ta fadi ne don ba ta ga dacewar ya hau ba, ko babu komai a yanda Haulatu ta dauki wannan kyawun da hasken, zai kara zama hatsari a keɓewarsu a rumfa haka. Shi kuwa dama haka yake so, don haka sai ya yi shiru, Zaituna ta miƙe da sauri ta nufi saman.

A lokacin Haulatu na falo ta yi shiru hankalinta gaba daya yana ƙasa, ta ga ya yi kyau abinsa amma kuma duk ya rame. Ganinsa da ta yi ya ƙara haifar da sabuwar ƙaunarsa a ranta. Koda Zaituna ta zo mata da batun ta je su gaisa, turo baki ta yi ta nuna ita ba ta son ganinsa. Zaituna ta dungure kanta.

"Ji gulma, matar da ke kwana kallon hotonsa. Malama umarnin Hajja ne, ko za ki nunamin ba ta isa da ke ba ne?"

Idanun Haulatu cike da kwalla ta dube ta.

"Yanzu Sis, apart from duk abinda ya yi min, kina ganin ya dace na manta da komai da wuri har haka?"

Murmushi Zaituna ta yi karo na ba adadi.

"Ki yi hakuri, ya maki laifi. Amma ki duba ki gani, yanda ya ce mana fa, yanzun shigowarsa garin kenan ko ɓangarensu bai ƙarasa ba. Kuma ni na tabbata don ke ya shigo nan ɗin. Shi ma fa an masa laifi, an hana shi ganin abin da zuciyarsa ke so na kwanaki da dama, don Allah ki manta komai ki je. Ni na tabbatar komai zai wuce kin ji ko?"

Da wadannan tausasan kalaman na Zaituna ta miƙe ta shiga daki, hijabinta mai kyau wanda Zaituna ta kawo mata matsayin tsaraba daga Malaysia, da kadan ya wuce gwuiwarta, hawa biyu ne da shi, dogo da kuma ƙara iyaka kirji. Fari ƙal. Ta fito ta sauka ƙasan.

Ganin Hajja kadai ya sanya ta ji har ranta ya ɗan yi babu dadi. Kafin ta tambaya ko ya tafi ta ji Hajja na fadin.

"Ki je yace ki same shi inda ku ke hira tunda kin kwace min miji."

Ta yi gaba kawai ta bar Baba Saude wacce ba ta jima da shigowa falon ba da dariya.

Ta iske shi zaune a rumfa sama kujera a farfajiyar gidan, hasken fitilu suka haska musu fuskokin juna tun ma kafin ta ƙarasa gare shi. A hankali take takawa har ta kai gefensa ta nemi wuri ta zauna. Kallonta kawai yake yi kamar ya samu waya a hannu. Sallamar da ta yi mishi ce ya sanya shi numfasawa sannan ya amsa. Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce.

"Kawai ki ce shirin zautar da Abeed Malumfashi ake yi, shi ne dalilin yi min rowarki? Bebi kar ki ɗauki alhakina. Ina sonki ina sonki, idan ya fi haka akwai matsala."

Ɗan runtse idanu ta yi kanta a ƙasa, tunda suke da Sadauki kalmar ina sonki ba dai ya firta ba amma kuma duka kalmominsa masu nuni ne da tsantsar so ɗin da ƙauna. Yau ga dukkan alamu dagaske ya je maƙura.

"Ki yafemin, ni mai laifi ne. Na ji zafin hana ni ganinki da Maama ke yi, sai aka zo ke ma madadin ki ji tausayina, sai ki ka biye mata. Tunanina ya ba ni ko dai ba ki wani damu da ni ba ne? Sai na ji ke kanki kin ban haushi, na yanke hukuncin mu zauna haka babu wayar ko tuntuɓar juna zuwa lokacin da kaf duniya babu mai cikakken iko a kanki sama da ni. Amma ba zan iya ba. Na kasa, ba zai taɓa yiwuwa ba. Ki yi hakuri kin ji? Ko na durƙusa?"

Ta kalle shi, idanunsa sun kaɗa, muryarsa ta narke gaba ɗaya, ya yi wani irin taushi fiye da baya. Ba ƙarya duk abin da ya ce ta yarda har cikin zuciyarsa hakan ne. Don haka ta girgiza kai.

"Aa my heartbeat, ni ba na buƙatar ka durkusa min. Na yarda da duk abin da ka ce. Na yafe maka na hakura, ni ma ina roƙon hakan daga gareka."

Ya yi murmushi.

"Ba kya laifi. Naki da nawan duka na haɗe su ya zama ni kadai ke da laifin. Bebi kyau kike ko babu kwalliya. Kin sauya, anya ba ki fi ƙarfin Abeed ba?"

Ta harare shi kadan, ya lumshe idanu yana shafar sumar kansa.

"Ki bari."

"Na bari." Ta amsa tana kauda kai. Sai a lokacin ta gaida shi da tambayar ko ya iso lafiya? Ya amsa mata ba tare da ya iya kauda kai daga dubanta ba.

Dakyar dai ta lallaɓa suka rabu ya wuce don ya huta, babu sallah a kansa face sallar isha'i da ake kira yanzu. Har sai da ta shiga gida kafin ya juya ya fice shi ma. Babu jimawa da rabuwarsu, su Maman Zaituna suka iso gidan. Murna ya karaɗe a ɓangaren Hajja, Umma ma a sannan sun dawo.

Ranar dai kwanan farin ciki Haulatu ta yi ga waya da suka sha da Sadauki kamar za su cinye juna.

***
Biki na ta matsowa, ana sauran kwana uku ne baƙi daga Malumfashi suka iso da yawa. Ga mutanen Kaduna da Kano kamar ba lokacin karatu ba don yara ba su yi hutu ba. Amma an taru sosai, masu yaran kanana kuwa sun bari sai juma'a ranar da za'a fara bikin za su iso. Ɗinkunan fitar biki babu ɗaya da ya fita daga hannun Umma, Abba Ridwan ne ya dauki wannan nauyin, shi da Momi Nuratu, sam ba ta yiwa Haulatu kallon suruka sai ƴarta. A sannan tuni an kawo lefe na gani na faɗa, saiti uku da kayayyakin ga kuma na Uwa da aka yi daban. Komai na cikinsa abin burgewa. Sadauki a zuwansa Dubai ya ƙara yo siyayyar abayoyi da sarƙa sai jakunkuna, ya kaiwa Maama bayan Momi Nuratu ta gani ta sa albarka.

An yiwa Haulatu komai a fannin jere, babu abin da ba'a zuba ba, nata kawai shiga gidan. Momin Mu'az da Mamin Khaleefa ko Allah ya sanya alheri na lefe ba su shigo sun yi ba. Akan hakan sai da Hajja ta yiwa mazajensu tas kan su ja wa matansu kunne kar su kawo rarrabuwar kai a zuri'a don ko yaransu ma ba su shigo ba idan ka cire mazan da ba su ko damu ba.

Aikuwa kowaccensu ta kwashi kashinta a hannu don Baban Mu'az har kusan sakin Momin Mu'az ya yi akan furucin da ta yi mene ne ya yi saura da zai burge ta a bikin ƴar bariki. Wannan ne ya yi sanadin da ya ce ta tafi gida amma bai kai ga sakinta ba. Ita kuwa Mamin Khaleefa da yake ba ta saba ganin ɓacin rai sosai daga Barr Dawud ba, sai ta yi shiru da ta ga ya rufe ta faɗa ganin kamar tana neman zagin Hajja wai tana haɗa husuma tsakanin mata da miji. Dole ta ja baki ta tsuke tana tunanin ya aka yi har ya iya ɗagamata murya? Kada dai aikin da take a kansa ya bar ci kwata-kwata?

***
Biki Buduri....




Ku ƙara hakuri, in sha Allah ko post biyar ba zai kai ba. Labari ya na dab da ƙaraye.
Ranar Alhamis aka sanya Haulatu a lalle. Umma har hawayen farin ciki ta fitar. A nan farfajiyar babban gida aka yi komai da yammaci aka ƙare. Sosai Amaryar ke fama da ciwon kai, kwanakin ba ƙaramar gajiya ta yi ba. Zagayen zuwa ƙunshi da kuma gyaran gashi ga kuma wani gyara na musamman da Maama ta zo takanas aka yi mata wanda dama shi an bar shi ne sai dab da biki. A wannan daren duk yanda Angon ya so su yi magana bai samu ba, bai takura mata ba.

Da wuri ta shige ɗakin Hajja inda babu mai takura mata ta kwanta bayan ta sha magani, ai kuwa ko mintuna biyar ba ta yi ba ta yi bacci. Ba kuma ita ce ta farka ba sai washegari da Asubahi. Nan ma Hajja ce ta tayar da ita domin yin sallah. Sai a sannan ne ta ji kan nata ya saki, babu wani ciwo.

Ranar kuwa ɗaurin aure ne da yini. Wannan yasa tana kammala yin kari, aka ce ta faɗa wanka. Kamar ta yi kuka ta dubi Maman Zaituna.

"Mama ba sai anjima ba?"

Maman Zaituna ta yi murmushi.

"Wane anjima kuma Haulatu? Ke da yau za'a shafa fatiha? Aa, je ki maza ki yi wanka ki fito ki yi shiri. Mai maki make-up ta fi awa da zuwa."

"Au, sai ma an lallaɓata za ta yi? Toh kodai a fasa ne a ɗaura da ni?"

Cewar Hajja dake zaune a falon wanda cike yake da iyaye, sai ko ita Haulatun da Maman Zaituna ta sa a gaba ta yi kari a kusa da ita. Aka yi dariya. Ita kuwa sai ta miƙe don yau babu baki balle ta rama zolayar Hajja.

Tana shiga ɗakin nan ma ta haɗu zolayar su Safina, wai sai wani murmushi take yi baki yaƙi rufuwa duk murnar ɗaurin aure. Ita dai ba ta ce musu uffan ba ta ɗauki babban tawul ɗin wankanta ta shige banɗaki.

***
"Khaleefa, wai lafiyarka ina magana tun ɗazu ka yi min shiru?" Hafsat ta faɗi ranta a ɓace tana daga tsaye riƙe da ƙugu yayinda shi kuwa ya maida hankali ga gyarawa ɗiyarsa kwanciya a cikin net ɗinta. Sai da ya kammala ya miƙe sanye da jallabiyarsa da nufin fita daga ɗakin zuwa nasa don yin wanka. Da sauri ta sha gabansa. Ya dube ta da idanunsa masu tsananin kwarjini da ya sanya ta duban gefe ta soma faɗar abin da ke ranta.

"Wai mene ne haka ka ke yi min? Gaba ɗaya tun sadda na haihu ka bi ka sauya, matuƙar ba ni na je maka da sunan buƙata ba, ba ka ko damu ka kalli inda nake ba. Na gaji Khaleefa. Ni ma fa mutum ce lafiyayya."

Daga cikin abin da ya tsana a wurin Hafsat, har da sunansa na kai tsaye da ta ke kira, tuni wani suna da ake kiran masoyi da shi ko kuma yi mishi alkunya da sunan ɗansa babu shi a zamantakewarsu. Ga ƙazantar da ta ninka ta baya. Ayyukan da ta jibgawa ƴar yarinyar dake mata aiki sun mata yawan da take kasa yin komai yanda zai fita fes. Tsaftar jikinta da ta ke mayar da hankalin a baya ma sai a hankali, idan ka cire rashin kula da tsaftar sai ko wasu sinadaran da ya ji babu a tattare da ita wadanda suka rage gamsar da shi tun bayan da ta haihu. Sam ba ya cikin yanayin buƙatarta a kwanakin nan, ya gaji da maganar tunda abin ya ƙi ƙarewa. Daga Mamarta har ta sa mahaifiyar babu wanda ke goyamasa baya sai ba da haƙuri da batun nan gaba ƴan aikin za su goge. Babu mai nuna mata kurenta.
Don haka sai kawai ya gifta ta zai wuce, ta ƙara riƙo hannunsa, dole ya tsaya gami da juyowa ya dube ta.

"Kar ki ɓata min rai Hafsat, kin fi kowa sanin ban da lokacin shirmenki yanzu ko?"

Cike da takaici ta tari numfashinsa.

"Haƙƙina fa Khaleefa? Wane ɓangare na shari'a ne ya ba ka damar tauye min?"

Ya ɗan runtse idanu. Yana son ce mata ni haƙƙoƙi nawa ki je tauye min? Fitar da ki ke ba da iznina ba, ko kuwa abincin da ba kya taɓa shiga ki girka sai dai wasu su yi? Sai dai ba shi da isasshen lokacin tunasar da ita baƙaken maganganun da take yaɓa masa duk sadda ya buɗe baki da zummar amayar da abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya, don haka ya sauke ajiyar zuciya ya dube ta bayan ya danne ɓacin ransa.

"Na ji, ko mene ne ki bari idan na je ɗaurin auren ɗan uwana na dawo sai mu yi magana."

Ta tsuke baki.

"Ok, ni motata ba mai, ina son kuɗi zan zuba." Ta yi tambayar ba don ba ta da shi ba, sai don kawai tada zaune tsaye.

Ba ya son jan magana don haka kawai ya ce zai ba ta idan ya kammala shiri. Daga nan ya fice zuwa nasa ɗakin yana kara ji a rai babu abin da zai hana ya ƙara aure face wani ikon na Ubangiji.

Koda ya shirya ya fito falon, bai ko shiga ɗakinta ba sai kudi da ya bar mata a saman dinning ɗinsu, Affan dama yana wajen Mami, tun sadda Hafsat ta haihu ya koma can don ta ce ɗawainiyar yaran zai mata yawa. Abin ya so zame musu rigima dalili kenan da Maminsa ta raba gardamar ta ce ya dawo gidanta, Hafsat ta fi shi gaskiya.

Ko irin wannan yana baƙantawa Khaleefa rai yanda ba shi da ikon yanke hukunci a gidansa, matuƙar bai zo ɗaya da ra'ayin Hafsat ba to fa zai samu matsala daga Mami, a dole ya ke haƙura.

***
Haulatu ta ci ado cikin leshi fari ƙal sai mayafi da ta yafa a kanta. Fuskarnan ta sha kwalliyar hoda da jan baki, kyan da ta yi za'a iya cewa ɓata lokaci ne gurin fayyace shi. A lokacin ƙarfe ɗaya saura, duka maza na gidan da ma waɗanda suka zo daga nesa sun wuce masallaci sallah da kuma ɗaurin aure. Mata kuwa ana ta hidima a gida, wuri ya cika babu matsaka tsinke. Ba ɓangaren Hajja ba, ba kuma can na Baba Alhaji da su Baba Dakta ba. Amarya Haulatu tun da ta ƙume a ɗaki ta yi shiru jikinta kuma ya yi sanyi. Ba don komai ba sai tunawa da irin wannan rana wanda babu wani tsayayye daga dangin mahaifinta. Tabbas za ta iya rayuwarta babu su ɗin, dama kuma babu ɗin, sai dai tana jin zafi ta yadda burin kowace ɗiya ya kasance mahaifinta shi ke ba da aurenta, amma ita na ta mahaifin bai da irin kwalliyar da za ta yi ado da shi har ma ta bugi ƙirji a ko'ina ta ce za'a yaba. Ba ta san hawaye ta ke fitarwa ba sai da ta ji muryar Zaituna a kusa da kunnenta tana rarrashinta.

"Kar ki ɓata kwalliyarnan please. Mene ne abin kuka a yau da ya kamata ki yi farin ciki? Ki yi hakuri ki bari."

Sai ta ji kamar ta ƙara mata dalilin kukan ai kuwa ta faɗa kafaɗarta ta shiga rera shi. Tun Zaituna da su Radiya na rarrashi, har da suka ga ta ƙi haƙura aka kira Maama. Ita ce ta bada umarnin duk su fice, a sannan ne ta hau ban baki, ƙarshe da dabara ta ji dalilin kukan. Har Maama sai da hawayen ya tahomata ta yi saurin dauke su kada ta gani, ta tabbatar idan ta gane ita ma abin ya sosa ranta, za ta ji har a zuciya cewa ita ɗin fa dagaske abar tausayi ce.

"Kar ki yarda wannan tunani ya ɓatamaki murnarki a wannan rana. Kowa fa da kalar ƙaddararsa Haulen Hajja, ke musulma ce da ki ka yi imanin Allah zai jarabce ki, jarrabawar nan kuma komai muninsa za ki karɓa da hannu bibbiyu hakazalika mai kyau. Ya yi maki ni'imomin da bai kyautu ki yi hawaye akan wannan ba, wasu fa su na can, auren ma ba ta hanyarsa aka haife su ba. Wasu kuwa an haife su da auren, amma hakan bai sa rayuwarsu ta gurɓace ba. Ke kuma Allah ya tsarkake ki, kin samu sauyi a rayuwa irin wanda ko a mafarki ba ki taɓa hasasowa ba. Kukan na mene ne toh? Shi ma mahaifin naki ai ba watsar da shi aka yi ba, shi ya sallama ki, ban da haka, mu ba ƙananan mutane ne ba da har za'a tashi auren ƴa a kasa tuntuɓar mahaifinta. Gatan da za ki daure ki yi ga mahaifinki shi ne kar ki taɓa gajiyawa da bin sa da addu'ar neman shiriya, Allah yana sauya baƙi zuwa fari. Duk fa abubuwan nan da Babanki ya ke aikatawa ko kuma ya aikata, Allah ba ruwansa, idan ya yi tuba cikakke, sai ya yafe masa har ma ki ga ya samu fadar da wani da ya yi shekaru cikin ibada bai same ta ba. Domin rahmar ta Allah ce. Kar na ƙara ganin kin tada hankali kan abin da ba ki isa ki sauya shi ba kin ji ko?"

A hankali ta gyaɗa wa Maama kai, zuciyarta har ta yi sanyi ba kamar a farko ba. Bayan ta gama lallaɓata, a karshe dai kwalliyar sai da aka ƙara gyara ta.

***
Misalin karfe biyu saura na rana, dubban mutane abokan arziki suka shaida ɗaurin auren Abeed Ridwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login