Showing 87001 words to 90000 words out of 177840 words

Chapter 30 - FITAR TSIRO COMPLETE HAUSA NOVEL BY RUFAIDA UMAR

11 Jul 2024

79138

yi baki sake, bai tsaya iyaka nan ba, Zaid gwani ne na tsara kalamai masu tausasa zuciya amma babu kalmarsa ko guda da ta yi tasiri a kan Haulatu. Ita mamaki ne ma da kallon abin kamar a fim ya sanya ta yin saroro tana duba da sauraron zantukansa tiryan-tiryan har ya rufe zancen da jefa mata tambayar ko ta aminta da shi?

Jin shiru, ya sanya shi ƙara magana yana girgiza kai duk ya bi ya susuce.

"Aa don Allah, please Noor kar ki ce min A'a. Komai nawa ya bar tafiya daidai, tun sadda na ɗora idanu a kanki zan iya rantse maki bana cikakken rabin awa ban tunaki ba. Ƙin karɓar soyayyata daidai ya ke da rusamin dukkan akalar rayuwa."

Wata ƴar ƙaramar dariya ce ta ɗan suɓucemata na takaici da ɓacin rai. Zaid dai wanda ƴar uwarta ke mutuwar so da ƙauna, shi dai da ta ke jin ba za ta iya rayuwa ba tare da shi ba, a yau shi ke ɓarin zantuka wai ya na sonta?

"Abin da ɗaure kai Yaya Zaid, ni dai ka ke so? Ko ka manta alaƙar da ke tsakanina da Anti Zaituna? Ko kuwa ka manta ni ɗin ma jikar Hajja ce? Tsohuwar da kaf gidan nan babu wacce ka raina irin ta?"

Ta ɗan fiddo idanu da ɗaga gira kaɗan.

"Ohhhh, na fahimci wani abu, a saboda haka ne ka ke ta ƙoƙarin komai ya wuce tsakaninka da Hajja? Ka fara shigowa sashenta? Ka yi kuskure Yaya Zaid, ka yaudari zuciyarka idan har tunaninka ya ba ka cewa ni Haulatu zan taɓa soyayya da kai. Da Haulatu da Zaituna abu guda ne, yanda ka ke ƙin Zaituna, to wataran ma Haulatun za ka farka daga bacci ka gane ba sonta ka ke yi ba.."

"Wallahi sonki nake yi."

Ya tari numfashinta da sauri, ƙirjinta sai bugu ya ke yi sakamakon zafin da kalamanta ke haddasa mishi. Har wani gumi ya ji a saman goshinsa.

Ta yi murmushin takaici.

"Uhum, na gode da kaunar, sai dai don Allah tunda ka ji amsa ta kar ka ƙara aikomin da saƙo. Sannan ka yi duk yanda za ka yi ma ka manta da ni da lamarina don abu ne ba mai yiwuwa ba har abada kuwa."

Daga nan ta gifta shi ta fice a gaggauce don yaran dake wurin sun soma maido hankula gare su. Hawaye ne ya zubo mata ta yi saurin gogewa da tafin hannunta. Wannan abu da me ya yi kama? Yaya Zaid ne ke son ta? Wato bai ko ji kunyar furtawa ba? Sai ta fasa komawa ɓangaren Hajja gudun kar wani ya fahimci yanayin damuwar da ta ke ciki kawai sai ta zarce ɓangaren su Radiya, nan ne take da tabbacin ba jama'a sosai. Ba ta kallon kowa ballantana a kula da yanayinta, ta san dai akwai mutane a filin gidan, amma ba ta ko damu da sanin su waye ba. Sai da ta kusa cimma ɓangaren su Radiya ta ji mutum a gefenta ta ɗago kai ba tare da ta fasa tafiyar ba. Shi ma ita ya ke kallo fuska a ɗan haɗe. Mu'az ne cikin shadda ruwan ƙasa har da babbar riga. Ɗan dakatawa ta yi fuskarta babu walwala ta ce.

"Lafiya?" Ya zaro idanu waje kaɗan.

"Lallai ma, wato ni ki ke cewa lafiya ko?"

Ta kauda kai ta yi shiru. Ita tsabar ma ranta a ɓace yake ba ta san sadda ta furta hakan ba.

"Ina ki ka shiga na karaɗe gidan na ban ganki ba? Kin manta nace za mu yi magana?"

Ta gyara tsayuwarta.

"Da ka kira wayata za ka same ni. Amma yanzu tunda mun haɗu ina sauraronka."

Ya ɗan yi tsai yana kallonta har sai da ta ƙosa. Sai dai kafin ta furta wani abun ya riga ta.

"Kamar akwai abin da ya ɓata ranki, ko mu bari ma yi zancen daga baya?"

Ta girgiza kai.

"Aa kar ka damu, babu komai. Ka faɗi kawai."

Ya jinjina kai gami da furzar da ɗan ƙaramin huci. Ya ji a ransa gwara ya furta ɗin kafin abin da yake tsoron faruwarsa ya farun don haka ya nutsu tamkar ba shi ba.

"Watakila abin da zan furta ya yi maki daɗi, wataƙila kuma akasin hakan ne. Kin san ni, ban iya wani ɓoye ɓoye ba, a baya ma da na yi shiru, ban gama fahimtar alƙiblar da na dosa ba ne. Amma lokaci guda kuma jiya wani abu ya afku da ya farkar da ni daga baccin da nake. In short, ina kaunarki, sonki nake yi da aure."

Ya ƙarashe da jin wani rauni na murya a dalilin kallon da ta watsa mishi. Sai kuma ta kauda kai, lokacin da wasu mata ƴan biki suka nufi ɓangaren Abba Ridwan, hawaye suka gangaro mata a kunci kafin ta haɗiyi miyau mai ɗaci ta dube shi.

"Na san da kalar zancen da wancan ya zo min irinsa zan tsinta daga bakinka. Sai dai ku sani, daga kai har shi ba kwa gabana. Kar ka juya akalar zumuntar da ke tsakanina da kai Yaya Mu'az, ina girmamaka ina kuma kallonka tamkar yayana da muka fito ciki..."

"Aa please, kar ki haramtamin abin da Allah ya halastamin mana. Ba mu fito ciki guda ba, mu ɗin ƴan uwa ne masu matukar kaunar junansu. Mene ne laifi don ina son kyautata alaƙar ta hanyar juya ta zuwa mataki wanda zai jagoran ce mu har ƙarshen numfashi? Sannan ni da waye ki ke maganar? Waye wancan ɗin da ki ka ambata?"

Ya na maganar tamkar wanda ya zare don tashin hankalin da kalamanta suka jefa shi ga ɓacin rai da zazzafan kishin Sadauki irin wanda bai taɓa zaton zai ji shi ba. Jikinsa ya ba shi cewa Sadauki take nufi, wato duk saurinsa sai da ya riga shi?

Haulatu kuwa kallonsa take ganin gaba ɗaya ya hargitse, ta share hawayen karo na biyu gami da ƙara tamke fuska, ta koma Haulatunta ta usuli. Wayarta na ta ƙara amma ko kallon fuskar ba ta yi balle ta ɗaga.

"Ba huruminka ba ne sanin ko waye shi ba. Ni na faɗamaka, har abada babu alaƙa ta soyayya tsakaninmu. Idan kuwa ka dage akan bakanka, ni kuma na yi alƙawarin yanke zumuntar da muke yi a yanzu. Babu aure a gabana yanzun ballantana kuma wai soyayya. Koda zan yi kuma, har abada na haramta yin ta da kai."

Daga haka ta juya ta cigaba da tafiyarta tana hawaye sosai, ga Zaid kuma ga Mu'az? Anya kuwa lafiya? Duk wai ita suke so? Har ta ƙarasa ɓangaren su Radiya ba ta bar hawaye ba, sai da za ta shiga falon ne ta share fuskarta. Maman Radiya ba su nan kamar yanda ta zata, duka ana can wurin Amare da Angwaye, da ƴar dattijuwar da ke zaune tare da su ta haɗu, suka gaisa sannan kai tsaye ɗakin Radiya ta shige nan ɗin ma babu kowa, kwanciya ta yi saman ƙaramin gadonta ta ci kuka son rai, tausayin Zaituna da Safina ke cin ranta fiye da ita kanta. Har gobe Zaituna ba ta fidda Zaid a rai ba, ga kuma Safina da abin nata kullum ke ƙara gaba kan Mu'az wanda bai san da zamanta ba. Sai gaba ɗaya ta ji su biyun duka suna ba ta haushi, a take ta buɗe lock na wayarta, saƙon Zaid ta ci karo da kiran Zaid har sau wajen uku. Nan take ta rufe lambobinsa ta goge, shi ma Mu'az ta goge nasa bayan ta rufe yanda duk su biyun babu mai kiranta da layukan da ta sani sai dai ko ta wani layin daban.

Sai da kiran Umma ya shigo wayarta ta ɗaga, Umma ta hau tambayar ina take. Ta amsa mata ga ta nan zuwa. A dole ta miƙe jiki duk ba ƙwari, kwalliyarta duk ta goge, gudun kar Umma ta gane wani abu ya sanya ta shiga banɗaki ta wanke fuskar, ta yi amfani da kayan kwalliyar Radiya na saman madubi ta ɗan gyara ta. Nan da nan ta fito fes idan ka cire idanunta da suka sauya launi kaɗan. Sai kuma ta ja wa kanta tsaki, to mene ne ma na kukan? Wato ta ma ɗauki batun nasu da muhimmanci, ita kaɗai dai ta yi kiɗa da rawarta a ƙarshe ta fice ta rufo ɗakin.

Ba ta yarda sun haɗu da Umma ba sai bayan ta shiga cikin ƴan uwanta annashuwarta ya dawo, hakanan a sannu idanun sun washe sannan ta ƙarasa gareta. Duk da haka Umma sai da ta tambayi ko ba ta jin dadi, ta gan ta wani iri. Ba ta yi mamaki ba don ba yau Umma ta saba ɗago ta ba idan tana cikin wani yanayin. Sai ta wayance da fadin kanta ke ɗan sarawa.

"Allah ya sauwaƙe, sai ki nemi wuri ki ɗan huta."

Ta amsa da toh. Ranar ko kai Amarya Raudha ba ta je ba, ba ta son ma ta faɗa motar wani a cikin samarin gidan, ita yanzu duk haushinsu take ji don gani take yi kowa da na shi abin. A gefe ana mata kallon budurwar Sadauki, nan kuma ga abin da ya fito daga bakin Zaid da Mu'az, ya zama dole ta yi takatsantsan da kowa tunda ita ba soyayya ce a gabanta ba. Ba ta taɓa sha'awar ta yi ta ba. Abu ɗaya ta sani, koda su Safina ke mata kallon kamar ita ɗin ma tana son Sadauki, ba ta ce musu uffan ba, kuma har a yanzu ba ta da amsar bayarwa a karon kanta ma balle har su ji.

Washegari kuwa aka ɗunguma tare da ƴan uwa zuwa Kano don kai Batulu. Koda sha'awa, Haulatu ba ta ji son bin su ba. To kusan ma babu sa'anninta a tafiyar, daga iyaye sai ƙawayen Batulu da kuma su Zaituna su Jannat. Umma ma ba ta je ba.

***
BAYAN SATI ƊAYA...

Suna tsaye a farfajiyar gidan an fito yiwa su Haj Nafisa rakiya za su tafi zuwa Kano don jirginsu na dare ne. Hawaye Zaituna da Haulatu ke yi tamkar ba za su ƙara ganin juna ba. Ita na Haulatu ban da na sabo, har da na tausayin Zaituna musamman hirarsu na ƙarshe a jiya inda ta ke hawaye take jaddada mata cewa ganin da ta yiwa Zaid da bikin nan ya ƙara tayar mata da wani miƙi na sonsa, tana kuma jin ba mace ɗaya ba, ko a ta huɗu ta zo idan har a gidan Zaid ne to fa tsaf za ta zauna kuma ta yi mishi biyayya ta nuna masa ƙauna tamkar su kaɗai ne a gidan. A ganin Haulatu sam Zaid bai cancanci wannan sadaukarwar ba tunda bai san halacci ba. Haj Nafisa ta rungumo Haulatu a kafaɗa tana rarrashi.

"Ki yi hakuri ɗiyata. Na so kwarai na tafi da ke Malaysia, amma har gobe ban fidda rai ba. Ummanki dai ta ce idan don ita ce, ta bar min ke halak malak, Hajjarmu ce ta ƙi goyan baya. Amma ko ba yanzu ba, duk sadda kika ji kina da buƙatar zuwa gurina ki sanar da ni. Kin ji ko?"

Haulatu ba ta san sadda ta ɗaga kai ta dubi Maman Zaituna ba, duban ƙauna da soyayya. Idan ka cire Ummanta, ita ce mace ta biyu da ta kwanta mata a rai wacce ke ƙaunarta tamkar daga cikinta ta fito. Murmushi suka sakarwa juna kafin Maman Zaituna ta sake ta ta shiga mota. Haka Haneef ya zo suka cafke yanda suka saba, ta yi dariya. Bayan duka sun shiga mota, direba ya ja suka tafi ana ɗagawa juna hannu tamkar kada a rabu. Kasancewar ranar babu islamiyya ya sa ta shigewa ɗaki, lokacin uku da mintoci.

Bacci ya soma ɗaukarta bayan tunane-tunanen da ta faɗa mai haddasa ciwon kai, ta ji kamar cikin baccin ana tashinta. A hankali ta buɗe idanunta, ashe zazzaɓi ne a jikinta don wani irin rawar sanyi ta ke yi ga kuma azababben ciwon kan da ya ninka na farko.

"SubhanAllah, Haule ashe ba kya jin dadi, ina ta mamakin wane irin bacci ne har yamma. Maza tashi muje a kai ki asibiti. Ke Na'imatu!"

Umma jin Hajja na kwalamata kira ta shigo dakin da sauri. Ita ma jin da ta yi Haulatun ba lafiya ya sanya ta ɗan taɓa jikinta. Nan ta taimaka mata ta saka abaya saman riga da siket ƴan kanti dake jikinta. Tsabar zafin ciwo ko'ina na jikinta kakkarwa yake yi ga wani uban jiri dake kwasarta. Karshe haka suka fito tana rungume jikin Umma, Hajja kuwa tuni ta kira direbansu a waya, Allah ya taimaka yana kusa. Dakyar Umma ta lallaɓa Hajjar ta zauna da zummar za ta kai ta. Kai tsaye asibitin su Khaleefa suka nufa.

***
KANO...

Biki Buduri...



Ina tafe gobe in sha Allahu idan har na samu dama, idan kun ji shiru, a yi min uzuri. 🥰🥰🥰Love you all.
*Littafin nan na kudi ne. Ki siya ki karanta hankalinki kwance gudun shiga haƙƙin marubuciyar.* *Ibrahim Rufaida Umar, *9034973645 Opaybank.* *₦500* *Idan kin biya ki aiko shaidar biya ta 09034973645*


********

A cikin wannan satin da ake, a garin Kano, an yi biki na gani na faɗi wanda a wannan shekarar a tarihin Kano shi ne bikin da ya mutane suka yiwa kallon wanda ya fi kowane biki ƙayatuwa da kuma kashe kuɗi tun daga kan lefe. Lefe ne aka kawo akwatuna saiti goma ga kyauta ta mota mai tsadar gaske ga Amarya. Tun daga nan Momi ta ƙara susucewa da lamarin surukin nata, ita kuwa Hindatu ta ƙara shiga tsantsar tashin hankali ta kuma gane dagaske dai Alhaji Ibrahim mai kuɗin gaske ne irin kuɗin da ba ta taɓa hasko su ba. Ba ta ƙara tsinkewa ba sai da aka shiga hidimar biki. Daga suturun da ta yi amfani da su wanda Ango da kansa ya haɗa ta da Hajiya Adama aka ɗinko mata su masu bayyana sura da kuma tsada, har wanda Angon shi ma ya yi amfani da su, abin kallo ne. Ranar kamu inda aka yi shi daban, haka yini. Da kansa ya ce a rarraba bai son a haɗe wani kamu da yini, Momi ta ƙara jin kanta ya fasu, ƴan fadarta da ma waɗanda a baya ke ganin sun fi ta kuɗi ita ɗin mai kawo musu kaya gida su siya ce, sai ga su nan kowa na neman shige mata da son cusa kai. Ta zama ita ce Boss ɗin, idan ka gan su daga ita har ɗiyarta ba ka ce su ne asalin Hindatu da Momi na baya ba. Sun sauya kalarsu ma ta goge sakamakon sauyi na rayuwa. Hatta da Momi kafin zuwan biki ta mallaki mota da kuma direban dake kai ta wurare. Har hotunan biki ta tura wa Alhaji Badamasi don ya ji haushi, sai dai ci kanki bai ce mata ba.

Gidan Hindatu a unguwar Tudun Yola yake, sabon ginin da Alhaji Ibrahim ya siya. Babu abin da bai saka mata ba na more rayuwa, tun kafin zuwan biki ya sa aka yi mata passport na fita ƙasashen waje. Bayan biki ko sati ba su yi ba, suka ɗaga ƙasar Dubai. Gaba daya ba ta samu damar yin waya da Haulatu ba, ta bar shi akan daga baya ta sanar da ita. Zuwa lokacin ta kurɓi zumar soyayya daga wurin Alhaji Ibrahim, sai ta ji nan duniya babu mai raba ta da shi, ba ta san me ya sauya ta ba, amma wani irin ƙaunarsa ta shige ta na bazata. Babban mutum amma fa ya gwanance a iya tafiyar da mace yanda za ta dulmiya kogin soyayyarsa.

Shi kuwa Ɗan Mutuwa dama tun farko ya kula da yanayinta na tsoro da fargaba akan auren, bai taɓa nunamata ba shi dai ya san ba na wasa bane, a barikin ma ai kowa da matakinsa. Na'imatun koda ba ta bayar da labari ba, su matan barikin dake maitarsa sun shaida. Koda dai dama ba son Na'imatun yake ba, kafin ma ya san da zamanta a shimfiɗa sai gumu ta yi gumu. Haka suka yi rayuwar suka ƙare.

***
KATSINA...

Suna isa asibitin kai tsaye wuri Haulatu ta samu a waiting room ta zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun sakamakon jirin dake kwasarta. Da file na gidan gaba daya aka yi amfani da shi, sai da wasu mutum uku suka fito sannan Umma ta taimakawa Haulatun suka shiga. Yana zaune yana danna tablet ɗinsa, ya sanya farin gilashi, tun da ya ɗaga file ɗin ya gane daga gida ne yake tunanin toh waye ba lafiya a gidan? Sallamar Umman ce ta sa shi saurin ɗago kai. Ya miƙe cike da girmamawa yana fadin.

"Umma? Dama ke ce?"

Ganin Haulatun ya sa shi gane ita ɗin ce marar lafiyar. Lokacin kuma Umma ke ba shi amsa da cewa Haulatu ta kawo.

"Oh." Ya furta kafin ya koma mazauninsa, bayan sun zauna ya gaida Umma ta amsa da kulawa. Ita dai tana kaunar Khaleefa tana jinsa tamkar ɗan cikinta.

"Meke damunta?"

Da bakinta ta amsa.

"Zazzaɓi ne sai kaina..ciwo."

Ta ƙarashe hawaye na zubomata. Ya ɗan dube ta kaɗan, tabbas tana jin jiki. Karon farko da ya ji tausayinta har ransa. Test ya bayar na jini, sai da ya tabbatar Malaria ce sannan ya rubuta magunguna don a nan ya saka Nos ta shigo aka ɗauki jinin ta fita. Magunguna da allurar jijiya na ranar da washegari, sai drip da za'a sa mata yanzun sakamakon jirin da take kuma Umma tace abincin ma yinin ranar gaba daya ƙin ci ta yi. Nan ma Nos ya ƙara kira a waya ya ba ta umarni. Jin allura ta zaro idanu.

"Allura kuma?" Ta furta da narkakkiyar murya na wacce ke jin ciwo tana dubansa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana mai kauda kai daga dubanta don Umma tuni ta amshe zancen.

"To haka za'a bar ki da ciwo a jiki Haulatu? Ai gwara a yi maki ko zazzaɓin ya sauka. Daure ki tashi muje."

Tana turo baki da yamutse fuska haka Umma ta taimaka mata suka fita a ɗakin. Bayan fitarsu ya fidda gilashin gami da jinginar da kai jikin kujera ya ɗan lumshe idanu. Bai kaunar ganinta cikin wannan damuwa da rashin lafiyar. Yana hankalce da ita tun soma bikin, duk wani taku da ma abin da ya faru na rigimar da ƙanwarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login