Showing 39001 words to 42000 words out of 177840 words
zuciyarta fari ƙal take jin ta, sosai ta ji dadin wannan fitowar da Maama ta saka ta yi.
"Maama ai gida zamu yi ko?"
Tana murmushi ta amsa.
"Zamu biya gidan Zaid. Watansa biyar da aure, Abuja yake da zama yana aiki a ma'aikatar CBN. Ɗa ne ga Malama Safiyya, za ki san su duka a hankali. Zaid shi ne babban ɗanta, shi yake riƙe da gidansu tun bayan rasuwar mahaifinsa, ba don ma aiki da ya kai shi Abuja ba, sam ba ya son ya yi nesa da mahaifiyarsa. Shi sam ba auren zumunci ya yi ba don a ra'ayinsa ma sam ba ya kaunar hakan tun sadda a sanadinsa wata fitinanniya a zuri'armu ta gwada shan maganin ɓera Allah ya kiyaye bai sa ta sheƙa lahira ba, shi kuma ya yi rantsuwa babu kaffara kan ba zai aureta ba. Ƙarshe sai haƙura ta yi amma fa har yanzu ma ba ta yi aure ba."
"Wace ce ita Maama?"
Murmushi Maama ta yi.
"Yar uwarki ce, ɗiyar Hajiya Nafisa ta Malaysia. Farko a hannun Hajja ta ke don a nan ta soma karatu, faruwar lamarin nan iyayen suka dauke ta, ta koma hannunsu. Ai ba za ta fi shekarunki ba, koda za ta girmeki bai fi da shekara ɗaya. Dalilin da yasa Hajja sam ba ta shiri da Zaid, wai ya kusa kashe mata jika kuma ya ƙi aurenta."
"Uhm" Abin da kawai Haulatu ta ce kenan. Ko ma wace ce yarinyar tunda dai jikar Hajiya Babba ce ta aikata abinda ya fi haka, a cewarta. Daga haka ta cigaba da sauraron hirarrakin abin da ke faruwa a zuri'ar daga bakin Maama har suka iso wani gida. Daga ganin gidan ka san ginin ba na yau bane sai dai tsaf bai nuni da alamun tsufa sosai ba.
"Nan gidan Malama ne, anan Zaid suka sauka. Shi bai kai ga kammala gininsa ba. Dama ba ki taɓa ganinta ba ko?"
Ta ƙarashe tana kallon Haulatu. Gyaɗamata kai kawai ta yi. To watakila ma ta taɓa ganin nata amma ba ta san wace ce ba.
Malama ta karɓe su fuska a sake, Haulatu dai daga gaisuwa ba ta ƙara cewa komai ba sai shiru da ta yi tana ƙarewa falon kallo yayinda suke ta hira da Maama.
"Kinga fa yarona na zo gani ba ke ba. Ya dage na zo akwai magana."
Malama ta ɗan taɓe baki cike da takaici.
"Au, kenan ke ya kira ki taushe ni ko? Aikuwa dai ina nan akan bakana. Ke kam kina son biyewa shiriritar yaran nan naki."
Maama ta yi turus.
"Toh kinga dai ban san komai ba, amma kin ɗauko hanyar fesamin. Wani abun ne ya faru? Ko kuwa bai kai girman da Zaid ya ɗadɗago ni ba?"
"Aa, ai ba kya ji a bakina ba. Waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ki dai je yana can wajen nasa tunda shi ya nemi ki zo. Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, duk za ku zo ku same ni."
Dariya Maama ta yi tana mai miƙewa.
"Allah ya kyauta toh. Har na matsu ma na je na ji meke faruwa. Haulatu ki jira ni."
Ta amsa da toh kawai, bayan ficewar Maama daga falon Malama ta ɗan girgiza kai tana duban Haulatu ta ce.
"Ke kam kin huta da alama ba ki da surutu ko? Koda dai gidan nawa ne ba abokan hira da yawa. Yarana duka ukun maza ne, mace ɗaya ce za ki iya ba ta shekaru biyu zuwa uku, ta jw makaranta amma nan kusa za ta dawo."
Murmushi Haulatu ta yi, wai ita ake cewa ba ta da hira. Lallai, don dai Malamar ba ta dan wace ce ita ba.
"Kina zuwa makaranta a can inda kike?"
Tambayar da Malama ta kara yi ya fahimtar da Haulatu dagaske hirar ta ke so, kuma ga dukkan alamu matar ba ta da girman kai, tun soma zancen fuskarta ma a sake take. Aikuwa ta gyara zama ta shiga labarta mata yanayin karatunta, hatta da irin hantarar da ake mata idan ta fita ana kiran gidansu gidan karuwai babu irin abin da ba ta kwashe ta faɗawa Malama ba. Sosai tausayinta kuwa ya mamaye zuciyar Malama Safiyya. Ta kuma karanci abubuwa da dama a kan Haulatun. Yarinyar tana buƙatar nusarwa akan wasu daga cikin ɗabi'u da ladabin magana. A yanayin da ta ke ba ta labarin tamkar da wata sa'arta, kamar misali takan yi amfani da 'Hum, ke na ga rayuwa fa.' Ko kuma ta ce 'Ke ba za ki fahimta ba.' Da dai sauransu. A shekaru da wayewa irin na Malama Safiyya sam ba ta ga laifinta ba duba da yanayin rayuwar da ta taso a ciki, itama mahaifiyarta ba lallai ta samu wadataccen ilimi ba da kuma wayewar mu'amala da mutane ba. Sai ta ji inama za'a yi mata kyautarta koda na watanni ƙalilan ne, ita kuwa za ta yi iya yinta don ganin ta gyara koda kaso sittin ne cikin ɗari na daga ɗabi'unta. Tun zuwan da suka yi gidan, sam ba ta taka ta je ba saboda ta jima kwance ba lafiya, kwanakin nan ne ta ɗan samu ta warware. Amma ta ji labari daga yan uwanta cewa Haulatun ba ta da kunya, wai kowa ya je tana dubansa ne ta maida mishi magana.
Haka ta yi ta kula da ɗabi'un Haulatun, ita kuwa ko a kanta, bilhaƙƙi take ba ta labari amma ko kusa ba ta ce ga mummunan sana'ar da Mahaifinta ke yi ba don tuni Umma ta kwaɓe ta da furtawa wani, ba kuma ta sa dalilin rufamasa asirin da Umma ke yi ba. Tana dai kokarin nunawa Malama yanda ta tsani ƊanMutuwa a rayuwarta.
"Allah ya shirye shi idan mai shiryuwa ne. Sai hakuri, abin da ya faru da ku, kaddara ce. Ki saka a ranki haka ya tsara maku. Kin ji ko?" Faɗin Malama Safiyya kenan a ƙoƙarinta na datse zancen iyaka nan ganin hirar ma babu daɗin ji ga ƙarancin ladabin magana da Haulatun ke da shi.
Aikuwa jin abin da Malama ta fadi yasa Haulatu yin wata dariyar.
"Aikam mun ga rayuwa. Tab din! Ai wallahi Hajja ta rufawa kanta asiri ma da ta karɓe mu idan ba haka ba wallahi daga nan har gidan rediyo."
Ita dai Malama ta cika da ɗumbin mamaki, shakka babu akwai tarin gyara da yarinyar ke buƙata. Ta yi shiru ba ta ƙara uffan ba, ba kuma za ta ce wai ta ji wani tsana ko haushin Haulatu ba face ma tausayin da ta ba ta. Ta san wahalar tarbiyya, ta yi msta uzurin kalar gidan da ta rayu a cikinsa. Murmushi ta yi kafin ta miƙe.
"Bari dai mu yi haramar sallah, na ga lokacin Magriba ya gabato. Tashi muje na nunamaki ɗakin Auta ki yi alwala."
Ta amsa da to, daidai sadda wata yar yarinya mai shekaru sha uku ta shigo da sallamarta rangaɗaɗau. Suka dube ta, tana sanye da kayan islamiyyarsu. Yarinya ce ƙarama amma fa akwai ƙiba masha Allah. Ba ta da hasken fata, sai karen hanci da hasken idanu. Ta shigo tana nishi gami da wurgi da jakar hannunta.
"Mama yunwa nake ji wallahi." Ta furta kamar ta yi kuka. Sai ma a sannan ta ankara da Haulatu, sai ta washe baki.
"Lah, Anti Mimi, yaushe ku ka zo Katsina?"
"Ba ita ba ce Bebi, wannan sunanta Anti Haulat, maza raka ta ɗakinki ta yi alwala ki zo ki ci abincin. Ki dauke jakarki kuma."
Ta amsa da toh kafin ta dauki jakar tana ƙara satar kallon Haulatu wacce itama ta ke tsaye tana jiranta.
***
Zaid El-Yakub. Matashin saurayi son kowa ƙin wacce ta rasa. Allah ya mishi baiwa ta iya lafazi da kuma ilimi na boko da arabi don idan Zaid ya juye harshe yana larabci kai kace balaraben ƙasar Saudia ne, kusan kaf a jikokin gidan maza, su biyu kacal Allah ya ba wannan baiwar ta jin harshen larabci sosai, Zaid da Abeed (Sadaukin Alhaji). Uwa uba kuma ga kyawun fuska ga kuma na gidan rana da Allah ya ba shi. Da murmushinsa kawai, sai ya narkar da zuciyar mace. Mutum ne da ya iya tausar mace musamman idan tana cikin yanayi na fushi da zafi. Sai dai duk da wannan nagartar tasa bai taɓa tara shirgin ƴanmata ba. Ba ya kuma ba da fuskar da ma zancen soyayyar za ta haɗa ku, komai alaƙarka da shi muddin ya fahimci daga ƴan uwantaka ka faɗa kogin kaunarsa to fa zai ja baya da kai ya sauyamaka baki daya. Ko Zaituna ƴar malaysia da ta yi mutuwar sonsa, daga sabo na zumunta ne ya juye a wurinta ya koma so ɗin. A duniya kuwa ba abinda ya tsana sama da auren zumunci, sam ba ya burge shi. Wannan na ɗaya cikin dalilan da ya sanya shi kawo maganar abokiyar karatunsa Jalilah, har a yanzu ta kai su ga aure. Sosai ya yaba da nutsuwarta tun ma zamanin da suke tare a makaranta, tana sonsa sai dai koda alama ba ta taɓa furtawa ba. A karan kansa ya gane hakan. Bai kuma ƙara tabbatarwa ba sai da ya fara zuwa gidansu da sunan zance. Ga shi a yanzu ta kasance mata a gareshi.
"Mutanen Abuja."
Ya ɗago kai daga saman laptop din ya dubi ƙofar, lokaci guda ya saki murmushi gami da shafar sumar kansa da ba ta da yawa.
"Maama, bismillah."
Bayan ta zauna ya gaishe ta cike da girmamawa. Kafin ta tambaye shi Jalilah. Anan yake sanar da ita ta je gidansu. Ba su wani ɓata lokaci ba yake faɗamata ƙudurinsa na tafiya da Bebi can Abuja wanda Malama ta ce sam ba ta amince ba. Harararsa ta yi kafin ta ja guntun tsaki.
"Ga ka nan dai wani lokacin idan ka yi abu kamar kai ne Autan ba Bebi Ayyush ba. Yanzu Zaid akan wannan ka sanya ni zuwa fisabilillahi? Wannan ai magana ce da a karan kanka ka san ba mai yiwuwa ba ne, Malamar ka ke son ta zauna ita ɗaya a gida?"
Ya yamutse fuska.
"Maama ta ina za ta rayu ita daya, ga Jafar, Nabeel duka, itama Juwairiyya gobe za ta dawo daga Malumfashi. Sannan ba fa hakanan zan tafi da Bebi ba, zaman shirun ne babu dadi, Jalilah na damuwa tunda idan na fita tun safe ba na dawowa sai Magrib. Aron Bebi da za ta ba ni na kwanaki kaɗan ne kafin su yi resuming school. Ina ce ma biki za'a yi nan kusa?"
"Hakane, to Islamiyyar fa?"
Ya yi murmushi.
"Zan koyar da ita a gida."
Maama ta girgiza kai.
"Da ace na san wannan dalilin ka sanya ni zuwa Zaid, tun a waya ba zan amsa maka ba. Ni ka ga tafiyata kafin Haulatu ta ƙosa."
Ya yi saurin riƙe gefen mayafinta yana mai narkar da wuya.
"Please mana Maama. Wace ce kuma haka da ba za ta iya jira ki taya ni wannan yaƙin ba?"
Takaici ya cika Maama.
"Tsakanin Khaleefa, Mu'az da Sadauki na rasa wanda ya fi wani mayar da ni abokiyar wasansa. Ni fa har yanzu ban dauki wannan magana da muhimmancin da za ka kira ni na zo ba. Wato kai mai mata ko?"
Ya ɗan haɗe fuska. Ta kuma san dalilinsa bai wuce na haɗa shi da Sadauki da ta yi ba. A duniya ta rasa dalilin rashin jituwar Khaleefa da Mu'az, haka Sadauki da Zaid. Idan ka ga kowannensu a wuri guda to tabbatar abu ne na dole babu yanda suka iya kowa cikin zuri'ar na wurin. Amma fa idan an hadun za'a gaisa. Magana mai karfi zai wahala ta shiga tsakaninsu dai. Zaid da Mu'az ke ɗasawa saboda barkwanci irin na Mu'az, Zaid kuwa na son ababen ban dariya. Khaleefa da Sadauki kuwa tasu ta zo ɗaya idan an haɗu za su yi ta tattaunawa akan abin da ya shafi matsalolin rayuwa da gwamnati. Kowa dai da nashi zaɓin. Alhaji ya yi nasihar da faɗan, amma ina. A cewarsu su fa lafiya suke zaune da juna kawai dai halayyar ce ta bambanta.
"Shikenan Maama, zan zo gidan gobe mu ƙara magana. Muje na taka maki."
Ya furta yana mai miƙewa gami da gyara zaman armless rigarsa kalar dark blue gami da zura hannu a aljihun dogon wandonsa marar nauyi fari ƙal. Gaba ɗaya damatsan hannunsa a waje, ko'ina na jikinsa gargasa ne mai laushi duk a kwance.
Maama ta girgiza kai ta yi murmushi, ta sani sarai sunan Sadauki da ta ambata ne ya ɓata hirar baki daya. A ganin Zaid, Sadauki fa mutum ne mai nuna isa da ganin ya fi kowa a zuri'ar kawai don Alhaji na ji da shi. Wannan ma yana daga dalilin da yasa sam ba ya son sabga ta haɗa su. Idan abu ya haɗa kuwa, koda wani ya kawo shawara, Sadauki zai nuna ba ta yi mishi ba. Nan da nan kuwa mutane da dama za su goyi bayansa. Wannan ma yasa shi ƙara nisanta kansa da shirginsa.
Har ƙofar falon ya takawa Maama hirarsu suke yi amma fa ta abin da ya shafi babban gidan, Maama ke ce masa ai tare ta zo da jikar Hajiya Babba wacce suka bayyana a gidan kwanaki ita da Ummanta. Ya jinjina kai gami da ɗan ɗaga kafaɗa.
"Na samu labari."
Ya furta cikin nuna ko a jikinsa. Hajja ai ta gama sire mishi a rai tun sadda ta tsinemasa albarka don bai auri jikarta Zaituna ba. Wannan ma daya ne cikin halin Zaid da sam ba ya burge mutane, riƙo. Shi mutum ne mai riƙo. Ko ya shiga babban gida, kallon ɓangaren Hajja ba ya yi ballantana ya taka ya shiga. Malama ta yi fada ta yi nasihar, amma ya gwammace su gaisa da Hajja idan ya haɗu da ita a tsakar gida ko kuwa falon ɗaya cikin kakannin nasu. A barandar suka rabu, ya koma don ɗauro alwala ya tafi masallaci yana magiya akan Maama ta yi jiransa. Ita kuwa ta shige falon.
***
Bayan idar da sallah suka yi shirin tafiya amma ina, Malama ta ce sai fa sun ci abinci a dole suka haƙura.
"Ai kin ji, nifa so nake na gudu kafin wannan yaron ya dawo ya tasa ni a gaba akan abin da nima ba zan goyi bayansa ba."
Dariya Malama ta yi jin batun da Maama ke yi.
"Ku dai ku ka sani. Dama ni na san ai babu inda maganar za ta je. To wa zai dauki wannan salon da ya zo da shi?"
Murmushi Maama ta yi. Suna cikin cin abincin sai ga shi ya yi sallama ya shigo. Wannan karon doguwar jallabiya ce jikinsa ruwan makuba mai adon zare ruwan madara. Tun shigowarsa Haulatu ta yi ɗif tana kallonsa kamar yau ta soma ganin wata halitta wai ɗa namiji a duniya.
"Shi kuma wannan wane ne?" Ta yi furucin ƙasa-ƙasa. Bebi ta dube ta murya a ɗan sama ta ce.
"Lah, Yaya Zaid ne. Ba ki san shi ba?"
Amsar da Bebi ta bayar ya sa Haulatu ɗan kama leɓɓanta, ashe zancen zucin da take yi ya fito?
'Wai! Hindatu ba don kin yi aure ba ai da nace ki zo ga miji. Wannan ai shi ake kira mijin novel.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa kauda kai ta yi daga kallonsa ganin sun haɗa idanu. Shi kuwa Zaid ƙarasowa ya yi ya zauna gefen Maama, har a sannan idanunsa ba su ɗauke daga kan Haulatu ba. Ya ji wani tun daga tsakiyar kansa har babban yatsar ƙafarsa.
"No! Innalillahi! Ya Salam!" Ya furta duka a lokaci daya can ƙasan ransa yana mai yin ƙasa da kai.
"Yauwa, ka shigo ko? To mu yanzu zamu wuce. Haulatu ba ki gaishe shi ba. Ga Haulatun da nake faɗamaka."
Ya ji zancen Maama, kwarai ya shiga kunnensa. Ya kuma kallon Haulatun karo na biyu. Wannan lokacin itama shi ɗin ta ke kallo da nata dara-daran idanunta na gado. Sai ta kasa sukuni da kallon da yake watsa mata, ita ba ta ma taɓa sanin tana da kunya ba sai a wannan rana. Ta gaida shi ya amsa da motsa leɓɓansa. Bai ƙara magana ba sai shiru, abinci kuwa cewa ya yi sai bayan isha'i. Maama har ta mike hakanan Haulatu da ta ke ji Zaid ya takura mata da kallo ta yi saurin mikewa da gyara zaman ɗankwalin abayarta.
Yana ji suka yiwa Malama sallama, miƙewa ya yi jikinsa babu kuzari don ya taka musu.
Ya dafa motar ya leƙo ta gefen Haulatu, ta ji numfashinta na neman ɗaukewa, ita ba ta taɓa jin namiji kusa da ita har haka ba. Kawai sai ta ji wani iri, shi kuwa kallonta ya yi kafin ya maida idanunsa kan Maama.
"Shikenan sai na shigo din?"
Maama na kokarin tayar da mota ba tare da ta dube shi ba ta amsa.
"Eh Zaid, sai ka shigo. Amma fa ba za ta sauya zani ba. Wancan maganar a bar ta."
Ya yi wani murmushi mai ƙara ƙawata fuskarsa ya dubi Haulatu. Ita dai ba ma kallonsa take yi ba don wannan kusancin ya ishe ta, ga ƙamshin turarensa da ya cika ƙofofin hancinta.
"Yes, an bar ta. Ganinki kawai zan zo."
"Ai shikenan. Allah ya kawo ka lafiya."
Maama ta ba shi amsa daidai sadda ya matsa jikin motar yana sauke numfashi, daga haka ta ja motar bayan Maigadi ya wangale ƙaton ƙyauren gidan ta fice. Ta ji sadda Haulatu ta sauke ajiyar zuciya.
"Gajiya ko? Sorry yau dai na saka ki nisa da Ummanki. Yanzu za ki gan mu a gida in sha Allah."
"Uhm." Shi ne kawai abin da ta ce. Daga nan ta ja bakinta ta yi shiru. Ita dai wannan Zaid din bai kwanta mata ba sam, haka kawai yana wani bibiyarta da kallo kamar zai hadiyeta. Ta ja guntun tsaki wanda har ya fito fili, Maama kallonta kawai ta ɗan yi ba tare da ta ce komai ba ta cigaba da tuƙi abinta.
***
Washegari haka Safina ta shigo har ɗakinsu tana jan ta da hira. A dole Haulatu ta sake don ta sani ba fa za ta iya rayuwa hakanan babu abokan hira ba tunda yanzu Hindatu ta yi mata nisa. Tun ba ta sake sosai ba har sai ga shi nan suna ƙyaƙyata dariya. A ƙarshe Safina ta yi ta roƙonta kan ta fito su zaga