Showing 21001 words to 24000 words out of 177840 words

Chapter 8 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79124

kamu haɗe da yini wanda za'a yi a wani ɗakin taro na musamman. Marar kati ba zai samu shiga ba. Tare zasu je da Umman amma yanda Hindatu ta dinga jera mata kira tana ɗuramata zagi kan ta taho inda ake mata kwalliya tare za su tafi yasa a dole Umma ta ce ta wuce kawai zuwa yamma ita sai ta tafi tunda akwai waya zasu yi magana kawai.

Sadda ta kammala daukar duk abinda take da buƙata a leda, ta fito a gaggauce suka kusan cin karo da Ɗanmutuwa, guntun tsaki ta ja kafin ta yi baya. Ta san da ace Umma ta ji wannan tsakin ranta ne zai ɓaci, shi kuwa shigowa ciki ya yi wannan karon ko arziƙin gaisuwar da ya saba ci bai ci shi ba.

Wayarsa ta yi ƙara ganin mai kiran ya sanya shi saurin shigewa ɗakinsa, daidai lokacin ita kuma Umma ta fito daga nata ɗakin, sam bai kula da ita ba, ta ƙarasa, kafin ta kai ga shiga ta yi saurin ja baya tana sauraron abin da yake faɗi. Tashin hankali! Gobarar gemu kenan.
Fitar tsiro
Page 11
"Yanzun nan ta fita, ku fara bin bayanta, duk inda ta sa ƙafa ku sanya. Ku tabbatar kun fesa mata hodar yadda ko kun kai ta ba za ta iya gane hanyar dawowa ba. A kuma faɗawa Hajiya Loma, ina nan tafe anjima."

Jin alamun zai katse wayar, jiki na rawa Umma ta fice zuwa ɗakinta. Jin kamar motsin mutum ya sa Ɗanmutuwa saurin juyowa gami da ɗan zura kansa ta tagar ɗakin, kasancewar tagarsa saitin ta Umma ce, hangota ya yi tana ta kiciniyar shiryawa. Ya yi tunanin ba ta ji komai ba don haka ya yi musu sallama da zummar zai ƙara kira kafin ya shiga ma'ajiyarsa na miyagun ƙwayoyi ya hau lissafa adadin da wasu suka buƙatar ya kai.

Ɓangaren Umma kuwa, shirin dole ta kama jikinta sai rawa yake. Babban burinta kar ta yi wani motsin da zai ankarar da shi ta ji. Hakan yasa ta shiga jan Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un a zuciyarta, sai da ta kammala saka kaya ta ji ya rufe ƙofar ɗakinsa ya fito.

"Na'ima." Ji ta yi ya kira sunanta, sai da ƙirjinta ya buga. Tsanarsa take ji sosai ga kuma tsoron abin da ake shirin yiwa ɗiyarta. Sai da ya kira na biyu kafin ta fito tana murmushin dole.

"Na'am, yi hakuri ina sauri zan shirya ne. Fita za ka yi?"

Ya yi wani murmushin mugunta.

"Eh Ɗawisuna. Ni zan fita. Ba sai an yi girki ba kar na wahalar da ke. "

Ta gyaɗa kai tana ƙara murmusawa a dole.

"Ina godiya. Sai ka dawo."

"Kema sai kin dawo. Ki kularmin da ɗiyarmu."

Daga haka ya fice, ta bishi da banzan kallo wanda take ji kamar ta shaƙo shi. Da sauri Umma ta koma ɗaki, hijabinta kawai ta zura, wayarta ta ciro ta shiga gwada kiran Haulatun sai dai ta ji a kashe. Hankali a tashe ta dannawa Hindatu kira, nan ma yana ta ƙara ba su ɗaga ba. Ƙirjinta ta dafe tana ambaton Allah da nufin ya samar mata mafita. Nan da nan Hajiya Mama ta faɗo ranta, da sauri ta fita ta rufe gidan ta faɗa gidanta. Hajiya Mama na zaune a falo tare da baƙuwa sai ganinta suka yi kamar an jefo ta. Nan da nan suka miƙe, sosai ta tsorata su.

"Maman Haulatu, lafiya?" Cewar Hajiya Mama. Cikin kuka ta riƙe hannunta jikinta ko'ina na rawa.

"Haulatu na cikin hatsari Hajiya, don Allah ku taimaka min. Naji Babanta na waya yana bada umarnin a bi ta a kama ta."

"Tana ina yanzu?" Ta tambaya a gaggauce.

Umma ta ɗan watsa yatsunta.

"Nima ban san inda ta nufa ba, na san dai wajen da ake yiwa Hindatu kwalliya ta nufa. Ku taimakamin don Allah."

Nan da nan Hajiya Mama ta fiddo waya ta kira mijinta ta sanar da shi, ya ba da umarnin su je gidan iyayen Hindatun a ji inda take. Shi kuma zai sa direbansa da Mujahid (Yayan Bahijja) su je wajen. Ya buƙaci a turo masa lambar Hindatun. Ba musu kuwa suka yi sallama, Hajiya Mama ta karɓi lambar wurin Umma ta aikamata. Haka suka ɗunguma har baƙuwar wacce ƴar uwa ce ga Hajiya Mama.

Momi ba ta yi gardamar faɗamusu inda Hindatun ta tafi ba ganin babbar mace kamar Hajiya Mama wacce da gani ka san ba daga rigija-rigijan gida ta fito irin nasu ba.

***
Haulatu kuwa tsabar takaicin kiran da Hindatu ke faman jeramata ne yasa ta kashe wayarta baki ɗaya, ko kusa ba ta kula da motar da ke biye da su ba. Mai adaidaitarsu kuwa tun yana ganin kamar ba binsu ake yi ba, har dai ya fahimci duk kwanar da suka yi nan motar da ta sha baƙaƙen gilasai ke yi. Dab da zasu ƙarasa wurin shagon Ayyush inda nan ne dai ake yiwa Hindatun kwalliya ta ji mai Napep din ya yi magana.

"Anya wannan motar ta baya ba mu take bi ba?"

Haulatu ta ɗan leƙa kanta kafin ta ja tsaki.

"Kyale ɗan wahala. Wataƙila zancen wofi suke son yi mana. Don Allah ƙara gudu ina sauri ne."

Shi kuwa jin haka ya ƙarawa napep ɗinsa gudu. Faɗi yake yi amma bai taɓa ganin maye irin wannan mai motar dake bin su ba. Da gani masu bin mace su ce su na sonta ne. Amma fa shi abin wai na ba shi mamaki yanda ko akwai sarari ba sa wani kokarin yin overtaking. A bayan dai suke bibiyarsu. Ita dai Haulatu ba ta ko tanka ba sai ma wayarta da ta kunna, daidai lokacin suka isa shagon, ta fito da sauri ta sallame shi. Ko motar ba ta kalla ba.

Su kuwa su Maada suna tsaye can gefen hanya, Duuna ya dube shi.

"Boss, wai idan ba anan area ba, ina kake tsammanin za mu cafke ta ba tare da an samu matsala ba? Tun ɗazu eh cewa nake ka yi overtaking amma eh ba ka yi ba."

Maada bai ko dube shi ba har sai da Mai Napep dinnan ya yi ribas ya wuce su har da leƙensu ya dinga yi amma ya kasa ganin ko inuwa. Haka ya haƙura ya yi gaba.

***
Hindatu ta yi kyau sosai kamar ba ita ba, duk wannan kwalliyar bai hana ta hararar Haulatun gami da ɗuramata ashar ba. Itama ta maida martani kafin kuma ta zauna a soma yi mata nata kwalliyar, Hindatu cike da masifa ta ke fadin.

"Ban taɓa ganin Aminiya irinki ba. Wa ya taɓa raba hanya da Amininsa ranar bikinsa?"

Ta harzuƙo za ta yi magana mai kwalliyar ta ba ta hakuri da fadin don Allah kar ta motsa ba a yiwa kwalliya haka. Dole ta yi shiru tana huci. Ita ji take kamar ma ta fasa kwalliyar. Wayar Hindatu ta yi ƙara sa'ilin da ake ƙoƙarin yi mata ɗauri.

"Madam tun fa ɗazu ake ta kiranki ya kamata ki ɗaga wayar nan. Wayasani ko Angon ne." Fadin Ayyush dake zaune can gefe tana cin abinci a robar takeaway ga drinks ajiye gabanta. Masu yin kwalliya a shagon mutum biyu ne ƙwararru.

Hindatu ta ɗauki wayar tana ɗan murmushi, ganin baƙuwar lamba ya sa ta ɗan yamutsa fuska da tunanin ko masu damunta da neman kwatance ne. Sai kuma kawai ta ɗaga, jin muryar babbar mutum ya sa ta amsa da sallama. Nan ya nemi kwatancen inda suke bayan ya sanar da ita shi din makwafcin su Haulatu ne kuma yanzu haka tana cikin hatsari. Nan da nan cikin Hindatu ya ɗuri ruwa, ta sanar da shi ya kashe wayar bayan ya ce kar ta sake ta sanar da Haulatun. Haka aka cigaba da shirin ita duk jikinta ya yi sanyi, Haulatu kuwa ana cikin yi mata kwalliyar ba'a kai ga kammalawa ba sai kawai suka ji tsayuwar mota. Hindatu ce ta dubi waje don gilashin ana iya ganin na waje amma shi ba zai ganka ba. Ganin wasu maza biyu kuma matasa sai ta yi zaton ko su ne masu neman Haulatun. Suka kwankwasa gilashin wurin. Ayyush ta mike tana mita.

"Su waye kuma? Maza ba sa shigomin wuri fa." Ta leƙa, ita Haulatu ko a jikinta, Hindatu kuwa ana ɗauri tana gocewa tana kallonsu sai da mai ɗaurin ta yi magana kafin ta nutsu amma kunnuwanta su na waje.

Ayyush kafin ta kai ga magana sai ga motar ƴan sanda ta faka.

Daga waje kuwa su Maada su na ganin motar hukuma ba shiri suka yi wani wawan ribas da ya ɗauki hankalin jami'an tsaron suka yi gaba, ganin haka tuni su dinma suka bi bayansu a guje. Ayyush dai ta gama tsorata, kirjinta ya hau bugu da ƙarfi. Mujahid ne ya fara tambayarta inda Haulatu take.

Jin an ambaci Haulatu ya sa Hindatu miƙewa har tana sa mai mata ɗauri soke hannunta. Haulatun ma miƙewar ta yi, gaba daya suka nufi ƙofa. Mujahid na ganin Haulatu ya sauke ajiyar zuciya. Ita kuwa ji ta yi gabanta ya fadi. Me zai kawo yayan Bahijja wurinta? Ta ya ya ma yasan cewa tana nan?

"Yaya Mujahid? Lafiya?"

Ya girgiza kai.

"Lafiya kalau, kar ki damu. Ki.."

Bai kai ga ƙarasawa ba motar su Hajiya Mama ta tsaya, su dinma duk a ruɗe suke. Haulatu ta yi saurin fitowa daga ita sai doguwar rigar ankon bikin na ƴanmata. Ta ƙarasa ga Umma jikinta na rawa, ta samu nutsuwa da ganin Umman don a farko ta yi zaton ko wani mummunan abun ne ya fari da ita. Umma ta rungumeta tana kuka, itama kawai ta ji kwalla sun cicciko mata tun kafin ta san dalilin kukan mahaifiyarta.

"Ya isa hakanan don Allah Na'ima tunda ga ta nan kin same ta cikin kwanciyar hankali. Allah ya kiyaye gaba."

Haulatu dai kallonsu take yi.

"Umma meke faruwa ne?"

Nan Umma ba ta labarin abin da ta ji Ɗanmutuwa na shirin aikatawa gareta. Haulatu ta yi wani dariya lokaci guda mai haɗe da hawaye.

"Umma kukan me kike? Mamakinsa ki ke yi? Dama ban faɗamaki ba? Ban faɗamaki mugun mutumin nan ba zai taɓa sauya hali ba? Ban ce maki yaudararki ya ke yi ba? Yau ga shi nan, wataƙila cinikina ya je ya yi ba tare da kin sani ba."

Ta karashe muryarta na dusashewa tsabar wani daci da maƙogwaronta ke yi. Hajiya Mama ce ta dakatar da zancen, ta nemi Hindatu ta shiga a ƙarasa yi mata shiri. Haulatu kuwa komai fita ya yi a ranta amma Hajiya Mama ta dage ta tsaya a yi komai da ita. Mujahid ke sanar da su an cafke mutum biyu cikinsu amma saura sun gudu. Wannan ne ya haifar da nutsuwa a zuciyar Umma sai dai kuma abin da ke binne a zuciyarta da kuma ƙudurin da ta yi na matakin da za ta ɗauka wanda zai fiye musu alheri ita da ɗiyarta. Ta yi alƙawarin tafiya Katsina neman dangin uwarta koda ace ita ba su shirya karɓar ta ba suna mata kallon shegiya, to za ta nemi alfarmar su riƙe mata ɗiyarta ko bayan ranta.

Bikin dai na Hindatu bai yiwa Haulatu dadi ba sam duk da irin burin da ta ci wa bikin na za ta yi rawa har sai jikinta ya yi ciwo. Gidan Hajiya Mama suka koma da rayuwa don ƙeyar Ɗanmutuwa ba'a ƙara gani a unguwar ba. Umma ta dauke duk wasu muhimman abubuwanta da ta sani zai sadar da ita ga dangin Mahaifiyarta Salma.

Bayan komai ya lafa da kwanaki biyar Umma ta soma shiri tun safe, ta kuma tashi Haulatu da ke bacci akan ta yi wanka ta shirya za su yi tafiya. Haulatu ta na mutsika idanu ta dubi Umman, tun faruwar lamarin ko digon fara'a ba ta ƙara gani a fuskarta ba. Ta sha farkawa ta gan ta saman darduma tana kuka cikin sujjada. Itama sai ta ɓoye kanta cikin zanin rufa ta sha nata kukan.

"Umma ina zamu je?"

"Katsina." Ta ba ta amsa kai tsaye, Haulatu ta yi shiru tana tunani, Katsina dai? Wa suke da shi a Katsina? Duk kokarinta ba ta iya cankar komai ba. Ganin Umman ta cigaba da aikin shirya jaka yasa dole ta miƙe ta faɗa wanka.
Fitar tsiro
Page 12
A ɓangaren Ɗanmutuwa kuwa, tun lokacin da suka yi waya da Maada yake ba shi lamarin ƴan sanda sun tarfa su, ya shiga mugun tashin hankali. A sannan yana kwance tare da abokiyar hutawarsa a ɗaki a gidan Hajiya Adama. A hargitse ya ja kayansa ya mayar ya fito ya nufi wurin Hajiya Adama ya sanar da ita komai. Hannu ta ɗagawa mai yi mata tausar ƙafa gami da ba ta umarnin ta bar falon. Rai a ɓace ta dube shi.

"Garin ya ya ka yi sake har wani ya ji wannan shiri? Ni na tabbata akwai sila, ba hakanan kawai labari zai kai ga ƴan sanda ba. Ko akwai munafuki a cikin yaranmu ne?"

Ɗanmutuwa wanda duk sanyin falon bai hana shi fitar da zufa ba, cikin tsananin ɓacin rai ya amsa.

"Ke ai kin san ni, ba zan yi sakacin da har wani zai ji wani abu ba. Na yi waya a gidana, amma ko alama babu wanda ya ji, asalima sadda na yi daga ni sai Na'ima, ita kuwa tana ɗakinta tana ƙura adakar fita biki. Yaran nan kuwa ƴan a mutu ne ko a yi rai kin san da haka."

Ran Hajiya Adama ya ɓaci.

"Ji fa, ashe ga inda aka haihu a ragaya nan. Kana tunanin za ka yi waya a gida amma Na'ima ta kasa fahimtar komai?"

Ɗanmutuwa ya girgiza kai.

"Ban maki musu ba, amma dai ina tabbatar maki cewa ba ta ji ba. Matsoraciyar mace irin Na'ima ban hangi ta inda za ta shanye tashin hankali irin wannan ba ta yadda ko a fuska ba zan gane ba."

Ɗan murmushin ba ka da wayo Hajiya Adama ta yi mishi. Sai kuma ta yi ƙwafa.

"Shikenan, muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Ai kare na yawo zabo na yawo wataran za'a haɗu, idan ka ji labari za ka ce na faɗamaka."

Aikuwa yin maganar da kwana ɗaya, labari mai zafi ya zo daga bakin Gwaska cewa ai Umma da Haulatu a yanzun sun tare gidan makwafcinsu Alhaji Mijinyawa. Ya kuma samu labari cewa ana zargin Ɗanmutuwan da yin garkuwa da ɗiyarsa Haulatun. Wannan magana ta jefa Ɗanmutuwa cikin tashin hankali.

"Ya akai wannan zance ya fito?"

"Ba ga shi nan ba! Ai na faɗamaka! Yanzu sai dai mu sa manya a gaba a kashe zancen. Raina kama kenan ka ga gayya. Yanzu ga shi nan ta shayar da kai mamaki."

Wannan amsar ya samu daga bakin Hajiya Adama. A ƙarshe suka yi duk wata ƙulla-ƙullarsu aka tura Ɗanmutuwa wai ƙebantaccen gidan gona na wani  babba a ma'aikatar Custom dake harƙallar miyagun ƙwayoyi da su. Kusan su na ji sosai da Hajiya Adama a fagen kasuwancinsu wannan dalili ya sa duk wata alfarma tana samuna wurinsu. Ɗanmutuwa kuwa ya zame musu wannan mutum mai sa'a, duk wani kaya da zasu damƙa a hannunsa to fa nan da nan zasu ƙare. Wannan yana daga dalilan da suka ɗauke shi da muhimmanci a tafiyarsu.

  Haka Ɗanmutuwa ya koma can Gwarzo inda gidan ginar yake, sai dai zuciyarsa ta kasa sukuni, ba kuma tsoron za'a cafkeshi yake ko wani abun ba, sai don jin bakin ciki da haushin Na'ima wacce ta jawomasa asarar maƙudai. Ya kuma sha alwashin idan komai ya lafa sai ya ɗauki mataki a kanta.

Wannan kenan.

***
Hajiya Mama da Mijinta zaune a saman kujera a falo, yayinda Umma da Haulatu ke gefe saman kafet. Ganin irin halaccin da suka yi musu ya sa Umma warware musu zare da abawa na asalin dalilin da yasa ta auri Ɗanmutuwa da kuma zamanta a cikin ƴan  bariki wurin mahaifinta. A ƙarshe ta miƙawa Abban su Bahijja hoton mahaifiyarta wanda ke ɗauke da sunan gari da kuma zuri'ar da ta fito.
Da mamaki tsantsa Abban Bahijja ya dubi sunan, ba don wai ya yi mai sunan keɓantaccen sani ba, a'a, sai don sunan ba ɓoyayye ba ne tun zamanin iyayensu har kuma zuwa yanzu da matasan jikokin gidan suke nasu tashe na kuɗi da ma ilimin boko da arabi. Ya maida duba ga Umma dake sharar hawaye na fargabar abin da za ta je ta tarar a cikin dangin mahaifiyarta.

"Na'ima, kina son cewa mahaifiyarki ɗiya ce ga Tsohon Attajirin nan Alhaji Bello Shu'aibu Malumfashi?"

Hajiya Mama jin sunan ya sa ta kalli Abban da mamaki kafin ta kai hannu ta karɓi hoton, matar kamar an tsaga kara tsakaninta da Umma sai ko ta juya ta ga rubutun. Asma'u Bello Shu'aibu Malumfashi. Katsina. Har da kwanan wata na sadda aka yi hoton.

"Ikon Allah." Shi ne abin da Hajiya Mama ta furta. Umma bayan ta amsa da Abban Bahijja da eh, shima jinjina kai ya yi cike da tsantsar mamaki. Ya sani akwai sauran rina a kaba a ɓangare na rayuwar Umma, bai ce ko ba za su karɓe ta ba ko wani abun makamancinsa ba, sai dai babban zuri'a ne da ya tara yara da jikoki. Yana da tabbacin wannan rayuwar da ta shimfiɗa a waje daga baya ta zo musu, za ta fuskanci wasu abubuwan dole kafin ta samu karɓuwa. A hasashen Abban Bahijja kenan. Ita kuwa Haulatu ta ma kasa gane me take ji, ita ba farin ciki ba ita kuma ba akasinsa ba. Ta dai sani Umman ta bata mamaki yanda ta iya ɓoyemata wannan hoto tun tsawon waɗannan shekarun da take nacin sai ta nemo danginsu.

Haka suka rabu bayan Abban ya sa direba ya miƙa su tasha, ya kuma ba Umma kudi masu ɗan kauri cewa su riƙe. Ba iya nan ya tsaya ba sai da ya bi ta da nasiha akan ta yi hakuri ta jure dukkan wani abu da za ta fuskanta a cikin zuri'ar. Umma ta yi godiya sosai. Haka suka kama hanya bayan sun shiga har gidan makwaciyarsu  Maman Hasiya itama sun mata sallama. Haulatu ko ta kan Hindatu ba ta bi ba don tun abinda ya faru Hindatun ba ta ko neme ta a waya ba bayan biki ta ji ya ake ciki wannan ya sa itama ta watsar da ita.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login